Showing 3001 words to 6000 words out of 75434 words
Chapter 2 - FULANIN DAJI COMPLETE Document from Abdallah.txt
kwabe wa joda kayanta daga ita se pant
Blanket tasaka tarufeta dashi hayakin dayajin suka dinga ratsa ta har ruwan yahuce sannan gwggaggo tadauko mata wasu kayan tasaka mata tarufe ta da bargo, taje tadauko kasko da garwashi aciki ta ajiye mata gefe inda tasan bazata shure ba,
Hansai tazo biyawa joda suje talla , gwggaggo ta sanadda ita joda ba lfy, tace gwaggo meke damunta, gwaggo tace yo hansai ai ta tsuniyar gizo bata wuce ta koki, hansai tace oh ni husainatu ko se yaushe wannan shegiyar murar zata sakemun yar uwa,
Gwaggo tace mura kam ai sedai ta mutu da ita Dan tagado ce tin kaka da kakani ansan fulani da mura balantana ma mu damuke fulanin daji, hansai tace to kenan yau bazuwa talla koh?
Gwaggo tace aikodai babu, hansai tace a'a gwaggo yanzu yadda za'ayi ki kawo dawon se nasamu yaro basa nera goma yakai mun kasuwa, gwaggo tace ba ayi haka ba ya zakiyi da sana'a biyu wazai dama miki furar wazai sayadda shinkafar, hansai tace to ai zuba shinkafa ba wuya , kawai ki kawo gwaggo bazan bari kiyi asara ba, Duk yadda gwaggo taso tabar shi amma firrr hansai tace zancen ba , dole gwaggo tabata dawon
A runfar mai shayi tayada zango, habu yace hansai lfy yau ina yar fillo, hansai tace wlh batajin dadi ne, habu yace ayya ki gaida ita Dan allah ba komai zataji
Mahmud yazo yazauna tareda sallamar shi, hansai takarba seda yayi Jim kadan sannan ya tambaya , cewa ko ina joda yau, hansai tace batajin dadi ne , meke damunta Mahmud ya tanbaya? Hansai tace mura ce , ayya kozaki kaini gidanku in dubata, Mey? Hansai ta tanbaya, Mahmud yace cewa nayi ki kaini gidanku in dubata,
Hansai tace kayi hakuri wlh za'a mun fada, Mahmud yace fadan me kuma? Hansai tace kaga mufa ko makwabcin mu ba abari muyi fira dashi, Mahmud yace to nifira nace zanyi dake gidanku nace ki kaini induba yar uwarki
Hansai tace naji babana zaice a ina nasanka kuma ya hanani kula maza sena girma, dafe kansa Yayi ganin yayi gabas tayi yamma, Duk yadda yaso ta fahimta takasa hakan yasa yakyaleta, badan yasoba yau ko furar bai sha ba yayi wucewarsa.........
Muje zuwa
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
9/28/16, 9:37 PM - Queen Safiyyert馃憫: FULANIN DAJI
N@ B aleeyu page 7
Kwanan joda 3 tana famada zazzbin mura, hansai kuwa tacigaba da fita da fura, haka Mahmud yake zuwa gurin kullum Yayi mita har yagaji akan hansai takaishi gidansu joda amma taki dole yahakura
Joda an warware yau tafito tallah duk tarame se laudi take kamar taliya, dama can haka take kamar zata karye, tafe suke suna firar yadda hansai ke gudanarda sana'arta biyu lokaci guda fura da shinkafa kenan,
Hansai tace ke bafa wani wahala , joda tace nagode hansai allah yasaka miki, hansai tace kinyi fa haramun, joda tace menayi kuma na haram? Hansai tace godiyarki mana, joda tace to Dan nayi miki godiya shine haram, hansai tace sosaima kuwa yaushe zaki godemun akan abunda yake wajibi akaina , idan banmiki wazai miki, Miye amfanin abotar mu idan ban taimaka miki ba musamman wannan lokacin dakikafi bukatar taimakon,
Joda tace hakika ke qawa ta gari ce, ba kowace kawa zata gane hakan ba , allah yarbamu tare ameen yarabbi,
Mahmud yayi tagumi yana kallan joda, kanwata kinrame dayawa fa, murmushi tayi tasadda kai kasa, to sarkin kunya zaki fara koh, hansai tace aifa inaga wannan kunyar tata ita zata bata wahala nan gaba, dariya Mahmud yadinga yi, yana mamakin irin yadda suke zance kamar wasu manya, yaran dabasu wuce 13 years ba,
Yau kam yasha fura kusan ta dari, sannan aka dama masa wata yatafi da ita, hansai tacewa joda, joda inagafa Mutumin nan bashida aibu , saboda haka mukaima gwaggo kudin nan inba hakaba wlh zata kidemu tamkar ganga, joda tace so kike gwaggon tawa ta bace ai wlh gwara tadakeni data bace kinaga Yan bunni da akace basa cin abuncin irin namu, amma shi wannan kullum seyasha furata, kofa shi babu
Hansai tace to wlh baruwana idan gwaggo ta dakeki ni zance bansaniba kona gayamata gaskiya, joda tace kada kimun haka hansai, hansai bata saurareta ba tayi wucewarta
Joda kuwa nazuwa gida ta ajiye kwaryar bakin kofar dakin gwaggo tasaka kudin aciki, tashige dakinta tana kuka sanin hukuncin ta, gwaggo nafitowa dakinta taci karo da kwarya bismillahi shine abunda tafada, joda! joda! Tashiga kwala mata kira, lfy kika ajiye mun kwarya a kofa kadan takadani, mtsss yanzu haka fitsari yakorota shine tayadda kwaryar anan
Adakinta tasameta ke bani ragowar kudin in baki ki auno mana dawa yau tuwo zamuyi dumm dumm taji gabanta yafadi , a rude tace gwaggo wlh muna gudu suka zube ahanya, gwaggo tace Mey? Wlh karya kike kwanan hansai ukku tana fita da furar nan amma bata taba batarda ko sisi ba seke koh, wlh yau kasheki zanyi, jin zancen gwaggo kuma tasan halinta zata iya zaneta tsab, yasa tafara kuka da karfi, gwaggo kuwa tafita neman bulala
Jin kukan joda yasa hansai fita aguje har tana tuntube , tana isa tafara Kiran gwaggo gwaggo tsaya nafada miki gaskiya, gwaggo tace oh dama kunsan abunda kukeyi dasu kenan, Hansai tace wlh gwaggo bakashewa muke, gwaggo tace to uwarme kuke Ci dasu, Nan hansai ta warware wa gwaggo komai
Gwaggo kam ta tsorata ainun tace aiko in haka ne kin dena tallar gabadai, bazan yarda kije ya salwantar mun dakeba, joda tafito daga daki tarungume gwaggo tana kuka, gwaggo tace kiyi hakuri yata ai dakin gayamun bazan dakeki tun farko ba, kiyi hakuri kinji bamazaki sake zuwa ba kinji koh, tagyada kai, hansai tace dajin ja a dakeki abanza se tsoron duka amma ba.....bata karasaba joda ta jefamata Dan kwalinta, to kinfada kinji dadi
FULANIN DAJI
N@ B aleeyu page 8
Sanin tanbaya da Mahmud zai mata yasa tacanza gurin zama dukda cike take da kewar joda,
Mahmud kuwa yazo gurin yayi taji ra yaji shiru gashi yau habu mai shayi bai fito ba, dole yahakura Yakoma gida cike da takaici ga yunwar dake da munsa
Joda sundawo daga makarantar allo tana rike da allonta da sauran littattafan ta, hansai tace joda Dan allah mubiya kogin kada muga wasar alkuku, joda Ta ware ido Mey? Wlh kyaje ke kadai nikam ba inda zanje kada yacinyeni, hansai tabata fuska kefa shegen tsoro ne dake daga kallo mezai kaimu aciki ne, Kinga tafiyata inbaki zuwa,
Joda ganin ran kawarta yabaci yasa tace to muje nidai amma wlh bazamu dadeba kinsan yau baffa na gida, hansai tawa she baki ai bazamu dade ba yanzu zamu dawo
Suna isa bakin kogin suka samu gefe guda saman dutse suka rakube suna kallan wasa, joda se juye juye take, ita duk tsoro takeji ga gurin da shegen sanyi , ita bawani kayan kirki tasaka ba, kayan fulani ne ajikinta ko mayafi babu tini tafara rawar dari, Nan danan tafara sneez, takalli hansai taga ita ko ajikinta, tace hansai mubar nan gurin allah gabana kefaduwa kuma kinga munyi nesa da masu wasar nan kada majici yazo, hansai tace aike illata dake shegen tsoron tsiya ne dake wlh, joda tace nidai natafi sanyi nakeji,
Dole hansai ta tashi tabita suka bi hanya koda suka zaga maza suncika gurin, dole suka koma bin hanyar baya inda babu taron mutane tafe suke joda na rawar dari hakoranta se bugun juna suke,
Hansai ce gaba joda baya, Wata hanya suka bullah mai shegen duwatsu manya2 dasu, hansai tace lah kinga joda daga munbi can se dajin damuke kiyo, aiko ma wannan tafi sauri wlh, joda dai ba tace komai ba se biyar ta take, can taji ta taka tasaya tace hansai na taka kaya fa zoki cire mun, hansai tazo tace kai yabakiyi kuka ba kayar babba cefa kuma ta shugeki , joda tayi tsaki dallah kici remun in zaki iya
Hansai taja dakarfi , Wata guguwa ta taso gurin kura tacika musu ido iska yadauki hansai sekan dutse kanta yabugu, joda kuwa mulmula tadinga yi hartakai gab da wani icce tarike shi gam tana, wayyo allah na kutaimakeni, hansai kuwa tana tasaki tasaka kuka dab bataga joda ba, can tadinga jin ihunta, dasauri taleka taga joda gab da ruwa ga kada can a gefe se bude baki take, tuni itama tasaka ihu
Ahmed dake gefen ruwan yana kallan Su duk haushi yacika shi, to inba iskanci ba meyakawo mata a kogin gurin da maza ke zuwa, abun haushi ma yadda suka cika gurin da ihu , karar da aka saki sakice yadawo dashi daga tunanin dayake dubawa da zaiyi ne yaga har tafada ruwan itakuma waccan mahaukaciyar se hauka take, acewarsa itakuma hansai ganin kada tayo kan joda babu ko tantama cinyeta zatayi
Dogon Tsaki yaja ganin irin ihun dasuke domin idan da abunda ya tsana baiwuce hayaniya ba musamman ma na mace ,kai mata jakai ne wlh mtssss , , , , nikuma asea nace harda uwarka
Gun naga yajanyo a aljihun rigarsa , yasaita dai2 kadar yahalba toni gurin yadau wani irin ruri nikaina seda na tsorata irin yadda kadar ke fitar da iska tareda wani ruri kamar ana kidan ganga sekuma ta tarwatse lokaci guda
Jacket dinshi yacire, yafada ruwan kai lallai Ahmed ya iya ruwa nibanma gansa ba yanutse a ruwan se can nahangosa yadauko joda tamkar gawa, sekuma yasake nutsewa, nemansa nake wai sai gashi agabana har yafito rungume da ita fuskarta acikin kirjinsa duk ta dungule da alama tasuma dakyar ya ban bareta ajikinsa duk ta San kare tsaki yasaki ganin duk tabata masa farar riga da shegen Jan bakin ta jacket dinshi yadauko yasaka mata
yajuya zai wuce kenan yaji kamar anrike masa hannu juyowar da zaiyi yaga ashe sarkar dake kan kunkurunta ce tasarkeshi janta yayi dakarki base gata tawatse ba , haushi duk yakama shi yawuce yadauko wayarsa da glass dinsa yawuce abunsa
Hansai taleka taga yabace tafito dagudu tazaga ya gurin da ya ajiye joda, ta aza kunneta kan cikinta taji tana Dan sheda kadan2, Alhamdulillah tace, sekuma ta tashi dagudu bata tsaya ko inaba se bakin kasuwa ta taro mai jaki , suka aza joda saman jakin suka yi gida da ita,
Suna isa kofar gidan tace ma jakin yashiga, gwaggo na surfen dawa taji kamar takun dabba dagowar dazatayi ne taga joda ajikin jaki, ai batasan randa tasaki tabarya ba tana subhanallah lfy hansai meya sameta, hansai tace gwaggo sauketa ,
gwaggo tasauketa takai ta daki hansai tace gwaggo bani nera ashirin in bashi , gwaggo ta kwance zaninta tabata, hansai tamika masa yayi godiya yawuce.......
FULANIN DAJI
N@ B aleeyu 9 page
Gwaggo tace hansai nifa banganeba meya sameta ne dubi yanda naganta duk gashin jikinta atashe gashi gabanta se faduwa yake kamar ma a some take, meyasameta naga jikinta duk ruwa ne kasan kafarta jini ??????
Hansai tafashe da kuka gwaggo tajanyota har tayi shiru sannan tagaya ma gwaggo abunda yafaru, takara dacewa ni dama ina tsoron wannan yaron Mahmud daganinsa bayahude ne, gwaggo kinga yadda yabidda bunduga (bindina) ya kashe kadar nan kwarankwatsa idan kikaji yanda tayi wani gurnani, gwaggo tace aikuwa duk dajin nan ba inda ba'aji ba,
Hansai tace kinsanme gwaggo wlh yanda yayi tsallen kwado yafada ruwa shike bani mamaki nutsewa fa yake a cikin ruwan tamkar kifi , gwaggo tasa dariya, tace nidai allah Yayi muku tsari da wannan bayahuden yaron ameen
Gwaggo tacanza ma joda tufafi ta hada mata ruwan wanka tareda ganyayyaki aciki tagasata sosai sannan kuma ta saka garwashi adakin, hansai taki komawa gida gefen kadon karan joda tazauna tana ta addua allah yasa kar murar joda ta tashi,
Joda ta warware sedai yar mura dake damunta gakuma yawan firgita datake yi data kwanta seta tuno wannan Ahmed din bakomai take tunawa ba irin yadda Yayi tsalle kamar aljani yanzu ko zata rufe idonta idan taga hakan
Hansai kam tadena fita tallah acewarta tsoron take tahadu da makashin nan, Mahmud yayi sintiri har yagaji baigansu ba, dole yahakura, Gashi sunkusa komawa tinda dama 2weeks ne zasuyi yanzu sunyi kwana goma
Ahmed kuwa yana zuwa gida yacire kayan jikinsa ya shanya Su wanka yasake yi yafi awa yana darzar jikinsa acewarsa yatabi najasa, domin kauyawa nazajasa ne agurinsa musamman ma wadannan na daji gwanda kauyawa da Su,
Mahmud dai yagaji da sintirin gurin yatanbayi mai shayi koya San gidan Su joda, mai shayi yayo masa kwtancen dukda baiganeba yace yagode, yabi hanyar gidan yana tanbaya abun mamaki duk Wanda ya hadu dashi se yaga suna guduwa, shi azatonsa duk kauyancinne
Nanko baisan kayan dake jikinsa suke tsoro ba, wato soldiers uniform dinshi, dayake ma farar riga yasaka wandon ne kadai na soldiers se hula, hansai yahango, wani farinciki yaji ya lullubesa yakarasa kanta yana cemata to gani a gidanku ay gidanku ba zaiyi wuyar ganewa ba tinda duka dajin nan ba kuyi 5 hundred ba,
Hansai tace Dan allah kada ka kasheni wlh banmaka komai ba, Shiru Yayi yana kallanta da mamaki in kasheki mekika yimun ko ance muki ni makashi ne,
Hansai tace nidai Dan allah kada harbeni kamar yanda ka harbi kadar nan ajiya, Mahmud yace wai mafarki kike kome kinga inane gidansu joda , tace wlh baxan nuna maba ka kasheta ay nasan ji yama ita kaso kashewa seka harbi kada wato kaga munki cin kudinka mubace koh mugu kawai
Ana haka Sega baffa yadawo dauke da kara yace hansai lfy naga kinyi narai2 da ido, ta nuna masa Mahmud, atake yace innalillahi wa inna ilaihir rajiun, yaro lfy meya kawo mana makashi anan
Mahmud ya mai mata makashi kuma? Se alokacin yatuna kayan dake jikinsa, Yace I'm so sorry dady, baffa yace ce maka akayi munajin wannan yaren naku na ya hudu da nasara,
Mahmud yasosa kai yi hakuri baba, yanzu duk ba wannan ba naxo duba joda ne inji ko lfy kwana biyu nadena ganinta kasuwa, baffa yace ai kafi kowa sanin halinda take ciki kazo kuma yanzu kana tanbayar mu,
Kaga mungode da taimakon da kayi mata Dan girman allah kayi tafi yarka, muba muyi yi muku komai ba kinzo kina wani zanse can nadaban, se a lokacin Mahmud yalura da yadda suke duminsu, abun ma seya bashi dariya
Ganin yadda Mahmud ke dariya yasa baba yin maza yasaka hansai cikin gidan yarufe ganbun........
Muje zuwa
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
9/28/16, 9:37 PM - Queen Safiyyert馃憫: 馃巹 FULANIN DAJI 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹
馃巹
N@ B aleeyu 馃挄 page 1鈨�0鈨�
Ahmed mura yakama shi sosai har ba'a jin zancen sa, sneez yake tamkar bunsuru 馃槀 , ga zazzabi yarufesa sosai, aransa kuwa allah ya isa ya keyiwa joda shegiyar bafulatana, natabbatarda sneez dinda take ne lokacin dana daukota aruwa shine ya shafeni ta likamun ciyon Su shaggun fulani, kuji Ahmed to waya saka dole ne 馃槒
Mahmud yashigo dakin da sallama bai amsaba dama kuma haka halinsa yake, tsaye yayi ganinsa acikin blanket, kafada yadaga , mutun kullum a kwance tamkar ruwa tsaki yaja yayi ficewarsa,
Tea yahada mai kauri yasha tareda cake , yagama sha yadauko system dinshi yana dubawa, wani video yaga ana forward na wasu terro a garin bauchi , yafara Kiran Ahmed! Ahmed! Zokaga Dan allah jin shirun Yayi yawa ko motsi baiga yanayi ba, yasa shi ajiye system din, yaje ya yaye masa bargon da yayi rufa dashi, gwale idonsa yayi ganin yadda Ahmed ke rawar dari gakuma hakoransa se haduwa suke da juna bai kara rudewa ba seda yakai hannun sa kan Ahmed yaji zafi radau gakuma jijiyoyin kansa se bugawa suke,
Subhanallah meyasameka man, Ahmed yakasa amsawa se kansa dayake nuna masa, ga atishawar data damesa dakuma Tari , Mahmud dafe kansa Yayi , mezanyi yanzu naji yafada, kome yatuna, naga yazubura da karfi, yadauko bag dinsu duk ya watse kayan amma baiga abunda yake ne maba,
Yanzu idan nakira gida zan tada hankalin Dadyn Ahmed da kuma kanwarsa Hafsa, to yazanyi wannan serious sick ne abunda yakai man kawance aiba karamun abu bane,
Fita yayi yabi hanyar kasuwa, har yakai cikin kasuwar ya tsaya yana tambayar ko akwai inda ake sayadda magani duk Wanda ya tanbaya dariyar sa suke, domin Su kowa shi yake yiwa kansa magani dakansa, dkyar yasamu wani tsoho yayi musa kwatancen wani gida yace nan ne a kullum baza arasa magani ba kowanne iri, Yace Dan allah baba kataimaka muje tare, bazan gane ba gidajen kamar iri daya ne,
Haka kuwa akayi tsoho yarakashi har bakin gidan, zai wuce ne Mahmud yace baba nagode amma kozaka iya mun sallama da mai gidan, tsoho yace mushiga bakomai gidan aminina ne, suka shiga da sallamar Su, gwaggo ta karba tace musu ai baffa yatafi daji , tsoho yace aidama gurinki mukazo, gurina kuma inji gwaggo? Tsoho yace ehh wannan yaron bakin dajin nan ne inaga daga bunni suke, magani yake tambaya nace bari na kawo shi nan kozai samu,
Gwaggo tadubesa da kyau tace wannan ai bayahude ne koh? Mahmud yayi murmushi yace inna nifa musulmi ne kesan mu Yan birni munada banbanci daku, amma kudena kiranmu yahudu, yahudawa fa, ba musulmai bane, gwaggo tasosa kai, tace to wane magani kake nema, Mahmud yace na mura da zazzabi da ciyon kai, gwaggo tayi dariya tace to ay duka ciyon guda ne murar Itake haifar da zazzabi da ciyon kai kafahimta , Mahmud yace ehh,
Gwaggo ta hura wuta dayake wutar karace nan da nan wutar ta ruru, ganyen shayi ta aza tareda citta da yaji da kaninfari , suka tafasa tajuye acikin wani kwano, inazuwa tace,