Showing 54001 words to 57000 words out of 165076 words
Chapter 19 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt
auren Halilu ce ta sake canja komai. Dan kuwa naci matuƙar wahala a lokacin. Komai aka nema sai suce a zo wajena shi da hajiya mama. Ko ɗan kwali ƙin saya sukai balle ƙwayar abinci. Idan nace ma Aliyu yayi yayta faɗa akan ai ya basu kuɗaɗe masu nauyi na hidimar nabar damunsa. Haka na shiga tsaka mai wuya a tsakanin. Duk ɗan abinda nake samu na haihuwa na ƙwaƙule nai hidimar Halilu dan nasan bazan taɓa fita a garesuba idan ma na nuna Aliyu baiyiba. to ashe yin danayi ma ba mafita bace dan sabon zancene ya tashi akan eh da gaske na mamaye komai ɗin. Bani da abin cewa dan haka nai musu shiru akai biki aka ƙare lafiya amarya ta tare a tsohon gidanmu da muka taso, dan da hajiya mama ta matsa anan zasu zauna tare damu tunda akwai ɗakuna. Aliyu yace sam bai yarda da wannan gwajin gwalar ba. Salon haɗa rikici. indama kowa da part nashine sai ya amince. Amma flat ɗaya ne a gidan iya na iyalinsa sai BQ. ita kuma tace Halilu bazai zauna BQ da matarsa ba ni ina ciki inacin daɗi. Bayan ƙurar data tashi ta lafa dan malam ya tsawatar suka yarda Halilu ya zauna acan. Sai dai kuma duk wani abu da zasuci acan bazai saya ba, sai dai yazo nan gidan direct ya ɗiba koda kuwa gishiri ne. Ban taɓa faɗama Aliyu ba sai da ya gani da idonsa. ranar naga asalin faɗansa. Dan murje ido yay yayma Halilu tas har nima na samu rabona a ciki. Wata sabuwar ƙurar ta sake tashi akan wanann magana, har takai Hajiya Mama ta nema Aliyu ya sallami Halilu da ga kasuwa shima ya rinƙa juya na kansa, kokuma su dinga raba ribar duk abinda aka tara a ƙarshen shekara. Ƙince musu komai yay akan hakan, yaƙi kuma bashi kuɗin ya ƙi sallamarsa. Shine dalilin da yasa Halilu ke ganin nice na hana shi da hajiya mama. Duk da kuwa a shekarar Aliyu ya biya mata hajji ita da malam da shi sukaje. Wannan karon na samu hutu, dan tun Usman babu wani labari. Hakan yamin daɗi, dan na samu sauƙin wasu fituntunin, duk da shi kullum mahaifinku cikin tambayata yake wai yaji shiru, danshi mutum ne mai son yara matuƙa. Shiyyasa kuka kasance ƴan gata a wajensa. Komai na buƙatunku baya sakaci da shi komai ƙanƙantarsa. Wanann yasa ake ganin ya lalace a kanmu. Shekara na zagayowa ya sake biya mana hajji ni da shi mukaje. Muna dawowa ya sayamin mota tare da danƙamin wani ƙaramin gida yace na zuba haya, sai jari na sana'a.”
“Musalta muku halin da na shiga awanan tsakanin bazai musaltu ba. Dan saida na gwammace da bai baninba. Dama akan tafiyarmu hajji ansha dabi hajiya mama tace bata yardaba sai dai ya biya musu shi da Halilu. Bansan miyazo kan Halilu a lokacinba shi ya nuna goyon bayan naje, harda nunama hajiya mama bayajin daɗin abinda takemin, ai koba komai na haihu da Aliyu ya kamata a ɗagamin ƙafa zuwa yanzun. Hakan da yayi ya saka malam jin daɗi. Tun daga sannan ma suka koma ɗasawa dan shi malam ya yarda da tuban Halilu ɗari bisa dari. A cikin wannan tarnaƙin na samu cikin Ammar. Wanda yazomin da matuƙar wahala da jigatuwa. Bani kaɗaiba hatta mahaifinku yaji a jikinsa kafin ALLAH ya sa na haihu ko nace akaimin cs aka cirosa. Babanku na ɗaukarsa ya gansa ƙato da shi ga kamanninsa sak nashi tako ina sai cewa yay “Lallai kaci suna Aliyu gadanga kodan wahalar daka bama matata”. Hakan ya sani murmushi, dan har cikin raina naji daɗin sunansa da zai maimaitamin cikin ƴaƴana. Ammar yaci suna Aliyu, a wannan sunan kam kowa ƙin zuwamin yayi, ƙiri-ƙiri suka nunamin jin zafina da suke, sai malam da Halilu da canjin nasa keta bani mamaki ne sukaita komai. Dama dangina nidai wani bai taɓa nemana ba, garama da maganar siyamin mota da gida ta fito su kawu Bello sunzo wai tayani murna. Bandamu da a yanda sukazo min ɗinba nai musu alkairi Aliyu yay musu suka koma. Bayan haihuwar Ammar babu jimawa Aliyu ya fara ciwo a tsaitsaye, inata fama da shi yaje asibiti yaƙi, har dai ta kaisa da kwanciya sannan ya yarda mukaje. A gwajin farko aka gano yanada ciwon ƙoda, yama daɗe a jikinsa dan harya harbi hantar sa. Hankalinmu ya tashi amma sai yayta kwantar mana akan shi ya samu sauƙi. Na jigatu a wannan tsakanin, daga zuciya har gangar jiki. Ban samu nutsuwa ba sai da jikin yay sauƙi ya koma kan harkokinsa. Ashe dauriya kawai yakeyi dan ganin hankalina ya kwanta. Haka mukaita lallaɓawa wataran ya kwanta kwana biyu ya mike ya cigaba da hidimarsa harna yaye Ammar. A watan dana yaye Ammar a watan ciwo ya kai Aliyu ƙasa, har takaisa ga kwanciyar jiyya. Dole Hajiya mama da Malam suka dawo gidan nan da zama muna kula da shi tare dan abin yayi tsanani. Da yake kwana ya ƙare kwanakinsa goma sha bakwai kacal a kwance ALLAH ya amshi abinsa. Mun shiga gigita, mun shiga ruɗani irin wanda bama zai musaltu ba. Dan har wata ƙaramar mahaikaciya na koma a tsakanin nan, sai da malam ya dinga min addu'a na dawo hayyacina. Hajiya mama taso a tafi ƙauye dani nayi zaman takaba. malam yace a'a a ɗakina zanyi. Ta dawo cewar yara su dawo hannunta. Nanma yace a'a ni zan cigaba da rike abina. Duk ta inda ta ɓullo sai ya goce, ganin babu mafita ta haƙura na cigaba da takaba. Su kuma suka koma ƙauye. Acikin zaman takabanne na fara laulayin cikin da ni nasan ina maƙale da abina tun cikin satin da Aliyu ya rasu, sai dai yana bayyana ga kowa Hajiya mama tace bana Aliyu bane..............✍
*_Bara mu dakata anan, naga page ɗin nata ƙara tsaho🚶🏻😖_*
ZAFAFA KARO NA FARKO
SUNAYEN SU:
1_GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDULL
2_KAI MIN HALACCI
NA MISS XOXO
3_BURI DAYA
NA MAMUH GEE
4_DAURIN BOYE
NA SAFIYYAH HUGUMA
5_SAUYIN KADDARA
NA HAFSAT RANO
DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500
SAI ZAFAFA TAKU NA BIYU
1-DAURIN GORO
NA HAFSAT RANO
2-ALKAWARIN ALLAH NA
SAFIYYAH HUGUMA
3_QAUNAR MU
NA MAMH GEE
4_IGIYAR ZATO
NA MSS XOXO
5_WUTSIYAR RAKUMI
NA BILLYN ABDULL.
DUKA BIYAR DIN AKAN NERA 500.
SAI ZAFAFA TAKU NA 3,
1_MIN QALB
NA MAMUH GEE
2_SARAN BOYE
NA BILLYN ABDULL
3_KIBIYAR AJALI.
NA MISS XOXO
4_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO
5_SIRADIN RAYUWAR BILKISU
NA SAFIYYAH HUGUMA
DUKA DOCUMENTS DIN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)
SAI ZAFAFA TAKU NA HUDU.
1-ALKIBLA
NA SAFIYYAH HUGUMA
2_DALAAL
NA MISS XOXO
3_UBAYD MALEEK
NA MAMUH GEE
4_MABUDIN ZUCIYA
NA HAFSAT RANO
5_MAKAUNIYAR KADDARA
NA BILLYN ABDULL
DUKA LITTAFAN BIYAR AKAN NERA DUBU DAYA DA DARI BIYAR (1,500)
SAI ZAFAFA KARO NA BIYAR DA AKE A HALIN YANZU, (ON GOING PAID NOVS)
1-SO DA ZUCIYA
NA MSS XOXO
2-TAKUN SAAKA
NA BILLYN ABDULL
3_HALIN GIRMA NA HAFSAT RANO
4_DAB'IZAR ZUCIYA
NA SAFIYYAH HUGUMA
5-DEEN MALEEK
NA MAMUH GEE
DUKA BIYAR DIN NERA DUBU DAYA NE( 1K)IDAN AN KAMMALA SU KUMA 1500.
YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:
ACCOUNT NAME: MUSAA ABDULLAHI SAFIYYAH..
BANK NAME: KEYSTONE BANK
SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:
08184017082
IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:
09134848107
*_Typing📲_*
*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
_________________________
*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻
_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_
*YERWA INCENSE AND MORE*
*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*
_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_
*_Muna da haɗin_*
_Turaren wuta kala kala na gidah_
_khumrahs_
_Kullaccham_
_Turaren wanka_
_Turaren Kaya_
_Turaren wanki_
_turaren mopping_
_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_
_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_
_Muna Gyaran jiki_
_Na amare_
_Da masu jego_
_Da sabulai masu gyara fata_
_Turaren tsugunno_
_zumar goran tula_
_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_
_Akwaisu kujeran tsugunno
_Dilke and halwa set_
_Burners da igniters da tong_
_turaren fesawa dana ruwa._
_wardrobe balls_
_scented pebbles_
_cotton wooly oudi incense_
_kabbasas_
_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_
_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_
_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*
_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_
_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.
100% TESTED AND TRUSTED_
••••••••••••••••••••••••••••••••
*_Chapter Eighteen_*
..............Tashin hankalin wannan magana yasa na yanke jiki na faɗi, dan ko sanda akai na Muhammad da sauƙi inada garkuwata Aliyu. Amma wannan ni kaɗai ce naketa ƙoƙarin kare kaina sai malam da Halilu da bansan miye manufarsa na bani kariyar ba. Kamar na Muhammad wannan ma malam yace sai a jira na haihu. Haka kuwa akai, na cigaba da rainon ciki Halilu nata hidima dani da ƴaƴa na. Abin na bani mamaki yana sakani a ruɗani., ya kuma bani tsoro Dan sam na kasa hango manufarsa a kan hakan har takai ALLAH ya saukeni lafiya na haifo ɗiyata mace a karon farko. Itama dai tunda ta diro duniya kowa ya shaida jinin Aliyu ce. Dan kamanni sak ta ɗebo nasa dana ƴan uwanta harma taso ta fisu ɗebo komai nashi, sai dai kawai dan ita mace ce. Bakin kowa ya mutu kam, dan ko tari ba'a sakeba akan batun na cigaba da shayar da ɗiyata da taci sunan mahaifiya Muhibbat. Bakowa bane da wannan aikin sai malam. Ya tabbatarmin da wasiyya ya cika shima. Mahaifina ne ya roƙesa dan ALLAH inhar ALLAH yasa na sami miji nai aure na haifi ɗiya mace duk rintsi yana son a saka mata suna Muhibbat sunan mahaifiyata. Sai ko gashi ALLAH yaja da ran malam ya cika wannan wasiya. Sakama Tanee sunan mahaifiyata shine abu na farko daya jawo mata baƙin jini itama a wajensu. Dan anata ƙananun magana Halilu ne kawai ke karewa. Haka dai sukayi suka gama har ƙura ta lafa. Bayan na yaye Tanee aka raba gadon ku, sai dai malam ya kirani gefe mukai maganar da kunyarsa bazata barni na bijire masa ba. Dan yamin hallaci irin wanda bai kamata ni na saka mishi da butulci ba.”
“A wancan lokacin bayan na samesa ya fara da faɗin, (Asiya ke ɗin ɗiyace ɗaya tamkar da dubu. Kuma ɗiya kamar sauran ƴaƴa. Dan baki da banbanci da su kamar yanda wasu suke gani. Baki da laifin komai dan bakece kika aikata laifinba. Ita kanta mahaifiyarki ƙaddara ce ta afka mata har aka sameki. Kiyi haƙuri na ɗakko miki wannan zancen ne saboda abinda nake hangowa da zaije ya dawo game da zuri'arki da wannan dukiyar tasu. Nasan baki wuce aure ba. Dan haka manema yanzu zasu fito gareki tako ina. Sai dai bai zama lallai su kasance dan ALLAH zasuzo ba ko dansu riƙe waɗan nan marayun. Banason bayan babu raina ki shiga gararin rayuwa. Dan mahaifinki kafin yabar duniya yayi matuƙar nadama ya duƙufa neman gafarar ALLAH, ya duƙufa neman ilimin addini a wajena batare da kowa ya sani ba. Shiyyasa ya danƙa amanarki a gareni. Kuma insha ALLAHU zan yi iya bakin ƙoƙarina naga na tsare wannan amanar har zuwa sanda nima ta ALLAH zata kasance. Asiya babu wanda yafi cancanta ya adana dukiyar ƴaƴanki sai ke da kanki, amma dole sai da taimakon namiji. Ni kuma gashi ƙarfina ya ƙare, dan bani da isashshiyar lafiyar nima tun bayan rasuwar Zaki (da yake haka yake kiransa). Amma inata nazari har zuciyata ta yanke min wata shawara da nake fatan zata zama mafita agaremu baki ɗaya. Halilu ɗan uwane ga zaki, duk da halayyarsu ta banbanta. Amma shima idan kin lura ya jima da dawowa hankalinsa. Rasuwar ɗan uwansa kuma ta sake lausasar dashi ko mahaifiyarsu baya son yaji ta aibantaki. Shiyyasa nake ganin mizai haka ki amince ki auresa ku haɗu ku riƙe wannan amanar da ALLAH ya bar mana ta yaran nan da dukiyarsu har sanda zasu kai girma. Na tabbatar hakan zai sakaki nutsuwa da kwanciyar hankali Asiya. duk runtsi babu mai rabaki da ƴaƴanki kema kina gidan mijinki tare da su. Ko sake haihuwa kikai dai duk zasu zama da ga tsatson jini ɗaya ba zaki rarraba kan zuri'arki ba. Amma bawai dole bane fa. Na baki dama kije kiyi nazari daga nan har wata guda. Hukuncin da kikaji ya kwanta miki a rai sai kizo min da shi. ALLAH yayi miki albarka, yayama yaranki albarka. ya baku kariya a dukkan motsinku da numfashinku). Cikin kuka na amsa masa da amin”.
“Tunda malam ya tafi ya barni ban huta ba dare da rana akan tunani da nazarin wannan tayi nasa nake. Na hanga na hango naga zancensa shine kawai mafita a gareni da ku kanku. Sai dai har cikin raina ina matuƙar tsoron abinda zaije ya dawo akan Halilu. Dan gaba ɗaya yanzu ba iya gane inda ya dosa nake ba kai tsaye. Ya riga yayma kansa lulluɓin biri da fatar kura. Ta wani gefe kuma ina kallon kima da darajar malam. ALLAH ne ya zaɓa min Aliyu matsayin miji shine ya zama sila kuma. Bai duba ni ɗin wacece ba, bai ƙyamaceni kamar yanda kowa ke ƙyamata ta ba. Ɗansa ya karɓeni da hannu biyu babu musu, ya nunamin dukkan soyayya da ƙauna. Ya bani farin ciki a ƙarƙashin igiyar aurensa. Koda suɓutar baki bai taɓa gorantamin akan asalina ba. Idan ma na faɗa ƙwaɓata yake ya nunamin ɓacin ransa. To nikan inba butulci ba mizai sa na bijirema zaɓinsa a karo na biyu. Ina ganin koda Halilu mutumin banza ne zanyi fatan dawo da shi hanya. Yanda mahaifinsa da ɗan uwansa basu ƙyamaceni ba shima bazan ƙyamacesa ba. Da waɗan nan kalolin tunanin na gama yankema kaina shawara, a ƙarshen watan da malam yazo ziyararmu tamkar yanda ya saba a kowane wata sai na nuna masa kawai na amince. Ya matuƙar nunamin farin cikinsa da jin daɗi. Yayta sakamin albarka da sakama ƴaƴana. Indai ta ƙaice muku zance da ga ƙarshe an ɗaura aurena da Halilu, auren da ya bama kowa mamaki, musamman da akaga Hajiya mama ko tari batai akansa ba balle asan bata so ko tana so. A farkon auren nan a kunyace nake da lamarin Halilu kota wane fanni, amma ina iya bakin ƙoƙarina na sauke haƙƙokinsa a kaina. Shima kuma yana bani kulawa da respecting ɗina. Hakama ƴaƴana ƙauna yake nuna muku tamkar mahaifinku. Hankalina ya sake kwanciya da shi, na saki jikina sosai tare da ɗaukar duka dukiyarmu na danƙa a hannunsa akan cewar sai kun girma za'a bama kowa nashi. Da farko ya nunamin bazai amsaba. Sai da naita roƙonsa da nuna masa muhimmancin zaman komai a hannunsa saɓanin ni mace. Da ga ƙarshe dai ya amsa da ƙyar. Sati biyu kacal da yin haka ALLAH yayma malam rasuwa. Ƙwarai da gaske na shiga ruɗani fiye da rasuwar mahaifina. Dan malam ya taka matukar rawar gani a rayuwata wadda baki bazai musalta ba. A wannan lokacin naje ƙauye rasuwar malam, duk da a ɗarare nake da kowa ban samu matsi kamar sanda ina rayuwa a ciki ba. Sai ma abin kallo da na zama ni da ƴaƴana saboda da kaina naja mota ta har can. Kwanan malam huɗu da rasuwa kakana ma ya rasu, mahaifin babana kenan. Ban wani ji tasa rasuwar ba. Dan da shi da babu a gareni duk ɗaya dai. Satina guda a kauye muka dawo tare da Halilu, inda tun shigowarmu na fara ganin sabbin al'amura da ga garesa da suka nema rikita mani tunani. Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja. Hajiya mama ta dawo nan da zama, hakama matar Halilu da ƴaƴansa. Ya cireku da ga makarantar da kukeyi ya maidaku ta gwamnati, nima ya haramtamin tuƙa mota. Al'amarin ya matuƙar gigitani da sani a tashin hankali, amma saina daurema zuciyata saboda halaccin mutane biyu da nake tunawa a koda yaushe. Kawu na da mijina. Komai ya sauya da ga salonsa. duk wata cusgunawa ita Halilu da Hajiya mama kemin harma da matarsa da yaransa. Ku kanku baku da sukuni a gidan koda nayin wasa ne. Abubuwa da yawa kullum cikin gorantamin su yake, tare da neman komai gareni ta ƙarfi (uwa ta gari kenan, maimakon tace yana mata fyaɗe saita sirranta domin mutunta kanta😭). Ɗawainiyarku duk ta dawo hannuna. Komai baya mana ya bari. sai ma filin garden ɗinmu da Aliyu ya kashe kuɗi sosai yayisa saboda mutumne mai tsananin son furanni da ƴayan itatuwa Halilu ya bajesa ya kafa wancan ginin, part ɗinsa da matarsa, sai part ɗin hajiya mama. Bayan an kammala suka koma can da zamam babu ruwansu damu balle yaya mukaci, sai tarin masifa da hantara a garemu. Gidan da Aliyu ya sai min da kuɗin hayarsa na cigaba da ɗaukar nauyin karatunku, sai taimakon Sheikh Aliyu Maina abokinsa. Dan ya matuƙar taka rawar gani akan rayuwarmu shima. kullum nunamin yake nayi haƙuri na cigaba da rayuwa da Halilu har kukai girma dukiyarku ta dawo hannunku sannan na rabu da shi. Wannan yana cikin dalili na na karshe bayan tuna halacci da ƙauna da mahaifinku da Malam suka nunamin a rayuwa, yayinda kowa ya gujeni har ƙannen mahaifiyata. Shiyyasa kukaga ina cigaba da jure komai har kawo iyanzu da insha ALLAHU komai yazo ƙarshe, zamu bar musu gidan duk da kuwa haƙƙinmu ne. Dukiyarku kuma idan ma bai baku ba ku barsa da ALLAH kawai tunda ya rufa mana asiri bamu rasa ci ba balle sha da suturar sakawa. Fatana kar wannan labarin ya sakaku tunanin ɗaukar wani mataki akan hajiya mama da Halilu. Ku barsu ALLAH zai muku maganinsu ta hanyar da bakuyi zato ko tsammani ba. Dan banason ya cutarmin daku. Dan ALLAH na roƙeku ku barsu mu rabu lafiya salin alin”.
Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu, sai faman sharar hawaye kawai sukeyi.