Showing 15001 words to 18000 words out of 75434 words

Chapter 6 - FULANIN DAJI COMPLETE Document from Abdallah.txt

08 Oct 2024

30106

yarda da kowa ba,


馃巹FULANIN DAJI 馃巹
N@ B aleeyu 馃挄 page 2鈨�3鈨�
Matar tayago masa da malt tamikawa gwaggo tace yar uwa ungo bismillah, gwaggo cike da fargaba tace a'a mungode, matar tace hava keko ba a maida hannun alkhairi baya, dole gwaggo ta karba tabawa joda cikin sauri kuwa joda tacinye Su tass,


Matar tace boyar allah meyasa baki siyama yarki abinci ba bayan kinsan tanajin yunwa, gwaggo tace toya zamuyi tunda yn kudin mu ba yawa ne dasu ba, matar tace to yanzu ina zaku, gwaggo tace munfito neman na kanmu ne


Matar tace idan na fahimta aiki kike nema ko muhallin zama, gwaggo tace ehh, matar tace bakida matsala da wannan ni dinnan yara da manya nake daukowa a kauye na kaisu gurin aiki garuruwa za abaki muhalli mai kyau iyakacinki kiyi goge2 ko kuma wanke2 da sauransu inkuma kin iya girkin zamani shikenan, amma da alama se an gyara ku akwai dinbin kauyanci acikinku,


Gwaggo tace indai zamu Ci musha da muhalli to wlh komi nene zamuyi bama bukatar ko sisi indai muna da wadannan ababen, matar tace inafa dole in wata yayi abiyaku naku salary din, gwaggo tace ina ruwan riba goma


Haka dai suka cigaba da fira har Suka isa kaduna, matar takirga kudin gwaggo tacika mata tabiya ta tajata tace zo muje gidana ,haka kuwa akayi suka tare taxi se gidan matar gidane babba mai kyau, Filin gidan kadai yana wani gida ga mota kusan ukku acikin gidan , har parlour Suka je, matar tace kuzauna ina zuwa , wanka tayi tacanza sutura sannan tafito takawo musu ruwa da abinci dakyar suke cin abuncin saboda basu sababa , seda ta tabbatar sun koshi sannan tace subiyota ta nuna musu masaukinsu,


Katon daki takaisu ciki mai katuwar katifa tashiga nuna musu abubuwan yadda suke toilet tashiga dasu tana nuna musu yadda ake amfani da komai Gwaggo kam imani yakamata joda kuwa ta matso safiya tawaye taje toilet din wani dadi yakamata jin ta bisa kaifa mai shegen laushi, ga bargo suyi rufa, salloli sukayi sannan suka kira safiya


Karfe bakwai matar tashigo tasamesu har sun tashi sukayi mata ina kwana gwaggo nata dada godiya, matar tace bakomai ay yiwa kaine ni sunana hjy binta inada miji yana abuja gurin wani aiki dana guda salim yana America gurin karatu, gwaggo tace allah yabarku da mai gidanki yakara zaman lfy ameen, hjy binta tace joda kinyi brush kuwa, joda tayi shiru Menene brush kuma hjy binta tace zo kiga tajata se toilet tazuba mata colgate a brush sannan tabata tace kinga yadda zakiyi tanata nuna mata kafin tafito kam rigarta sharkaf da ruwa


Joda tace gwaggo kinsan abunnan danayiwa hakorana allah dadi ne dashi kamar minti yake, nikuma se tsotsewa nake, gwaggo tace to uwar kwadayi, hjy binta takawo musu tufafi joda kuwa nata duk kananan kaya ne, se dadi takeji ita ke nuna mata yadda ake sakawa da yadda ake cirewa


Ahankali take nuna musu abubuwan zamani, yanzu dai sundan rage tsoro da kyauyanci, tinda har TV suke kallo lfy lau, hjy binta kuwa batayi kasa a gwiya ba tacigaba da wayar musu dakai seda ta tabbatar yanzu basuda matsala da komai sannan tashiga nuna musu yadda gyaran gida da yadda ake tsara parlour sundau kusan wata tana nuna musu abubuwa asara kam tashata agun joda saboda joda akwai barna kamar mage haka take


Yanzu suna kan girki ne tinkan Su semo har zuwa abuncin zamani yanzu komai sun iya itada joda wata biyu kenan, hjy binta tace to gwaggo yanzu ko yaushe zaku iya barin gidannan saboda yanzu nasan kun kware akowani fanni sannan kuma ni kunga tafiya zanyi so kafin in wuce zan nemo muku gidan aiki mai mutunci joda tace hjy mu munfi son zama dake kinfi kowa kirki aduniya hjy binta ta kyalkyale da dariya tace injiwa keko joda har wanda suka fini akwai


Ahmed zaune a garden yana shan iska yana kallon tsuntsayen dake wasa agurin zuciyarshi fall, gefensa tire ne shike da kayan marnari, kamar ance duba ya waiga bayan sa mezai gani, amina ce sanye da base iya cibiyarta se wando baiwuce gwiwarta ba, rike da kujerar roba zata shiga ruwa, baki yasaki yana kallanta Keee yadaka mata tsawa, seda ta tsorata Dan batama San yana gidan ba


Wani irin iskanci ne zaki zauna ma mutane tsirara haka, Nan gidan kine ko dakin ki, amina tace to naga dai ai bamai shigo mana gida, Ahmed yamike tsaye zanci ubanki wlh, muba maxa bane ko angaya miki yahallata ko uwarki taganki ahaka ballantana mu maza


Amina ta murguda baki Kaji dashi can tafada cikin ruwa se ihu take, Ahmed yafusata ainun, ya zare belt dinsa ya nufi swimming pool din hannu sa yazura yacabko gashinta tuni tabuga ihu kafarsa yasa yabuge mata baki seda yamata liss sannan yabarta agurin


馃巹 FULANIN DAJI 馃巹
N@ B aleeyu 馃挄 page 2鈨�4鈨�
Hjy binta tashiga tunanin inda zata kai Su gwaggo batareda sun takura ba gidan dai da bataso dole can zata kaisu, tagayamusu Su shirya zasuje gidan aikinsu ba musu suka shirya tin safe bayan sunkarya suka dau hanyar abj , hjy binta tayi horn mai gadi yabude gate din saboda yasanta bata bukatar wani bincike akai,


A parlour Suka yada zango, hjy binta tadauko wayarta takira hjyr gidan, amma kafun tafito sunfi karfin minti talatin, sanye yake cikin riga red se wando 3 Q yasan ya Farin glass hannunsa rike da system yafito daga dakinsa,


Hjy binta tace a'a Ahmed na baida go fuskar shiba seda yakai bakin kofa sannan yace ehh, tace ygd yakaratu, cike da haushin tambayoyin yace lfy, batareda yajira wani que ba yafice , gwaggo tace wannan kuma fa, ?Hjy binta tace dansu ne shine babba, gwaggo tace to allah yakauta, ameen


Hjy tafito se wani dagawa take tasamu guri tazauna, tace hjy binta yagari , hjy binta tace lfy lau, hjy dama bawani abu bane yazo dani wadannan dakike gani baki ne daga daji suka fito kuma mijinta yarasu bada dewaba amota na hadu dasu zuwa zauna gurina kusan wata biyu da Yan Kwanaki zuwa yanzu sun waye suna iya kowane ayki na gida, shine nakawo miki Su ko akwai bukatar Yan aiki nan gidan,


Hjy tace no binta bana bukatar Yan aiki wadanda ma ke gidan wlh sun isheni, binta tace to hjy kozasu zauna gunki ne kafin in dawo daga zaria, hjy tace binta bana mgn biyu fa, hafsa dake saukowa downstairs duk taji abunda suke tattaunawa, taje tasame Ahmed tamasa bayani yace tomezan musu ne kiji ance fulanin daji ne me zamuyi dasu ne, Hafsa tace yaya taimako nefa kuma binta tace data dawo inba ma bukatar Su zata koma da abunta


Ahmed yace Hafsa stay away 4rm here, hafsa da takaici yacikata garden dinsu kawai tawuce cike da takaicin halin yayanta, Ahmed kuwa glass dinsa yasaka ya nufi parlour din hjy nazaune tabawa TV amana, Yace lfy wadannan kuwa? Hjy tace aiki suke nema kuma bama bukata munada isassun ma'aikata, Ahmed yace wannan ba kawar ummah bace, binta tace ehh nice Ahmed ashe zaka shaida ni, Ahmed yace kije kawai za'a basu ai kinyi, binta tace nagode sosai Ahmed allah yaji kan mahaifiyarka ameen


Hjy tace yazance bana bukatar Yan aiki sannan kuma kadaukesu, Ahmed cike dagadara yace kozaki hana ne nan gidan ubana ne inada right din duk abunda nakeso , hjy tace kai kake da wannan right amma sauran basuda shi, Ahmed yace zaku iya jira inkira kanwata tamuku masauki kunjiko , se a lokacin joda tadago fuskar ta takalle shi, 馃槼 Iye makashi tuni ta kwala ihu, Ahmed yadafe kunnuwansa dajin wannan ihun abunda ya tsana hanyar dakinsa yayi se faman tsaki yake


Binta tace lfy ke joda gwaggo tashiga jijjigata ke lfy, tace gwaggo wlh mubar nan gidan, gidan makashi ne shine Wanda yakashe kada aruwa shine Wanda ya harbi ganbun mota kadan in mutu, binta tace kai joda akwai shiririta wlh yoshe akayi haka wanda baya ko fita kullum yana dakin shi in kuwa ki ganshi yafita Tokuwa gurin aiki zashi, dole joda tayi shiru cike da tsoron zama agidan,


Hjy tabar parlour tayi dakinta, ba'ajimaba Sega Hafsa tafito, Lah inna kece dama gwaggo tace nan ne garinku dama, hafsa tace sosai nanma gidanmu ne ina joda, Gwaggo tace ta fita tayo fitsari, Sega ta kuwa ihu tasaki taje gurin Hafsa tace yar uwa, hafsa tace ashe allah zaiyi mugamu , hjy binta tayi musu sallama tawuce cike da jin dadi Dan tasan Hafsa akwai kirki


Seda Suka sha fira sannan Hafsa ta fita dasu zuwa sashin masu aiki tanuna musu masaukinsu, sannan takoma dakinta ,dasafe tazo tanbayar Su abunda suka iya koda ta gwada Su sunsan abubuwa da dama, tayi matukar mamakin ganin yadda suka Dan rage hauka da kauyanci


Joda ita ke taya mai gyaran gidan aiki gwaggo kuwa kitchen takebin mai aiki suyi tare, kwarai da gaske suke jin dadin zama da gwaggo saboda batada kissa ko kadan komai tsakani da allah take yinsa,


Tin ranar joda batasake ganin Ahmed ba sedai tayi ta jin kamshin sa idan yabi ahanya , kullum da jacket dinshi take kwana ko ana zafi seta sakata take iya bacci itama kuma Batasan dalilin hakan ba, tofah jama'a kuji joda meke damunta ne oho 馃槦


Muje zuwa 馃巹
ASEEYAH BASHEER ALEEYU 馃挄
9/28/16, 9:37 PM - Queen Safiyyert馃憫: 馃巹 FULANIN DAJI 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹 馃巹
馃巹 馃巹
馃巹
N@ B aleeyu 馃挄 page 2鈨�5鈨�
Joda har ansaba da gida ko ina shiga take har cikin parlour abunda sauran masu aiki basayi, hafsa tasa ta ajiki sosai, haka zata yi tadibar kayanta tana bawa joda , Yauma kamar kullum tafito daga kitchen tanata wake2 abunta hanunta rike abunci, karab taji taci karo da mutum, gabanta yashiga dukan 3 Dan koba ta dagoba tasan ko waye , tsawa yadaka mata keeee mahaukaciyar inace kina gani kin takani kuma kin wani tsayawa sororo , jikinta yashiga bari tace Dan allah kayi hakuri wlh banganiba, mari taji mai kyau, to ubanwa zai goge mun talkamina,


Dasauri tacire Dan kwalinta tashiga goge masa kafarsa bata ankaraba tashar awa wandonsa manja, yana dubawa yace bura uba wlh sena karya yarinyar nan, jikinta yakara bari tafara kuka, tashi tayi zata gudu taji ancabko gashin ta, kalansa take ido cikin ido, Yace ni zaki yiwa iskanci shin waima ubanwa yakawoki nan gidan shegiya mai fuskar jaba, joda tace Dan allah kayi hakuri ba a kaine ka karbemu aiki ba, yakara fusata, Dan ubanki yaushe kika taba ganina, yawulgata dakarfi, se asamam kafar wani


Durkushewa tayi tana kuka cikin muryar Su ta fulani tace Dan allah kiyi hakuri wlh bada gayya namiki hakan ba, wanda tafada kan kafarshi yadagota idonta arufe yake tana hawaye jikinta se karkarwa yake, joda kuwa seta rike masa hannu, tana Dan allah kayi hakuri, abunda ya tsana kenan kalmar hakuri, Tasake cewa dan allah fah nace, wanda tarike yadaka mata tsawa you shout up, dagowa tayi tana kallan sa tuni ta ware ido ganinsa cikin kayan soldiers, ubanwa yabaki izinin shigowa parlour nan, Iye, mari yakai mata ba dake nake mgn ba, kucakar banza, hannunta yacire kan nasa, seyaga ta Su lale ashe har tasuma, tsaki yaja ya tsallake ta yawuce,


Abdallah yace kai tafa suma, Ahmed cike da tsanar zancen yace to mezan mata, abdallah yace tsawar dakamata ne kana abu se kace wani lion, Ahmed yace shine ai, yayi gaba abunsa, abdallah yadauko ruwa a fridge yazuba mata, ahankali tabude idonta , tana ganin sa tamaza tarufe, abdallah yace kuji shegiyar yarinya to ai sekiyi ta, rufewa ya hankadata yawuce sama ,


Ahmed kuwa tubewa yayi yasaka jallabiya zai shiga wanka kome yatuna sekuma yafito dasauri, a parlour yasameta ta kudundume guri guda se rawar dari take, Yace kee wai nan parlon ubanki ne da bazaki fita ba, joda takara matse jikinta, tadanne kunnuwata, abun se yakara fusata tashi , wato bata son jin zancensa kenan, Yace kee wlh zan karyaki kibar nan parlon nace, rerafe tadinga yi har takai bakin kofa sannan tawazga aguje se dakinsu tafada kan gado tana cigaba da rawar dari,


Hafsa tadawo daga islamiyya tabiya dakinsu joda, a parlour tasamu gwaggo tana yiwa husaina kitso, tace inna ina JODA taje, inna tace kishi ga daga ciki, Asaman gado tasameta ta yaye bargon ke lfynki kuwa, joda tace zazzabi kedamuna, hafsa tace Ayya sannu kinsha magani kuwa , joda tace a'a Hafsa tace to bara nakawo miki mgn kinji koh,


dakin Ahmed tashiga tayi sallama yabata izinin shigowa dakin, kan gado tasamesa kwance yana shan wakar Kenny G , tace bros maganin zazzabi zaka bani, kina zazzabi ne? tace no bros joda ce ba lfy, Yace you get out banasan renen hankali, tace bros yarinyar daka..... Ahmed you yadaka mata tsawa shout up , bana bukatar sanin kowacce magani bazan bayar ba dz oll


Hafsa tafita daga dakin cike da haushi batama koma dakinsu joda ba, sallah tayi tayi wanka tasake kaya sannan tasauko kasa danyin lunch, amina na kan 3 star tana kallon star movies , tawuce ta ta hau dining tazuba crab cakes da honeydew peach cooler, tana ci cike dajin dadin abincin, tace amina wlh duk zaman husaina mai girki bata taba mana irin wannan ba, amina tace to waya tanbayeki da iskanci


Hafsa tace kece da iskanci wlh daga magana zakice mun da iskanci, amina ta taso ni kike gayawa mgn, hafsa tace angaya miki tsoronki nake, tuni hafsa takai mata mari abaki bata sauke hannunta ba, hafsa takai mata nanko fada yakaure atsakaninsu,


Ahmed dake son yin bacci yahaniyarsu ta tada shi, fusace yafito rike da belt, turus yayi ganin Su hafsa na danbe , yadunfaresu tuni hafsa ta sake amina tayi hanyar waje tsalle daya yayi yacabkota yashiga zuba mata belt Dan ubanku da girmanku zakuyimana danbe agida Iye seda yamata liss sannan yabi amina da tun tuni tayi sama tasakama dakin hjy key


Hjy tace ke lfy kika fado mun daki ko sallama babu, amina da idonta keta wani wuki2 tace bros Ahmed ne zai dakeni, hjy tace to me kika masa ne? Amina tace wai yar iskar kanwar shi ce take gayamun mgn nikuma na bibbigeta shine zai dakeni itama yazaneta, hjy tace to ai kinmun dai2 kada kitaba yarda taranaki.........


馃巹 FULANIN DAJI 馃巹
N@ B aleeyu 馃挄 page 2鈨�6鈨�
Ganbun dakin aka bugo dakarfi bugu daya yayi masa da kafarshi amma yabude se huci yake , hjy tace wlh karka kuskura kayaba mun yarinya, cike da tsana yake kallonta koke idan kika kara mun zan dakeki balantana yarki, ke kuma ki kawo kanki inda keki inba hakaba wlh idan nakamoki da hannuna senayi miki wanda yafi wanda nayi niyyar miki, komawa tayi bayan hjy tana hararanshi,


Ahmed yadunfaresu, hjy takara tareda mike hannayenta, Ahmed yace kijace wlh ko in hada dake, hjy da ranta yagama baci tace shege kake idan baka dakeni ba, tuni Ahmed yacabko ta tareda wulgata se kan gado yajanyo amina yashiga dukanta tin tana kuka har takasayi sannan ya yada belt yawuce yabarsu,


hjy tayi ta kururuwa har tagaji, daga karshe tadauko phone takira abdallah ta tsara masa karya da gaskiya, abdallah kuwa yana zana wata exam baisan tym dinda ya yaga papers dinba yabar hall din dasauri baima tsaya Jan mota ba yahau Dan achaba yana zuwa gidan yabude ganbun parlour dakarfi, can gefe ya hango hafsa na kuka bakinta se jini yake, yabuga tsaki yawuce wato ko kanwarshi bai bariba, tun kan ya isa yakejin kukan amina


Rungume da hjy yasameta tana kuka, abdallah yace hjy tell me meya miki hadda ke yadaka, amina tashare kwalla wlh bros hadda ita yayita zuba mata belt, abdallah yace to wlh yau gidannan za'ayi kashin kai , hjy tace look son kada kayi fada dashi wlh kasan yadda zuciyarshi take tamkar ta kafiri wlh zai iya illata mun kai abdallah yace komai zai faru sedai yafaru amma wlh ba shegen daya isa yataba uwata yakwana lfy


Fita yayi daga dakin yadum fare dakin Ahmed amma me seyaji kofar a kulle haushi duk yaci kashi juyowar da zaiyi yaci karo da dad dinsu, dad yarike kuqu yace kayo shan ne shi isa naga kazo zaka ballamasa kofa , abdallah yace dad bansha komai ba amma wlh za'ayi kashin kai agidan nan, dad yace subhanallah Abdullahi mekake fada haka, abdallah yace yes dad , Ahmed yace shege kafasa nida kai , dukansu suka juya suna kallonsa yafito daga kitchen rike da cup din coffee,


Abdallah yadunfaresa, Ahmed ya ajiye cup din coffee, yatartara hannun rigarsa , dad yace muhammad kada kasoma kaima Abdullahi kada ka fara wlh dukanku zan sabamuku kusameni after magrib, dukansu kowa yakama gabansa, hafsa kuwa tana tashi taje tahada ruwan zafi taga sa jikinta, se baccin wahala, amina kuwa ruwa hjy tahada da towel tagasa mata jikinta tahada mata tea tasha sannan tasauya mata kaya


Bayan magrib dad yabukaci ganin Ahmed da abdallah , yadau few minutes sannan yace, Abdullahi lfy kake neman fada da yayanka abunda baka saba yiba ? Abdallah yace katanbiyesa mana , dad yadaka masa tsawa, naki na tambiyesa kai dashi wanagani , abdallah yace dad ya za'a yi ace wai Ahmed yana dukan uwata ina raye in kyale ai wlh bazai yuba , dad yace ya isa kai muhammad meyafaru


Ahmed yazayyane ma dad komai yakara dacewa, dad idan yayi yunkurin tabani da sunan wai zaiyi danbe dani, am so sorry ku kunsan abunda zan iya yi dawanda bazan iyaba yana kai nan yafita dad yace muhammad na sallameka ne, Ahmed yace sorry dad ina bukatar hutu ne idan inajin wadannan abubuwan komai zai iya faruwa so allah ya huci zuciyarka , abdallah yace ahaka dad za kace mun yafini kirki dubi yadda yake gaya maka mgn sekace.......dad yace ina ruwanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login