Showing 15001 words to 18000 words out of 94393 words

Chapter 6 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt

Advertisement

Mrs A.M   

03 Aug 2024

17032

isa gurin ta "nace me kike yi ne Mimi"


Dagowa tai ta zuba min idonta da suka sani Jin cikina ya karta tace "Maa ina yiwa babyna wanka tayi datti"


Murmushi kawai nai mata na mike na shiga palour, ajiye takaddun nai a dakin mu na fito Palour daidai fitowar Umma daga dakin su, Zama nai ina bata labarin yadda muka yi photo copy din takaddun mu.


Cikin nutsuwa Umma tace "lafia kike kuwa Batul mene yake damun ki"


Gaba nane ya yanke ya fadi cikin damuwa na shiga tunanin shin na fadawa Umma mutumin da na hadu dashi yau ko kuma kar na fada mata.......














Comments Nd share plz














Mrs A.M🥰


[12/08, 21:24] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️


*TASWIRAR KADDARA*


♠️♠️♠️♠️♠️




Written by
Mrs A.M🥰


Page 9


Gaskia Azlan Ka fita idon Innar Nawaz don ta kawo min karar Ka cewa Ka na Mata signal kuma Ka kusa tara mata jama'a yau a titi sbd fitsarar ka🤣🤣


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Dan yatsina fuska nai nace "Umma wani ne ya kusa markade min kafafuna fah, kuma wai sbd mugunta ni ban masa rashin kunya ba amma ya nemi ya zage ni"


Kura min ido Umma tai cikin rashin yadda da abinda na fada mata tace "anya Batul meya hada ku toh"


Turo baki nai nace "Umma kawai fa daga nace masa ya kula sbd gaba in ni ya kusa kade ni banyi magana ba wasu in ya musu sai sun zage sa shiknn ya fara zagina"


Girgiza kai Umma tai tace "da ban sanki badai Batul amma na tabbata kin masa rashin kunya ne ko kuma kin fada masa maganar da ba haka ba wallahi ina hanaki wannan tsiwar taki amma bakya ji"


Langwabe kai nai nace "ynxu Umma da an kawo miki ni ranga ranga fah ya take min kafa fah"


Tsaki Umma tai tana juyawa cikin kufula tace "Allah ya nuna min ranar da zakiyi hankali"


Sakin baki nai ina kallon Umma, sai kuma na mike na fita kitchen don dora abincin dare.






**********


Junaid ne ya mike da sauri yazo ya janyo Azlan yace "lafiar ka qalau kuwa Azlan me kake shirin yi taya zaka cire wando don Allah"


Kasa kasa da murya Azlan yai ta yadda Junaid ne kadai zai jisa yace "kai mai Ka maida ni ne ina da hankali fah taya zan cire wando na barazana ce kawai ai ko aure nai kafin na cire wandon nan sai an hada da nasiha"


Ajiyar zuciya Junaid yai don shifa lamarin Azlan tsoro yake basa mutum kamar aljani don da ya fara tunanin ma ko aljanu ne da Azlan din sai daga baya ya fahimci cewa kawai tsabar tsageran cine.


Dan daure fuska Azlan yai yace "Ka barni Junaidu na cire mata wandon na nuna mata budurcina da nake tana dawa iyalina" ya karashe yana kamo hantsar wandon sa yana wani zunkuda kafada.


Abie ne ya mike yace "in baka daina wannan shirmen ba sai na Saba ma wallahi mara kunyar banxa da wofi"


Murmushi ya saki yana maida zip dinsa, juyawa yai ya kalli Baffa yace "tsoho zan iya fecewa"


Baffa da tunda yai magana sau daya ya zubawa sarautar ALLAH ido yana mamakin shakiyancin jikan nashi ya daga masa kai kawai yana binsa da addu'ar shiriya.


Cikin takunsa ya karaso kusa da Mami ya tsugunna yai mata kiss a kumatu yace "sai anjima MAA" daga haka ya juya ya fice daga palourn.


Mummy ce ta kalli Baffa cikin rawar murya tace "ynxu baffa kana kallon yaron nan abinda yai min amma baxa ka masa fada ba"


Murmushi baffa yai yace "Hafsatu knn ai dama koda kika zo da maganar wannan hadin a take a gurin nace Miki ba lallai ne wannan abun yai ba sbd sanin halin sa danai amma kika dage akan a tuntunbe sa aji gashi ynxu ai ya fada bashi da ra'ayi kuma gaskia ni baxan masa dole ba tunda ya fadi dalilin sa"


Abie ne yace "Amma Baffa ai mune muke gaba dashi kuma duk abinsa haihuwar sa akai shekarar sa 33 amma har ynxu yaki hankali ni a yadda nake ganin take taken Sama ba aure sam a gaban sa"


Dan hade rai Baffa yai ya kalli Uncle M da yai shiru yana kallon su yace "Mustapha rufe mana taron da addua"




*********


Washe gari muka je muka karbi Admission dinmu inda zan karanta architecture shi kuma cilla zai karanta library science, sosai muke murna don mun fara jin kamshin Zama cikakkun yan University.


Da daddare muna zaune ina bawa Abba labarin yadda Makaranta take Mimi na kwance akan cinyata tana bacci.


Murmushi nai nace Abba nan da wata daya fah zamu fara zuwa koh wallahi na matsu sosai.


Murmushi Abba yai yace Allah yasa ku fara a sa'a Batul ki maida hankali sosai ba ruwanki da biye wa kawayen banxa dama nasan Alhamdulillah ke ba mai biye biye bace, amma ina Kara tuna Miki bake ba lecturers tsakanin ki dasu karatu ban yadda kina zuwa office din lecturer ba ke kadai ko kiranki yai kuje keda wasu ki kama mutuncin ki Batul, kuma kiji tsoron Allah a duk inda kike sannan ki maida hankali akan karatu don Allah duk da baki da Wasa amma still ina kara tuna Miki wannan karatun da irin Wanda kika saba bane sai kin dage sosai Allah ya bada sa'a.


Kaina a kasa na amsa da "Ameen" sai kuma naji jikina yai sanyi. Kallon Umma Abba yai yace "Umma baki ce komai ba"


Dan murmushi Umma tai tace "ai Ka gama fadin komai Abba sai dai kawai Nima nace ki kula sosai ki rike mutumcin ki Banda kawayen banxa sannan ki dage da karatu jami'a ba wajen wasan yara bane"


Daga Kai nai na kalli Abba nace "Abba ni kun fara tsorata ni in kuna cewa na dage da karatu Allah"


Dariya Aisha tai tace "ai tunda kika tsoro ta mu kuma fah Ya Batul ai sumu inaga tun ranar da muka samu admission zamu fara zawo har ranar da zamu fara lecture"


Hararar ta nai kawai na juya gurin Abba daya miko min kudi, kallon sanai ganin haka yasa shi fadin "ungo 15k ne kiyi siyayyar hijabai da takalmi sai jakar makarantar da zaki yi amfani dasu".


Cikin farin ciki na karbi kudin nace "angode sosai Abba Allah ya kara arziki ya Kara lafia da nisan kwana mai albarka ai kuwa gobe Insha Allah zanje kasuwa na siyo yadikan hijabai guda da kuma material ko Umma sai na siyo jaka a gwanjo mai kwari wacce zata dinga dauke min komai guda biyu"


Khalil ne yace "Ya Batul zan raka ki don Allah"


Da sauri kamal yace "ni zan raka ta ai ba Kai ba"


Tabe baki nai nace "ba wanda zanje da shi ni kadai zanje na dawo"


Kallon Umma nai nace "Umma wannan kudin da nake ajiye wa a gurin ki don Allah in zan samu sai na hada dasu goben na siyo material da dan yawa Wanda zan na Sawa dama nai WA Aunty zainab magana Zan dinka abina da kaina"


Gyada kai Umma tai tace "mai zai hana ki samu kuwa suna nan na ajiye miki dama ai su munyi dake zaki siyo material ne goben in Allah ya kaimu sai na baki"


Murmushi nai cikin Jin dadi na mika mata kudin da Abba yaban nace "Toh gashi Umma ki ajiye min wannan ma"


Mikewa nai na dauki Mimi na kwantar da ita, Nima kwanciya nai don gobe da wuri nake son zuwa kasuwar, lumshe idona nai saidai kuma duk yadda naso baccin ya dauke ni ya kasa zuwa sbd fuskar wannan mutumin kawai kemin yawo, a hankali na bude idona na zuba akan fuskar Mimi gani nake kamar Mutumin ne kwance a gefena.


Mikewa nai na zauna ina kallon Aisha dake shirya littafan ta acikin jaka nace "Aisha kinsan me"


Dan juyo wa tai tace "A'a Ya Batul"


Ajiyar zuciya na sauke nace "wani abin mamaki na gani wallahi jiya nida Cilla bayan mun fito daga cafe wani ya kusan take min kafa, kin san Mutumin yana kama da Mimi sosai kamar yayi kaki ya tofar har yadda yake magana da yadda yake bata fuska duk irin na Mimi ne"


Xaro ido Aisha tai tace "kuma kin fadawa Umma Ya Batul"


Girgiza kai nai nace "ban fada mata ba bana son na kama Mata ciwon da take kokarin rufe wa ne"


Zama tai a gefena tace "Ya Batul kina tunanin xai iya xama baban Mimi"


Da sauri na yatsina fuska nace "Allah ya kiyaye insha Allah ma ba shi bane babanta, toh meye ma ya dame ni da sanin ko waye baban nata, bana ma fatan sanin sa don duk ranar da muka hadu nida shi Allah ne kawai zai kwace sa a hannuna"


Tagumi Aisha tai tana kallo na ganin yadda nake faman tsinewa baban Mimi Wanda ko kalar fatar jikin sa ban sani ba.


Haka nai bacci sbd sa abin a raina har mafarki nai wai mutumin dana hadu dashi yazo yace na basa Mimi yar sa CE, ai kuwa haka na tashi raina duk a bace, da kyar naje kasuwar na siyo duk abinda zan bukata na tahowa da Mimi dogayen rigunan Yan gwanjo guda uku na siyo mata sabon takalmi.




Kwanci tashi har mun fara shiga university muna bude file nida Cilla muke tafiya komai tare muke yi kafata kafarsa har muka gama, gobe Insha Allah dukkan mu zamu fara lecture gaba daya cikin zumudi muke koda aka ban time table sai da naje nai photo copy daya ba barsa a cikin jakata daya kuma na sa salatif na manna a jikin bangon dakin mu.


Yau sbd zumudi da wuri nai bacci bayan na shirya kayana dazan sa goben in Allah ya kaimu..












*********


A hankali yake gyada kansa kamar salihi yana Jin abinda Abie yake cemasa.


Girgiza kai Abie yai yace "don Allah Azlan Ka dinga zuwa duk ranar da kake da lecture kar kasa shiririta kuma Ka dinga suturta jikin Ka kaji"


Daga Kai yai yana lumshe idon sa sam wannan lecturing din da zai fara kawai don ba yadda zai yi ne amma ayyukan office kadai ma aka barsa dasu na sun ishe Shi ga kuma wannan nauyin an Kara dora masa.


Shiru yai yana jin Abie da Mami suna masa nasiha Shi dariya ma suke basa yadda suke wani lallabasa akan lecturing din toh sun san halin sa a goben da yake da class zau iya kin zuwa ya kwanta yai baccin sa hankalin sa kwance.

Sai da suka gama masa nasihar sannan ya mike ya fita bayan yai musu sai da safe
















Comments Nd share plz












Mrs A.M🥰
[13/08, 15:50] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️


*TASWIRAR KADDARA*


♠️♠️♠️♠️♠️




Written by
Mrs A.M🥰


Page 10


Dedicated to ♠️TASWIRAR KADDARA♠️ Group ina jin dadin comments dinku sosai Allah ya bar zumunci🥰


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Washe gari karfe 7 a BUK tai min kasancewar muna da class karfe 8, hall din da zamuyi lecture din na shiga na samu front sit na zauna, ajiyar zuciya na sauke ina gyara zaman sabon hijab dina.


Ban dade da zama ba hall din ya fara cika, kusan kowa a gaba yake zama karfe 8 dai dai lecturern da zai mana maths ya shigo, sai da ya fara da introduction kafin ya fara mana revision akan maths din da muka bari a secondary school, sosai na maida hankali kansa ina saurara wasu abubuwan kuma ina jotting a book dina dana ware don haka.


Sai karfe 9 ya fita amma lecturern da zai mana physics bai shigo ba hakan yasa kowa ya fara sha'anin gaban sa tunda dama physics din muke da 9-10 daka nan kuma muna da interval har sai 1:30.


Maths din da aka mana na maida hankali sosai ina dubawa har lokaci yaja sosai, sai da na gaji na ciro wayata na shiga WhatsApp ina duba status, ina zaune wata tazo ta miko min wayarta tace in sa mata number na za'a bude group ne na yan course din ta yadda za'a na fadan duk abinda ya shafi course din, ban musa Mata ba na sama ta number din.


Sai karfe 1 na mike na fita don zuwa masallaci nai sallah, ban wani sha wahalar neman masallacin ba sbd lokacin da muka zo bude file anan nake sallah, ban dade ba na koma sbd class din da muke da shi tym din, a sit din dana zauna anan na zauna ina Zama lecturern na shigowa, sai karfe 3 muka fito.


A gajiye na fito cikina in banda karar yunwa ba abinda yake yi, cikin gajiya na daga wayata na Kira cilla don shi ma kusan tare muka fito, ina tsaye ya karaso shima dai kallo daya zaka masa kaga gajiya tattare da shi.


Kallona yai cikin kulawa yace "uwar dakina wallahi na gaji ga yunwa dake ta kwakwula ta"


Ajiyar zuciya na sauke nace "Cilla nima nan a gajiyen nake ai baxan sake wannan kuskuren na kin cin abinci ba Allah kuma sai na dinga tahowa da cake da doughnut da zobo muna ci muna rage zafi in bamu koshi ba muje cafeteria muci abinci ko mu siya waina ko gurasa"


Murmushi yai yace "toh hakan dabara ce sosai don baxan iya wannan horon yunwar ba nifa SBD yunwa wannan lecturen ta karshe da mukai ba abinda na fuskanta"


Dan dariya nai nace "Allah ya shirye ka cilla wallahi ynxu kace ba abinda Ka kwashe kawai Zama kai kana kallon malamin"


Gyada kai yai yace "rass ma kuwa Uwar dakina ai kinsan irin wannan yunwar daina gani ma take sa mutun yi"


Haka muka cigaba da hira har muka fita school din Shi ya tarar mana adaidaita muka hau, ni aka fara sauke wa shi kuma za'a karasa dashi kofar gidan su.


Cikin gajiya nai sallama na shiga gida, da Umma na fara cin karo tana tankade garin dan wake tana gani na ta saki dariya tace "kaga Yan jami'a ya naganki haka kamar wacce aka koro"


Turo baki nai nace "Umma ina wuni"


Dariya tai tace "lafia qalau ya makarantar"


Zama nai akan tabarma nace "Hmmn Alhamdulillah Umma duk abinda aka mana yau na gane sai dai yunwar dake cinye min yan Hanji"


Da mamaki tace "ba Abba ya baki kudI ki sayi abinci ba in kinji yunwa"


Mike wa nai nace "Hmm Umma tsautsayi yasa nai tunanin baxan ji yunwa ba ai kuwa na azabtu ai daga yau da cake zan na zuwa Allah"


Kitchen na shiga na zubo abinci na zauna ina bawa Umma labarin yadda yau ta kasance a school, sai da na koshi naji dai dai sannan naje nai wanka, ina fitowa sallar la'asar nai na mike kafafuna na kalli Umma dake kan sallaya tana jan carbi nace "Umma kuma wai a haka fa don karfe 3 na dawo yau gashi gobe har 6 zan Kai tab ashe haka ake Shan wahala"


Tabe baki Umma tai tace "tukunna ma yarinya"


Daren ranar gaba daya nayi Shi ne ina bawa su Abba dasu Aisha labarin makarantar da yadda take.


Cikin satin sosai na maida hankali na akan karatu duk da bawai an shiga cikin karatun bane introduction kawai ake mana amma na nutsu kullum in ina school in har bamu da class zama nake nayi karatu na in kuma cilla shima bashi da class muje mu zauna a cafeteria muci cake dinmu kowa ya duba littafi ko kuma muyi hira, sosai Amincin mu da cillah ya Kara daduwa sbd tare muke zuwa mu dawo sai dai in zan rigasa shiga lecture ne shine kawai nake rigasa tafiya.


Ban Kula kowa a course mate dina tsakanina dasu gaisuwa ce shiknn sai dai kuma ina maida hankali ina karantar su wasu tunda ga satin farkon zaka gane sun shigo show off ne kawai duba da yanayin shigar su.


A cikin satin farko lecturer da zai dinga mana physics shi kadai ne bai shigo mana ba, muna da physics har biyu a sati amma bai shigo ba sai dai an fada a group din da aka bude cewa uzuri ne ya hanasa zuwa amma sai shigo wani satin insha Allah.


Ranar Monday kamar yadda muke da lecture tun karfe 8 da wuri na shigo school kuma na samu front sit bakin window na zauna, har malamin da zai mana maths ya shigo ya fita, yana fita Wanda zai mana physics ya shigo.


Jin class din yai shiru kamar anyi ruwa an dauke yasa ni dagowa don ganin dalilin dayasa class din Shiru haka, tun daga kafar sa na soma kalla gabana yana bugawa da karfi yana sanye da takalmi boots black colour sai wandon jeans fari kar sai Riga daya sa black wacce ta dan kamasa kansa sanye yake da p-cap, a hankali idona ya fada cikin nasa daya sha kwalli sosai sai sheki yake, kallo daya yamin kusan a tare muka janye idanun mu.


Cikin faduwar gaba nake tunanin badai shine malamin namu ba tab, jinai cikina yayi kugi da yasani saurin dafe cikin ina tuna rashin kunyar danai masa.


Azlan kuwa kallo daya yai mata ya janye kansa a ransa yace lallai wato shiyasa tai masa fitsara ashe tashen balaga take yi ita zata shiga jami'a, kankance idonsa yai bayan yadan lashi jajayen lips dinsa ya fara bayani cikin harshen turanci.


Yadda ya hade rai yana bayanin yasa ni maida hankali sosai ina jotting duk wani Abu mai muhimmanci don jikina naban yadda nai masa rashin kunyar nan tsaf zai iya bani carry over.


Hour daya ya dauka ya fita bayan ya dauki attendance kuma bai fita ba Saida ya bamu assignment yace ayi submitting gobe karfe 8 in ya wuce 8 baxai karba ba, yana fita aka fara magana akansa matan ajin sai zuzuta kyan sa suke suna fadin shine sabon lecturer da ake maganar sa Ashe.


Nidai tagumi nai na zubawa assignment din ido, ganin hakan baxai fishshe niba yasa na fara solving assignment dina tunda yace gobe karfe 8 yake so ayi submitting nasan class rep za'a bawa, saukin tama goben muna da class karfe 8.


Sai da na gama assignment din na kara dubawa na tabbatar nayi daidai sannan na mike na fita don zuwa cin abinci, a inda muka Saba haduwa da cilla na gansa yana zaune yana cin meat pie da lemo, yana gani na yace "uwar dakina tun dazu nake zuba ido ai naga baki fito ba ina shirin in na gama ci naje na duba ko lafia sai gaki lafia kuwa?"


Zama nai na sauke ajiyar zuciya nace "Hmm cilla ina ruwa kusa da Kada wallahi"


Da mamaki yace "lafia wani abun ya faru ne"


Sosa gira ta nai nace "ai komai ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login