Showing 60001 words to 63000 words out of 94393 words
Chapter 21 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt
sai murna Mimi take, ajiyar zuciya na sauke kawai ina Jin wani abu yana ratsa zuciya ta game da Daddyn Mimi.
Da azahar muna zaune nida Iya a Palour kallon Hausa film muke muna yi muna hira iya na ban labarin kauyen su, door bell aka danna iya dake zaune a kasan Carpet ta kalle ni tace "in bude Maa"
Daga mata Kai nai ina gyara zamana akan kujerar, Yakumbo ce ta fara shigowa sai uwani da Hama sai Shamsiyya a bayansu, mikewa nai daga kan kujerar na nufi Yakumbo ina fadin "wa nake gani haka"
Dakuwa Yakumbo tai min tace "nice nan ko na koma ne"
Dariya nai nace "na isa nace ki koma"
Zama sukai na gaishe su ina daga gefen Yakumba, kallon Shamsiyya nai nace "sannun ki Shamsiyya ya gida"
Cikin daga kai tace "lafia" tana kara bin palourn da kallo dake tashin kamshin turaren wuta ga sanyin AC.
Kallon Iya nai nace "iya a kawo musu ruwa"
Mikewa tai ta shiga kitchen bata dade ba ta fito rike da babban tray dake dauke da ruwa da drinks, ajiye wa tai a kan center table tace "Maa ko za'a dora wani abu"
Mike wa nai nace "muje iya inga ya kamata Kam"
Tabe baki Uwani tai cike da Hassada tace "daka zuwan mu an fara maganar a dora abinci kamar wasu mayu"
Gyada kai Hama tai tace "ai mayun aka dauke mu ke kuwa tunda an shigo gidan daula ba dole a nuna mana iyakar mu ba"
Yakumbo dake jinsu tace "amma ku kuwa kunji kunya, Hassada har ina ashe shiyasa kuka damu dole sai kunzo ashe ba zuwan Allah da annabi bane"
Shiru sukai dukkan su basuyi magana ba sai hura hanci kawai da suke.
Ni kuwa da ban damu da abinda suka ce ba kitchen na shiga ruwan shinkafa na dora wacce zanyi dadan yawa har dare sai na fara hada miya, sai da na hada miya dama ina da soyayyar kaza a fridge sannan na fita nasa iya ta yanka min Kayan vegetables din dazan hada coleslaw.
Zama nai muna hira da Yakumbo su kuwa su Uwani TV kawai suka zubawa ido suna kalla, kallona Yakumbo tai tace ni kuwa banga Mimi ba tun dazu nake baxa ido
Murmushi nai nace "sun fita ita da Daddyn ta zasu gidan sune ba lallai su dawo ynxu ba"
Haba Yakumbo ta rike tace "lallai Mimi kuma sun Saba da Yan gidan nasu"
Daga kai nai nace "sun Saba mana Yakumbo, da yace mata zasu ma baki ga murna ba"
Yakumbo tace "shikmn kuwa ta huta"
Uwani da gulma ke cinta tace "Ashe ku biyu aka aura masa sbd dan gata ne Shi koh, ai sai daga baya muke ji nace inaga wancan din itace wacce suke soyayya ke kuma aka hada ku koh"
Kallon ta nai na seconds kafin na dauke kaina nace "ban da masaniya ashe haka abin yake"
Cikin kufula Hama tace "kina nufin baki san ita kishiyar taki itace wacce yake soba Ke kawai hada ku akai"
Dan murmushi nai nace "da yake bai taba fada min haka ba shiyasa ban sani ba ai"
Shamsiyya da ta gama shakar ganin yadda nake raina musu hankali tace "to ynxu gashi kin sani koh sai ki daina ma mutane gani gani sbd kin auri mai kudi"
Hade rai nai nace "kiyi shiru koh kinsan maganar ta manya ce"
Kallona tai zatai magana Yakumbo tace "ya isa haka kudai kunji kunya wallahi meye amfanin irin wannan maganar da kuke fada mata da girman ku"
Ban yi magana ba kitchen na koma gurin aikina, sai da mukai la'asar sannan na kai musu abincin dinning Yakumbo kuma na zubo mana tare nida ita na ajiye mana acan carpet, suna hade rai suka kame akan dinning suna cin abincin.
Ko kallon inda suke ban ba muna cin abincin mu nida Yakumbo tana min nasiha da yadda zan zauna da kishiya ta, nidai kawai jinta nake yadda take cewa na yi hakuri da kishi Sam bana Jin kishin ta ko kadan ko mai yasa oho.
Bayan mun gama iya ce ta gyara gurin ko ina yai tsaf ta kunna turaren wuta da fesa freshner.
Mikewa yakumbo tai tace "muje koh bana son muyi dare"
Da sauri Nima na mike nace "Yakumbo badai tafiya zakuyi ba"
Daga mun kai tai tace "kinga har karfe 5 bana son muyi magriba ana gaskia gwanda mu tafi"
Kamar zan kuka nake kallon ta daki na shiga na dakko 5k a jakata su Uwai kuma na zuba wa kowaccen su turaren wuta dan daidai na sa musu a leda.
Fitowa nai sanye da hijab iya gwiwa, ledar na fara mikawa uwani tace "gashi Uwani keda Hama turaren wuta ne," sannan na mikawa Yakumbo kudn nace "gashi tsohuwa asai goro"
Murmushi Yakumbo tai tace "da dai zance baxan karba ba amma toh bara dai kawai na amsa"
Dariya nai nace "Allah ya shirya mana ke tsohuwa wallahi da son kudin ki"
Compound muka fito don rakasu, muna fitowa motar Shi na shigowa kallon Yakumbo nai nace "gasu ma sun dawo"
Sai da ya daidai parking dinsa sannan suka fito hannun Mimi ya riko suka nufo inda muke dayan hannun nasa kuma rike da leda, gaishe su yai Mimi kuma ta rungume Yakumbo tana fadin "oyoyo Yakumbo tazo gidan mu"
Kallon sa nai ganin yadan saci kallona a hankali yadda Shi kadai zaiji kasancewar yana daga ta gefena nace "kakata ce sai matan su Kawu Nasiru"
Daga kai yai yace biyo ni ki karbar musu sako, kallon Yakumbo yai yace bara nasa a maida ku
Murmushi Yakumbo tai tace "ayi haka kuwa"
Dan murmushi ya saki yace "hakan za'a yi Insha Allah"
Kallona yai yasa na kalli Yakumbo nace "ina zuwa Yakumbo bara na dawo"
Binmu da kallo sukai dukan Su yayin da Shamsiyya take Jin da tana da hali ba abinda zai sa ta kwace wannan mijin da ya auri Batul don ita kallo data ta masa ya tafi da imanin ta.
Ta main kofar palourn na shiga ina shiga ban gansa ba sai Zeey dake zaune sanye da Riga da wando ta wani hade rai da alama ranta a bace yake, kallona tai tace "me kika zo yi nan ko kin manta yau ba kwanan ki bane, shine zaki biyo miji har daki."
Kallo daya nai mata na watsar sai Zama danai a kan kujera ina danna waya, bakin ciki ne ya zo mata wuya ta mike a fusace ta zo gurina wayar da nake dannawa ta dauka ta jefar nan da nan ta tarwatse.
Mikewa nai na karasa inda wayar ta tarwatse na dauka dubawa nai naga t dauke ma son screen din yayi fatsa fatsa, nan da nan bacin rai ya bayyana a fuska ta don na fukanci wannan wawiyar hauka ke damunta ta raini.
Cikin mugun hade gira na karaso gaban ta nace "me ye dalilin ki na fasa min waya"
Harara ta watsa min tace "an fasa din karamar yar iska, kin makale wa mutum baya sonki sai da aka aura masa sbd rashin zuciya, ni da kike gani na wallahi tsaf zansa yayi waje dake kawai na kyale kine kidan murmure tunda babu a house".
Wani malalacin murmushi na saki ashe bata da man kai da naso nayi sa'in sa da ita, Amma zan nuna mata ita karamar shegia ce, da sauri na juya jin tahowar sa.
Cikin tafiyar da nasan duk ilahirin jikina yana shaking na nufe sa gabana in banda duka ba abinda yake, sai da na tsaya a gabansa sannan na turo baki ina Kwal kwal da ido nace "Baby Kaga ta fasa min waya ko kuma ba abinda nai mata," na karashe ina jijjiga kafada ta yadda boobs dina sukai wani tsalle.
Zaro ido Azlan yai da ya zubawa kirjin ta ido yace Astagfirulla waya fada Miki waya kuma
Kara narke wa nai cike da shagwaba nace "Ina zaune kawai ta taso ta jefar min da ita kaga fa ta fashe kuma banda wata" na fada ina fashewa da kukan karya
Baisan sanda ya janyo ta jikinsa ba ya rungume yana sauke ajiyar zuciya don yadda take wannan shagwabar tana jijjiga kirji tuni yadau chaji, shiyasa ya rungume ta ko ya samu sassauci, kallon Zeey yai data daskare tana kallon ikon Allah yace "Ke meye haka wani irin shirme ne zaki fasa mata waya"
Bude baki tai tace "Yaya karya take min Allah"
Da sauri na dago kaina daga kirjin sa nace "baby wallahi ba karya nake Mata ba kalli fa don Allah" turo baki nai Zan sake fashewa da kuka yai saurn cewa "yi Shiru kinji maman beauty zan siya Miki wata sabuwa mai kyau dena kukan"
Zeey dake kallon su wani tukuki na taso Mata a kirji kawai ta kwasa a guje zuwa part dinta tana kuka.
Kallon ta nai sannan nai saurin matsawa daga jikin sa ina turo baki, kallona yai yace "kema wai karama dake kin iya iskanci koh, ni kike cewa baby sbd rashin kunya"
Turo baki ina kauda fuskata, murmushi yai yana matso ni yace "ynxu dai tunda kin ce min baby toh bani Nono nasha"
Da sauri na kalle sa nace "na shiga uku wai Kai don Allah baka Jin kunya ne"
Kafada ya daga yace "Naga kamar suna miki kaikayi ne nan fa kika dinga girgiza min su toh ba sai na duba miki ba, ko so kike na dan latsa ne"
Da sauri nace "Astagfirulla wallahi bakyau maganar iskanci kuma nidai ba ruwana".
Zaro ido yai yace "kamar ya ba ruwanki toh shikenan nawa ya isa kawai"
Da sauri na kalle sa ina zaro manyan idona na toshe baki Jin katuwar maganar daya fada.......
Comments Nd share plz
Mrs A.M🥰
[12/09, 14:59] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️
*TASWIRAR KADDARA*
♠️♠️♠️♠️♠️
Written by
Mrs A.M🥰
Page 32
Dedicated to Baby Beauty lounge🥰💓
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃
*Mrs Dnah perfumes nd more*
*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*
*Muna Saida*
*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.
*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*
*Phone number*
+234 702 577 7778
Location kano
Dariya yai ganin yadda ta zaro ido yace "ungo jeki basu kar suga kin dade su dauka ko bar ruwa muka tsaya yi"
Nidai sauke kaina kasa kawai nai ina mamakin rashin ta idon baban Mimi, kudin daya miko min na kalla mint din 200 ne 20k knn Kallonsa nai nace "Angode Allah ya saka da alkhairi ya kara budi"
Murmushi yai yace "Ameen ya rabbi"
Wayar tawa ya karba yace "jeki kai musu don nasan sun gaji da Jira"
Juyawa kawai nai na fita daga palourn, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon wayar hannun sa ynxu shiknn ta karya masa alwalar sa, murmushi yai shifa bai tabbatar da cewa lafiyayye bane shi sai a kwanakin nan don marar sa har kara nauyi tai.
A mota na same su kudin na basu nace Shi yace a basu, sai addua Yakumbo take masa muna kallon su har saida suka fita sannan naja hannun Mimi muka koma ciki duk jikina a sanyaye.
Washe gari da safe ta kama Sunday kuma ranar zan karbi girki, ina idar da sallar la'asar na shiga kitchen nida Iya Mimi tana palour tana wasa kamar yadda ya tsara masa karfe 6 girkin ki ya shiga shiyasa na tanadi duk kayan gyaran part din da zanyi, don jiya dana shiga naga alama ita yar ji dakan bata Kula dashi.
Tuwon shinkafa nayi miyar kubewa bushasha sai zobo dana hada na zuba mishi a jug nasa a fridge, nasa daban a flask dinsa na ajiye akan dinning.
Karfe 6 kuwa na bude kofar na shiga ko ina a kashe da alama tun safe daya fita bai dawo ba, a nutse na shiga gyara masa ko ina na chanja masa bed sheet din dakinsa, turaren wuta na kunna a dakin da palourn sannan na koma nawa part din bayan na jera masa kayan abincin akan dinning.
Sallah nai ina zaune akan sallayar har akai Isha'i Saida na yi shafa'i da wutiri sanna nashiga wanka fitowa nai na shafe jikina da Humra, yar karamar rigar bacci nasa iya gwiwa na feshe jikina da turare.
Addu'a nai wa Mimi data dade da kwanciya har na zauna ina duba takadduna na tuna ban Kai masa zobon saba, dan tsaki nai na mike ina fadin Allah yasa bai dawo ba dai hijab na sa had kasa sannan na dau zobon na nufi part dinsa.
A hankali na shiga sai dai addu'a ta bata karbu ba don yana zaune akan kujerar dining gabansa wani table ne dauke da kayan Zane da alama Zane yake, ajiye jug din nai akan dinning na tattare kayan abincin da yaci ina mamakin cin abincin sa tuwo malmala biyu ya cinye.
Dan satar kallon sa nai gaba daya hankalin sa yana kan zanen da yake, kallon zanen nai ya dau hankalina gida ne yake zanawa cike da kwarewa da nutsuwa, a hankali na tsaya ata bayansa ina kallon zanen, yayi kyau sosai na shagala da kallon zanen cike da sha'awa da kuma yadda yake sarrafa pencil din hannun sa cikin kwarewa.
Dagowa yai ya kalle ni ganin yadda take kallon zanen yasa yace "ko zaki zana ne"
Dan ware ido nai nace "baxan iya ba"
Murmushi yai yace "xaki iya mana kawai dai baki sa kanki ba wuya"
Girgiza kai nai nace "ba ynxu ba dai wannan zanen sai kwararru"
Tabe baki yai yace "mai kika kawo ne"
Dinning din na kalla nace "Zobo ne"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "zubo min plz ishi nake ji"
A hankali na nufi dinning din na zuba masa zobon, miko masa cup din nai nace "gashi"
Ba tare daya kalle ni ba yace ki bani a baki mana kinga aiki nake bana son na katse abin da nake
Turo baki nai nace "toh kai baby ne da zan baka a baki"
Murmushi yai yace "kwarai kuwa ko baki sani ba, ba jiya kika gama cemin baby ba"
Hararar bayansa nai nace "ai subutar baki ne"
Dagowa yai ya kalle ni yace "ynxu dai zaki bani ko baxan samu ba"
Kau da kaina nai na tura masa cup din bakinsa, hannuna ya kama ya daga cup din sai da ya shanye sannan yace "masha Allah waye ya hada zobon nan"
Hararar sa nai nace "nice nan na hada abina"
Dan kallona yai yace "waya koya Miki"
Idona akan zanen da yake yi nace "Umma ce ta koya min kuma a gida ai ina Sana'ar zobo da kunun Aya"
Dagowa yai ya kalleta yace "sai ki siyar da zobo"
Daga kaina nai nace "eh mana har da cake nake yi ana kaimin shago kuma ciniki nake sosai"
Daga kai yai yace "meyesa ni baki taba min cake din ba"
Zaro ido nai nace "baka ce kana so ba ai"
Tabe bakin sa yai yace "ynxu nace ina so toh ki min"
Shiru kawai nai ina kallon zanen ba tare da na sake magana ba har ya gama, mikewa yai ya janyo wani kwali dake gabansa yace "ungo"
Kallon sa nai na kalli kwalin na waya ne cikin rashin fahimtar nace "me zanyi da shi"
Gajeran tsaki yai yace "karbi mana waya ce taki ta lalace shine na siyo miki wata"
A sanyaye na karbi wayar nace "angode sosai Ubangiji ya Kara Arziki mai albarka ya rabaka da iyayen Ka lafia"
A kasan leben sa ya amsa yana Jin dadin addu'ar ta kallon dinning yai yace "in tuwon yai ragowa ina son dumame gobe"
Daga Kai nai nace "sai da safe"
Bin ta da kallo yai har ta fita ajiyar zuciya ya sauke ji yake kamar yace ta dawo, hannun sa yasa a gashin sa yana hargitsa sa, sai da ya Kara Shan zobon sannan ya shiga daki don a matukar gajiye yake.
Zama nai akan gado ina bude kwalin wayar zaro ido nai cikin mamaki iPhone 13 pro max ce silver sabuwa fil ga wani case mai kyau na Mata shima a jikin wayar, murmushi nai ina kunna wayar har SIM dina da akwai a ciki ya samin kuma yamin downloading applications da yawa.
Murmushi nai na shiga dudduba wayar tunda na iya amfani da ita kasancewar Aisha tana da iPhone, ban yi bacci ba sai da na bude WhatsApp da Snapchat da Instagram kuma nayi downloading apps din dana ke so, charji nasa ta na kwanta cike da farin ciki.
Washe gari naso na makara ina idar da sallah kitchen na shiga tuwon jiya na dumama masa na kai masa part dinshi a gurguje na gyara masa nasa turaren wuta sannan naje na shirya Mimi saukin tama bata zuwa da abinci ana basu a makarantar.
Wanka nai na shirya cikin doguwar rigar abaya, yane kaina nai da mayafin abayar na dau jakata hannu na rike da wayata.
Tea muka sha nida Mimi mukai wa iya sallama muka fito, a tsaye na tarar da bashir driver yana jiran mu gaisawa mukai muka shiga back sit nida Mimi.
Hoto nai mana a sabuwar wayata jina nake babbar yarinya, Mimi dake shafa wayar tace "Maa Daddy ne ya siya Miki sabuwar waya"
Murmushi nai nace "uhm shine"
Dariya tai tace "Daddy yana sonki sosai ko Maa"
Shiru nai nace "yimin shiru bana son surutu"
Sai da aka fara Kai mimi sannan ya ajiye ni, duk ji nake ba dadi tunda Asma'u bata zuwa.
Karfe 2 mun fito daga lecture ina shirin Kiran Bashir wayar Asma'u ta shigo dauka nai nace "Assalamu alaikum mai juna biyu"
Dariya tai tace "Na'am Uwar gidan Mr Wicked"
Tsaki nai nace "bana son shakiyanci fa, ya kike"
Dariya tai tace "na haihu fah dazu da safe"
Da mamaki nace "Wasa ko gaske"
Dariya tai tace "wallahi na haihu ina asibiti har ynxu dai ba'a sallame ni ba"
Kamar zanyi tsalle nace "wayyooo Allah dadi mai muka samu namijin ne"
Dariya tai tace xshine wallahi kin gansa can hannun mamax
Murmushi nai nace "Allah ya raya yai masa albarka bara na tambayo Daddyn Mimi Allah yasa ya yarda inzo in ga baby kafin na koma gida"
Da sauri Asma'u tace "kar ki damu wallahi ba lallai sai kin zoba amarya ce fa ke ko sati uku baki yiba"
Tsaki nai nace "ai ba ke Zan zo gani ba babyna Zan ganu"
Wayar na kashe nasa a jakata na nufi office dinsa a raina ina addu'ar Allah yasa ya barni na gano babyn.
Knocking nai sai da aka ban izinin shiga na shiga bakina dauke da sallama yana zaune akan kujera yana danne danne