Showing 87001 words to 90000 words out of 94393 words
Chapter 30 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt
nidai yunwa nake ji"
Sakwara na zuba a plate na zauna naci sosai, ina gama sha nasha maganin da aka bani a hospital a gajiye na mike na nufi part dinsa ina danna wayata.
Dan kishingida nai bansan lokacin da bacci ya dauke niba.
Shigo wa yai hannun sa rike da leda mai, lumshe ido yai Jin kamshi mai dadi ya bugi hancinsa, a hankali wani murmushi ya subuce masa yasan cewa ynxu ta hakura knn.
Ajiye ledar yai akan center table ya zuba min ido yana kallona, ganin yadda take baccin hankalin ta kwance yasa shi sakin murmushi.
Peck yai mata a goshi ya nufi dinning yana murmushi, abinci ya zuba yana ci yana gyada kai har ya gama ya tashi ya dawo palourn ya zauna.
Lokacin dana tashi tare na gansu shida Mimi yana koya mata homework, murmushi nai na mike na shiga dakinsa fitsari nai nayi alwala na fito.
Tare mukai sallah nida shi, muna idar wa na dauki ledar kifin na bude na shiga ci ina lumshe ido na sbd dadi.
Ranar tare muka wuni a part dinsa nida Mimi sai da tayi bacci na kaita dakinta nayi wanka Nima na tafi part dinsa.
Washe gari da safe ban je school ba, Samira matar Junaid ta kirani tace zasu zo itada Mami.
Tun da na tashi nida Iya muke kitchen muna girke girke, kafin 1 mun gama komai an jera a dining, Kara gyara palourn iya tai aka kunna turaren wuta.
Wanka nai masa doguwar rigar atampa, tamin kyau sosai kuma kasancewar ta a shape bata nuna cikina daya dan turo gaba ba.
Shiya Mimi nai itama tunda yau Friday an dauko ta da wuri, mayafi na dauka na yafa muka fito Palour muka zauna zaman jiran sa.
Lumshe idona nai ina Jin jiri kadan kadan, tun da na tashi nake jin jirin kawai daurewa nake.
Wajen 2 su Mamin suka zo, sosai na musu kyakkyawan tarba sai sunkuyar da kai nake sbd kunya bama yadda suke ta jeramin sannu.
Samira tace "ai nayi fushi Batul baki taba zuwa gidana bafa".
Murmushi nai kaina akan Mimi nace "kiyi hakuri Aunty Samira sbd school ne shi yasa".
Mami dake ta murmushi tace "kar kiga laifin ta fah Samira ai laifin na Azlan ne dabai kawo ta ba, Allah dai ya shirya mana Shi kawai".
Murmushi nai ina sunkuya da kaina, abincin muka kawo musu nan nida Iya, sunci sosai kuwa Mimi na kan cinyar Mami tana ta zuba mata shagwaba.
Lumshe idona nai jin Yana Sara min ina dan yamutsa fuska, kallona Mami tai tace "lafia mene, tun dazu naga kina dan yamutsa fuska wani abun ne yake damunki".
Shafa goshina nake nace "kaina ne yake min ciwo, kuma ina ganin jiri".
Kallona Mami tai sosai tace "subhanallah tun yaushe?"
Kamar zanyi kuka nace "tun jiya"
Kallon Samira tai tace "muje Samira mu kaita hospital a duba ki, ba'a wasa da wannan lokacin kinji duk abinda kika ga ba haka ba kifa da, Maza yafa mayafin ki mu je".
Daukar waya tai ta Kira Azlan ta fada masa tace ya samu a hospital din.
A motar Mami muka je ban da Mimi da aka barta gun iya, Samira na gaba ita da driver sai nida Mami a back sit.
Da muka je asibitin nida Mami muka shiga gurin doctorn, duba ni yai yace na kula sosai din BP dina yake son hawa ya rabuta min magani.
A harabar hospital din muka hadu da Azlan shigowar knn, da sauri ya taho guna ya riko min hannu cike da kulawa yace "kina lafia Baby?".
Hannuna na zame daga cikin nasa nace "ba ruwana nidai, Mami tana kallo fa".
Kallon Mami yai yana sosa keya "sorry Maa, tana lafia".
Girgiza kai Mami tai tace "Alhamdulillah, BP dinta ne yake Son hawa amma an bata magani, Ka Kula da shan maganin ta sosai".
Daga kai yai yace "insha Allah, kallon Samira yai yace a'a kanwata har da ke".
Hararar Wasa ta masa tace "ai ni kam ba ruwana dakai Ya Azlan baka taba kawo ta fa gidana ba".
Dariyar yai yace "to kiyi hakuri mana ke kuwa, ai ba'a ji kanmu ba".
Kallon Mami tai tace "Mami ko zai kaimu mu duba sai ya ajiye mu a gida kawai".
Daga Kai Mami tai tace "yafi sauki ma kuwa, kallon sa tai tace muje Ka kaimu gidan ta zamu duba abu a gidan"
Zubawa Mami idonsa yai yace "Maa mai zaku duba"
Samira ce tace "curtains nake son chanja wa kafin Ya Junaid ya dawo shine zamu je nida Mami mu duba sbd inason chanja har carpets da".
Daga kai yai yace "sannu yar gayu, lallai yarinyar nan kudi ne dake".
Motar sa muka shiga dukan mu bayan Mami ta cewa drivern ta ya tafi, tafiya 15 minutes ta kaimu gidan.
A bakin gate yai parking ya fito yace "muje toh, fatan kin fito da key ko".
Fitowa tai tana dariya tace "na fito da su mana ai gate man din ya tafi kauye"
Kallona Mami tai tace "fito kema mu shiga tare"
Fitowa nai a tare muka shiga gidan bayan tasa key ta bude kofar gate din, lokacin da muka isa kofar palourn har tasa key a jiki ta murda taji kofar a bude, kallon mu tai tace "badai ban kulle kofar nan ba a bude naji ta"
Girgiza kai Mami tai tace "garin saurin ki ma zaki iya mantawa, bude toh in zamu fita sai ki tabbatar kin rufe sosai"
Tura kofar tai muka shigo gaba dayan mu, abinda na gani a Palourn ne ya masifar daga min hankali da sauri na sunkuyar da kaina kasa ina fadin Innanillahi wa innanillaihir raji'un.
Samira da tai mutuwa tsaye cikin rawar jiki tace "innanillaihi wa innanillaihir raji'un" kawai ta fadi kasa a sume.
Domin magana da marubuciyar kai tsaye
09066728387
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[29/09, 18:34] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 44
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Tunda nayi mistake din fara turo muku dazu gashi🥹
Ba komai ne ya sumar da Samira ba sai Junaid data gani kwance akan carpet daka shinfida duvet shida wata mace dukan su tsirara suna sex sai ihu suke.
Wannan salatin da Samira tai shi ya jawo hankalin Junaid ya dago da sauri yana kallon su, a razane ya zare jikinsa daga na karuwar yana rawar jiki, wandon sa ya janyo yasa yana kallon Mami data sunkuyar da kanta kasa tana hawaye.
Ni kaima jikina rawa yake Sbd tsoro, ban taba tunanin Junaid zai aikata abinda na gani yana yi ynxu na, ashe duk sunkuyar da kan da yake tantiri ne.
Mikewa yai da sauri ya dauki car key dinsa ya fita a guje, yana fita ya bude gate jikinsa sai rawa yake, mota ya shiga ya kunna ya fita ko rufe motar bai yiba ba abinda yake sai kuka.
Dai dai kwanar da zai fita daga unguwar sukai aran gama da babar mota tazo zata shiga, juyawa motar sa ta fara yi har taje ta bugi da bishiyar dake kan kwanta.
Da sauri mutane suka taso suna salati kayi kansa ganin motar ta fara hayaki, da kyar aka samu aka fito dashi wani mai adaidaita ya sashi a baya suka tafi kaishi asibiti mafi kusa tunda baya numfashi.
*******
Azlan kuwa duk da abin ya duke sa amma sai yayi namijin kokari gun kama Mami, yana rike ta kawai ta fada jikinsa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, shafa bayan ta yake yana fadin "Maa kiyi hakuri, ki daure mu kai Samira hospital ta Suma".
Damke hannun sa tai cikin kuka tace "kace min abinda na gani ynxu karya ne, kace ban ga daidai ba".
Shiru kawai yai idonsa ya Kada yayi jajir, tunda yake da girman sa bai taba ganin kukan Maa dinsa, Maa ta kasance mace mai dauriya sosai ba karamin abu bane zai sa kaga gazawar ta, kallon karuwar dake ta rawar jiki yai cikin bacin rai yace "zaki fita ko kuma sai nazo nayi ball dake".
Da sauri ta dauki jakar ta ta fita a guje, da kyar ya lallashi Mami muka kama Samira nida ita muka fito shine ya rufe gidan da key ya bude mana mota muka sata a back sit.
Zaman kurame mukai a motar har muka isa hospital, muna zuwa aka karbe ta mu kuma muka tsaya a waje, Zama Mami tai ta dafe kanta tana hawaye.
Zaro wayar ta tai a jaka dake ta faman ringing tun dazu, ba tare da ta iya ganin mai Kiran ba ta dauka, cikin tashin hankali Abie yace "kina ina Hajia?, duk inda kike ki Maza kixo AKTH Junaid yayi accident yana can".
Cikin rashin damuwa tace "Allah ya sauwaka", kawai ta kashe wayar.
Kallon Baffa Abie yai yace bata damu bafa Baffa, kawai cewa tai Allah ya sauwaka.
Dafa sa Baffa yai yace "Ka jira zuwa anjima, dama na fada ma da akwai wani abu da bamu sani ba, yaron nan tsawon sati biyu knn baya nan a tunanin mu ya je neman magani, kawai kuma sai ace yayi hatsari bayan munsan dai ba ynxu ne lokacin dawowar saba".
Shiru Abie yai gaban sa yana faduwa, kasa nutsuwa wai ya Kara kiran Mami, wannan lokacin tana dauka bata basa damar magana ba tace "Muma muna asibiti Samira ta suma", kawai ta kashe wayar.
Kallon Baffa yai yace "wai itama suna asibiti Samira ce ta Suma, nidai Baffa hankali na duk ya kasa kwanciya".
Murmushin manya Baffa yai yace "kar Ka damu, insha Allah komai zai zo da sauki bara muji yashi Junaid din yake sai muje can asibitin muma".
Suna tsaye har doctorn ya fito, gaisawa sukai yace su same sa a office.
Zaune Baffa da Abie suka a gaban doctorn cikin rashin fahimta Abie yace "ban gane mai kake nufi ba doctor".
Takardar gabansa ya tura ma Abie yace "gashi, kamar yadda na fada ma dai a sakamakon hatsarin da yai baxai iya haihuwa ba gaba daya".
Cikin mamaki Baffa yace "amma likita dama can ai ance baxai iya haihuwa ba, don yana ta zuwa ganin doctor ma a kasashen ketare yana shan mamaki".
Girgiza kai doctor din yai yace "gaskiar mudai a binciken mu lafiyar sa qalau zai iya haihuwa, ynxu ne dai matsalar daya samu ta kashe masa kwayayan halittar sa".
Innanillaihi wa innanillaihir raji'un kawai Abie yake fada yana fifita da hannun sa, ya kasa magana gaba daya.
Baffa ne yayi jarumtar cewa likitan "kamar yaushe zai farfado, kuma bayan wannan ba wani matsala koh? ".
Gyada kai doctorn yai yace "muna saran yau da daddare ko gobe insha Allah, bayan wannan kuma Insha Allah muna saran komai daidai"
Godia suka yima doctorn suka fito an rasa Wanda zaiyi magana.
Daga nan asibitin da aka kwantar da Samira suka je, da Azlan suka fara cin karo koda suka tambaye sa abinda ya faru cewa yai su tambayi Mami.
Sun samu samirar ta farfado amma ba yadda basuyi da Mami akan cewa ta fada musu abinda ya faru ba tace sai an sallami Junaid.
Sai da muka kai su Mami gida sannan muka koma, nidai jikina duk yayi sanyi tausayin Samira da Mami ya gama lullube ni duk sona da abinci ban iya ciba sosai yau.
Kamar yadda doctorn ya fada a daren Junaid ya farfado, tunda ya tashi yake kuka kamar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa.
Satin sa daya a asibiti aka sallame sa, tunda ya kwanta kuma Mami ko Samira basu zo sun duba saba, Wanda wannan ya Kara sa Baffa da Abie a cikin rudani, Azlan ma sau daya yazo ya duba sa bai Kara dawowa ba.
Yau din kafin su tafi sai da ya roki Baffa Alfarmar ya kirawo kowa da kowa hadda iyayen Batul don yana son yayi magana a gabansu, ba tare da Baffa ya tambaye sa dalili ba ya tara duk Wanda yafada a gidan sa don shima dama sun boye masa cewar ance baxai sake haihuwa ba.
Kowa da kowa ya hallara a Palourn Baffa, ina gefen Umma hannu na cikin nata, cikin sati dayan nan har ramewa nai sbd tashin hankali, kullum Daddyn Mimi in ya fita tun safe bata dawowa sai wajen 11, komai baya min dadi ko school naje ba dadi nake jiba.
Shigowar Junaid da Baffa ne ya sa palourn yin shiru daga hayaniyar da ake sama sama da, Zama sukai kan Junaid a kasa.
Baffa ne ya bude taron da addu'a ya dora da fadin "kamar yadda na tara ku anan Nima ban san dalilin hakan ba, Junaid ne ya nemi da yana so a tara masa ku zaiyi magana daku toh amma kafin nan Nima ina son na fada masa wani Abu sbd kaina ya shiga rudu ina son ya fayyace min komai"
Kallon Junaid yai yace "abin mamaki likita yace sakamakon hatsarin da kai baxa ka taba iya haihuwa ba, bayan kuma anan kowa yasan cewa tun tuni ance ba lallai Ka iya haihuwa ba, sai kuma likitan yace a da kwayoyin haihuwar Ka lafia qalau suke ynxu ne dai baxa Ka iya haihuwa ba kwata kwata".
Kuka Junaid ya fashe dashi yace "Baffa ynxu yace baxan iya haihuwa ba gaba daya karya yake wallahi Baffa lafiya ta qalau".
Abie ne ya miko masa takadda yace "karanta ai likita ne kai nasan zaka fahimci abinda ke ciki".
Cikin rawar jiki ya bude ya soma karantawa, innanillaihi wa innanillaihir raji'un kawai yake fada yana kuka.
Kallon Samira yai wadda ta rame sosai tayi baki kamar wacce ta shekara tana ciwo yace "don Allah ki yafe min nasan hakkin kine ya fara kamani".
Kallon Mami yai ganin ko Kallonsa ba tayi ya sunkuyar da kai kasa, cikin rawar murya yace "ina haihuwa lafiya ta qalau, ina bawa Samira maganin hana daukar ciki aduk lokacin da xamu kwanta tare, tun lokacin dana fara bata na cemata maganin zai taimaka gurin saurin sata ta samu ciki, shiyasa bata taba tambaya ta ba akan me ko kuma wani irin magani nake bata ba."
Salati aka dauka gaba daya, kuka Samira ta fashe dashi tana sunkuyar da kanta kasa.
Kallon sa Mami tai tace "amma ka cuce ta kuma sakayya ynxu Ka fara ganin ta wallahi"
Kallon Baffa tai kawai ta fashe da kuka tace "Baffa gidan sa muka je sbd Samira dake son ta chanja wasu abubuwan a Palourn ta amma sai muka same sa shida karuwa suna aikata alfahari, a gidan auren sa Baffa", kawai ta Kara fashewa da kuka.
Kuka yake sosai yace "ku yafe min don Allah wallahi sharrin shaidan ne, duk lokacin dana ce muku na tafi neman magani ba kasar waje naje ba, ina zaune a nan ne gurin Mata amma ba'a gidana ba, wannan Karan ne kawai tsautsayi yasa na zauna a gidana".
Kallon Samira yai da kanta yake kasa yace "ki yafe min, ko ina nan wani lokacin ina kaiwa dare ko na kwana a waje gurin mata nake zuwa sai na ce miki aiki ne ya rike ni".
Mari Abie ya kifa masa cikin bacin rai yace "Allah wadaran ka Junaid kayi asara wallahi ban san haka kake ba, kullum sai na yabe Ka har gori nake yiwa Dan uwanka nace yayi koyi da halin Ka Ashe Ashe kai kama fisa iya shege"
Kuka kawai yake kansa a kasa, da rarrafe ya isa inda Azlan yake dafa kafar sa yai yace "Dan uwana don Allah Ka bani yata, kana ji ance baxan sake haihuwa ba Ka taimaki rayuwa ta inason na haihu wallahi"
Wani irin kallo Azlan ya masa yace "wacce yar taka ce a hannu na, a iya sanina baka da yarinya a hannuna".
Rike hannun sa yai sosai yace *"MIMI"*
Domin magana da marubuciyar kai tsaye
09066728387
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[30/09, 01:44] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 45
Dedicated to Maman Husna(Daughter)🥰
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Hannu Azlan yasa ya hankada sa baya, cikin bacin rai daya fito baro baro a fuskar sa yace "bana son iskanci banxa Malam, kasan dai bana wannan wasan banxan dakai koh".
Kuka Junaid ya sake fashewa dashi, juya wa yai ya kalli Abba da tunda aka fara magana kansa yake kasa, da sauri ya rarrafa gunsa kafar sa ya rike cikin rawar baki yace "wallahi nine mahaifin ta nine nan na Mata fyade ba Azlan bane, kuma abin hannun da yake gurin batul nawa ne bana Azlan ba".
Ganin Abba bai magana ba ya saki kafar sa ya dawo gurin batul, kallon ta yake yana kuka yace "wallahi nine Wanda kika jiwa ciwo a hannu kinga", hannun rigar sa yaja baya ya nuna mata hannun sa da tabon ciwo yake gun, cikin rawar baki yace "shine ciwon da kika jimin, ki tuna nine nan don Allah ku bani yarinyar ta inason ta wallahi".
Banxa na masa kaina a kasa ina kuka, don ynxu komai yake dawo min sabo tsaf kamar ynxu abin yake faruwa.
Juyawa yai ya kalli Abie duk ya rude abin hannun sa ya cire yace "Abie na Azlan ne ba nawa bane ku yafe min, ranar da abin ya faru dana ga Batul tazare min abin hannu na sai na sami Azlan a ranar nace masa ya taimaka ya bani nasa, nawa ya bata ban san inda ya shiga ba nace masa kuma Samira tana sonsa sosai bana so taga baya hannu na, shine ya bani kuma ni na roke sa don Allah kar ya fadawa kowa ya bani abin nasa shiyasa bai fada ma kowa ba".
Kallon Azlan Abie yai yace "kasan ba kaine Ka aikata abin da ake zargin Ka