Showing 96001 words to 99000 words out of 165076 words
Chapter 33 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt
yake gwanace ta taurin kai da kafiya sai tai ƙasa da kai kawai bata miƙe ta bashi hanyar data tare masa ba.
Sake raɓawa ta gefenta yayi zai wuce tamkarma bai gantaba. Sai dai yanda ta durƙusa a gabansa hawaye na zirara a kan fuskarta ya sakashi satar kallonta ta ƙasan ido yana ɗan takawa ya wuceta, sai da ya kama handle ɗin ƙofar sai kuma ya ɗan rumtse idanunsa yana cijar lip nasa tare da dakatawa.
Jin ba'a buɗe ƙofar ba yasa Hibba fahintar bai fita ba, bazai tanka mataba ne ya sata fara magana cikin raunin murya na drama ɗin data shirya masa cikin ƙanƙanin lokaci, dan halin da Ummi zata iya tsintar kanta a ciki kawai take hangowa. “Na roƙeka dan ALLAH ka maidani ga ahalina. Mahaifiyar mu tana da rauni na ciwo da kan tashi a dalilin damuwa. Rashina kuma yana ɗaya daga manyan abinda zai iya tada mata shi. Indai nice na janye alwashina, bana buƙatar wani TAKUN SAƘA da kai. Da ga karshe ina roƙonka dan ALLAH ku barmin ahalina. Ku duba maraicinmu da raunin mahaifiyarmu🙏🏻”.
Ta kare maganar da haɗa hannayenta waje guda alamar roƙo kukan gaskiya na suɓuce mata yanzu kam. Jin bai tanka ba yasa ta ɗago idanunta da hawaye ke cigaba da mata zarya a kumatu ta dubesa. Har yanzu idanunsa a rumtse suke, kuma bai juyoba bai kuma saki ƙofar ba, sai dai sarai yana jinta. Amma tsabar ƙasaita da mulki yamayi tamkar bai san da kasancewarta a wajen ba.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka sake ziraro mata na tsananin tausayin yayunta da begen Ummin ta. Tana buƙatar zuwa garesu kodan ta sanar musu abinda taji ga Abbah, shiyyasa ta ƙudiri ɗaukar duk wani wulaƙancinsa, indai hakan zaisa ta dace da fatanta na komawa gida.
Tsahon mintuna biyu bai tanka ɗin ba, yana dai sauraren kukanta dake ƙara saka jijiyoyin kansa miƙewa. Ganin haƙanta bai cimma ruwa ba ya sata miƙewa da nufin barin wajen, dan ta gama sallama taurin rai da rashin tausayinsa. Takunta biyu ana uku Ƙasaitacciyar muryarsa ta sakata dakatawa.
“Ni bana magana biyu”.
Wani irin ɗaci da jin zafinsa ne ya soki zuciyar Hibbah. Ta cije lips ɗinta da ƙarfi tana matso hawayen da suka sake ciko mata idanu. Cigaba tai da tafiyarta wani duhu-duhu na mamaye idanunta.
Da ƙyar ta ƙarasa saman gadon kuka na sake kufce mata. Tana tsoron rasa Ummi da yayunta, tana takaicin fasiƙi azzalumi irin Abba ya samu galaba akansu. Sai a yanzunne take jin matuƙar takaicin biye masa tun farko harta maida murtani. Dan zuwa yanzu ta fahimci irin wannan mutumin ba'a cinsu da yaƙi ta ƙuru-ƙuru sai ta siyasa da taku. Hakan na nufin kuma sai ka kwantar da kai wajen fara fahimtar su ɗin su wanene kafin ka samu damar kutse a lamuransu. Inama ɗazu shiru tai masa har yayi ya gama. (Dole ne yanzu ta sake sabon shiri), ta ayyana a ranta tana miƙewa zaune. Mamaki ya kamata ganin bai fita ba. Ya saki ƙofar ya juyo hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya tokare ƙafarsa ɗaya jikin ƙofar daya jingina bayansa. Sai idanunsa da ke matuƙar hanata sukuni da tsiwa da ya zuba mata yana wani kallonta tamkar a ɗage.
Kanta ta maida ta duƙar tana share hawayen. Lumshe idanun yay ya buɗe yana ɗaukesu da ga kanta ya maida kansa ga ƙofar ya jingina. Ta ƙasan ido ya koma kallonta batare da tasan yana cigaba da kallon nata ba duk da tanajinta a takure har yanzun.
“Zan iya baki dama bisa sharaɗi”.
Da sauri ta dubesa jin abinda ya faɗa. Tai saurin miƙewa ta nufosa cikin sassarfa. “Dan ALLAH Yaya kana nufin zaka barni in tafi wajen Ummi na?”.
Ta faɗa tana matsoshi gab batare da tasan tayi hakan ba saboda zumuɗi. Idanunsa ya buɗe da ƙyau a kanta jin yanda ta kusanta kanta da shi. Yanda ya zuba mata idanun ya sata tura baki tai ƙasa da kanta.
Warware hannayensa yayi yana miƙewa da ƙyau ya tsaya kan ƙafafunsa. Hakan sai ya sake kusancin nasu matuƙa. Baya ta ɗan ja tana sake ɓata fuska. Takowa yay ya sake matsawa suka koma yanda suke, bayan ta shiga jan ƙafafunta. Shi kuma ya cigaba da takawa yana binta har suka dangane da mirror. Hannayenta duka biyu ta dafe mirror ɗin da su tai ɗan baya saboda yanda ya tsaya mata ƙiƙam tamkar soja. Bakinta ne ya shiga motsawa alamar akwai magana amma babu damar faɗa.
Fahimtar hakan ya sakashi fara magana a daƙile yana bin fuskarta da kallo. “Zakiyi aiki na wata guda tare da mu....”
Zabura tai babu shiri, hakan ya sata faɗawa jikinsa saboda kusancinsu. Bai riƙeta ba, dan haka ta sake komawa baya jikin mirror ɗin tana faɗin, “Kana nufin nima na fara sata?”.
“Itama sana'ace ai”.
Yay maganar yana tura duka hannayensa a aljihu da lumshe ido ya buɗe lokaci guda.
“Tab wlhy ban yarda ba. Ƴar yahoo fa kenan mai datsan accaunt ɗin mutane, zamb.......?”
Tai saurin rumtse idanun da bakinta batare da ta ƙarasa ba saboda ganin ya ɗora hannayensa saman mirror ɗin yayo kanta. Saurin maida lips ɗinta tai cikin baki ta matse tana ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka, dan yanda ya kusanto da fuskarsa da tata har yana busa mata numfashinsa sai ka ɗauka wani abu zai mata. Janye fuskar tasa yay ya maida saitin kunnenta yana sake tsuke fuska. Cikin wani irin Slowly voice da ke nuna gajiyarsa matuƙa ya fara magana yana shaƙar ƙamshin da gyararren gashinta keyi duk da ya ɗan mimmiƙe ta gaba dan tun gyaran ranar ɗaurin aure. “Ashe zaki dawwama tare da Master har tsufanki babu ganin Ummi”.
“ALLAH ya kiyaye na zauna da mai homo, wlhy kota katanga sai na haura”.
Baki ya taɓe da ɗage kafaɗa irin I don't care ɗinnan. Batare da ya sake ko kallonta ba ya nufi ƙofa abinsa cike da takun ƙasaitarsa da izza. Kukan ƙarya Hibbah ta fashe da shi duk da dai har cikin ranta tanajin raɗaɗi da takaicinsa. Baiko nuna yasan tanai ba ya buɗe ƙofar ya fice abinsa.
“Mugu danginsu Halilu. Na rantse sai kayi dana sanin satoni wannan gidan naka, dan saina addabi kowa. Da wani idanunsa abin tsoro”.
Oho shi baima san tanai ba. Dan tuni ya kai downstairs. Kamar yanda ya saba a duk dare sai da ya leƙa ɗakunan su Salis ya tabbatar suna lafiya. Waɗanda basu kashe fitila ba ya kashe musu. Wasu ma har barguna ya gyara musu a ransa yana ɗan mamakin kwanciyar tasu da wuri yau, sai da ya ƙara musu addu'ar barci kamar yanda ya saba sannan. Compound ya fito ya dudduba. Sai da ya tabbatar komai normal ma anan sannan ya dawo ciki ya kashe sauran fitulun ya haura sama. Ƙarasa shirin barcinsa yay ya haye gado yana godema UBANGIJI da ya kaisa wanann lokaci da rai da lafiya bayan wasu na asibiti wasu ko na gida cikin jiyya matsanciya. Cikin ƙanƙanin lokaci barci yay awon gaba da shi dan yayi matuƙar gajiya. Gashi dama yasha maganin ciwon kan.
A ɓangaren Hibbah kam sai da ta gama sharce-sharcen ƙwallarta ta cire hijjab ɗin bayan taje ta murzama ƙofar key. Kayan daya ajiye ta warware. T-shirt ɗinsa ce mai gajeren hannu da three quarter wando sai mayen ƙamshinsa sukeyi. Ta ɓata fuska tana cillar da kayan. “Ni bazansa kayan ƴan homo da yahoo ba”. Tai maganar tamkar zatai kuka.
Abincin da ya ajiye ta ɗauka da bottle water ɗin da suma ya ajiye ta zauna a bakin gado ta fara ci dan da gaske yunwa takeji. Taci sosai tasha ruwan sannan ta miƙe. Kayan ta sake harara dan harga ALLAH tana buƙatar saka sutura a jikinta. Bazata taɓa iya barci da guntun ɗankwalin dake ɗaure a jikin nata ba. Hakama kayan data cire ƙyanƙyaminsu take bazata iya maidasu jikinta ba. Wando da rigar data gama mita a kansu ta ɗauka ta saka. Sai ga three quarter ita ya zamar mata dogo, dan kaɗan ya rage ya rufe idon sawun ƙafarta. Hakama rigar tai mata burun-burun tamkar kaita mata dariya. Baki ta taɓe da yamutsa fuska tana duban kanta a mirror, dan ba karamin addabarta ƙamshin turaren nasa yayi ba.
Idonta ne ya sauka akan tab ɗin daya ajiye mata. Ita sam tama manta da ita. Ɗauka tai da saurin tana faɗin, “Stupid me. Wai mima ya kaini masa magana bayan ga maganin kukana anan”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariya. Ta dira tsalle ta ɗane gado ranta fal farin ciki. Babu lock a tab ɗin, hakan ya bata damar sauke idanunta akan hoton su Habib su bakwai sai shi na takwas a tsakkiyarsu, duk sun wani kanannaɗe masa jiki tamkar tata. Shima ya shafo fuskar Adam da Khalid dake gefe da gefensa yana ɗan murmushi. Daga ƙasa Habib da Idris suna zaune sun ɗaura kawunansu bisa ƙafarsa ɗai-ɗai sun kwantar. Sai bayansa Musbahu, Zaidu, Salis suna akan kafaɗarsa suma. A kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar ƙaunar da sukema juna. Ta ɗan taɓe baki da faɗin, “A haka dai kamar mutanen kirki, sai dai ALLAH kaɗai yasan tsiyatakun da kuke aikatawa.”
Kauda hoton tai da nufin shiga inda applications suke taci karenta babu babbaka sai taga saɓanin haka. Dan kai tsaye ga shagon da zatai sayayya ya kaita. Cikin takaici tai ƙoƙarin fitowa amma hakan ya gagara. Tamkar zata fasa kuka dan haushi. Har tayi niyyar ajiye tab ɗin sai kuma ta tuna bata da sutura kota yin salla. Da bai taimaketa ya bata waɗan nan ba ma da batasan yaya zatai ba. Kaya ta fara zaɓa harda underwears tanata faman ƙunƙuni. Yanda taketa zaɓar abubuwa zaka fahimci harda mugunta a ciki. Dan sai faman taune lip take tana murmushi. Sai da ta gama yayar kaya san ranta sannan ta dangwarar da tab ɗin tana hararta ta koma ta kwanta duk da bata tunanin zata iya yin barci saboda kewa da damuwar rashin ahalinta a tare da ita.
*_WASHE GARI_*
Kamar yanda ya saba shine ya tashesu suka wuce massallaci duk da kuwa bayajin daɗi, dan ciwon kan har yanzu bai sakesa ba duk da yayi barci. Koda suka dawo su kaɗai suka shiga ɗakin motsa jiki shi sama ya dawo. Bai ko kalli ɗakin da Hibbah take ba. baima nuna ya tuna tana gidan ba ya shige abinsa.
A ɓangaren Hibbah ma ta farka dan ta saba. Sai dai tana idar da salla ko azkar batai ba ta haye gado ta koma barci. Barci sosai ta sha har kusan goma saura. Tana buɗe ido da ledoji taci karo manya-manya guda uku. Fahimtar kallo daga nesa bazai mataba ya sata sakkowa taje garesu. Ɗan bubbuɗewa tai sai taci karo da kayan datai shopping jiya da dare ta online. Babu shiri ta shiga sungumar ledojin duk da akwai nauyi tana kaiwa saman gado ta dinga ɗagasu tana zazzagewa.
Mamakine ya bayyana a saman fuskarta ƙarara. Dan duk abinda ta zaɓa ɗin an sako mata. Harma da wanda bata zaɓa ba na fanin kayan shafa, sabulai, kayan gyaran gashi, da kayan yan kunne sai takalma. total na kuɗaɗen da aka sakko ta shiga dubawa mamaki na neman halakata. “Anya mutumin nan yana da man kai kuwa? Koda yake ina ɗan yahoo ma yasan zafin kuɗi tunda wasu suka tara ya wawasa. ALLAH ya gani naidai tunda badani ya sato ba ko naci banda zunubi”. Ta faɗa cike da yarda da kai.
Dama azababben ƙamshin turaren kayansa ya isheta, dan haka ta faɗa wanka. Bata wani jimaba ta fito dan dama bata daɗewa a wanka, da sabbin kayan shafanta tai amfani, dan tana son fara aiwatar da shirinta na yanda zata kuɓuta a gidan nan. Tai kwaliyarta gwargwado ta shirya cikin wata doguwar riga maroon mai laushi da tabi jikinta kasancewar kamar roba take. Sai dai bata fidda mata jiki ba. Dan daga sama an mata wani ado da yay tamkar mayafi ya rufe ƙirjinta duka hakama ya sauka bayanta har kasan mazaunai. Ita kanta tasan tayi kyau gwargwado. Dan haka ta tattare sauran kayan tasa a Wadrobe ɗin ɗakin ta ɗauka gyale karami dake cikin kayan ta yana a kanta. Tab ɗinsa da plate ɗin da taci abinci jiya ta ɗauka ta fito, dan yanzun ma yunwar takeji.
Babu kowa a falon saman sai ƙamshin air Fresheners da mayataccen ƙamahin turarensa alamar ya gitta falon. Baki ta tabe da nufar ƙasa. Kasancewar hankalinta na kan tab ɗin yasa bata kallon gabanta, so take ta fito a shop ɗin jiya amma har yau yaki, da alama shi yay hakan dan karta samu damar shiga ko ina.
“Good morning Aunty Queen!!”.
Su Zaidu dake kan dining suna karyawa suka haɗa baki wajen faɗa dai-dai Hibbah na taka step ɗin ƙarshe zata dire ƙafarta ƙasa tamkar wasu ɗaliban makaranta. Fasa saukar da kafar tai ta ɗago aɗan razane ta dubesu. Kawunansu sukai saurin maidawa ƙasa suka duƙar saboda harar da boss ya gallaro musu da ga inda yake zaune can gefen falon saman ɗaya daga cikin kujeru biyun da aka ajiye dan hutawa ta musamman yana ta faman sarrafa lap-top.
Fuska Hibba ta ƙwaɓe itama tana hararar su, dan sam bata lura da Master ba. “ALLAH idan baku daina cemin auntyn nan ba sai na haɗaku da jarababben uban gidankun nan da wata ɗaurarren face ɗinsa kamar mala'ikan ɗaukar rai.”
Idanu suka waro waje tare da saka hannu sukai saurin ɗorawa a saman bakunansu, saboda dariya dake neman kufce musu babu shiri. Yayinda ita kuma ta kaɗa kanta ta cigaba da tafiya fuska a kumbure. Turus taja ta tsaya saboda cin karo da wanda batai tunanin gani ba zaune a falon, duk da yayi tamkar baya jinsu sarai tasan duk abinda tace masa akan kunnensa ne. Ita kanta baba Saude dake daga kitchen dariya ta shigayi, yayinda wani sashe na zuciyarta ke ayyana mata (inama ace....)
Hibbah ta ɗan saci kallon fuskarsa da ke a tsuke ta ganta babu alamar rahama, wani irin sake tsargawa cikinta yayi, dan ta tabbatar zai iya mata walmakalifatu. Dabara ce tazo mata, dan haka cikin ɗan raunana murya da langaɓe kai gefe ita a dole kalar tausayi tace, “Yaya Master dama tab ɗinka ce na kawo maka ko zaka nema. Kuma na......”
Wani shegen kallo daya watso matane ya sakata saurin duƙewa ta riƙe ciki da faɗin, “Wayyo Ummi na cikina. Yaya Muhammad!!...”
Da sauri baba saude ta fito a kitchen, hakama su Khalid duk mikewa sukai duk zatonsu gaske takeyi tunda kansu a duƙe yake basuga harar da yay mata ba. Amma sunji mitace akan tab. Baba saude data ƙaraso ta kamata ta tayar tana jera mata sannu. saman doguwar kujera ta kaita duk ta rikice. Hakama su Habib falon suka nufo a rikice suna tambayarta dama bata da lafiya ne?.
Murƙususun ƙaryar da takeyine ya hanata basu amsa. Baba Saude dake a rikice ta dubi Master da yay kunnen uwar shegu da su kamarma baisan sunai ba. “Babana ko akwai wani maganine da zata sha a cikin maganinta?”.
Idanunsa ya ɗago a hankali ya dubi baba Sauden, kafin ya janye ya maida kan Hibbah data haƙiƙance ita ciwo cikinta ke mata da gaske. Lip ɗinsa yaɗan ciza ta gefe yana mikewa da ajiye lap-top ɗin saman table ɗin kujerun. Cikin halin ko in kula ya nufa inda suke cike da ƙasaita. Musbahu ya kalla a ƙasan maƙoshi yace, “Ɗakko min maganin feshin flowers ɗin nan a bata yana maganin ciwon ciki....”
“Kaji mugunta”.
Hibbah ta faɗa tana mikewa zaune dingangan. Ta dubi baba saude data wangame baki tana kallonta. “Baba wlhy so yake ya kasheni kawai mutumin nan dama ba ƙaunata yake ba”.
Babu shiri su Habib suka kwashe da dariya. Sai kuma sukai saurin gimtsewa saboda kallon da yay musu. Hibbah ta mike zumbur ganin ya nufota. Bayan baba Saude ta koma ta maƙale.
“Wayyo baba!, wayyo baba saude!!”............✍
*_fajin he tsaho ike😌🙄😏🚶🏻_*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa