Showing 81001 words to 84000 words out of 94393 words
Chapter 28 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt
zargin ta akai ba amma yayi mirsisi ya dinga shuka mata rashin mutunci.
Kamar Wanda aka tsikara a zabura ya mike ya nufi part dinta, a zaune take tana sanye da free doguwar riga shinkafa da wake take ci a cikin tray na zabga yaji tana ci tana kallon Indian hausa.
Zubewa yai a gabanta kansa a kasa, a dan tsorace na kalle sa nace "lafia"
Dora kansa yai akan cinya ta kawai ya fashe da kuka........
Team Batul kuna inaaa💃💃💃💃💃💃
Shin wani mataki kuke tunanin Azlan zai dauka akan Zeey?
Batul zata yafewa Azlan kuwa?
Tukunna ma waye yake zagaya wa gurin karuwa?
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[26/09, 16:53] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 41
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Tsoro ne ya kamani ganin yadda yake kukan kamar yaro, hannuna na dora akan sa nace "lafia"
Dagowa yai ya zuba min idonsa da har lokacin hawaye suke zubuwa, hannuna ya rike sosai yace "Ban san ta inda zan fara baki hakuri ba Baby"
Hade rai nai nace "waye kuma baby"
Girgiza kan sa yai yace "don Allah ba dan niba kiyi hakuri ki yafe min, na san bai kamata ki yafe min ba sbd na miki laifi babba amma ki duba"
Kallon sa kawai nake a kaikaice nace zlaifin me kamin ni kuma batul da har kake son na yafe ma".
Shiru yai yana kallona ganin naki dauke idona a kansa yasa shi fadin "na zarge ki akan laifin da ba ke kika aikata ba, Zeey ce ta hada komai wallahi kiyi hakuri ynxu naji suna maganar ita da kawar ta, ki yafe min na bata miki rai sosai".
Mikewa nai tsam na dauki tray din abinci na, kallon sa nai nace "ai ni baka min komai ba duk abinda kamin gani kai na cancan ci kamin shine". Daga haka na wuce dakina, ina shiga na rufe kofar da key.
Lumshe idona nai nace "Alhamdulillah ya Allah"
Wayata na ciro daga aljihun rigata na Kira Aunty Bilkisu bata dade ba tana ringing ta dauka.
A nutse nace "Ina wuni Aunty Bilkisu"
Murmushi tai daga can bangaren tace "lafia qalau Maman Mimi y kuke?"
Yar dariya nai nace "Alhamdulillah yasu Nana, ina gaishe su sosai".
"Zasu ji insha Allah"
Dan shiru nai Kan nace "Aunty kinsan me?, ynxu Daddyn Mimi yazo yana kuka wai na yafe masa"
Da sauri Aunty Bilkisu ta mike daga kwancen da take tace "me kika ce masa kuma"
Turo baki nai nace "nuna masa nai ni ban san wani abu daya min ba kawai na tashi ta shige daki"
Dariya tai tace "da kyau ynxu so nake ki nuna masa darajar ki kafin ki nuna masa kin yafe masa, kar ki sauko da wuri ki dan basa wahala kinji koh".
Dariya nai nace "toh insha Allah Aunty Bilkisu".
Mun jima muna wayar tana Kara koya min dabarun jan hankalin sa da yadda zan dinga kunnasa ina masa kwalele.
A Palour kuwa da mamaki Azlan ya bi bayanta da kallo ajiyar zuciya ya sauke ynxu kuwa ya tabbatar yana ruwa don bai ga alamun sassauci ba a gun Batul.
Lumshe idonsa yai yana fito da wayar sa daga aljihun sa, sunan Baffa ya gani kamar kar ya dauka sai kuma ya daga yana sa wayar a kunnen sa.
Cikin dakewar murya da bada umarni Baffa yace "duk inda kake kazo ynxu ina neman Ka".
Cire wayar yai daga kunnen sa Yana jan gajeran tsaki shifa sam bai shirya fita ynxu ba amma ba yadda ya iya dole ya fita sbd cika umarnin Baffa.
Part dinsa yaje ya dauko car key dinsa ya fita.
Yana zuwa gidan Baffan rufe motar yai ya shiga palourn, turus yai ganin Zeey a kasa tana kuka Mummy na Sama akan kujera sai cika take tana batsewa sai kuma Abie da Baffa.
Hade rai yai sosai ya shiga ciki, a gefen baffa ya zauna yace "ina wuni"
Ba tare da Baffa ya amsa masa ba yace "me ya sa Ka kori matar Ka daga gidanta har kana cewa in ta kara 5 minutes a bakin auren ta"
Sunkuyar da kansa yai don baya son magana ma kwata kwata ransa ba karamin baci yai ba da ya ganta anan wato ita karamar yar iska koh ai kuwa zai nuna mata shifa Azlan ya fita iya shegantaka.
Tsawa Abie ya daka masa yace "ba magana ake ma ba kayi wa mutane banza sbd ga sa'annin ka koh".
Dagowa yai ya kalli Zainab cikin dacin murya yace "ki fada musu abinda kika aikata da Wanda kika sani nake aikata"
A tsorace ta dago ta kalle sa tace "uhm Mene"
Hade rai yai yana jifan ta da wani mugun kallo yace "kin san Allah in har baki fada musu abinda kika aikata ba a nan gurin zan warware dukkan igiyar auren mu, don dama na gaji da ke".
A tsawace Baffa yace "kana da hankali wai zaki kasan mai kake cewa kuwa"
Ba tare da ya bawa Baffa ansa ba yace "zaki fada ko kuma na sallame ki".
Da sauri tace "kayi hakuri Zan fada" tiryan tiryan ta fada musu dukkan abinda ta aikata tun daga maganin mallakar data ke zuba masa har zuwa samun cikin da yadda ta dinga karya sbd yana spending tym tare da ita ranar girkin Batul da kuma zubar da cikin da tai.
Cikin kuka tace "kayi hakuri sharrin shaidan ne"
Kifa mata mari Mummy tai tace "amma kin bani kunya Zeey, duk irin fadan da nai miki ashe baki ji ba ynxu sbd hauka har zubar da ciki kikai kina da hankali kuwa".
Shiru Baffa yai yace "kayi hakuri kaji Ka dau matar ka ku tafi"
Kallon Baffa yai yace "sai dai kuyi hakuri baxan iya zama da itaba gaskia, dama can din dauriya nake kawai bata gyara min part dina bata min abinci mai dadi da alama masu aiki take bawa suke min kuma ni kawai na gaji nefa".
Kallon Mummy Baffa yai yace "ku tashi ku tafi zamu yi magana da shi"
Rarrafowa gun kafarsa Zeey tai cikin kuka tace "Yaya don Allah kayi hakuri wallahi sharrin shaidan ne ina son ka yaya baxan iya rayuwa ba tare da kai ba".
Dauke kansa yai kamar bai san mai take cewa ba don shifa ko kallon ta baya son yi, fizgo ta Mummy tai suka fita sai Kiran sunan sa suke.
Suna fita Azlan ya dago ya kalli Baffa kamar zai fashe da kuka yace "Baffa don Allah kazo muje Ka tayani bawa Batul hakuri, nayi mata laifi sosai har kauracewa ganin ta nai na wajen 3 weeks kuma nace kar ta sake tazo shinfida ta, nidai ynxu ban san me zanyi ba".
Kallon sa Baffa yai yace "Ashe baka da hankali Zaki ina ganin Ka kamar kasan mai kake yi ashe baka da tunani ynxu ko da gaske ne abinda Ka zargeta sai ka hana ta ganin Ka, kuma kace ta daina zuwa shinfidar ka kar Ka manta hakkin ta yana kanka Ka Kula da cinta lafiyar ta, toh nidai ba ruwana kaje Ka same ta da kanka".
Marairaice wa yai yace "kayi hakuri Baffa nasan nayi laifi kuma ina gane gaskia gurin ta naje amma sai ta nuna min ita bata son abinda nake nufi ba, ni tsoro ma take bani ynxu duk ta daina damuwa dani".
Tagumi Baffa ya cire yace "toh meye zata damu dakai bayan kaima baka damu da itaba"
Girgiza kai yai yace "Baffa nifa Karya nake mata ma dana ce mata bana sonta, amma itama kawai sai cemin tai ai bata sona itama haba Baffa tamin adalci knn".
Tabe baki Baffa yai yace "kaima kai mata adalci dakace mata baka sonta"
Da sauri yace "nidin banxa ai ban isaba Baffa kawai dai fada nai fa don ta ji haushi"
Ajiyar zuciya Abie yai yace "kayi laifi sosai kuma tun a lokacin sai da nace ma Ka nutsu Ka kara bincike ba lallai abinda Ka gani iyakar gaskiar knn ba".
Marairaice wa yayi yace "Abie na gane kuskure na nidai ku tayani bata hakuri nasan zata hakura".
Kallon sa Baffa yai yace "ba ruwan mu kai da Ka bata Mata rai kai ne zaka lallaba ta ba ruwanmu atoh".
Kifa kansa yai akan kujera yana fadin "Innanillahi wa innanillaihir raji'un "
*********
Cikin nutsuwar sa yace "Mami goben insha Allah zan tafi, munyi magana da doctor din yace ana saran komai yayi daidai insha Allah"
Cikin tausayin sa tace "Allah yasa Junaid, insha Allah muna sa ran wannan karan komai ya tafi lafia"
Murmushi yai kansa a kasa yace "Samira tace nan zato zo wannan karan."
Murmushi Mami tai tace "masha Allah, Allah ya kawo ta lafia ai baxa ka dade ba ko"
Daga kai yai yace "2 to 3 weeks ne in na gama da wuri ma kafin nan Zan dawo".
Sosai ta masa addu'a Kan ya mike ya Mata sallama akan sai goben insha Allah da wuri zai kawo ta tunda flight din safe yake da.
Lokacin daya isa gida a daki ya samu Samira tana hada kayanta, rungume ta yai cike da kaunar ta yace "zanyi missing dinki Hubby, da kin amince ai tare zamu tafi kinsan dai yadda zanyi kewar kiko"
Juyowa tai tana dariya tace "A'a Hub basai na raka ka ba ai kamar yaune zaka dawo Insha Allah, muna fatan a dace kawai".
Shiru yai ya zauna a gefen gadon ta fuskar sa cike da alhini yace "ynxu in naje ba'a dace bafa"
Da sauri ta dora hannun ta akan lips dinsa tace "plz Ka daina irin wannan maganar, Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi kawai"
Janyo ta yai yace "Ameen Matata"
********
Ni yau yinin farin ciki nai sai cika cikina nake da abinci hankalina kwance, wajen 11 ina zaune akan carpet plate din Dan wake a gabana ina ci ina kallo ya shigo sanye da jallabiya.
Bin ta da kallo yai yana hadiyar yawu ta masa kyau sosai kuma ta ciko duk da dama can ita a cike take sai dai ynxu ta kara cika sosai sai glowing take, Zama yai a gabanta yana kallon tray din data cika sa da dan wake.
Da mamaki ya kalle ta yace "ynxu duk wannan zaki cinye ke kadai kuma da tsohon Daren nan"
A gajarce nace "uhm"
Zama yai yana kallona yace "inci nima don Allah"
Ba tare dana kalle saba nace "taya zakaci Ka sani ko na zuba wani abun da zai iya cutar da kai".
Jikin sane yai sanyi shifa sai ynxu yake tuna wasu maganganun da ya fada mata, a hankali yace "kiyi hakuri Baby sharrin shaidan ne".
Murmushi nai nace "ba sai Ka bani hakuri ba ni wace da zaka bawa hakuri, ai kar Ka damu kawai duk hakkin ka kana sauke wa kaga ba dole sai Ka rarrashi wacce ba digon sonta a zuciyar kaba.."
Kafin ta karasa yayi saurin cewa "I love you Batul"
Da sauri na dago na kalle sa, zuba min ido yai yace "ina son ki Batul ban taba son wata mace ba sai akan ki ina kaunar ki wallahi, duk abinda na fada waccan karan bacin raine ya jawo".
Girgiza kai nai nace "kana tunanin Zan yadda ne, ai ko yadda ya zarge ni ya isa mun shaida cewa baka sona kuma baka taba sona ba".
Hannuna da yake rike da wayata ya rike yace "wallahi tun ranar dana fara ganin ki a titi na kamu da sonki, a lokacin kusan kullum sai nazo daidai titin nayi ta neman ki ko Allah zai sa na ganki amma ban ganki ba kawai sai gaki a school na hadu dake kuma kina course din da ni zan ke daukar ku, sbd ke nake cigaba da lecturing university din kawai sbd kar na ajiye na daina ganin ki bawai din ina son lecturing din ba, ki yadda dani ina son ki Batul".
Zare hannuna daga jikin nasa nai nace "ngd toh da son da kake min".
Sororo ya tsaya yana kallona yace "baki ce kina sona ba ni?"
Ba tare da na kalle saba nace "bana son yin karya akan abinda ba haka ba".
Daukar abinci na nai na dau wayata na shige daki, a sanyaye ya mike ya shiga kitchen dinta samun abinci yai a fridge yayi microwaving yaci sannan ya koma part dinsa cike da dana sanin abinda ya aikata.
Washe gari da wuri na tashi don ranar zamuyi resuming school, tsayawa nai agaban Mirrow na sauke towel din jikina ina kallon yadda gaba daya na chanja, zubawa cikina ido nai ganin ya dan dago kamar ya kumbura hannu na dora akai ina matswa Jin tauri tauri.
Nifa gani nake ba lau ba don kusan sati knn dana ke jin cikin yana motsi bama in na kwanta bacci, sosai kuma nake Jin motsin da sauri na dora hannuna akai jin yadda cikin nawa yake motsin ynxu ma, na dade ina kallo kafin na shirya ganin ina batawa kaina lokaci.
Bashir ne ya kaini Wanda dama munyi waya dashi tun jiya na fada masa yau zanyi resuming school.
A hall na samu Asma'u tazo tana dauke da danta Areef, rungume ta nai cike da farin ciki nace "Mum Areef sannu da zuwa".
Dariya tai tana miko min Areef din tace "Ke me kika ci ne haka da hutun nan kinyi fresh kinyi kiba tubarkalla kodai kodai ne uhm".
Hararar ta nai nace "kodai kodai me?"
Dariya tai muna zama tace "ki fada min gaskia kodai kanwa ko kani za'a yiwa Mimi da Areef ne"
Girgiza kai nai nace "kina da damuwa amma, ni dinnan bani da wani ciki"
Lecturer ne ya shigo yasa muka maida hankali, karfe 10 ya fita Sir Azlan ya shigo, tunda ya shigo ban yadda mun hada Ido na kaina yana kasa ina jotting abin da yake fada, sa da ya gama ya tak cikin takun sa na jarumta, a kaina ya tsaya cike da kulawa ya miko min hannu yace "Baby zo muje office dina kinji"
Dagowa nai na kalle sa na juya na kalli hall din ganin mu ake kalla yasa na basa hannuna kar ya yarfa sa a gaban students dinsa jakata ya daukar min Yana rike da hannu na har muka fita.
Muna fita na cire hannuna nace "meye haka fisabilliahi zaka dinga min irin wannan abin a class"
Marairaice fuska yai yace "baby kiyi hakuri kinji ki yafe min, nayi kuskure baxan sake ba".
Dauke kaina nai nace "wai ni wani laifi kamun ne da kake ta cewa nayi hakuri baxa Ka sake ba"
Kamo hannayena yai yace "ki daina fadin haka nasan na bata miki rai kiyi hakuri duk hukuncin da zaki min zan yadda amma banda wannan sharenin plz"
Tabe baki nai nace "Ka sake ni zanje cafeteria naci abinci yunwa nake ji"
Da sauri yace "muje toh kinji ki siyo sai kici a office dina bana son kici a gun mutane"
Shiru nai ina tunani nifa ynxu bana fushi da abinci kai na gyada masa nace "muje toh"
Zabar abubuwa da yawa nai shidai nasa biya don yasan ba iya cinyewa xanyi ba, ko shawarma guda biyu na karba kuma manya ga take away na fried rice biyu sai take away din meat pie da samosa da kuma wainar fulawa dana siya guda biyar.
Haka muka nufi office dinsa dauke da ledoji, muna shiga na karbi ledojin jikina har rawa yake min, zama nai akan kujera na cire hijab dina na ajiye a gefe abincin na fara ci kamar wacce bata ci komai ba tun jiya don yunwa.
Tagumi yai yana kallon ta yadda take cin abincin kamar wacce ta shekara bata Ciba, ga mamakin sa cikin abinda bai fi 20 minutes ba ta cinye dukkan abinda suka siyo, baisan lokacin daya mike ba yazo yana dudduba gefe gefen ta.
Kallon sa nai ina galla masa harara nace "lafia mai kake dubawa"
Da mamaki yace "wai da gaske kece kika cinye dukkan wannan abincin ynxu ynxu"
Hararar sa nai ina dauke kaina nace "nidai gaskia bana son sa ido gaskia, a bar mutum yaci abincin sa yadda yake so ai lafia CE"
Daga kai yai yace "amma ynxu dai kin koshi koh ke da abinci sai dare ko gobe koh"
Girgiza kai kawai nai na mike na shiga toilet na wanko hannuna, hijab dina na mayar nace "tnx sai anjima"
Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar ta yace "Alhamdulillah ai tunda ynxu na gane kina son abinci gashi har kin biyo ni office ynxu kam kullum sai na siyo miki kayan kwalam na kawo har ki sauko duka"
Domin magana da marubuciyar kai tsaye don bata shawara
09066728387
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[27/09, 20:02] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 42
Dedicated to Innar Nawaz🥰
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Lokacin dana tashi Bashir ne yazo ya dauke ni muka tafi, ina zuwa na sami Mimi itama an dawo da ita.
Da gudu ta taho ta rungume ni cikin murna, Nima hannu nasa na rungume ta nace "My lovely baby nayi missing dinki sosai".
Washe kananun hakoran ta tayi tace "Maa ynxu ba baby bace ni na girma I'm 5 yrs old fah".
Kumatun ta naja nace "ehe yaushe kika girman nidai har ynxu ke baby ce a guna".
Turo baki tai tace "toh ki siyo min baby mana sai ki daina cemin baby, nima na dinga wasa dasu".
Kama haba nai nace "har nawa kike so na siyo miki babyn"
Da sauri ta dale kafata tace "guda 10 nake so"
Dariya nayi kawai na tashi nace "sannun ki gaskia, kallon Iya nai dake zaune tana kallon mu sai murmushi take nace sannu iya, fatan abinci na