Showing 54001 words to 57000 words out of 94393 words

Chapter 19 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt

Advertisement

Mrs A.M   

03 Aug 2024

16971

mai kamar net ko bra babu a jikinta, rigar ta fallasa surar ta ko ina a shafe, gabanta plate din abinci ne da ta gama ci tun dazu amma ta kasa dauke plate din sbd son jiki.


Da sallama Azlan ya shigo, da sauri ta dago ta kalle sa mikewa tai tana wani turo shafaffen kirjin ta kamar na wacce ta fara kirgan dangi, sai wani kwarkwasa take yi.


Dan gajeran murmushin Azlan yai yace "kizo part dina ynxu"


Daga haka ya juya y fita, tsalle ta buga tana wani turo kirji sai da ta shafa turaren da Mummy ta aiko mata dashi sannan ta nufi kofar daya fita.


Cikin yanga ta shiga bakinta dauke da sallama, dagowa nai muka hada ido da ita a tare gabanmu ya buga amma sai nai saurin dauke kaina ba tare da ko murmushi nayi Mata ba don na ga kalar kallon da take min da kuma shigar ta.


A bangaren Zeey ma wani irin bacin rai ne ya bayyana a fuskar ta har ta kasa boyewe, Zama tai a kujerar dake nesa dani tana wani harare Harare.
Ko kallon ta ban ba don tsaf na bawa banxa ajiyar ta Wanda hakan ba karamin kona Mata rai yai ba.


Mun kusa 10 minutes a zaune sannan Azlan ya fito hannun sa rike da robar ruwa, Zama yai a kujerar dake kallon tamu gaba daya, sai da ya dan jingina bayansa da kujerar sannan yai sallama.


Amsa mishi mukai dukkan mu, nidai kaina yana kasa ina wasa da hannu na.


Addu'a ya farayi tukun sannan yace "na taraku ne anan sbd rashin damar hakan da ban samu yiba jiya, fatan zaku hade kanku don bana son hayaniya kamar yadda kuma kuka sani dukkan ku nan zabin Baffa don haka in na samu zabina zan iya auro ta koda gobe ne kuwa".


Dagowa nai da sauri na kalle sa ganin ya kalle ni ne yasa na juyar da kaina ina turo baki, murmushi yai sannan yace "kamar yadda yake a addini ana yiwa budurwa sati a dakin ta haka Nima zanyi ke Batul kefe uwar gida daga kanki zan fara yau insha Allah, in kin gama satin ki sai kema zainabu nai miki sati daga nan kuma sai a koma kwana biyu biyu haka nake da ra'ayi ko da akwai Wanda hakan bai masa ba"


Shiru nai ina maimaita maganar sa knn raba mana kwana yai.


Ganin nayi shiru yasa Zeey da ta cika tai fam sbd takaici cikin Iyayi tace "hakan yayi Yaya"


Gyada kai yai yace "sannan duk mai girki ita zata dinga gyara min bangare na da Kula da abinci na, bana wasa da cikina shiyasa nake fada muku tun ynxu, kowaccen ku tana da kofar da zata sada ta da part dina a cikin palourn ta don haka basai ta fita ba, in kuma bake ce da girki ba Zan kulle Miki kofar ta yadda baxa ki iya shigowa ba sai dai ni nazo na same ki, fatan hakan duk ya muku"


Wannan karan ma Zeey ce ta amsa shi, kallon zainab yai yace _sai da safe zaki iya tafiya"


Kamar zata fashe da kuka ta mike tana jin zuciyar ta na tafarfasa, part dinta ta wuce kwalla ma zubo Mata.


Kallona yai yace "zaki iya tafiya kema in kuma a dakina kike son kwana baki da damuwa"


Da sauri na kalle sa nace "yaushe nace zan kwana a dakin Ka?"


Kafada ya daga yace "alamu na gani, tunda gashi kinki tashi kina zaune"


Kamar zanyi kuka nace "kaine fa baka cemin na tashi ba"


Idonsa nakan TV yace "ynxu na baki dama in kina so ki koma part dinki ki kwana ni dama ban Saba kwana da mace ba a daki daya".


Harara na maka masa nace "Nima ai ban saba kwana da namiji ba"


Kallona yai da idonsa da suka shanye sai lumshe su yake, wani Abu naji ya tsaya min a wuya hakan yasa na mike da sauri ina turo baki nace "sai da safe"


Gyada kai kawai yai ya juya yana kallo.


Ina zuwa daki hijab dina na cire na shiga toilet nai alwala, kwanciya nai akan gado bayan nayi addu'a tunani na fada akan zeey wacce take kishiya ta yadda take harara ta da yadda take wani iyayi yasa ni Jan tsaki, haka kawai naji tana bani haushi.


Ganin tunanin zai Jani zuwa wani wajen yasa na rufe idona ina karanta suratul mulk har bacci ya dauke ni.




Washe gari da safe bayan na idar da sallah dan gyara part din nawa nai sama sama don baiyi datti ba, ina gamawa na dauki tsintsiya da mop da rag na nufi part din oga.


Shiru yake ko ina fitilu a kashe da kyar na samu makunnar na kunna, share palourn nai na goge sosai kitchen din na shiga ba kayan tarkace daga gas sai kettle sai ko ina tsaf, gyara shi nai na fito kofofi biyu ne Wanda nake tunanin dakuna ne kuma yana cikin daya knn, kofar da ta kusa da dining na bude ba kowa aciki hakan yasa ni saurin gyarawa na fito.


Ban yi gigin shiga dayan ba na bar sa kawai anjima in na tabbatar ya fita sai na gyara.


Komawa part dina nai a gaggauce na shiga kitchen tea na dafa na soya dankali sai kwai dana soya masa, dibar masa nai a flask nawa kuma nasa plate, ajiye basket din dana sa miki nai akan dining na shiga wanka.


Ban dade ba na fito sai kamshi sabulun Mrs Dnah perfumes and more nake, Zama nai na shafa body cream din shima sannan nabi jikina da humrar ta mai sanyi da dadin kamshi.


Ganin 9 yasa na zira doguwar riga ta atampa, light make up nai na fesa turare sannan na janyo hijab nasa, daukar basket din nai bayan na dauki turaren wuta da fresher na Mrs Dnah perfumes and more na tafi dasu part din.


A dinning na jera masa flask din, show glass din palourn na bude dake dauke da set din plates da cups da jugs, plate da cup na dauko masa na ajiye a akan dining din.


Turare na kunna a burner sannan na koma part dina, abinci naci na koshi na koma bacci daki.


*******
Yau sati na daya kuma yau Zan fita girki knn, ji na nake cikin farin ciki don dama duk a takure nake gashi gobe zamu koma makarant ma.


Cikin satin ba abinda yake hada mu dashi sai gaisuwa, kullum zan masa breakfast da dinner kuma Zan shiga part dinsa na gyara masa na bade masa shi da turaren wuta, ynxu ma haka ina kitchen sanye da Riga da skirt da suka kamani sun min kyau sosai, jallof din taliya nake dafawa yar daidai tunda baxan yi abincin dare da shi ba na fita duty na, kuma a iya sani na baya dawowa da wuri.


Na gama ina wanke tukunyar data baci kamar a mafarki naji muryar Mimi tana cewa "Maa kina ina gani nan"


Da sauri na fito hannuna da ruwa sbd son tabbatar wa, ai kuwa ina zuwa tsakiyar palourn na ganta tana sanye da doguwar riga ware ido nai nace "Mimi ta"


A guje ta taho ta rungume ni tana ihu, Nima rungume ta nai ina lumshe idona nayi kewar ta sosai.


Dago ta nai nace "yaushe kika zo waye ya kawo ki"


Dariya tai tace "Daddy nane ya dauko ni, yace ynxu na dawo nan da Zama shiknn kullum zan dinga ganin ku"


Daga kai nai na kalle sa Yana tsaye ya rungume hannu yana kallon mu, fuska ta dauke da murmushi nace "Umma ta yadda ka kawo min ita"


Lumshe idonsa yai yace "gashi kuwa kin gani, mai kika dafa ne nake Jin kamshi"


Turo baki nai nace "nawa ne ni kadai fa ai na fita daga girki yau"


Kallon agogon sa yai yace "baki fita ba tukun don Magriba batai ba"


Sauke Mimi nai ina turo na shiga kitchen daura plate din nai akan tray na sa masa fork sai ruwa da glass cup dana sa mishi, a zaune na same sa a kan dinning ya daura Mimi akan dinning din tana game a wayar sa.


Ajiye masa tray din nai, bai ki kalle ni ba ya janyo ya fara ci bakinsa dauke da bismillah, yarinyar ta bata sa da taste din abincin ta da kallon wacce bata iya komai yake mata ba amma tuni ya daina mata wannn kallon, kullum bangaren sa kamshi yake gashi ko ina tsaf ga kuma abinci lafiyayye tana basa, shidai a jikinsa yana jin har kiba ya Kara.


Ina zaune daga kan kujera ina Kallonsa shiga Mimi sai surutu take masa yana biye mata Yana bata abincin a baki, kallon katuwar akwatin Mimi nai janta nai zuwa dayan dakin dake kusa da nawa.


Sbd kar na koma palourn yasa na shiga gyara mata kayan a wardrobe, kasancewar kayan a ninke suke nan da nan na gama.


Murmushi nai ina jina cikin nutsuwa sbd zuwan Mimi, fito wa nai har lokacin suna zaune akan dining sai dai sun gama cin abincin, plate din na dauka nakai kitchen na wanke.


Ina fitowa na gansa a tsaye yana yiwa Mimi magana, kallona yai yace "Zan wuce amma ku shirya gab da magrib kamar 6 zamu je gida ku gaida su Mami"


Daga kai nai nace "Allah ya kaimu, sai Ka dawo Allah ya kiyaye".


Daga kai yai yana amsawa a ransa, sai da ya shafa kan Mimi sannan ya fita ta kofar palour.


Har na zaune sai kuma na mike don ganin ya kamata na musu wani Abu na kai musu kar naje hannu haka, kitchen na shiga nida Mimi tana bani labarin yadda tayi missing dinmu nida Aisha, ina biye mata kuma itama ina bata wani abun tana tayani kamar miko da bare magi.


Kafin 5 na gama yi musu kubsa da miya sai kunun Aya da nai nasa a fridge, a kan dining na ajiye flask din na ja Mimi dakinta, wanka nai mata ta shirya ta cikin riga da skirt na atampa na daura mata Dan kwali, turare na fesa mata naja ta palour kallo na kunna mata sannan na shiga dakina Nima don yin wanka na shirya.


Shiryawa nai cikin blue lace na sa jaka da takalmi blue sai mayafi white dana dora tun daga kaina, banyi wata makeup sosai na don ko jambaki ban saba, turare na fesa sannan na dibar wa Mami turaren wutan Mrs Dnah perfumes and more a wata karamar kwalba.


Jakata na dauka na fito Palour ina fadin "Mimi fatan baki bata jikin kiba koh"


Jin Shiru yasa ni dagowa a tsaye take a jikinsa shi kuma ya tsugunna suna magana kasa kasa sai dariya take shi kuma yana murmushi, kallo daya yai mun ya juya yace "ki fito ynxu"


Daga masa kai kawai nai har suka fita daga palourn shi da Mimi, ajiyar zuciya na sauke kitchen na shiga na dakko kunun Aya a fridge sannan na dauki basket dina nasa a ciki, flask din suma nasa a cikin basket din na dakko na fita.


Ajiye basket din nai na kulle kofar palourn nasa key din a jaka sannan na dau basket din na juya, wannan shine karo na farko dana fara fitowa compound din gidan, babba ne Wanda yaji flowers masu kyau, sai parking space dake dauke da mota biyu lafiyayyu bayan wacce ya fito da ita.


Gurin motar na nufa ina tafiya a hankali, Zeey dake tsaye sanye da atampa Riga da skirt ta dame ta sai yalolon mayafi data yafa a kafada hannun ta rike da jaka, tun da ta fito ta gansa rike da Mimi ta hade rai don tasan wannan itace shegiar yar tasa ko ba'a ce Mata ba don ga kama nan ta gani, ranta bai Kara baci na sai da ta ganni na fito.


Ni kuwa ko a jikina gurin motar nazo na tsaya, kallon mu yai yace "muje koh"


Zeey ce tai saurin kama handle din front sit zata shiga, kallon ta yai yace "tsaya, daga yau in zamu fita tare ku duku duk wacce take da girki ita zata dinga zama a gaba, ynxu kuma girkin Batul ne itace zata zauna a gaba a dawowa nasan tym din munyi dare girkin ki ya shiga knn sai ki zauna a gaba ke"


Kamar zata fashe ta bude back sit ta shiga, kallona yai yace "meye wannan"


Basket din hannuna na kalla nace "abinci ne nayi ma su Mami zan kai musu"


Har ransa yaji dadi amma bai bari hakan ya nuna ba yace "muje"


Sai da na fara ajiye basket din sannan na zauna duk a darare, Mimi tana baya tana wasa da iPad din daya bata.


Motar tayi shiru baka jin komai har muka isa gidan, parking yai sannan yace "muje koh"


Fitowa nai na gyara mayafi na jakata na mikawa Mimi ni kuma na dau basket din, a hankali muke bin sa a baya har muka shiga part din Mami sai kamshi yake.


Tana zaune a kan kujera cikin shiga ta alfarma, tana ganin shigowar mu ta saki murmushi.


Tsugunnawa nai bayan na ajiye basket din hannuna a gefena cikin girmamawa nace "Mami ina wuni"


Murmushi tai tace "lafia qalau Batul ya gida"


Kaina a kasa nace "Alhamdulillah"


Zeey data cika tai bam sbd a nata tunanin Mami zata kyale batul ne ta Kula ta tunda ita tafi sani amma sai taga sabanin haka, cikin cinkushe murya tace "ina wuni"


Murmushi Mami tai tace "lafia qalau Zainab ya gida"


A takaice tace "Alhamdulillah"


Kallon Mimi Mami tai tace "zo Mimi"


Kallona Mimi tai sannan ta kalli Azlan, daga mata kai nai sai ta tafi gurin Mami, dora ta tai akan cinyar ta tace "kin san wace ni"


Girgiza kai Mimi tai tace "A'a"


Murmushi Mami tai tana shafa kumatun ta tace "granny dinki ce ni maman Daddy"


Ware manyan idonta tai tace "dama bayan Umma ina da wata granny din"


Daga Mata kai Mami tai tace "sosai ma gashi nn kin ganni nice maman Daddyn ki kinga granny knn koh"


Dariya Mimi rai tace "eh haka ne Granny"


Dariya itama Mami tai tana Jan kumatun ta, ajiyar zuciya na sauke don dama adan tsorace nake kar mutanen gidansu su nunawa Mimi tsana, amma da alama ta samu karbuwa agun Mamin.


Shagwaba fuska Azlan yai yace "Mami ni baki ganni ba"


Kallon sa tai tace "ya kamata dai kasan ka girma ynxu atoh"


Idon sa akan Mimi yace "ban girma ba har ynxu nine fa autan ki, Amma in kika sake haihuwa sai na yadda na girma"


Dakuwa Mami tai masa tace "gidan ku Azlan"


Dariya yai kawai yana shafa gemun sa.


Ni kuwa sosai ya ban mamaki Ashe yana zolaya haka, basket din dake gefena na janyo gabana nace "gashi Mami"


Kallona Mami tai tace "Mai muka samu haka"


Sunkuyar da kai nai kasa fuskata dauke da murmushi, mai aiki Mami ta kirawo tace ta kai kan dinning ta ajiye zata fara dibar wa Abie tukun.


Zeey data Kara cika kasa kasa yadda ni kadai zan jita tace "aikin banxa kawai neman gurin Zama"


Banza nai mata Kai na akan wayata, Mufeeda ce tazo cikin murna sbd zuwan mu ita ta raka mu muka gaida Mama sannan na dawo ita kuwa Zeey kin komawa part din Mami tai.


Mimi dai taga gata don sbd sangarta har goyata Mufeeda tai, bayan Abie ya dawo ma tare muka je muka gaishe sa yai mana nasiha sosai sannan kuma ya ya bamin da abincin da na kai masa.


Sai wajen 10 muka tashi tafiya lokacin Mimi tayi bacci, turaren wutan na bawa Mami ai kuwa taji dadin sa sosai.


Har waje Mami ta rako mu tare da sabuwar mai aikita Iya duk da ba wani tsufa ne da ita sosai ba amma babba ce, a baya muka zauna nida iya da Mimi Zeey an kame a gaba sai hura hanci ake.


Muna zuwa na dauki Mimi da basket din iya kuma ta dauki jakar kayan ta, bude kofa nai muka shiga maida kofar nai na rufe.


Kallon Iya nai nace iya bara nazo ynxu xan kwantar da Mimi, dakina na shiga na kwantar da ita ta cire mata kaya sannan na koma dakin ta na dauko mata kayan bacci.


Shirya ta nai na kaita tai fitsari na kwantar da ita, addu'a nai mata sannan na fito Palourn.


Dakin dake dauke da katifa na Kai iya nace mata da safe zan Mata bayanin yadda zata dinga aikin.


Ina komawa dakina shiga wanka, kayan bacci nasa Nima kwanta kawai sai na samu kaina da tunanin ko me yake ynxu wata kila Zeey taje gunsa da sauri na kawai da tunanin ina istigfari...








***********


Yana zaune sanye da three quarter da vest Zeey ta shigo sai bada kamshi take tasha wata shegiar riga iya cibiya da wando Wanda da kadan ya rufe mata mazauna, wani murmushi ta saki tana kallon sa shima dagowa yai ya zuba mata ido yana mamakin ta yadda take bayyana masa jikin sa Mai take nufi da Shi ne.


Duk da yadda take Jin tsoron sa amma kuma hudubar Maliki aminiyar ta yasa ta ke bawa kanta kwarin gwiwa, Zama tai a a gefensa ta kwantar da kansa akan kafadar sa, cikin shagwaba tace "Yaya....."
















Comments Nd share plz
















Mrs A.M🥰
[09/09, 19:41] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️


*TASWIRAR KADDARA*


♠️♠️♠️♠️♠️




Written by
Mrs A.M🥰


Page 30


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃




*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*




*LOCATION KANO*


08062073990




Da mamaki ya ke kallonta ganin yadda ta kwantar da kanta a kafadar sa sai wani shafa masa hannu take, cikin nutsuwa yace "Zainabu"


Lumshe ido zeey tai tace "na'am Yaya"


Gyada kai yai yace "yaushe kika zama jarababbiya da har zaki kawo kanki gun miji"


Da mamaki ta kallesa tace "Yaya kamar yaya?"


Juyar da kansa yai yace "ynxu wannan shigar da kikai da kuma yadda kika zo kika kwanta a jikina seducing dina kike so kiyi ko me".


Dagowa tai daga jikinsa ta kallesa, gabanta ne ya fadi ganin yadda ya hade rai kamar Wanda aka aiko masa da sakon mutuwa.


Jin tayi shiru yasa shi juyowa ya kalle ta cikin ido yace "bana sha'awar mace ynxu lokacin da su Baffa suka yanke min auren mace sama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login