Showing 42001 words to 45000 words out of 165076 words

Chapter 15 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt

05 Nov 2024

74007

tsugunno na Matan aure kad’ai)_
_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_


_Muna Gyaran jiki_
_Na amare_
_Da masu jego_
_Da sabulai masu gyara fata_
_Turaren tsugunno_
_zumar goran tula_
_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_


_Akwaisu kujeran tsugunno
_Dilke and halwa set_
_Burners da igniters da tong_
_turaren fesawa dana ruwa._
_wardrobe balls_
_scented pebbles_
_cotton wooly oudi incense_
_kabbasas_




_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_


_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_


_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*


_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_


_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.
100% TESTED AND TRUSTED_


••••••••••••••••••••••••••••••••




*_Chapter Fifteen_*


.........Kamar yanda doctor Bilal ya faɗa a ranar suka sallami Ummi tare da sharuɗan da za'a kiyaye game da lafiyarta. Su Yaya Abubakar sun amsa masa tare da tabbatarwa. Wannan ɗin ma akasi aka samu kawai. Da ga haka sukai masa godiya suka tafi da sanyin idaniyarsu gida.
Koda suka isa gidan babu wanda yayma Ummi zancen Abbah, hasalima su sun manta ma. Hidimarsu suka cigaba da yi hankali kwance har dare. Sai da zasu kwanta ne Ummi taji shirun gidan yayi yawa take tambayar Hibbah data maƙale a ɗakinta zata kwana. Bargo Hibbah taja har saman kanta tana sake bajewa a gadon na Ummi. “Ummi nima ban saniba. Ƙila sunje ƙauye ne”.
Shiru Ummi tai tana nazari, tasan Momy ko kowa zaije ƙauye ita dai bazataje ba. Hakama ƴammatan ƴaƴanta. Hajiya Mama da Abban ne kawai suke zuwa, suma idan aikin sharrinsu ya tsikaresu, kuma Abba ma ai bai jima da dawowa ba. Ajiyar zuciya ta sauke da kauda zancen a ranta itama ta kwanta tare da kai hannu ta janye bargon da Hibbah tasa har saman kai.
Duk yanda Ummi taso yin barci gagararta yayi, sai ma dulmiyawa da tai a ƙololuwar duniyar tunani da neman mafita. Taja tsahon lokaci tana ƙullawa da kwancewa kafin ta sami mafitar da take addu'a da fatan ta zame musu alkairi ita da zuri'arta.


Da asuba bayan sun idar da salla Ummi ta dakatar da Hibbah da ga barcin da take ƙoƙarin komawa gado tayi. Cike da shagwaɓa ta lafe a jikin Ummin tana faɗin, “Wayyo Ummi ALLAH barci nakeji, kinga yau weekend ne babu makaranta sai islamiyya, su Yaya bazasuje aiki ba na san suma barcin zasuyi”.
Murmushi kawai Ummin tayi, zuciyarta najin tausayin autar ta bisa hukuncin data yanke akan lamarin duk ƴaƴanta a daren jiya. “Muhibbat!”.
Ta kirayi sunan Hibbah dake lumshe idanu babu wasa. Idanu Hibbah ta buɗe tana kallon Ummin, dan yanda ta kirata da cikakken sunanta babu wasa tasan ƙwarai magana ce mai muhimmanci.
“Na'am Ummi”.
“Tambayarki zanyi?”.
“To Ummi, ALLAH yasa na sani”.
Numfashi Ummi taja da kafe Hibbah da ido. “Duka yayunki babu mai neman aure ne dama?”.
Ɗan jimm Hibbah tai alamar nazari. Kafin tace, “Ummi wai kina nufin sunada ƴammata?”.
Kai Ummi ta jinjina mata kawai.
Hibbah ta ƙyalƙyale da dariya tana kwantawa ta ɗaura kanta a cinyar Ummi. “Uhm ai Ummi fa dama tun kwanaki nakeson na baki labari Yaya Umar ya gargaɗeni. Wai so suke suyi miki surprise ne. Kinga Yaya Muhammad yana da budurwa, Maimunatu (Kausar) ɗin gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina abokin Daddyn mu, mai islamiyyarmu kuma ɗiyar kawarki.......”
Wani irin farin ciki da sanyi ne ya lulluɓe zuciyar Ummi lokaci guda. Ta katse Hibba cike da zumuɗi. “Da gaske Tanee?”.
“Wlhy kuwa Ummi. Kin dai santa babu ruwanta ga hankali, kina zuwa gidansu, suna zuwa nan gidan kinsan tarbiyyarsu. Gata malama a Islamiyyar tamu. Akwai wani dabino da zam-zam da zuma da Yaya Muhammad ya kawo miki kwanaki na rantse itace ta bada a baki. Amma yace idan na faɗa sai ya fasan baki.”
Yanda Hibbah ta ƙare maganarne ya saka Ummi ƙyalƙyalewa da dariya. “Kai Mamana har yanzu dai ke sakara ce ALLAH, basai ki gayamin a sirri ba. Sam baki biyo mai sunanki ba. To Abubakar fa?”.
Cikin dariyar zancen Ummi Hibbah tace, “Tab na Zahidah kenan.”
“Wannan Zahidah ta gidan Auntyn ku Kulu dai dana sani?”.
“Eh wlhy Ummi. Amma yace karsu faɗama kowa sai ta gama makaranta. Nima basusan na ganeba a ɓoye sukeyi”.
Nanma dariyar farin ciki ce ta bayyana akan fuskar Ummi. Har ranta zaɓin Yaya Abubakar da na Yaya Muhammad sun mata hundred percent. Hibbah ta cigaba da faɗin, “Shi kuma Yaya Umar Nafisa ce nasan kin sani dama. Yaya Usman kuma Hafsat itama kin sani. Zakin ki kuma babu kasuwa har yanzun”.
Sosai Ummi taji matuƙar daɗi, dukkan damuwarta sai ta gushe a lokaci guda. Taji ƙwarin gwiwa bisa ga abinda take shiryawa. Dukkan fargabarta ta gushe. A ɓangaren muhalli bata da matsala da yaranta, duk gine-ginensu sai dai ƙarashe. Dan suna fara aiki suka haɗa hannu wajen fara ginin filin da taketa tattali da kaffa-kaffa domin su. Burinta ita da mahaifinsu yanda suka tashi kansu a haɗe su cigaba da rayuwa a waje guda. Shiyyasa koda ya sai filin sai ya damƙashi hannun amininsa kuma malaminsa har sai da suka fara aiki ya basu. Shiyyasa har yanzu Abba da Hajiya Mama basusan da zancen ginin ba........
“Ummi inje in kwanta?”.
Hibbah ta katse mata tunani. Shafa kanta Ummi tai tana murmushi. “A'a ban gama da ke ba. Dan banji ita autata tana da saurayi ba ko a'a?”.
Da sauri Hibbah ta ɓoye kanta tana dariya. “Kai Ummi ni banda wani saurayi. Nifa bazanyi aure ba muna tare mutu karaba”.
“Tab, to auta an taɓa haka kuwa. Muma ai munason zaman gidanmu aka ɗakkomu aka kawo mu naku gidan muka haifeku.” Ummi ta faɗa tana dariya.
“Ni dai bazanyiba ALLAH Ummi. Banason nesa da ke da su Yaya. Indai zanyi aure sai dai mutafi tare ko mijin yazo ya zauna a gidanmu to”.
Dariya sosai Ummi keyi, irin wadda ta jima batayi ba a rayuwarta. Tanee ɗinta kayan shirme da wauta kenan. Da ana haka da ƴaƴa da yawa na tare da iyayensu ai.
Tashi Hibbah tai da gudu ta haye gadon Ummi ta kudundune a bargo ita a dole kunya ta kama ta. Ummi da ke dariya tace, “To shikenan ai ke baki da matsala tunda Junaid ɗan gidan nan ne sai kiyi zamanki tare dam......”
“ALLAH Ummi bana sonsa. Da na auri mugun nan gara na mutu”. Hibbah tai saurin yaye bargon idanunta na cikowa da hawaye. Yayinda fuskarta ke nuna tsananin tsoro da tsanar Junaid ɗin da Ummi ta ambata.
“To shikenan naji. Amma ai kina son Isma'il ko?”.
Idanu Hibbah ta zaro waje a firgice. “Wane Isma'il ɗin Ummi?”.
“Mai zuwa nan gidan mana”.
“Ni dai wlhy a'a Ummi. Shi yayana ne dan ALLAH kibar faɗa.”
“Oh ALLAH, ke kuwa Tanee wa kike so a rayuwarki? To ko wanda yazo dubani a asibiti jiya? Muhammad Shuraim ko?”.
Baki Hibbah ta turo amma batace komai ba. Ummi ta cigaba da faɗin, “Tanee kinga shima alamunsa sun nuna mutumin kirki ne nutsatstse. Ina ƙyautata masa zaton alkairi insha ALLAH. Amma zansa ai bincike a kansa inhar kina son nasa”.
Kwanciya Hibbah tai ta juyama Ummi baya. “Ni Ummi ALLAH ya cika iyayi. Gashi baida fara'a. ga shishshigi ”.
“Duk shi kaɗai?. To lallai tunda kika iya gano waɗan nan kina sonsa kenan, zaki kuma auresa”.
Da sauri Hibbah taja bargo da cewa, “Nifa Ummi a'a baiminba. Sai naje China na dawo zanyi aure”.
“Tanee wannan mafarkinki ne. Amma ban fidda miki ran zaki cikashi ba idan kinyi aure mijinki ya kaiki da kansa”.
Shiru Hibbah tayi dan an taɓo mata inda kuma bata son. Itama Ummi sai bata sake tankawa ba ta cigaba da hidimarta da lissafin ƙullawa da kwancewa.


Zuwa takwas Ammar ya shigo ya tada Hibbah dansu haɗa breakfast su wuce islamiyya duk da sunyi latti. Hibbah kamar zatai kuka ta bisa. koda sukaje kitchen ɗin suna aikin suna faɗa har sai da Yaya Abubakar ya shigo ya tsawatar musu saboda kuka da Ammar ya saka Hibbah.
Suna kammalawa sukai shirin islamiyya. karyawar ma a tsaitsaye sukayita suka fice.


★★★

A yinin ranar su Yaya Muhammad duk a gida sukayisa. Suna tare da Umminsu suna shan hira. Basu sake mata maganar tarinta ba, itama batai musu ba. Sai bayan sallar zuhur suma suka wuce islamiyya. Ganin dai har zuwa yamma babu motsin Abbah da su Hajiya Mama yasa Ummi fita wajen maigadi ta tambayesa ko sunyi tafiya ne.
Baiyi mamaki ba. Dan yasan kaf yaranta a fusace suke da Abban. Bayanin faɗuwar Abban ya bata da kaisa asibiti da akai. Kuma har yau babu wanda ya shigo gidan tun jiyan. Duk da abinda suke mata bataji tayi farin ciki da tsautsayin daya afkawa Abban ba. Sai ma komawa tai falonta ta faɗa duniyar tunani........


_________________________________


A ɓangaren Abba ba ƙaramar jigata yay ba kafin safiya. Ƙafafu sun kumbura suntum. hakama fuskarsa tamkar ƙwaɓun fulawar sabon burodi. Sauƙinsa ma allurar barci da likitocin sukai masa ganin yanda yake rusar kuka ƙafarsa na masa zogi.
Sai kusan huɗu na maraice mai gyaran yazo, a cewarsa sun sami lalacewar motane a hanya. Sai dai kuma a zahirin gaskiya ƙaryama yake bai taho ba sai da safen. Komai likitocin basu ce ba. Sai ma damar yaje yay aikinsa da suka bashi, dan haka suka basu sallama.

Ummi na tsaka da tunaninta taji shigowar motoci, mikewa tai ta leƙa ta windown falonta sai ta hango ana fita da Abbah da ga motar Junaid tamkar gawa. Wani irin faɗuwa gabanta yay. Babu shiri ta fito zuwa tsakar gidan itama. Kusan tare suka shiga sashen Momy da su Hajiya mama da ke biye da mai-gyara da Junaid da suka ɗakko Abba ranga-ranga.
A tsakkiyar falon momy aka shimfiɗe Abba. Sai dai ganin yana numfashi yasa Ummi batace komaiba tabi layin ƴan kallo. Mai-gyara ya fito da kayan aikinsa. sanin abinda zaije ya dawo ya sashi faɗama Junaid cewar ya samo wanda zasu tayasa riƙe Abba dan shi kaɗai bazai iyaba. Badan Junaid yaso ba ya mike ya fita. Babu jimawa sai gashi tare da mai-gadinsu da na maƙwafta. Sai wasu yaran makwaftansu su biyu sa'annin Ammar.
“Yauwa kayi farar dabara da kukazo da yawan”. Cewar mai gyara yana gyara zamansa sosai a gaban kafafun Abba da sukai suntum har ƙyalli sukeyi.
Junaid da mutanen daya gayyato baki ɗaya suka zagaye Abba mai-gyara ya fara aikinsa. Sai dai abin mamaki duk da barcin da Abba keyi ana taɓa ƙafar yay wata iriyar mahaukaciyar zabura da ballara ihu. “Wayyyyyyyoooooo!!!!!! ALLAH na zasu kasheni na shiga uku ni Halilu!!!”.
Babu wanda ihun Abba bai gigita ba a falon. amma ahaka mai-gyara ya cigaba da aikinsa ko tausayi babu. Ihu Abbah yake da iya ƙarfin iko. Tun yana zufa har takai ga sakin fitsari. Can fa abin mamaki da kunya sai ga kashi.
Hanci su Ameerah suka shiga toshewa. Su kansu masu riƙon nashi ji suke kamar su sakesa su gudu dan azabar warin kashin. Suma kuwa yayi ya farfaɗo yafi sau uku. Tun yana ihu da murya mai kauri har ya koma siririya. Daga baya ma akabar jinta gaba ɗaya.
Duk yanda Ummi taso daurewa sai da taji hawaye sun ciko mata idanu. Tai ƙasa da kanta saboda tausayi.


A cikin wannan halin su Hibbah suka fara dawowa gidan. Ihun Abba ne ya ringa jan hankalinsu suka dinga nufo sashen duk da sun manta shekarar karshe da suka shiga sashen. Su kansu tsoro ya kamasu ganin yanda Abban ya koma. Badan sun so ba dole suka dinga toshe hancuna suma saboda wari.
Mai gyara ya ɗora kafa da hannun Abba. Sauran raunikan ma aka gyara. Ya shafa magani ya bada wanda za'a cigaba da masa amfani da shi. Kafin a cake masa ƴan kuɗaɗensa masu nauyi. Aka kuma kaisa masauki dan yace sai da safe zai wuce yamma tayi.
Sai lokacin Hajiya Mama ta farga da su Ummi da yaranta. Ido ɗaya ta kanne ta shiga zazzaga bala'i wai sunzo ganin ƙwaƙwaf. Cikin subutar baki Hibbah taja wani wawan tsaki da faɗin, “Kaɗan ma ya gani. Ummin mu yaso gani a wanann kwatankwacin bala'in sai shi ALLAH ya tsundumasa. In takamarsa zalunci wataran ƙafar za'a guntule.....”
Wata muguwar cafka Hajiya mama ta kaima Hibbah ta ko kwasa a guje tabar sashen. Zata bita Junaid ya riƙota cikin masifa. “Barta kakus. Nine nan zanci uban uwarta, wancan bakin nata mai kama da na reza yau sai na ɓaɓɓarkasa wlhy. Shegiyar yarinya mai bakin akku. Idanma an sakata tazo ta faɗa ne to ina dai-dai da kowane shege a gidan nan. Wama ya sani ko kada mana shi akaiyi. Kai bama zan yardaba ALLAH sai munje kotu”.
Tsaki Ammar yaja tare da kama hannun Ummi suka fice. Su Yaya Muhammad ma kai kawai suka girgiza sukai gaba abinsu da barin su Hajiya mama da takaici. Dan so sukai su tanka su kwashe komai sukai wajen ƴan sanda. Daga nan a wuce kotu har ALLAH yasa sukai gaɓar da suke fata. To sai akai rashin sa'a yaran Ummi masu lurane suka manna musu hauka.
Koda suka koma sashensu basuga Hibbah ba. Sun san ta boye kanta a daki ne saboda tasan tayo laifi, tunda suma suna hanata rashin kunyar. Alwala ma duk sukayi suka fice masallaci. Ummi ma ta nufi ɗakinta gabatar da tata duk da tana jiyo hayaniyar su hajiya mama daketa zage-zage har yanzun.
Koda suka dawo bayan sallar isha'i Hibbah bata yarda ta fitoba har suka ci abinci sukai hira kowa ya tafi makwanci. Babu kuma wanda ya nemeta dan a tabbatar mata batai dai-daiba.


Tun a daren maƙwafta ke shigowa duba Abba dan sunji ihun da yayta zugawa. Duk wanda ya shigo sai su hajiya mama suce yaran Ummi ne suka jima Abban ciwo. Da yawa ba yarda suke ba, saboda sunsan halin matsi da Ummi ke fuskanta a gidan da yaranta tun suna kanana. Dan tunkan ma Hajiya mama ta dawo gidan da zama idan tazo da ga ƙauye haka zataita zubda tujara wa Ummi kala-kala, tunda kuwa mijinta ya rasu ta dawo da zama baki ɗaya sai Ummi ta shiga uku ta lalace itada ƴaƴan ta, gashi nan har yanzu basu huta ba.


*_______________________________*


Shiru kakejin Master da yaransa tamkar basa ƙasar. Babu kalar takalar da jami'an tsaro basu masa ba a kafafen ƴaɗa labarai yay kunnen uwar shegu da kowa. Ko randa zancen kai matar gwamna koto ya fito da ga hukumar yaƙi da ta'annatin kayan gwamnati babu wanda yaji ko tarin master. Shi dama ba sanin taka mai-mai accaunt na duka handles nashi akai ba. Dan kullum cikin canja salo yake.
Sun cigaba da saka idon ganin kozai tanka amma shiru, dan haka suka cigaba da shirya masa tarkuna ta ƙarƙashin ƙasa dan sunsan tabbas zaije kotun.


★★


Yau da yamma Hibbah na makaranta ta fito class cike da gajiya da yunwa. Fatanta kawai ta samu motar komawa gida da wuri dan su Hafsat tuni sun wuce saboda ba department nasu ɗaya ba. Su kuma yau duk lecture ɗin safe sukayi. Ita kaɗaice tayi na yamma.
Ta samu da yawan ɗalibai dake ta tutsutsun shiga motar da duk tazo wucewa. Dan haka tai gaba saboda kanta dake ciwo. Cikin sa'a kuwa tana matsawa gaban sai ga wata taxi ta faka gabanta. Batare da tunanin komaiba ta afka ciki bayan ta sanarma direban inda zai kaita, shi kuma ya faɗa mata kuɗin. Ko ragi bata nema ba dan buƙatarta kawai taje gidan da wuri. Saboda tana tsoron abinda zaije ya dawo ne musamman akan dangin Abbansu dake cike da gidan nasu dubiyar Abba. Dan zuwa yau da yake cika kwana uku jikin nasa da sauƙi.
Ƴan can asalin kauyensu ne sukazo mota guda duba shi. Sai dai hakan ya bama Ummi mamaki da su kansu, dan sam da ga Abba har hajiya mama bason mu'amula da ƴan ƙauyen sukeba yanzun.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login