Showing 90001 words to 93000 words out of 94393 words

Chapter 31 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt

Mrs A.M   

03 Aug 2024

16890

dashi ba mai yasa bakai magana ba Ka dauki laifin".


Turo baki gaba yai yana hade rai yace "sbd yata ce nine nan mahaifin ta ina sonta".


Baffa shima da ransa yai kololuwar baci yace "dama tun da Ka amsa nace kwokwonto sbd basan baka karya kawai dai nayi shiru ne, don ban taba kawo wa Junaid zai iya aikata wannan mummunan aikin ba".


Girgiza kai Abie yai yace "Azlan dama kasan cewa Junaid yana aikata wannan abin baka taba fada min ba?".

Sunkuyar da kai yai yace "ban sani ba Abie amma abinda na sani shine wani yana amfani da fuskata yana yawon zuwa club, ni kuma ana yawan min magana akan cewa an ganni a club ina rawa da yan mata ko kuma mun shiga hotel dasu, duk zuwa club din da nake yi ba wai zuwa nake naji Kida ba, in har naje club to an fada min cewa an ganni ne shine nake zuwa don naga Wanda yake amfani da fuskata yake zuba iskancin sa a matsayin nine".


Kallon Junaid yai yace "bansan cewa Junaid bane sai bayan aure na lokacin da wata student dita dake son na aureta tazo tayi threating dina tana nuna min hoto na a club da yan mata akan cewa in ban yadda na aure ta ba zata nuna muku su, a lokacin ne na gane Junaid ne ta takalmin kafar sa da wandon sa, tunda a daren ranar mun hadu dashi kuma tabbas Naga takalmin da wandon a jikinsa sai ya daura jallabiya akai".


Mai da kallon sa yai Kan Abie yace "Abie na taba zuwa na same Ka akan kasawa Junaid ido duk lokacin dayai tafiya, ba don komai nafada maka haka ba sai na taba ganin sa a hotel zasu fita shida wata mace, bayan kuma a iya sanina yace ya tafi India ganin doctor, sai da na bisa na tabbatar shine sannan nazo na same sa amma sai fada Ka kamani dashi kace ban ji kunya ba zance Ka Sawa Junaid ido shida yake mutumin kirki, bayan nine tantirin".


Kallon Mami yai yace "ko Mami zan fadawa kullum ta tashi min fada sai tace ku biyu kadai Allah ya bani Azlan, dayan shiryayye ne Alhamdulillah kaima ina fatan Allah ya shirya min kai wata ran", murmushi yai mai ciwo yace "baxan iya fada mata ba Sam".


Samira dake kuka kasa kasa ya kalla yace "ko zuwa zanyi na sami Samira na fada mata, a ko yaushe tana alfahari da mijin, ni kaina tasha fadamin cewa kullum tana godewa Allah daya bata miji mai hankali da Addini irin Junaid".


Mai da dubansa gun Junaid yai yace "Amma tabbas ban san cewa yana bawa Sameera maganin haka daukar ciki ba dana sani ba abinda zai hanani daukar mataki a lokacin, bayan wannan ni bansan komai ba".


Wani Kallo yai ma Junaid yace "kuma wallahi Ka sani har abada kar na Kara ji Ka Kira yarinya ta da taka, tawa ce ni kadai nine nan mahaifinta Khadija Azlan shine sunan ta"


Murmushi takaici Mami tai tace "kaji kunya wallahi Junaid, Ka jira sakamakon abinda Ka aikata", paper da pen din dake jakarta ta ciro Mika masa tai tace "sakar min yarinya ta ynxun nan"


Zaro Ido yai yace "Mami kiyi hakuri baxan iya sakin taba wallahi ina sonta".


Cikin karaji Sameera da tunda abin ya faru bata magana sai kuka tace "wallahi sai Ka sake ni Junaid bana sonka na tsane Ka Allah ya saka min abinda kamin".


Hannun ta zai rike ta wafce da sauri tana kankanme jikinta, kuka ta Kara fashewa dashi tace "Ka cuce ni wallahi, na dauki yadda ta na baka ban taba tunanin ko kallon Mata ka nayi ba Wanda musulunci ya hana, kullum ka fita binka nake da addu'a zuciya ta bata taba dasamin zargin Kaba, ko kwana kayi a waje haka nake hakura duk da tsoron da nake ji ashe ga abinda kake aikata da mai na rage Ka Junaid na tsane Ka".


Kuka ya sake fashewa dashi yana girgiza kai yace "don Allah ki daina cewa kin tsaneni, ki yafe min wallahi na gane kuskure na baxan Kara ba ki yadda dani".


Wani kallo ta masa tace "na yadda dakai har abada, ina son yara sosai ina son na haihu amma sbd kai nake daure wa ina nuna ma kamar ban damu ba sbd kar na daga ma hankali ashe kashe ni kake ban sani ba".


Zai sake magana Mami ta Mika masa papern tace "Maza sakar min yarinya ta ynxun nan".


Juyawa yai ya kalli Baffa yace "Baffa kasa baki wallahi baxan iya sakin taba ina sonta sosai Baffa".


Wani murmushi Baffa yai yace "baxan iya cewa komai ba, komai ya faru kai kajawa kanka Ka saki yarinyar mutane kawai".


Hade rai Mami tai tace "Junaid in har baka saki Sameera ynxu ba Allah ya tsine ma albarka".


Zaro ido yai ya dora hannu akai yace "innanillah wa innanillaihir raji'un, don Allah Mami don Allah".


Zare masa ido tai tace "zaka sake ta ko kuwa"


Da sauri ya karbi takardar hannun sa na rawa ya rubuta "ni Junaid na saki Sameera saki daya", yana gama rubutawa ya dora takardar a fuskar sa ya fashe da kuka.


Hannu Mami tasa ta warfe takarbar tace "Allah raka taki gona".


Sosai Baffa yayi nasiha mai ratsa jiki ya dora da fadin "sannan magana mai muhimmanci shine duka yaranmu mu dinga musu addu'a gaba daya akan Allah ya shirya mana su, bawai mu ware daya ba kawai sbd muna tunanin shine mara Jin magana, kar mu manta suna sauran mutane ne kamar kowa, Allah yasa mu dace".


Kallon Azlan Junaid yai yace "Ka yafe min don Allah duk abinda nake yi, Ka bani Mimin kaji".


Tsaki Azlan yai yace "kan Ka da motsi inaga, kar Ka Kara cewa na baka yarinya ta har abada baxa ta taba zuwa hannun Kaba".


Mikewa yai zai tafi Baffa yace "Ka dauki matar Ka Zainab ta koma dakin ta yau"


Daga kai kawai yai yace "kuzo muje"


Mikewa mukai nida ita muka bi bayansa, a bayan mota na zauna ta shiga gaba fuskar ta washe da farin ciki.


Nidai jikina duk yayi sanyi da wannan tashin hankalin da na tarar yau, a sanyaye na shiga part dina bayan mun koma duk wani iri nake jina.


Dawowar Zeey bai chanja komai ba dake faruwa a gidan, kowa ya dauki girkin sa da muhimmanci don ynxu ita ma ta daina wasa tuni ya watsar da Malika, muna gaisawa jefi jefi sai dai kowa kishin sa yana ransa.


Bayan wata biyu da wannan abin Alhamdulillah komai ya dawo daidai, a ynxu cikina watan sa 8 yayi girma sosai kamar wacce zata haihu ynxu da kyar nake komai amma duk da haka Daddyn Mimi bai bar jan kaya ba.


Fitowa ta knn daga wanka doguwar riga nasa bubu na tsaya ina kallon kaina a mirror gaba daya na chanja nayi kiba sosai cikina kamar zai fashe sbd girma.


Ina tsaye a gun naji ana shafa cikina ta baya juyo wa nai na kalle sa nace "mene ne, nidai Ka kyale ni nasan tsokana ta kawai zaka yi"


Dariya yai yace "Queen tawa ni kadai na isa na tsokane ni ni kuma uhm beauty ta".


Kukan shagwaba nasa masa nace "baga shi nan ba kana cemin beauty bayan duk nayi muni hancina yayi katoto"


Dariya yake kunshe wa yace "ban ga wani munin da kikai ba, ni kyau ma naga kinyi sosai sosai Queen".


Dukan wasa na masa nace "kai ko ba ruwana da kai munyi fada"


Da sauri yace "kiyi hakuri don Allah in kika ce ba ruwan ki ai na shiga uku, ina zan dinga shiga ina swimming".


Girgiza kai nai nace "kaidai baka da kunya wallahi ba ruwana"


Murmushi yai yace "ki shirya muje mu karasa shopping din babyn kinji, sun kusa zuwa fah insha Allah".


Turo baki nai nace "sai dai kai Ka karasa shirya ni gaskia"


Kiss yamin a lips dina yace "an gama tauraruwar heart dina".


Shi ya karasa shirya ni muka fito tare hannun sa cikin nawa, gyara hijab dina nai ina kwalawa Mimi Kira.


Da sauri ta fito daga kitchen hannun ta rike da chocolate, tana ganin Daddyn ta tayi tsalle ta fada jikin sa tana fadin "oyoyo Dadyna".














Domin magana da marubuciyar kai tsaye




09066728387












Comments Nd share plz
















Mrs A.M🥰
[30/09, 02:51] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️


*TASWIRAR KADDARA*


♠️♠️♠️♠️♠️




Written by
Mrs A.M🥰


Page 46




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃




*Mrs Dnah perfumes nd more*


*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*


*Muna Saida*


*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.




*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*




*Phone number*
+234 702 577 7778


Location kano




Daga tai sama Yana dariya yace "wacece wannan".


Dariya tayi tace "beautyn Daddy ce"


Sauke ta yai suna dariya yace "Maza jeki yi sa hijab kizo muje muyi shopping wa siblings dinki".


Ihu ta saki tana dariya ta nufi dakinta, girgiza Kai nai nace "Allah ya shirye ku gaba daya".


Kashe min ido yai yace "Ameen matar".


Wayata ce ta shiga ringing, fito da ita nai daga jakata na dauka ganin Umma ce.


A nutse nace "Umma ina wuni, yasu Kamal"


Murmushi tai tace "lafia qalau, suna nan lafia, ya Mimi da kuma jiki jikin"


Sunkuyar da kai nai nace "Alhamdulillah Umma".


"Toh Masha Allah, Aisha ta haihu ynxu muna asibitin ma tun dazu"


Zaro ido nai nace "da gaske Umma tana ina".


"Wanka take in ta fito amma nasan zata kiraki".


Ihu na saki nace "mai ta Haifa Umma".


Tsaki Umma tai tace "ki shiga hankalin ki fa bana son shirme meye na ihu kuma, namiji ta Haifa".


Turo baki nai nace "Allah ya raya sa Umma ki turo min hoton sa don Allah kafin nazo, fita zamuyi ynxu Insha Allah zan shigo nasan zai kawo ni".


Cire wayar nai daga kunne na bayan munyi sallama.


Kallon sa nai yadda ya zuba min ido yana kallona, murmushi nai nace "Baby Aisha ce ta haihu mun sami baby boy".


Murmushi yai yace "Masha Allah, Allah ya raya ya masa albarka saura ke".


Dariya nai nace "kaji kamar haihuwar ba wuya".


Shafa kumatuna yai yace "baxai Miki wuya ba Insha Allah Queen".


Lumshe ido nai cike da Jin dadin wannan sunan da yake kirana da shi.


Key din motar ya miko min yace "gashi bara naje nayi ma Zainab sallama bata son zamu fita ba"


Murmushi nai masa kawai banyi magana ba, a raina kuwa kishi ne yake taso min ina kokarin controling dinsa.


A Palourn ta ya same ta tana chatting, TV a kunne tana kallo.


Zama yai yana janye kafar ta tare da mata tafiyar tsutsa yace "princess mai kike yi ne uhm".


Gyara zaman ta tai tana dariya tace "Hub chatting fa nake yi kawai".


Murmushi yai yace "kina lafia dai koh, baki bukatar komai".


Shafa gemun sa tai tana kwanciya akan kirjinsa tace "bana bukatar komai Yaya, duk abinda nake so kana min tun kafin na tambaya".


Murmushi yai kawai yana shafa kanta, shifa har mamakin Zeey yake ta chanja sosai kamar ba ita ba, tana kokari wajen ganin ta faran ta masa rai duk abinda yake so tana kiyaye wa, kawai dai matsalar ta shine ragwanta a shinfida bata iya dadewa sosai a kunne😉.


Mikewa yai yace "bara naje zamu fita da Maa din Mimi, ina son na gama siyayyar kayan babyn yau ne gaba daya dama kuma kadan ya rage".


Murmushi tai tace "Allah ya kiyaye, sai kun dawo ina gaida Mimi".


Kiss ya Mata a kumatu a fita, ajiyar zuciya ta sauke bayan ya fita, idon ta na kawo kwalla tana kishi sosai akan sa ba karamin daurewa take ba duk lokacin da zata tuna cewa ba ita kadai bace matar sa.


Lokacin daya fito a mota sa same mu, Mimi tana zaune a baya ina gaba, muna magana da ita kamar ina hira da babbar mace.


Zama yai yace "sorry Queen na barki kina Jira".


Turo baki nai kawai ina juyar da kaina, murmushi yai ya tada motar muka tafi.


Sosai mukai siyayya kamar me, duk abinda ya gani ya masa kyau sai ya dauka na mace da namiji, sai da aka cika motar da Kaya Mimi ta koma gefe sosai sbd kayan dake bayan.


Daga nan asibiti ya ajiye mu ya tafi, bai shiga ba sbd sauri yake Mami na kiransa.


Lokacin dana shiga dakin a zaune na sami Aisha a Kan gado tana Shan tea, Umma ce a dakin da Aunty Bilkisu sai yakumbo a zaune akan carpet.


Zama nai da kyar a gefen gadon bayan mun gaisa dasu Umma, kallon Aisha nai nace "sannu Aisha ya jikin".


Murmushi tai tana kurbar tea tace "Alhamdulillah Ya Batul, kar ki wani damu ba wuya haihuwar fa".


Harara na maka Mata nace "ni zaki mayar karamar yarinya, nidai ki fada min don Allah da wahala".


Ajiyar zuciya ta sauke tace "maganar gaskia wallahi da wuya bala'i, tabdijan Allah yasa mu dace kawai amma ko da dinki aka bar ki an gama magana kawai".


Kwal kwal nai da idona nace "ki rantse da wahala".


Xatai magana Aunty Bilkisu tace "zaku mana shiru ko sai na mammake muku baki, ke kuma tsaya kina tambayar ta da wuya ko ba wuya, kowa da yadda take zuwar masa Allah dai kawai ya sauke ki lafia".


Miko min babyn Umma tai tace gashi ko kallon sa baki yi ba kin zauna kina surutu.


Dariya nai ina shafa fuskar sa nace Masha Allah dani yake kama Umma.


Girgiza kai Umma tai tace Karya da ciwo bada ke yake kama ba gaskia angona yafi ki kyau.


Dariya mukai duka ina kallon sa, sosai muka sha hira naji sai bayan Isha'i ya dawo daukar mu, sai da ya shigo suka gaisa dasu Umma sannan muka tafi tare.


Tunda akai haihuwar kusan kullum sai ya kai ni gidan Aisha, har sai da Umma tamin fada tace kar na Kara zuwa sai ranar suna haka na gama turo bakina na hakura, ranar suna yaci sunan Abba zamu dinga ce masa Asad.




*******


Kwanci tashi asarar Mai rai cikina ya cika watan haihuwa, na Kara Chanjawa sosai cikina ya girma kamar me.


Da kyar nake iya tafiya ynxu, zuwa ynxu kuwa Daddyn Azlan ya daga min kafa don bana iya masa komai a shinfida da kyar nake yiwa kaina wasu abubuwan ma.


Yakumbo ce ta dawo guna ta zauna duk da iya nanan amma sai Azlan ya bukacu yakumbon tazo itama sbd baya son naje gida wanka.


Yau tunda na tashi nake jina wani iri dauriya kawai nake, zama nai a hankali akan kujera ina mike kafafuna.


Kallona yakumbo tai dake cin pepper chicken tace "sannu uwar biyu, jikin ne koh".


Murmushi nai kawai nace "uhm yakumbo ni baxan yi magana ba".


Dariya tai tace "sannu kinji Allah dai ya raba lafia".


A hankali nace "Ameen Yakumbo"


Shigowa yai sanye da jallabiya a jikin sa sai kamshi yake, Zama yai ya kalli Yakumbo yace "uwar gida na barka da dare".


Murmushi tai tace "barka kadai angona, ya gurin aikin?"


"Alhamdulillah Yakumbo ya zaman waje daya".


"Mun gode Allah" daukar plate dinta tai ta nufi daki tace "bara na baku guri nasan gunta kazo kar kace na takura muku"


Dariya yai yace "Allah ya kara lafia Yakumbo".


Kallona yai ganin yadda nayi wani irin ina yamutsa fuska yace "Mene Queen, baki jin dadi ne".


Dan murmushi nai nace "Alhamdulillah baby"


Riko min hannu yai yace "kina lafia dai koh, duk naga kinyi wani iri ne".


Girgiza masa kai nai nace "Alhamdulillah kawai dai mara tace take min ciwo kadan kadan".


Rudewa yai ya shiga cemin ko zamu tafi asibiti, da kyar na lallabasa akan ciwon bai tsanan taba sannan ya kyale ni.


Cikin dare ciwon yai tsanani muka tafi asibiti nida Shi da Yakumbo, muna zuwa suka shiga dani labour room kasancewar haihuwar ce tazo gadan gadan da alama ta dade tana labour a tsai tsaye.


Bamu yi hour daya da zuwa ba na sauka lafia, na haifo yarana guda biyu mace dana miji masu tsananin kama da Mimi.


Sai da Nurse din suka gyara mu nida su sannan ta miko min namijin tace "gashi karba shine Hassan din".


Murmushi nai na sa hannu na karbe sa ina kallon sa, rungume sa nai hawaye yana xubo min a Kan fuskata.














09066728387








Comments Nd share plz












Mrs A.M🥰


♠️♠️♠️♠️♠️


*TASWIRAR KADDARA*


♠️♠️♠️♠️♠️




Written by
Mrs A.M🥰


Page 47


Dedicated to My Fans🥰💓


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃




*Mrs Dnah perfumes nd more*


*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*


*Muna Saida*


*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.




*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*




*Phone number*
+234 702 577 7778


Location kano


🔚🔚🔚🔚🔚




Kiss na masa a goshi a hankali nace "Allah yayi ma rayuwar ku albarka".


A tsaya na gansa a kofar labour room din, muna fito wa ya karaso da sauri ya rungume ni, murmushi nai nace "ungo toh"


Saki na yai yana kallon babyn da nake mika masa, hannu yasa ya karba yana fadin "masha Allah"


Dariya nai masa kawai, Mika ma yakumbo macen nurse din tai tace "muje dakin da zata zauna toh".


Muna shiga na kwanta a Kan gado ina fadin Alhamdulillah, nan da nan bacci ya dauke ni.


Shi kuwa shida Yakumbo basu iya bacci ba a daren sai kallon babies din suke suna magana kasa kasa, a daren ya musu huduba.


Washe gari da Asuba ya dannawa Baffa Kira, daga wa Baffa yai yace "lafia zaki irin wannan Kira haka da asuba".


Dariya yai yace "alkhairi ne tsoho, Queen ta sauka lafia tun cikin dare an samu namiji da mace".


Kabbara Baffa yai yace "Allahu Akhbar, Masha Allah duk suna cikin lafia dai koh".


Murmushi yai yace "Alhamdulillah Baffa, duk lafia qalau suke, bacci ma suke gaba dayan su".


Daga nan ya Kira Mami da Umma ya fada musu, kafin 10 dakin ya cika da mutane sbd murna.


Nidai ina Kan gado na sake wanka ina sanye cikin doguwar riga nayi kyau sosai bama yadda na sace kamar na nice na kumbura ba da.


Ina zaune nida Asma'u muna magana kasa kasa Zeey ta shigo cikin shiga ta kamala hannun ta dauke da basket.


Gaisawa sukai dasu Umma da Mami ta nufo gun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login