Showing 51001 words to 54000 words out of 94393 words
Chapter 18 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt
hana amma baffa yace ai ya dauke ki matsayin jikar sa sunyi kyau koh haka su Bilkisu sukai ta Santi"
Murmushi nai zuciya ta cike da kaunar Baffa nace "Angode sosai, Umma a bawa Mimin mu gaisa."
Karba Mimi tai wacce dama tunda Umma ta fara waya taji an Kira sunan Maa dinta tayi tagumi tana kallon Umma, a shagwabe tace "Maaa"
Dariya nai nace "uhm Babyn Maa ya kk, kinyi bacci jiya?"
Daga kai tai tace "uhm Maa Umma tace kin koma gidan Daddy na da Zama wai Nima zan dawo gurin ku in banyi kuka ba, baxan yi kukan ba ai Maa"
Cike da tausayin ta nace "kar ki damu kinji Mimi na kin kusa dawowa gurina muyi ta wasan mu tare"
A darare tace "hadda daddy zamu dinga wasan?"
Hadiyar yawu nai nace "uhm hadda Shi"
Dariya tai, mun dade muna hira ina biyewa shirmen ta kafin na katse wayar, Abba na Kira shima na gaishe sa ya Kara min nasiha sosai sannan na dannawa Aisha kira.
Tana dagawa ta fashe da kuka, haba na rike nace "mun shiga uku lafia ke daga kira sai kuka"
Kara sautin kukan ta tai tace "Ya batul Ya Yusuf mugune wallahi"
Dariya na fashe da shi ina fadin "subhanallah, Aisha lafia meye na muguntar ina ke kike murna za'a miki aure kiji abinda ake ji toh meye na kuka"
Gyada kai tai tana share hawayen ta tace "bkm wallahi ta batul don na fada Miki abinda yake damuna shine zaki dinga min", ta karashe tana kara fashewa da kuka
Dariyar dake son kwace min nayi kokarin controling nace "kiyi hakuri toh Aisha kin shiga cikin ruwan zafi"
Daga kai tai tace "ya sakani amma ban Kara shiga ba ya fita ya siyo min magani"
Murmushi nai nace "kiyi hakuri kinji ki Zama mai dauriya banda ragwanta ynxu kafin ya dawo ki kara shiga ruwan xafin, ko zaki ji zafi ki daure"
Daga mun kai tai sai kuma tace "Ya Batul kece fa uwar gida kar ki barwa amarya kwanan ki wallahi don yadda naji muryar ki kamar ba'a gunki Daddyn Mimi ya kwana ba"
Hade rai nai a raina ina fadin yazo yamin ne amma sai nace "mata je kiyi abinda na fada Miki kin tsaya surutu"
Dariya ta kwalkwale dashi tace "Allah ya kaimu lokacin ki kema ya Batul muga ya zakiyi," da sauri ta kashe wayar tana dariya don tasan tsaf Zan iya zaginta..
Bin wayar nai da kallo nayi kwafa ina fadin "kin shiga gonar manya dole ki raina ni"
***********
Zeey dake zaune a Palourn ta tana sanye da kayan baccin ta ko wanka batai ba ga yawun bacci nan a fuskar ta kiran Mummy take amma bata daga ba.
Tana ajiye wayar Mummy na biyo bayan Kiran, da sauri ta dauka ta fashe da kuka, dafe kai Mummy tai tace "lafia Mene kuma"
Cikin kuka tace Mummy bai shigo bafa jiya har 3 ina zaune a Palour ina jiran shigowar sa amma ko knocking door banji anyi na, nasan yana can gurin waccen mamar shegiar yar tasa
Tsaki Mummy tai tace "ke kam kamar mai brain dn kifi ya kamata ace ynxu kinsan waye Azlan, in har Azlan din dana sani ne bazai shiga part din wannan shegiar ba, ni ba wannan bama wai ashe Baffa tare ya muku set din kujerun nan?"
Cikin Mamaki Zeey dake share hawayen ta tace "wani set din Mummy kar kice min na palour na"
Tsaki Mummy tai tace "komai har gadon, na dauka ke da Azlan din kawai yayi ma Ashe wai hadda ita banbancin colour ne da naki kawai nata golden, naki silver mama tace min nata ma yafi kyau kuma nata colour daya ne dana Azlan"
Kuka Zeey ta kara fashe wa dashi tace "Mummy mai yasa baffa yake min haka wai kamar baya sona wallahi Mummy, ni ji nake ma kamar yafi son wannan shegiar"
Ajiyar zuciya mummy ta sauke tace "ki kwantar da hankalin ki zan aiko Miki da wani turare, duk lokacin da kika zan zaki hadu da Azlan ki dinga shafawa xaki mallake zuciyar sa sosai zai ma manta da waccan yar iskar"
Murmushi tai tace"yauwa Mummy na, ina sonki"
**********
Ina zaune na kunna kayan kallo naji ana bude wata kofa da dazu na gwada budewa naji a rufe, da sauri na maida hankalina kan kofar ina mamakin taya za'a bude kofar ko wani ya kwana a gidan ne.
A hankali ya shigo yana lumshe idonsa Jin wani sassanyan kamshi dake tashi a Palourn, da sauri na mike tsaye tun daga kasa nake kallon sa yana sanye da kananun kaya as usual sai bada wani fitinannan kamshi yake.
Idonsa daya sha kwalli yake kankance yana kallon ta ba abinda yafi daukar hankalin sa sai hips dinta da suka fito sosai da kuma kirjin ta Wanda yai kamar balloon aka hura, tabe bakinsa yai yana lasar lips dinsa.
Ni kuwa da sauri na shiga rufe kirjina da hannuna, kallon abinda take yai ya saki wani murmushi cike da shakiyanci yake takowa har ya iso inda take a tsakiyar palourn, tunda ga Sama har kasa yake sake kallon ta dan yatsina fuska yai yace "me kike yi anan"
Da sauri na dago na kalle sa sai dai kwallin dake idon sa yasa ni dauke kaina, bana son ganin sa da wannan kwallin, hade rai nai cikin rainin hankali kamar yadda yamin magana nace "kai Zan tambaya mai kake min a gida"
Zaro manyan idonsa yai ya zura hannayen sa a aljihun wandon sa yace "A'a lallai mai gida"
Juyar da kaina gefe nai duk a takure nake jina sbd rashin mayafi a gabansa, tabe baki yai yace "sai kawai ga Mr Wicked ya zama mijin ki"
Da sauri na kallesa, dage min gira yai yace "Uhmm ko dayake dole akai miki kamar yadda aka min koh"
Harara na watsa masa nace"Ashe madai kasan dole akai min.. " kasa karasa wa nai ganin ya matso kusa dani har muna Jin numfashin juna, baya nai ina kallon sa.
Tabe baki yai yana hade rai yace "ki kiyaye ni bana daukar raini, in kika ce zaki raina ni karya ki Zan" ya karashe yana zare min idon sa kamar Yana ma yaro warning
Nima zaro idona nai nace *kai ma Kar raina ni don Ka ganni karama Allah"
Yunkurawa yai da karfi kamar zai kamo ni, da sauri na kwashi gudu zuwa bedroom dina ina fadin "wayyooo Allah Ummana"
Murmushi yai yana shafa gemun sa, juya wa yai ya koma ta kofar daya shigo, kofofin a Palourn sa suke daya zata Kaisa cikin palourn Batul ba tare daya fita kofar compound ba dayar kuma palourn Zeey zata Kaisa.
Ta palour Zeey din ya shiga a hankali yake bin palourn da kallo tana kwance akan kujera tana chatting ga robar lemo nan ta yar akan carpet tayi nisa da chatting din ko shigowar sa bata ji ba.
Gyaran murya yai da sauri ta mike tsaye, Dan kallon sa tai wani kaunar shi yana sake ratsa ta, hade rai yai yace "meye haka baki wanka ba?"
A dan darare tace "ynxu nake son naje nayi Yaya yunwa nake ji shine nasha lemo"
Tabe baki yai yace "baxa ki iya girki ba ko ba kayan abinci ne?"
Cikin rawar murya tace "da akwai yaya"
Gyada kai yai ya kalli agogon hannun sa yace "ba abinda kike bukata Zan fita"
Kamar zata yi kuka tace "Yaya jiya baka shigo ba kuma ko kazar amare baka siyo min ba"
Zare ido yai yace "Zainabu yaushe kika koma mayya, kaza ce baki taba Ciba da dole sai na siyo miki"
Fashewa tai da kukan bakin ciki wai zainabu, hada Azlan ya rike yace "Zainabu mai ya faru zaki sa kuka duk sbd kazar ce"
Girgiza kai tai tace "Yaya don Allah Ka daina cemin Zainabu ynxu in kishiya ta taji ai sai ta raina ni"
Dan hade rai yace "toh in ba Zainabu ba Abu kike son na dinga cewa"
Girgiza kai tai tace "Yaya toh Ka dinga cemin Zeey don Allah"
Daga kai yai yace "Shi zeey din haka dama aka rada miki ban sani ba Zainabu"
Girgiza kai kawai tai tana share hawayen ta iyea wallahi ta manta ma Zainabu Azlan yake ce Mata sbd ta dade bata ji ya ambaci sunan taba
Ganin tayi Shiru yace "na fita sau anjima"
Bin sa da kallo tai har ya fita, fashewa da kuka tai ta dauki wayar ta ta dannawa aminiyar ta Malika waya don fada mata halin data ke ciki daga kaita gidan miji..
*******
Kallon Azlan Baffa yai yace "ango mijin Mata biyu, ya Ka baro min jikokin nawa"
Shiru ya masa yana shan kankanar sa, ganin yayi shiru yasa Baffa cewa wai tsoho baxa Ka daina sa wannan shegen kwallin ba naga ynxu kayi aure wane farin jini kuma kake bukata.
Kallon Baffa yai kamar baxai magana ba sai kuma yace Baffa ai duk matan da kuka aura min na zabi na bane ynxu Nima zan nemo zabina nayi ta uku da ita.....
Hangame baki Baffa yai yana kallon sa yace...
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[07/09, 21:29] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 28
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Hangame baki Baffa yai yana kallon sa yace "ynxu mata biyu gare kafa Zaki sai Ka Kara ta uku"
Cikin tabbatar wa yace "sosai ma kuwa Baffa ai tunda kuka fara min da biyu naji dadin haka nace toh cikashe biyun kawai zanyi nayi hudu, kaga in na tashi sai na samo guda biyu a Kara aura min su rana daya"
Kama baki Baffa yai yace "zaki Ka kuwa san mai kake fada, rike mata hudu ba abu bane na rago bane bafa"
Kankance idonsa yai yace "tsoho da kuka aura min Mata biyu baku tambaye ni ko zan iya Kula dasu ko baxan iya ba, sannan ai kaga ba laifi bane in na karo hudu ko baxan iya daukar nauyin su ba bani da fargaba tunda ina dakai"
A mamakance Baffa yace "ban gane tunda kana dani ba mai zan ma?"
Wani killer smile ya saki yace "sai Ka hado min magungunan gargajiya Wanda zai Kara min kuzari da karfi irin Wanda kuke sha a zamanin ku kaga ne ai".
Dakuwa Baffa yai masa yace "ungo nan zaki"
Dariya sosai Azlan ya saki yana lumshe idonsa, da sauri ya bude idona sbd hoton Batul dake masa yawo a kansa.
Cikin nutsuwa baffa yace "zaki Ka Kula da amanar yaran nn don Allah, ynxu nauyin su ya dawo kanka cinsu shansu suturar su lafiyar su Ka Kula don Allah sannan kayi kokarin yin adalci a tsakanin su, nasan baka da mugunta kuma kana da fahimta don Allah ka Kula"
Dan murmushi yai yace "insha Allah Baffa"
Ganin da Baffa yai ya nutsu yasa shi cigaba da masa nasiha....
***********
Fitowa nai daga daki ina sanye da hijab din danai sallah, karar door bell ce kawai ke tashi a Palourn tun dazu ake dannawa kuma ina sallah.
Bude kofar nai ina dan matsawa baya yadda zan bawa wanda suka zo damar shigowa, yan mata ne su biyu suka shigo za muyi sa'anni da su.
Zama sukai a kujera nima duk da ban san su amma sai na saki fuska don nasan baxai wuce yan uwan sa bane, kitchen na shiga na kawo musu ruwa da lemo, Zama nai nace "sannun ku da zuwa"
Cikin fara'a suka gaishe ni, ajiyar zuciya na sauke a raina nace suna da kirki ashe, amsa musu nai nima fuskata a sake.
Mufeeda ce tace "sunana Mufeeda, nice autar su Ya Azlan kuma nice kadai mace" ta kada tana murmushi.
Dan ware idona nai nace "ke kadai ce mace baki da sister?"
Dariya tai tace "babu sai Aunty Samira matar Ya Junaid ynxu ma gaki nn kin zama sister na"
Dariya nai nace "insha Allah"
Nuna ta gefen ta tai tace "wannan Zahra ce dyar Uncle M kanin Abie"
Murmushi nai nace "Ashe namesake ce"
Dariya zahra tai tace "eh amma ni zahra ake cemin"
Murmushi nai nace "ni kuma Batul"
Mufeeda ce tace "amma Aunty Batul kamar na taba ganin ki a BUK"
Dan Murmushi nai nace "ina karatu can ai"
Zahra ce tace "laaaa Aunty Batul kema acan kike muma nida Mufeeda acan muke, muna karanta micro biology level 1 muke"
Cikin Jin dadin hirar da muke nace"nima level 1 nake ina karanta Architecture"
Zaro ido sukai suka kalli juna sai suka sa dariya, cikin dariya Mufeeda tace "Aunty Batul Ya Azlan yana lecturing dinku knn?"
Tuno Shi da nai sai nadan hade rai nace "uhm yana mana"
Mufeeda ce tace "tab kuma wai kuna ganewa?"
Da mamaki nace "mai meyasa baza mu gane ba, sosai ma in Ka mayar da hankali zaka gane in kuma Ka tsaya Wasa ba abinda zaka fahimta, Amma Mai yasa kika tambaye ni"
Gyada kai tai tace "ai kowa yasan Ya Azlan baya son yana koyawa mutum karatu, haushi yake ji sosai shiyasa nake taso na samu daya daga cikin students dinsa na tambaye su wai suna ganewa"
Dariya nai nace"ai kuwa sai na fada masa"
Xaro ido tai tace "don Allah kiyi hakuri wasa nake yi"
Dariya kawai na Mata nace "Nima wasa nake miki"
Basket din dake gefenta tace "Mun manta zeey mun tsaya hira, Aunty Batul ga abinci inji Mami tace a kawo muku"
Mikewa nai na karbi Basket din nace "angode sosai kuwa, mu biyu ne?
Girgiza min kai Mufeeda tai tace "A'a Banda Ya Zeey itama mun kai mata"
Murmushi nai nace "angode," kitchen na nufa ina maimaita sunan Zeey knn Zainab sunan kishiyar tawa, tabe baki kawai nai.
Bayan na dawo daga kitchen din na karbi numbern Mami da Mama da Abie da Baffa, sai Aunty Sarah maman Zahra, a gurin na kira Mami cikin mutuntawa muka gaisa sai sunkuyar da kai nake don haka kurn naji wani irin kunyar ta ta rufe ni, a nan take fada min za'a kawo min Mai aiki wacce zata dinga taya ni aiki.
Godia nai Mata sannan mukai sallama, mun sha hira sosai tare muka ci abincin da Mami ta kawo, sai wajen 6 suka tashi tafiya.
Kitchen na shiga na wanke flask din Mami, kai wa palour nai na ajiye daki na shiga na dauki pose dita 2k na dauka a ciki sannan na sa musu turare a ciki.
Fitowa nai na mika musu, godia suka min sosai
Zahra ce ta kalli Mufeeda tace "zamu shiga gurin Ya Zeey ne muyi mata sallama"
Tabe baki Mufeeda tai tace "wallahi ba inda zani, kyaleta taji da wulakancin ta"
Nidai ban tanka musu ba har na rakasu, daga kofar palour na rakasu ban fita ba.
Bayan tafiyar su duk sai naji ni wani iri, Zama nai na kunna zee world don an saita komai, ina son kallon india amma a gida kuma bana kalla don Umma bata bari kasancewa in har zamuyi kallo tare muke kalla gaba daya har dasu Kamal.
Bayan Isha'i ragowar abincin da mami ta kawo naci na wanke kayan dana bata, wanka nai nasa doguwar rigar bacci iya gwiwa, humra na shafa na fesa turare Mai sassanyan kamshi, hula na dora akaina na fito Palour hannuna rike da wayata..
Turus naja na tsaya ganin sa tsaye sanye da jallabiya mai gajeran hannu yayi kyau sosai kuma fuskar sa tayi fresh alamun daga wanka ya fito
Diricewa nai sai janyo rigata nake ina rufe kafata duk da ba abinda take rufewar, ga kuma gaban rigar Kai v.
Murmushi Azlan yai yana shafa gemun sa sai kallon ta yake.
Turo baki nai cikin tsiwa nace "ni Ka daina kallona"
Shafa kirjin sa yai yace "ki same ni ynxu a part dina, ta kofar nn zaki shigo"
Zaro ido nai nace "Mai zan yima?"
Kankance idonsa yai yace "mai mata take yiwa miji a irin wannan lokacin?"
Gaba nane ya buga da karfi amma na kasa magana.
Juyawa yai yace "kizo ynxun nan bana son maimaita magana"
Bin bayansa da ido nai har ya fita, kamar kar na je sai dai kuma ina tunanin illar hakan.
Cikin sanyin jiki na koma daki hijab dina nasa sai na samu kaina da sake fesa turare, a hankali na nufi kofar dayake shigowa na murda na shiga palourn..
*ASSALAMU ALAIKUM*
Banso yin magana ba amma a gaskia raina ya baci, in mutum baiyi typing ba sai a dinga fada masa maganganu mara sa dadi, ku sani fa shima writer din mutum ne kamar ku wata tana da aure da yara wata tana gaban iyayen ta, dole tana da aiyukan da zata dinga yi bawai zaman banxa take ba da take da lokaci ko yaushe tana free da zata dinga typing.
Ya kamata ku na yiwa writer uzuri sannan masu yimin magana kamar suna bani Umarni akan mai yasa banyi typing ba su dinga turo min emoji na yatsine duk na gode, shifa rubuta bawai anayi ne na 15 to 30 minutes ba angama magana ce ta hours kana zaune kana typing ga ciwon hannu ga na ido duk haka kake hakuri don kawai mu faranta muku rai, a dinga yimana uzuri plz..
Ngd da fahimta🤝
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[08/09, 16:14] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 29
Dedicated to Adorable Hausa Novel🥰 Uncle Azlan yana gaishe ku kuma yace a fada maku ku sa date zai zo ya raka ku gurin da yake siyo kwalli🫣
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Kamshin freshner ne ya doki hanci na, lumshe ido nai na shiga bin palourn da kallo yaji furnitures masu kyau da tsada, ajiyar zuciya na sauke na samu guri na zauna aka kujera a darare.
Zainab na zaune sanye da rigar bacci iya gwiwa