Showing 93001 words to 94393 words out of 94393 words

Chapter 32 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt

Advertisement

Mrs A.M   

03 Aug 2024

16981

nake, ajiye basket din tai a kasa tace "sannu Maa, ya jikin"


Murmushi nai nace "Alhamdulillah"


Gyada kai tai tace "Masha Allah bara na dauki yaran nawa"


Mika mata namijin Asma'u tai tace "ga Hassan din"


Karba tai tana zama tace "masha Allah Yana kama da Mimi sosai"


Dariya Asma'u tai tace"Ai dukan su suna kama sosai har macen"


Nidai banyi magana ba sai murmushi kawai da nake, bayan la'asar aka sallame mu muka koma gida tunda komai lafia.


Sosai mutane suke zuwa barka abin sai sam barka, kullum cikin baki muke har akai suna suka ci sunan Abie da Umma muna Kiran su Noor da Noora.


Yau satin su biyu kuma sai ynxu bakin suka dan soma janye kafa, ina zaune a daki ina bawa Noora Nono, Noor yana gun yakumbo a palour.


Shigowa yai bakinsa dauke da sallama, daga kai nai na kalle sa nace "sannu da zuwa Baby".


Murmushi yai yana Zama a gefena yace "yauwa Queen, nonona ake bata ne".


Dariya nai nace "uhm gashi nan kuwa, suna ta shanye ma Nono".


Langwabe kai yai yace *daina fada min haka kinji Matar wannan abin takaici yake bani sosai, ina gani suna Shan min nono ba yadda zanyi sauke ta kinji nima nadan sha ko kadan ne".


Dariya nai nace "ko kunya baka ji wai ynxu sai kasha kuma".


Kankance ido yai yace "ko zaki gwada ne uhm, da gaske nake ba abinda zai hanani Shan nono abuna"


Murmushi kawai nai ina cire Noora daga nonon, Mika masa ita nai nace "karbe ta na gyara rigata".


Mikewa nai na nufi mirror na fesa turare, duk na gaji har ynxu gajiyar bakin da muka dinga yi bata sake ni.


Kwanciya nai a Kan gado nace "sai da safe baby bacci nake ji"


Kiss ya min a goshi ya fita gurin yakumbo hannun sa rike da Noora.


Sai da mukai Arba'in sannan Yakumbo ta tafi bayan mun hada mata abubuwan arziki sosai, yawo Arba'in muka je cikin satin sosai amma fa ranar naci gidan mu a hannun Oga.


Cikin farin ciki nake Kula da yarana su uku, Alhamdulillah komai yana tafiyar mana yadda ya kamata cikin farin ciki, Mami ta Karo min mai aiki yarinya sbd Kula dasu Noor, tunda ynxu iya baza ta iya ba.


Suna da shekara daya na karamun ciki kamar xanyi kuka, amma haka ya rarrashe ni na yaye su aka mikawa Mami su yaye.




*********


Cikin shekara daya abubuwa da dama sun faru, Samira ta Kara aure ta auri wani tsohon saurayin ta da ya so ta kafin tai aure amma taki yadda sbd Junaid, yana jin an sake ta kuwa ya fito ya aure ta matsayin matar sa ta biyu ynzu haka cikine da ita karami.


Tana zaune lafia qalau ita da kishiyar ta don kamar yadda ta kasance bata da damuwa haka ma kishiyar tata take, shiyasa zaman su yake gwanin ban sha'awa.






********


Bangaren Junaid ya shiryu sosai, kuma bai Kara neman aure ba sai ynxu da yake son wata yarinya sbd hankalin ta daya yaba dashi.


Kullum cikin shigar mutunci take, salaha ga kunya ko zance yaje har suyi su gama bata daga kai ta kalle sa.


A haka akayi bikin su aka kai masa amaryar sa gidan sa, sai dai kuma a daren da aka kai masa amaryar ya fuskanci cewa bata kawo mutuncin taba gidan sa.


Koda ya mata magana bata boye masa ba tace gaskia da tayi rashin ji har ciki tasha zubarwa daga baya ne ta nutsu shine kawai ta daina.


Ba Shi data cewa haka yaja bakin sa yai shiru, Yana Kara dana sanin abinda ya aikata a baya.




*********


A yanxu kuwa Zeey ta fara damuwa sosai da rashin samun cikin ta kullum cikin fadawa Azlan take, dole yasa shi daukar ta suka je hospital aka duba ta.


Sakamakon maganin zubar da cikin data sha ne mai karfi shine yayi sanadiyar taba Mata mahaifa, magungunan aka dora ta akai kuma ana fatan insha Allah zata samu cikin...








*After 15 years*


Sakkowa nake daga kan stairs cikin doguwar riga ta atampa nayi kyau har na gaji ina fadin "Noora, wallahi ki shiga hankalin ki ban hana ki wasan jakai ba wai"


Kamar zatai kuka tace "Maa kiyi hakuri na daina Maheer ne yake tsokana ta kamar bani ce yayar Saba"


Da sauri Maheer ya mike yace "Maaa karya take min, itace nan take dukana wallahi"


Tsaki nai ina karasowa gun su, kallon Noor nai nace "baka Jin suna fada maimakon ka raba su kawai sai Ka zauna kama kallon su".


Dago kansa yai ya kalle ni yace "Maa sorry bana son hayaniya ne kawai".


Tsaki nai nace "ke Noora ba part din Mummy nace kije ba ko baxa a miki lallan bane".


Kamar zatayi kuka tace "Ba naje ba Ya Mimi ta koroni"


Girgiza kai nai nace "wuce muje ina sultan yake"


Maheer da yai shiru kamar baya gun yace "yana gurin Ya Mimi wai shima sai an masa lallan"


Girgiza kai kawai nai na tasa keyar Noora zuwa part din Mummyn su(Zeey).


Acan na samu yan matan ana musu lalle, Zeey dake zaune ita da kanwar ta tasa dariya tace "ynxu nake fadawa Hafsa cewa nasan zaki shigo sbd baza ki iya nesa da Mimi ba"


Girgiza kai nai ina dariya nace "kai Mummy abin harda tsokana kuma".


Samira tada shigo ynxu tace "Ashe kuna nan, ynxu naje part dinki ban ganki ba".


Zama nai nace "Aunty Samira ynxu na shigo Nima taso keyar Noora nai nasan halinta da rashin son lalle".


Dariya sukai nan muka zauna muka cigaba da tsare tsaren bikin Mimi da za'a fara yau.


A shekarun nan bayan Noor da Noora na kara haihuwar Maheer da Sultan, yayinda Zeey kuma ta ke da yara biyu Asma da Usman.


Alhamdulillah muna zaune cikin farin ciki, mun hade kai muna shawara da juna akan duk abinda ya shafi yaran mu, na rungumi yaranta kamar yadda itama ta rungumi nawa.
Cikin shekarun nan munyi baban rashi na Baffa Wanda lokacin daya rasu zarewa ne kawai Azlan baiyi ba sbd tashin hankali, ya shaku da Baffa fiye da yadda ya shaku da iyayen sa.


Bamu yi wasu events na hauka ba, kamu ne kawai sai yini, yau takasance daurin aure bayan an daura za'a wuce da amaryar tunda a Abuja zata zauna ba'a Kano ba.


Dauriya nake sosai don kar nayi kuka amma Zeey data kasance uwar amarya kuma itace wacce zata Mika ta zuwa dakinta tana zaunar da ita agabana tace na Mata fada kawai na rungume ta ina fashe wa da kuka(Ni kaina Batul kin sani kuka🥹😭) Kasa Mata fada nai sai rungume ta danai sosai muna kuka, da kyar Umma da Mami suka lallashe mu don ita kanta Zeey din kuka take.


Duk Wanda ya sanmu yasan shakuwar dake tsakanin mu nida Mimi, koda ta girma ni ce nan Aminiyar ta komai dani take shawara kamar yacce Nima na maida ta aminiya ta.


Kasa mata nasihar nai sai albarka danake Sa mata kawai, ina kallo aka fita da ita sai kuka nake Husna matar Junaid tana rarrashi na.


Da daddare da kyar nayi wanka na shirya na nufi part din Oga, a dakin sa na same sa yana Zane.


Ina shigowa ya dago kansa Yana kallona, kallon sa nima nake girma yaja don ya kusa hamsin ynxu, hannu ya bude min kawai na tafi da gudu na fada jikinsa ina fashewa da kuka.


Bai hana ni kukan ba sai shafa min bayana da yake, sai da ya tabbatar na amayar da abinda nake ji sannan ya dago ni yace "Mene na kukan uhm Queen, Mimi ce ko"


Daga masa kai nai ina marmar da ido, shafa kaina yayi yace "to ya muka iya, itama ta girma tana son taji ya zuwaira take".


Zaro ido nai ina dukan kirjinsa cike da Wasa nace "nidai ba ruwana gaskia kafa girma".


Kunne na ya tsotsa yace "ai baxan taba girma ba akan fadar zuwaira, Nima zo ki ji tawa zuwairar sai begen gidan dadi take ki agaza ki bani Nono nasha"


Dariya mukai a tare muna fadawa Kan gado, janyo ni yai jikinsa yace "ina kaunar ki Matata sosai sosai".


A hankali nake shafa gemun sa nace "ina kaunar Ka Uncle Azlan Mai budurci".


A tare muka fashe da dariya yana sanya bakinsa acikin nawa...




Gonna miss u Uncle Azlan Nd Batul🥹


*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*


Allah na gode ma daka bani ikon gama littafin nan lafiya, abinda nafada daidai Allah kasa mu amfana Wanda na fada ba daidai ba Allah ya yafe mana. Ina godia sosai fans bani da bakin gode muku Allah ya bar mu tare sai mun hadu a saken book dina Amma da shi ba free bane😂😂😂






Mrs A.M


09066728387










Comments Nd share plz












Mrs A.M🥹🥰🥰

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login