Showing 123001 words to 126000 words out of 165076 words

Chapter 42 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt

05 Nov 2024

74022

ya ɗaga wayar cikin kuka da ga can yake sanarma Abba ai suna asibiti, tunda yaga yasar da Master yay masa shima ya yanke jiki ya faɗi. A yanzu haka ma likita ya sanar musu paralysis ta kama shi.
Rawa jikin Abba ya kamayi, sai kuma ya fashe da sabon kuka yana jeroma Master tagwayen ALLAH ya isa da tsinuwar alkaba'i kala-kala. Takaici yasa Momy fisgar wayar a hannunsa ta fara dubawa. Dan yaki musu bayanin da zasu fahimta gashi yana rusar kuka tamkar wani ƙaramin yaro.
Komai bata fahimta ba, dan haka ta dangwarar masa da wayar tana jan tsaki tabar wajen, hakan yasa suma su Ameera bin bayan uwarsu suma cikin takaici suka bar Hajiya mama ita kaɗai tsaye akan Abba.
Sai daga baya suka fahimci abinda ke faruwa ta hanyar kunna tv. Hankalinsu ya tashi suma matuƙa. Dan a take momy ma tai zaman ƴan bori da ƙwala ihu. “Na shiga Uku dadyn Junaid kai ko miya haɗaka da Master har ka shiga lissafinsa?”.
“Tsautsayi!. Wlhy Tsautsayi ne ni Halilu na shiga uku. A.G ka gama da rayuwata. Nayi dana sanin sanin matsiyacin yaron nan mai kama da bokan tsauni”.

*_________________________*


Har zuwa yammaci abu ɗaya ke maimaita kansa a kowacce kafa ta yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Manyan masu fashin baƙi nata famanyi tare da jami'an tsaro da jama'ar gari ƴan bani na iya. Babu wanda yasan da ga ina hoton Hibbah da ahalinta ya fito sai gashi yana yawo. Master dai babu ma wanda ya sansa balle ya fidda hoton nashi. Sai dai hotunansa na ɓadda kama da keta yawo wanda yake a cikin fuskoki kala-kala da ko yatsansa ba'a gani.
Ana tsaka da wannan kace nace kuma sai ga sabon zance ya fito da ga su A.G cewa anyi kidnapping ahalinsu har gida. Hatta da ma'aikatan gidansu ba'a bari ba sai masu gadi kawai.. Dan shi A.G ma securitys ɗin da ke a gidansa suna bada tsaro saboda kasancewarsa babban jami'i kansu an kwashe harda su.
Komai ya sake tashi sabo anata kace nace na hasashen dalilin yin hakan da Master yayi, sai dai abinda ke ba mutane mamaki a wannan gaɓar miyasa Master ɗin zaiyi hakan? Tunda kowa yasan a baya iyakarsa satar kuɗi ba'a taɓa jinsa da yin garkuwa da mutane ba.
A gefe kuma na manya irinsu A.G da wasu kasashen ƙetare na ƴan bani na iya har wasu na iƙirarin saka sunan Master ɗin a jeren ƴan ta'adda na duniya. Sun kawo hujjoji da dama na cewar hakan da hasashensu ya basu. Musamman da a wannan karon al'amarin nasa ya fito fili da kuma sabon salo. Sai kuma hasashen yana da yara masu masa aiki a wajeje daban-daban.


Har zuwa dare dai Master bai sake cewa komai ba tun wayarsa da A.G. Duk da kuwa yana ta bibiyar shafukan sada zumunta da ganin dukkan labaran da ke yawo duk da tsananin buƙatar son hutu da yake a ciki. Ga mura da ke nuƙurkusar rayuwarsa har yanzu. Ya jima zaune a falon salla kawai ke tashinsa har isha'i. Sai da su Zaidu suka fito suna masa shagwaɓar yunwa sukeji sannan.
Da farko bai kulasu ba. Sai da yaga zasu addabi rayuwarsa dan su a ɓangaren ci babu wasa ne, sannan ya ɗauka waya yay musu order ɗin abinci yana hararsu. Tattare kayansa yay ya barsu a falon. Duk da baice musu komai ba sun san za'a kawo abincin.
Koda ya koma ɗakin kwance ya tadda Hibbah a tsakiyar gadon ta ƙudindine. Sai dai da alama ta tashi tayi dukkan salloli. Daga tsayen da yake ya kai hannunsa mai ciyo ya ɗan janye bargon data lulluɓa har akan fuska. Barci takeyi. sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci bana jin daɗi bane. dan ta wani nannaɗe kanta a waje guda kamar wadda take a firgice. Kusan kallon mintuna huɗu yay mata kafin ya janye idanunsa yana furzar da iska mai ɗaci.
Toilet ya shiga yay abinda zaiyi ya fito yai shirin barci. Zama yay a gefen gadon kusan mintuna goma yana kallon Hibbah da sauraren hayaniyar su Idris da alamu ya nuna an kawo musu abincin. Sai kuma ya zame a hankali ya kwanta yana matse fuska alamar dai bayajin daɗi sosai. Kwanciya yay a rigingine ya lumshe idanunsa, tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lula duniyar tunani.
A yanda yake ɗin sai ka ɗauka barci yake, sai dai yanda yake murza babban yatsan kafarsa dana kusa da shi zaisa kasan ido biyu yake ran mazane a wuya kawai. Shi mutum ne mai matuƙar fushi da zafi idan aka ɓata masa rai. Shiyya su Habib kanyi matuƙar taka tsantsan da shi idan yana a cikin irin wannan halin. Ya jima a haka yana ƙullawa da kwancewa akan shirinsa na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu kafin barci ɓarawo ya sace sa.


*_WASHE GARI_*


A safiyar yau tamkar yanda ya tsara ya fidda video a karon farko na tarihin rayuwarsa. Video ne da ya ƙunshi abubuwa da yawa da suka danganci jerarrun tambayoyi da ga kalaman su A.G ɗaya bayan ɗaya. Dama duk wani babba da ya fito ya tofa albarkacin bakinsa dan gane da abinda ya faru jiya.
Da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “Ina da abin cewa da yawa, amma bazan ce ba, saboda lokacin cewar baiyi ba. Sai dai inason kamar yanda nai tambayoyin nan ga duk waɗan da na ambata su amsa min su. Da ga ƙarshe ina mai tuna muku acikin awa ashirin da huɗu saura awanni goma sha ɗaya suka rage muku akan ahalinku, Idan har kuna buƙatarsu ku sakarmin nawa nima na baku naku, dan ko ƙwarzane ya samu ɗaya daga cikinsu babu fashi sai na rama. Dan Master baya yafiya wa abokin gaba koda akan harara ne............🔥


(Tofa turƙashi, bara mu kama kanmu kenan master).


*_Ku sani a addu'a na bar posting dare ɗin nan🤦🏻😥🚶🏻_*





TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*









*_Chapter Thirty Seven_*


..........Gaba ɗaya komai ya sake ɗaukar zafi a ɓangaren jami'an tsaro. Dan kuwa dai zuwa yanzu an tabbatar da ahalin su A.G suna hannun Master, sai dai kuma su su A.G sun tabbatar ma da duniya su Ummi basa tare da su. Kawai dai sun faɗa zasu kamasu domin master ya bayyana kansa. Kuma koda sukaje sai basu samesu a gidan ba kwata-kwata.
Wannan magana ta fara canja salon zantikan bakunan mutane harma da wasu a manyan masu fashin baƙi da ke faɗa aji na ƙasar. Da yawa suna faɗin anya kuwa babu wani abu a ƙasa da ke tsakanin su A.G da Master. Dan kuwa dai kalamansu suna kamanceceniya da wanda sukai amai suka lashe abinsu.
Master dai da duk keji da ganin komai bai sake ko tari ba. Tunda ya baje a falo dai ya duƙufa akan aikin da suma su Habib basu san na miye ba. Dan tundama suka shigo suka gaidashi duk sai suka koma ɗayan sashen inda yake kamar matsayin nasu har baba saude. Nan kuma ya zama nashine shi da iyalinshi su madam Hibbah mai zamani😜.
Har kusan sha ɗaya na safe baiga Hibbah ta fito ba, shi kuma tunda ya fito a ɗakin bai komaba saboda busy da yayi. Sanin dalilin rashin fitowar tata ya sashi aika Habib kiranta lokacin da ya kawo masu breakfast. Tana zaune bakin gado bayan tayi wanka ta shirya harda gyara ɗakin akai knocking ƙofar. Cikin sanyin murya ta amsa tana miƙewa. Habib da ke tsaye da ga waje ya faɗa mata saƙon Master.
Tamkar tana gabansa ta kwaɓe fuska zatai kuka. Sai dai sanin babu damar tsallake kiran yasata warware ƙaramin mayafin jallabiyar kanta ta naɗashi.
“Good morning”.
Habib ya faɗa fuskarsa sam babu walwala. Ɗago kanta tai ta dubesa a karo na farko. Sai dai kafinma tace wani abu shi yayi gaba abinsa. Idanu taɗan rumtse tana haɗiye abinda ya zo maƙoshinta ya tsaya mai ɗaci. Sai kuma jikinta ya sake yin sanyi dan sam bataso taga mutum yana fushi da ita. Ko sadda tana gaban Ummi inhar tai laifi akai mata faɗa takan yi kuka ta manta, amma inhar taga Ummi cikin ɓacin rai da yayyenta saita kasa zaune ta kasa tsaye. Shiyyasa a yanzu ma duk ta firgice da fushin Master duk da tasan itace mai gaskiya.
Koda ta iso falon tsaye ta iske Habib na tambayarsa a haɗa masa abinci. Batare da ya ɗago akan takardun da yake dubawa a hannunsa ba ya girgiza masa kai da faɗin, “Barshi ta zuba”.
Kai Habib ya jinjina masa. “Okay, bayan hakan babu abinda kake buƙata kuma?”.
Yanzun ma bai ɗago ba ya bama Habib ɗin amsa. “Da ga yanzu itace zata ringa komai anan sashin”.
Daɗi ya ratsa zuciyar Habib. Ya ɗan juyar da kansa gefe yana murmushinsa da ya kasa ɓoyuwa. Ya haɗiye hawayen da ke neman kufce masa tare da duban Hibbah da ke tsaye tana saurarensu, dan kalaman Master ɗin ruɗar da ita sukayi. Ita dake fatan ya barta ta koma ga ahalinta ake kuma ƙirƙirarma aiki. Kallon karki sake cutarmin da ɗan uwa Habib ɗin yay mata, cikin nuna alamar rauninsa da bata dukkan amana. Batare da ya furta komai ba ya juya ya fice a falon tana binsa da kallo harya fice......
“Amana ya baki, duk da bayada tabbacin zaki riƙe masa. Dan a farko sun baki dukkan yarda babu shakku ko ɗar game da ke, amma sai kika sauya musu tunani....”
Master yay maganar har zuwa yanzu idanunsa da hankalinsa naga lap-top ɗin da takardun hannunsa. Idanunta dake kallon ƙofar har yanzu ta lumshe a hankali hawaye masu ɗumi suka ziraro mata. Takai tsugunne gabansa, “Nima iyayena sun yarda da kaine suka baka aure na da tabbacin bazakaci amanarsu ba amma sai kaci Yaya Master. Ka tausaya musu dan ALLAH dan Ummi na da ƴan uwana sunada rauni a kaina tamkar yanda ƴan uwankama kai ne rauninsu. Nima sune dukanin hope ɗin rayuwata. Bani da kuɗin dazan baka sama da wanda su Abba suka baka akan musu aiki. Sai dai inada kalaman roƙo da ban haƙuri a gareka kaji tausayin maraicinmu. Dan ALLAH a wannan gaɓar ka barni na koma ga ahalina su auramin wanda zuciyarsu tafi so da nake da tabbacin bazaici amanarsu ba......”
Tunda ta fara magana bai ɗagoba bai kuma daina uzurin gabansa ba sai yanzu. Idanunsa da har yanzu suke da kalar ja ya ɗago ya zuba mata. Duk son danne ɗacin dake kan harshensa da yayi ya gaza sai da ya bayyana acikin muryarsa. “Wanene shi?”.
A yanda yay maganar ne ya saka Hibbah ɗagowa ta kallesa cikin mamaki. Amma ganin ita ɗin yake kallo shima sai tai azamar maida kanta ƙasa cikin suɓutar baki da fashewa da kuka tace, *_“Yaya Isma'eel!”_*.
Numfashi Master ya fesar a hankali da lumshe ido....
Hibbah da bata san yanayi ba ta cigaba da faɗin, “Yaya Isma'il ya kasance abin alfaharinmu a tun farkon haɗuwa. Sannan shi abin so ne ga ahalina, sun so inama ace shine ya zama zaɓina tun farko, sai dai kash yazo a makare. A makaren da ka rigada kaima rayuwata kutse da yazo bisa alƙalamin ƙaddara ta, sai dai inaji zuwa yanzu a zuciyata tamkar bai makara ba. Gani gabanka gwiwa biyu ina roƙonka domin daraja da rahamar wanda ya haliccemu dan mu bauta masa, ka sawaƙemin aurenka dake kaina ka kuma maidani garesu. Sannan kayi haƙuri akan kuskuren da nai jiya gareka, nima bani da wani zaɓin da ya wuce hakan ne. Ahalina na cikin tarkon masifar ƙanin mahaifinmu, kai kuma ka kawoni nan ka ajiye kana musu aiki bayan suma burinsu ka kammala musu aikinne su ɓadda rayuwarka. Bazan tambayeka miyasa kake biye musu ba, sai dai zan sanar da kai kaima ba komai bane a garesu, lokaci suka ajiye domin ka. A zahiri dai kanada ibada da kiyaye dokokin ALLAH, amma a baɗini kana saɓa masa da babban laifi da ƙazantarsa da muninsa yasa ko'a kan harshe yake da ɗacin faɗa. Miyasa ka zaɓi saɓa masa bayan ni'imar lafiya da yay maka, ya baka ilimin addini, ya baka damar tarbiyantar da marayu, ya baka dukiyar da kake ci kake sha kake tufafi da shimfiɗa abubuwan jin daɗin rayuwa. Yayo ka a musulmi da baya barin lokutan salla biyar su wucesa sai da kuskure. Kaji tsoron ALLAH ka barsu tun kafin kai ALLAH ya barka......”
Duk yanda yaso cigaba da abinda yakeyi hakan ya gagara, dan kalamanta ba zuciyarsa kawai suka daka ba jinin jikinsa da ɓargonsa suke daddatsawa da tsinkawa a lokaci guda. Batare da ya shirya ba bakinsa ya suɓuce wajen faɗin, “Miyasa kike tunanin Isma'il ya fini nagarta?”.
Duk da bawai cikin lallashi ko taushi yay maganar ba sai Hibbah ta samu kanta da sakin murmushi tana ɗan dubansa. “Saboda bai taɓa cutar da mu ba. Kullum burinsa ya bama Ummi da mu kariya a wajen azzalumi Halilu. Bai taɓa tunanin rabani da Ummi na da su Yaya Muhammad ba. Kana ganin kuwa akwai sama da wannan nagartar wajen ƙayatar da yarinyar dake neman mijin aure?”.
Shu'umin murmushi shima ya saki da maida kansa ga aikin gabansa batare da yace mata komai ba. Sai da yaja kusan mintuna uku harma ta fidda ran samun amsa sannan ya bata amsar batare da ya kalletan ba yanzun. “Duk manta da waccan nagartar ta Isma'il ɗin da tunanin mi nake aikatawar ki riƙe Muhammad Shuraim (MASTER) dan a yanzu shine ƙaddararki. Na baki damar farko da zaki iya komawa ga ahalinki amma bakici jarabawar ba saboda gaggawa da ci da zuci irin wanda ke kai rayuwar da yawan mutanenmu ƙasa. Ba ko mai ne akema TAKUN SAƘA ba. Kamar yanda bada kowa ake kafa tubalin ginin TAKUN SAƘA ba. Dakinyi juriyar bina a yanda na ɗoraki da yanzu ba wannan matsayin muke ba. Amma zan miki alfarma a karo na biyu, zakije ga ahalinki, sai dai da sharaɗin tsarabar JINI NA”.
Hibbah da sam bata fahimci ma'anar furcin ƙarshe ba tai saurin jinjina masa kanta, “Na yarda da sharaɗinka, ko wanene jinin naka ka haɗani da shi muje wlhy baza'a taɓa cutar da shi ba koda da harara”.
Kallonta yay cike da salon izza yana sakin wani shaiɗanin murmushi da ɗage gira sama. “Kin tabbata?!”.
“ALLAH shine zai zama ahaidarmu”.
Hibbah ta faɗa cikin sauri da kaguwa.
“Da ga yanzu zuwa ko yaushe zaki iya ganin kanki gaban ahalinki da Isma'il ɗinki, amma ni minene makomar igiyoyin aure na dake kanki?”.
“Zan tayaka addu'ar ALLAH ya baka wadda ta fini”.
Maimakon amsa sai ya nuna mata kayan breakfast ɗin da Habib ya ajiye. Da sauri tace masa “Banajin yunwa”.
“Nike ji ai”.
Ya bata amsa kansa tsaye. Hankalinsa nakan aikinsa. Batare da musu ba Hibbah ta haɗa masa komai gabansa tana satar kallon takardun dake barbaje a ƙasan carpet da bata san na minene ba.
Shi dai duk da yana lure da kallon kurillar da takema takardun bai nuna ya gani ba. Sai ma turesu da yay gefe yaja abincin data haɗa masan ya hau ci hankalinsa kwance, kai kace baida wata damuwa. Sai da yasha kusan rabin cup na tea ɗin sannan ya miƙa mata. Kai ta girgiza masa batare da ta kallesa ba. Shima batare da yace komai ba ya kamo hannunta cikin nasa. Yanda yay ɗin ya tilastata ɗago idanu ta kallesa. Kofin ya ɗaura mata yana ɗan wani cizar lip da ƙanƙance idanunsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login