Showing 48001 words to 51000 words out of 165076 words
Chapter 17 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt
ƙasar China ko wata ƙasa daban yin karatunki. Abinda kawai zakiyi shine neman yardar mijinki”.
A take wani irin farin ciki ya baibaye Hibbah. Ta ɗaga hannu tana addu'ar godiya ga UBANGIJI da fatan nasara akan alƙawarinta.
Shiko dattijo A.G na tayata da amin. Sai da ta sauke hannayenta sannan ya tura mata takarda da pen.
Ki rubutamin dukkan sunayen ƴan gidanku da duk wanda kike tunanin kawo tangarɗa akan auren yayunki anan”.
Takardar ta jawo gabanta tana wani irin dariyar ƙeta. Dan babu wanda take hangowa a idanunta sai Hajiya Mama da su Kawu Hannafi. Bayan ta gama zana masa ya bata wata bag dake ɗauke da tarin files da suka shafi Master. Ya ɗora da gargaɗinta akan muhimmancin riƙe musu sirrinsu.
“Dukkan abinda zaki buƙata da ya shafesa na tanadar miki anan, dole ne sai kin fara shiga kansa, kinyi irin tunaninsa. Ke mace ce, kuma ƙaramar yarinya. Inaji a jikina kafin ya ganoki ko ya farga da ke kin kammala aikin nan insha ALLAH. Kisa a ranki ALLAH na tare da ke, kuma duk inda kika shiga akwai jami'an dana tanada zasu dinga bibiyarki ke da ƴan uwanki domin baku kariya.”
Kai kawai Hibbah ta jinjina masa. Da ga haka ta fito mai taxi ɗin da ya kawota station ɗin ya sake ɗaukarta domin maidata gida.
★★
Kamar yanda Hibbah tai fata koda ta shigo gidan nasu bata sami kowa a falo ba, yayunta babu wanda ya shigo, Ummi kuma tana ɗakinta. Ɗaki ta wuce ta adana bag ɗin da tazo da ita sannan ta fito ta sanarma Ummi ta dawo.
Sosai Ummi ke binta da kallon mamaki ganin tanata washe haƙora kamar ba itace ta fita da ɓacin ran zancen aurensu ba. Komai Ummi batace mata ba akan walwalar tata. Sai ma ce mata da tai idan ta gama taje tai mata list na kayan kwalliya da kayan underwears.
Cike da zumuɗi Hibbah ta fice dan tasan na kayan lefen yayunta ne da za'a haɗa a gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra'uff Maina. A gurgije tai wanka ta kimtsa kanta. Ko abinci bata nema ba duk da yunwa da ciwon kan da ke damunta har yanzun, tai zaman rubuta list ɗin bayan ta kunna wayarta ta shiga WhatsApp ɗinta tana bugar cikin Hafsat da Zahidah akan kalo da sayis ɗinsu.
Cikin awa ɗaya ta kammala komai ta fito ɗauke da takardar. Kai tsaye ɗakin Ummi takai ta ajiye sannan ta fito wajen yayunta suka cigaba da hira. Su kansu sunyi mamakin ganin yanda taketa faman walwala tamkar yanda suka santa tun fil'azal. Sai dai komai basuce mata ba suma.
*________________________*
Kwana uku da faruwar haka Muhammad Shuraim yazo gidan su Hibbah a karon farko. Ya sami ƙyaƙyƙyawar tarba da ga wajen su Yaya Umar, inda aka saukesa ƙaramin falonsu da Dadynsu kan sauke baƙi kafin rasuwarsa.
Da farko Hibbah catai ita bata gayyatarsa, dan haka bazataje ba. Sai da Ummi tai mata jan ido sanann ta zumbula hijjab ta fita ɗauke da karamin tire da aka ɗora ruwa.
Tunda ta shigo da sallama ya kafeta da idanunsa manya da ke neman rikitata. Tiren ta ajiye saman Centre table ɗin falon tana harararsa da kumbura fuska.
“Malam lafiya?”.
Ta faɗa cike da tsiwa.
Kansa ya ɗan girgiza kawai yana lumshe idanunsa dake a kanta ya sake buɗewa. “Ina tausayin bakin nan naki saboda tsiwansa, amma babu komai lokaci kaɗan ya rage ya daina”.
Baki ta taɓe da kaiwa zaune cikin kujera tana faɗin, “Karka ɗauka maganin da kaima iyayena suka yarda da kai lokaci guda nima ya cini. Wasu dalilai ne kawai sukasa na yarda da aurenka badan kayi dai-dai da ra'ayin mijin da naima kaina buri ba”.
“A hakanma na gode. Na kuma sake tabbatar da cewa nazo inda ya dace neman aure. Dan biyayyar da kikai ga iyayenki kawai cikakkiyar amsace akan nagartaciyar tarbiyyar da kika samu da ga garesu mai inganci.”
“Humm” kawai Hibbah ta faɗa batare da tace komai ba.
Shuraim ya murmusa batare da ya nuna damuwa da yanayin nata ba. “Kamar yanda na faɗa miki sunana Muhammad Shuraim Aliyu. A garin nan aka haifeni, anan na tashi, anan na girma, anan nai karatun addini dana boko har zuwa secondary. Kafin na ƙetare wajen ƙasar nayo karatun jami'a har zuwa matakin degree na biyu. A yanzu haka ina akan haɗa degree na na uku tare da harkar kasuwanci tamkar yanda na taso na gani anayi a gidan mu. Abinda ban faɗa miki ba bayan wannan kuma na baki damar yin bincike a kaina dan ki sani. Ƙwarai da gaske naji daɗi matuƙa na samunki musamman da ya kasance ban zaci hakan ba. Abinda zance kawai kiyi haƙuri banyi kamar yanda samarin wannan zamanin keyiba na fara shimfiɗa soyayya kafin aure. Ni sam hakan ba ra'ayina bane ba, shiyyasa tun farko ban taɓa zuwa ƙofar gidanku ba kai tsaye sai dai bibiyarki kawai. A randa kuma iyayena sukazo domin neman izinin zuwa zance gunki sai akace anma bani ke, dan ƙa'idarku ku ba'a barinku dama yin zance. Nagode ƙwarai da gaske Muhibbat. Ina fatan zaki amsheni da hannu biyu batare da tunanin nayi miki kutse cikin rayuwarki ba?”.
Har ga ALLAH kalamansa sun sanyaya ranta. Taji matuƙar kinarsa da girmansa. Sai dai maganarsa ta kusan ƙarshe-ƙarshe akan ba'a barinsu zance ta tsaya mata arai. ta kuma sake tabbatar mata akwai abinda Abba ke ƙullawa game da auren nata da Shuraim, wanda shima da alama baida masaniya akai.
Numfashi taja tare da duƙar da kanta ƙasa, dan a karon farko taji kunyarsa da nauyinsa ta lulluɓe ta. Cikin sanyin muryar da batasan tana da ita ba tace, “ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”.
“Amin ya ALLAH” ya faɗa yana murmushi dan ya fahimci dukkan abin cewar data shigo da shi falon ya gudu.
Ba wata hira mai tsayi sukai ba, sai ɗan guntun tarihinta itama data bashi sukai sallama ya tafi itama ta shige ciki. Dama ALLAH-ALLAH take ya wuce ta tafi ga aikin da ke gabanta akan files ɗin da dattijon jami'i ya bata (kamar yanda ta raɗa masa suna😂). Dan tun randa ya bata washe gari ta kwashe Computer ɗinta da ga falo ta maida cikin bedroom. Koda Ummi ta tambayeta dalili sai tace babu komai zata ajiyesu ne dan ta daina amfani da su sai nan gaba.
Ummi ta gamsu da bayaninta ɗari bisa ɗari. Sai dai abinda bata sani ba tuni Hibbah ta haɗa kayan a ɗakinta harma ta fara aiki akan abinda aka sakata. Ta samu bayanai na laifukan da Master ya aikata kashi-kashi, sai flash drive guda uku dake ɗauke da wasu rubuce-rubucensa na yanar gozo, da fuskokin da yake amfani da su. Abinda ta yanke na farko shine zaman yin nazari da kutse na musamman akan facemasks da yake amfani da su. Haka kawai taji a ranta tana son samo ainahin fuskarsa ta ainahi da take kallo a matakin farko na aikinta. Zatayi hakanne ta wasu hanyoyi da take ganin zasu taimaketa duk da ko farcensa baya bari a gani rufesa yake. Sai duka handles ɗinsa na yanar gizo da ya taɓa amfani da su ta hanyar tura saƙo. Da nambobin waya da yay kira dasu masu tsananin tsaro.
Yanzu gaba ɗaya lokacinta da hankalinta duk sun koma akan binciken Master da ayyukansa. Ta matuƙar maida kanta busy batare da kowa ya sani ba. Sai da safe ne idan Yayunta suka ga idanunta duk a kumbure suyita tambayarta miya hanata barci?. Takance karatune na exam da zasu fara. Tanason ta dage ne saboda shirye-shiryen exam ɗin zai haɗe mata da hidimar biki.
Duk sun gamsu da bayanin nata, dan haka sukai mata nasiha kawai akan ta ringa sassautawa tana barci dan karta saka kanta a matsala. Insha ALLAH zataci.
★★★★★
A lokacin da Hibbah keta kaikawo akan ƙoƙarin yin kutse cikin lamarin Master a gidansu shirye-shiryen biki ake tuƙuru ta fanin su Hajiya Mama da Abba da ke faman jiyyar ƙafarsa da hannu. Shiri suke na bikin ƴaƴan gata ta kowanne fanni. Dan hatta da gidajen da su Yaya Muhammad zasu zauna da amare Abba duk ya saka abokinsa ya nema musu haya, ya kuma biya kuɗin hayar da kudinsa acewarsa zai biya na farko daga haka su cigaba da biya.
Komai dake faruwa Ummi na kallo. Sai dai ta maida kanta makauniyar ƙarfi da yaji bata taɓa nuna alamar tana fahimta ba. Sai ma faman nata shirye-shiryen da takeyi ita da Sheikh Aliyu Maina da iyalansa itama. Dan a yanzu haka ma anata shirin miƙa akwatunan lefen auren su Yaya Muhammad da suka haɗama kansu da kansu zuwa gidan amarensu. Gidansu kuma na gab da kammaluwa sai sam barka da fatan alkairi.
*______________________________*
Kwanakin biki sun cigaba da turawa, shirye-shiye na ƙara faɗaɗa a kowanne ɓangare. Sai dai kuma a ɓangaren Hibbah ita hankalinta a tashe yake matuƙa bisa dalilai biyu. Na farko shine har yanzu bata sake ji da ga jami'an tsaro ba, musamman akan binciken da sukace zasu mata game da Muhammad Shuraim da zuwa yanzu shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakaninsu. Dan tun daga waccan ranar duk bayan kwana biyu sai yazo gidansu. Bawata hira sukeba mai yawa, mafi yawanci ma akan karatu ne dan tafi sakin jiki da shi.
Na biyu ganin yanda su Abba ke shirye-shiryen auren duk da yana kwance har yanzu yana fama da ƙafa sai yake ɗaga mata hankali take ganin tamkar tarkon data ɗana musu domin kuɓutar da yayunta bamai yuwuwa bane a garesu. Cikin ɓacin rai yau ta tattara dukanin kayan da A.G ya bata ta maida a bag ɗin. Dama addu'a taketa faman yi ALLAH yasa Ummi ta fita zuwa gidan malam da taji tana faɗa zata.
Tana samu yayunta suka fita, Ummi ma ta fita gidan malam ɗin tare da su sai itama ta samu ta siɗaɗa ta fice da addu'ar ALLAH yasa har taje ta dawo Ummi bata dawo gidan ba.
Tana shirin shiga napep aka dakatar da ita. Tai saurin juyowa a rikice jin an ambaci sunanta. Kallon sama zuwa ƙasa taima matashin saurayin da batasan daga ina ya fito ba. Shima batare da wani damuwar kallon da take masanba ya miƙa mata ƙaramar jakkar hannunsa.
“Babu buƙatar ki sake komawa can. Zaki sami dukkan bayanan da kike buƙata anan. Akwai waya yace zai kiraki tanan zakuyi magana. Kiyi komai da kula”.
Batare da ya jira cewarta ba ya juya ya barta tsaye galala da jikka a hannu tana binsa da kallo. Takaici da haushi yasa mai napep jan napep ɗinsa yabar wajen yana masifar an bata masa lokaci.
Itama Hibbah juyawa tai ta koma gida jiki da sauri..............✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
_________________________
Chapter Seventeen_*
............Haushi da takaicine ya turnike Hibbah lokacin da ta iso gida ta buɗe jakar da saurayin ya bata. Babu komai a ciki sai ƙaramar waya da ko number guda ɗaya babu a ciki. Sai wani shegen voice recording guda ɗaya da taji bata buƙatar sanin kona uwar miye. Wadrobe ɗinta ta buɗe ta cilla wayar ciki tana jan tagwayen tsaki.
Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai fita harkar waɗan nan ƴan sandan. Dan ta fahimci babu abinda zasu mata sai amfani da ita domin samin cikar burinsu tamkar yanda Yaya Abubakar ya faɗa. Inko hakane tayi alƙawarin bazasu sake ganinta ba........
Sallamar Ummi da tajiyo ne ya sata ajiye komai ta fito tana amsawa. Ummi ta kalleta da mamakin ganin yanayinta. “Tanee kina lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau Ummi, kainane kawai ke ciwo amma nasha magani.”
“To ALLAH ya ƙara sauƙi. Kije ki kwanta kozai faɗa miki mu gani”.
Kanta ta jinjinama Ummin dan dama haka take buƙata. Da wannan damar ta koma ɗakinta ta cigaba da nazarin neman mafitar da ya dace ta kuɓutar da ahalinta da ga abinda ƴan uwan mahaifin nasu suke shirin ƙulla musu.
Koda Yayunta suka dawo ma tana jinsu ta kasa fita ayi hira da ita. Tana jiyo duk wanda ya tambayeta sai Ummi tace tayi barci kanta ke ciwo. Duk sun jajanta tare da nuna damuwa tamkar yanda suka saba. Daga nan suka ɗan taɓa hira kowa ya kama gabansa zuwa makwanci.
Duk yanda Hibbah taso yin barci a wannan daren ya gagara, babu abinda take sai saƙawa da kwancewa har asubahi, tana kuma idar da salla ta yo waje ta hau aiki. Lokacin da yayunta suka dawo salla suka samu tana aikin ba ƙaramin mamaki bane ya kamasu. cikin jan faɗa Ammar ya rike baki da faɗin, “Auta halan yau mafarkin zakici bulala hanun Ummi kikai ko? Inba hakaba kece yau da aiki a wannan sanyin safiyar”.
Fuska Hibba ta ƙwaɓe kamar zatai kuka. “Yaya Muhammad ka gansa ko! Ni dai ai ban tankashi ba zai kama jana faɗa da safen nan”.
Ranƙwashi Yaya Muhammad ya kaima Ammar akai, shi kuma ya kauce da sauri yana dariya da yima Hibbah gwalo. Su kansu su Yaya Usman dariyar suke ƙoƙarin dannewa. dan kowa dai yasan ɗan karan lalacin Hibbah akan aikin safe. Tanada kazar-kazar ɗin aiki amma banda na safe saboda shegen son barcinta. Ganin idan suka cigaba da tsiwa zata kufce musu yasa suka bar wajen da sauri. Itama sai ta cigaba da aikinta kawai.
Ranar ita kaɗai tai aikin gidan, ta haɗa musu breakfast mai sauƙi sannan taje tai wanka ta fito. Yanzun kam gaba ɗayansu ido suka zuba mata ganin bata da walwala sam. Sai da taja kujera ta zauna Ummi da ke kallonta tace, “Ciwon kanne har yanzu?”.
Kanta ta girgizama Ummi a sanyaye. “Ya daina Ummi, kawai dai banajin daɗin raina ne”.
Shiru duk sukai suna kallonta cike da nazari. Yaya Usman da ke motsa shayi yace, “Auta akwai abinda kike ɓoye mana ƴan kwanakin nan. Sasai walwalarki ta ragu, kin bar zama hirar dare, ko yaushe kina cikin ɗaki. Shin kodai matsalar Shuraim ɗin ce har yanzun baki haƙura ba?”.
Cikin ɗan rawar murya Hibbah tace, “A'a yaya ba shine ba. Ai nace muku na haƙura zan auresa. Dan nima zuwa yanzu na fahimci mutumin kirkine. Kawai dai ina tunanin ku ta yaya za'a raba ku da auren su Ameerah kamar yanda na samu kubuta daga auren Junaid. Yaya inaji a jikina akwai abinda su Abbah suke ƙullawa game da ku. Ni na rasa miyasa basa son mu? Mi muka tare musu ne a gidan nan? Minene laifinmu a garesu?....” takai ƙarshen maganar da saki kuka mai cin rai da ya saka su ajiye cokulan hannunsu su duka suka zuba mata idanu.
Ummi ta rumtse kofin dake hannunta da ƙarfi. Wani irin ƙuna da ɗaci na sukar zuciyarta. Batare data farga ba harshenta ya suɓuce wajen faɗin, “Baku musu laifin komai ba Tanee. Sun tsaneku ne kawai saboda ni mahaifiyarku da ƙaddara ta kawoni cikinsu matsayin bara gurbi”.
Gaba ɗayansu suka maida dubansu