Showing 78001 words to 81000 words out of 94393 words
Chapter 27 - TASWIRAR KADDARA BOOK COMPLETE PDF .txt
part dinta ya Kaita.
Sauke curtain din palourn nai na sauke ajiyar zuciya, hijab nasa na dauki basket din dana zuba masa abinci, duk da ba ranar girkina bane amma sai da na masa girki tunda ina kyautata zaton Zeey baza ta iyaba.
A nutse na tura kofar palourn nasa na shiga, yana zaune akan kujera yayi baya da kansa yana shafa wuyansa da alamar gajiya a tattare da shi.
A hankali na ajiye basket din a Kan center table, dafa kafar sa nai cikin Kwantar da Murya nace Daddy ina wuni
Banza yai min kamar bai ji mai nace ba, ajiyar zuciya na sauke a hankali na Kara fadin Ina wuni
A harzuke ya mike yace "bana son gaisuwar ki plz meye kika zo min nan"
Sunkuyar da kai na nayi hawaye yana kokarin zubo min, dauke hannuna daga jikin sa nai ina wasa da yatsun hannuna nace "don Allah kayi hakuri Ya Azlan wallahi bani nasa mata maganin ba baxan taba iya aikata Mata haka ba"
Zuba min ido yai deep down a zuciyar sa yana son yadda da abinda take fada amma kuma in ya tuna a gaban sa ta kawo zobon kuma dai shine abinda tasha na karshe sai yaga cewa karya kawai take ita ta zuba mata sbd tana bakin ciki kamar yadda Zeey tace masa.
Mikewa yai yace "tashi ki ban guri plz bana son ganin ki"
Da sauri na dago kaina na kallesa hawaye suna zubo min, shiru nai kafin nace "ko xan tashi kaci abincin plz"
Tabe baki yai yana dage girar sa yace "bazan ciba na sani nima ko kin zuba min wani Abu a drink dina".
Kuka kawai nasa masa ina kifa kaina akan kujera, kallon ta yake so yake ya lallashe ta amma in ya tuna asarar data sa sukai sai yaga bakinta sosai.
Ya bude baki zai magana Zeey ta shigo tana sanye da English wear tayi makeup kamar ba itace ta sami miscarriage ba, a yatsine ta kalli Batul kafin ta marairaice tana tafiya a hankali.
Da sauri ya karasa gunta ya riko ta sai sannu yake jera Mata, cikin nuna kulawa yace "meyasa kika zo, bana son kina stressing kanki da zan shigo da kaina ai".
Marairaice fuska tai tana kwantar da kanta a kirjin sa tace "Yaya so nake na ganka kawai na kuma baka hakuri akan rashin da mukayi, da ban matsa ba da hakan bai faru ba inaga".
Shafa kanta yai yace "bkm ke ya kamata na bawa hakuri insha Allah nan kusa zamu Kara samin wani"
Narke masa tai a kirji sai shagwaba take zuba masa, kallona tai tace "Yaya mai take yi anan?"
Hade rai yai yace "muje ki rakani nai wanka in zaki iya bana son damuwa plz"
Wani far tai da ido tace "mai zai hana Mine"
Riko waist dinta yai suka tafi dakin sa, bin bayansa su nai da kallo hawaye yana zubo min, da kyar na lallashi kaina na mike tsaye ina share hawaye na.
Daukar basket din nai na koma part dina, ina zuwa na samu Aunty Bilkisu tazo.
Ajiye basket din nai a dinning na karasa palourn ina kakalo murmushi akan fuskata, durkusawa nai nace "Aunty Bilki ina wuni yasu Nana"
Bina tai da kallo ba tare data amsani ba tace "lafia kike kuwa, Mai ya same ki"
Shiru nai ina kokarin controling kukan da yake neman kwacemin, ganin haka yasa ta kamani muka shiga dakina.
Muna shiga na fada jikinta na fashe da kuka, shiru tai ta dafa ni a hankali tana shafa bayana ba tare data min magana ba, sai da ta bari nayi kukana yadda raina yake so sannan tace "mene ne Batul ban san ki da da ragwanta na ko mai yasa ki wannan kukan nasan babban abu ne"
Ajiyar zuciya na sauke sannan na fada mata duk abinda ya faru na dora da fadin "wallahi Aunty Bilkisu ban sa mata maganin zubar da ciki ba Kuma ni banma san wani magani bane balle nasa, ko fita fa bana yi".
Shiru tai tace "wannan makirci ne kawai ta hada miki Batul, kiyi hakuri kinji ki tashi ki daina bacci kina sallah duk da nasan Alhamdulillah yaya ta hore ku da haka amma ki dage kina kaiwa Allah kukan ki Insha Allah komai zai bayyana, shima ki rabu dashi ki basa iska ki daina wannan nace masa gun ganin dole sai ya saurare ki, a halin da yake ciki ynxu banjin zai saurare ki sbd yana Kan dokin zuciya nasan in gaskia ta bayyana zaiyi nadama sosai".
Daga Kai na nayi ina jin relief, ta dade tana bani shawara sai da taga na kwantar da hankalina sannan ta sani muka fito parlour tare, abinci muka ci tana kara kwantar min da hankali.
Sai bayan Isha'i ta tafi, fitowa nai rakata ina rike da Mimi a hannuna, dan tsayawa mukai tace min "kar ki fadawa Yaya wannan maganar kinji, zata tashi hankalin tane kawai nasani".
Murmushi nai nace "insha Allah Aunty ngd sosai".
Murmushi tai ta dafa kaina tace "Allah yai miki albarka ya warwarw Miki dukkan damuwar ki"
"Ameen" na amsa ina daga Mata hannu.
Sai da ta tafi sannan na juya Zan koma part dina idona ne ya sauka akan sa Yana tsaye a kofar palourn sa ya harde hannun sa, dauke kaina nai kamar ban gansa ba na wuce dakina....
Ban Kara bi ta kansa ba sai washe gari tunda nasan ranar girkina ne, kamar yadda na saba na gyara masa part dinsa na kunna turaren wuta, jera masa abincin sa nai akan dinning.
Daki na koma na shirya cikin simple rigar bacci ta, Hijab nasa dogo bayan nai ma Mimi addu'a yau ban kaita dakin ta ba Qur'ani na kunna mata a Bluetooth speaker na ajiye mata a gefen gadon.
A nutse na tura kofar palourn nasa na shigo yana zaune daga shi sai gajeran wando yana danne danne a system dinsa.
Bai dago ya kalle niba idonsa yana Kan system dinsa yana dannawa.
A gefen kafar sa na zauna a hankali nayi tsamo tsamo kamar wacce aka tsamo a ruwa, kaina a kasa nace "barka da dare"
Bai amsani ba sai da aka dau wajen 5 minutes sannan yace "mai kika zo yi nan?"
Da mamaki nace masa "ban gane ba?"
Ture system din yai ya zuba mun lumtsattun idonsa, cikin hade rai yace "abinda kika ji, mai kika zo yimin part"
Cikin mamakin da ya kasa barina nace "girki nane fa"
Dauke kansa yai yace "daga yau bana bukatar ki a part dina ki daina shigo min plz har sai ni da kaina na neme ki"?
A tsorace nace "ban fahimta sosai ba, na daina girki kake nufi ko me?"
Dage girar sa yai yace "haka nake nufi, ki daina girki kawai bana son ganin fuskar ki plz".
Tunda abin nn ya faru ban taba Jin wani irin bakin ciki irin wannan ba hakan yasa na mike nace "in kai baka bukata ta amma ni ai ina da bukatar Ka ko, ko shima baxan samu ba"
Relaxing yai akan kujerar yace "bana bukata ko zaki tursasa nine, wai tsaya ma tukun don kinga ina sakar miki fuska kin dauka San ki nake", girgiza kai yai yace "ko kadan kawai ina sauke miki hakkin kine amma ba sonki nake ba, naga yadda kike wani kokarin ganin kinyi amfani da son da kike tunanin ina miki kisa na manta abinda ya faru toh ban manta ba".
Wani abu daya tsaya min a rai tun lokacin daya ce baya sona kawai yana sauke hakkin sane na hadiye, wani munafikin murmushi nai ina kallon sa cikin ido nace "Allah sarki ai da yake nima kasan bana sonka ko kadan kawai ina ma biyayya ne sbd ya zama dole da kuma bin umarnin iyaye na, shiyasa nake Kula da kai Ashe kaima ba sona kake ba toh hakan ma daidai ne"(Inji Mrs Umarπππ)
Kan dinning na nufa na tattare flask din abincina na nufi part dina ko Kallonsa ban yiba.
Yana ganin ta fita ya mike da sauri yana nanata kalmar ta a garesa itama wai bata sonsa biyayya kawai take masa ina Wallahi karya take dole ma tana sonsa, kamar wasa maganar ta mugun dakar sa duk ya rasa nutsuwar sa ga shi ta kwashe abincin ta.
Yunwa yake ji sosai amma yaki cin abincin da Mummy ta masa tayi sbd yana tunanin zai ci girkin ta dama plan dinsa shine in yace ta bar masa part sai ya ci abincin ya cika cikinsa ragowar ya fitar da gate man yadda zata ga flask din a gunsa tayi tunanin bai ci abincin ba.....
Ni kuwa dana koma part dina sai da nayi kuka sosai sannan na tayar da sallah, na dade akan dadduma ina karatun Qur'ani kafin na mike ina hamma don wani bacci ne mai mugun karfi ya dauke ni.
Tun daga ranar na watsar da lamarin sa duk da kuwa abin yana raina kuma ba karamin missing dinsa nai ba kawai daure wa nake, ba abinda ya dame ni rayuwa nake cikin nutsuwa.
A kwanakin nan nayi wani irin haske dani kaina tsoro yake ban ga bacci kamar kasa, ko me nake bacci ne yake daukata ga cin abinci bana 30 minutes ba tare da kaga bakina yana motsi ba.
Fitowa nai daga daki ina hamma kamar ba tashi na daga bacci knn fa, Zama nai akan dinning ina zuba tuwon da nasa iya ta tukamun da asuba, sai da naci malmala uku sannan na sha ruwa na mike ina gyatsa.
Palour na koma na zauna akan kujera, dan kwanciya nai ina lumshe idona nan da nn bacci ya dauke ni cikin bacci nai mafarkin Amala.
Ina farkawa kuwa nasa iya ta tukamun alamar, sai na da naci nai nak sannan na kora da zobo mai zanyi.
Har na zauna na mike na shiga kitchen bowl na dauka na kwaba madara da milo na sa zugar da ruwa, Kan dinning na nufa na zauna akai ina sha ina gyada kai sbd dadin da yamin.
Ina cikin sha ya shigo yana sanye da manyan kaya, ta kofar palour ya shigo zuba mata ido yai yana kallonta, 3 weeks knn bai sata a ido ba, ba karamin missing dinta yai ba dauriya kawai yake amma gaba daya ji yake kamar ya zauce.
Yai missing komai nata, abincn ta ita kanta kamshin ta komai ma yayi missing dinsa, rabon part dinsa da gyara tun Wanda tai masa gaba daya komai nasa ya jagwale ga zuwairar sa dake kewar ta sosai.
Zuba mata idonsa yai takaici nakasa ganin ita bata ma damu ba sai kyau da takara da kiba, amma shi har ramewa yai.
Hade rai yai ya karaso dinning din, duk da nasan da shigowar sa sai nayi kamar ban sani ba.
Tsaye yai a kaina ciki ciki yace "baki iya gaisuwa ba"
Banxa nai kamar banji ba sai dangwalo hadin madara ta danai ina kaiwa baki gami da lumshe idona.
A dan tsawace yace "ba magana nake miki ba"
A nutse na kalle sa da fararen idanuna nace "eyya sorry banji ba shiysa Mai kake cewa"
Da mamaki yace "ban gane ba"
Dirowa nai daga kan dinning din ina girgiza jikina da yake ina sanye da Riga da wando ne wanda suka kamani sosai ko ina sai rawa yake tubarkalla.
Cikin yanayin da nasan dole sai yaji a jikinsa na shiga taku ina girgiza jikina cike da wani salo
Hadiyar yawu yai yana Jin yadda zuwairar sa take cewa bata yadda ba sam da abinda ke faruwa, hade rai yai sosai yana matse kafafu yace "bansan iskanci a tunanin ki wannan abin da kike zaki iya seducing dina"
Juyowa nai ina turi kirji na hadi da girgiza su da Azlan baisan lokacin da yace innanillah wa innanillaihir raji'un ba. Kallon sa nai ina kankance ido gami da fito da tongue dina na lashi lips dina cike da wanu salo nace "Ni na isa nayi seducing dinka, ai matar so ce kawai take iya seducing mijin ta koh, sannan ni bani da ra'ayin seducing dinka ma Sam"
Shiru yai don baya son magana ya fallasa kansa, gaba yai kawai yace "ki fito ynxu zamu je gidan Baffa yana neman mu"
Ban amsa masa ba daki kawai na shiga na sako abaya akan kayana, turare na fesa Sama Sama sai da na shiga kitchen na yi packaging snacks a robar takeaway Wanda zanci a hanya kafin na fito ina rataye da jakata a kafada, Mimi dama bata nn tana gidan Mami Mufeeda data zo ta tafi da ita 4 dayz knn.
A mota na same su suna zaune hannun su sakale dana juna, Zeey ta kwantar da Kanta a kafadar sa.
Ban ko kalle suba na shiga back sit, ina Zama na bude takeaway dina na soma ci a hankali ina danna waya ta.
Shiru motar sai sune da suke mgana jefi jefi kasa kasa yadda baxan jiba ko a jikina duk da can kasan raina kishi yana nukurkusa ta amma na daure nai kamar ban san sna yiba.
Wayata da take ringing na kalla bansan lokacin da na saki murmushi ba na dauka, cikin farin cikin daya kasa boyuwa a murya ta nace "Cilla Cilla nawa na amana".
Daga dayan bangaren Cilla ya saki dariya yace "uwar dakina tawa knn".
Dariya nai nace "Allah ya shirya min kai Cilla, ya kk ya Mama".
Murmushi yai yace "tana lafia da uwar dakina, kwana dubu kin buya"
Juya ido nai ina tura katon samosa guda nace "kaine ya buya dai cilla ko a school fa bamu haduwa"
Murmushi yai yace "ai tsoro nake ji kar Oga ya ganmu tare ya balla ni"
Tsaki nai nace "amma ka bani kunya Cilla yaushe Ka fara tsoro haka banda labari Cilla"
Dariya yai yace "A'a uwar dakina ynxu ma na biyo ta unguwar kune shine nace bara na kiraki duk da ba shigowa Zan ba"
Cikin dan mamaki nace kace "Allah kana unguwar mu?"
Dariya ya kyalkyale da ita yace "karya nake wallahi tsokanar ki nake"
Mun dade muna waya dashi sai da muka kusa karasowa sannan mukai sallama, ta mirror na kalli fuskar sa aiko muka hada ido kallo daya zaka masa kagano tsantsar bacin rai akan fuskar sa.
Cikin kishin da be boyu a muryar saba yace "da wa kike waya haka kina dariya"
Cikin nuna halin ko in Kula nace "Cilla ne"
A dage yace "waye kuma cilla"
Gira daya na daga nace "Yayana ne"
A kufule yace "bana son maganar banxa ni kike fadawa yayan kine"
Shiru nai ban masa magana ba kawai sai maida kaina da nayi Kan mirror ina kallon hanya, raina fess ko ba komai nasan ya shafa sosai.
Kwafa yai ganin taki masa magana, bai Kara magana ba har muka isa gidan Baffa.
A tare muka shiga kaina a kasa, bayan mun gaisa na dauka zai yi maganar miscarriage din Mimi amma sai naga sabanin haka sbd nasiha yai mana sosai da kuma kara bamu shawarar mu cigaba da hakuri.
Kallona yai yace "komai dai lafiya ko Batul"
Murmushi nai nace "Alhamdulillah Baffa"
Gyada kai yai yace "Masha Allah, Allah yayi muku albarka gaba daya"
Ameen muka amsa, sannan muka tashi muka fita.
A hanyar mu ta komawa ma ba Wanda yayi ma Dan uwansa magana har muka isa, ban Kula kowa a cikin suba na dau jakata da take away dina a nufi part dina.
Washe gari a gajiye Azlan yake dawowar sa daga company knn, kallon part dinsa yai duk yai Kura ga datti shiba wannan ne damuwar saba ma yunwa ce kawai take damunsa.
Part dn Zeey ya nufa don ta Sama masa abinci kuma tazo ta gyara part din don gaskia kyankyamin sa yake ji.
Ba kowa a Palourn sai ya nufu dakin ta yana kyautata zaton acan zai same ta.
Har ya dora hannun sa akai zai murda yaji maganar Zeey data sashi kamewa a gun.
Cikin shewa Zeey tace "Ai Malika brain dinki yana ja, kinsan cewa ynxu komai yana tafiya according to our plan abinda nake Jira ynxu kawai ya saki shegiar ta Kara gaba".
Gyada kai Malika tai tace "ke an fada miki ni ta wasa ce ai na fada miki dama tunda baki son cikin baki shirya haihuwa ynxu ba kuma shi gogon yana son cikin sosai da shi zamuyi amfani mu cimma manufar mu, gashi ynxu kin zubar da cikin kuma kin netsan tasu da juna".
Ajiyar zuciya Zeey ta sauke tace "bari kawai Aminiya wato ai dama in fada miki tunda na balli maganin kinsan kin fada min dama biyu kawai zansha kuma na tabbatar ina sha zubar da sauran a inda ba wanda zai gani, balla nai na boye a cikin bra dita, inda Allah ya taimake ni ina zuwa na same ta a part din ta kawo masa abinci ai kuwa nace tamin zobo inaso".
Tsaki Malika tai tace "ita kuma shashasha tayi Miki dake bata da wayo".
Tafawa sukai, Zeey tace "eh mana tana kawo min ai na faki idon Yaya na sa maganin a bakina na kora da zobon, kuma na shanye zobon duka kar ma yasha kinga plan dinmu zai rushe ".
Shewa sukai Malika tace "tunda shi asiri baya kamasa ba sai a masa makirci na Mata ba gashi nn komai ya tafi daidai, Ince dai baki fadawa Mummy ba"
Tsaki Zeey tai tace "waya aike ni fada mata ai tunda nace mata kin bani magani na dinga zuba masa a abinci ta dinga min nasiha tun daga nan na daina fada Mata komai".
Tabe baki malika tai tace "kin huta kuwa, ynxu dai shiri zamu yi babba wanda zai sa ya sake ta Su tarkata su tafi ita da shegiar yar ta".
Shiru Zeey tace tace "mai kike ganin zamu yi Mata"
Cikin rashin tsoro tace "sharrin Zina zamu yi Mata kawai"
Banko kofar Azlan yai jikinsa sai rawa yake masa, kallon su yake yama rasa mai zai ce musu, kallon Zainab yai yace "5 minutes kawai na baki ki ficemun daga gida"
Da sauri ta mike tana Dora hannu aka tace "Yaya don Allah kayi hakuri wallahi duk ba laifi na bane Malika ce ta sani".
Hankada ta Malika tai ta kwasa a guje ta fice da part din gaba daya ko takalmi bata tsaya sawa ba.
Kallon Zainab yai yace "na rantse da Allah in kika Kara 5 minutes a gidannan a bakin auren ki", daga haka ya juya ya fice hannun sa rike da kansa.
A zabure ta ja mayafi ta yafa wayar ta kawai ta dauka ta fita daga gidan sai sauri take tana duba wayar ta.......
Shi kuwa Azlan ya dade yana tunano irin abinda ya adinga yiwa Batul da yadda take kuka tana fadin ya yadda da ita ba zata iya aikata abinda yake