Shiyyasa har ƙasan ranta takejin akwai wata a ƙasa da suke ƙullawa.
Wasu hawayen tausayin Ummi da su kansu ya cika mata ido. bayan hannu tasa ta share tare da kwantar da kanta jikin sit ɗin ta lumshe idanu ko kanta zai sassauta sara mata.......
Ummi nacan na dakon jiran dawowar Hibbah itama, dan yau da kanta ta soyama Hibbar wainar filawa da tasan tana matuƙar so. Yayinda can ƙasan ranta ke cike da fargabar taruwar dangin mijin nata da nata a gidan. Dan tasan akwai abinda suke ƙullawar da gaske. Sai dai kuma ta saka a ranta komi zasu ƙulla insha ALLAHU ta gama shirya musu a wannan karon. dan itama tun a jiya data fita ta gama tsara komai akan makomar ƴaƴanta. Nasu kawai take jira yanzu ta ɗora da ga inda ta tsaya.
Ilai kuwa hasashen Ummi yayi dai-dai, dan tana tsaka da wannan tunanin akai kiranta sashen Abba ɗin. Hijjab ta saka har ƙasa ta tafi. Tun a falo Maomy ta sakar mata wani habaicin da ya tsaya mata a rai. Sai dai batace komai ba ta ƙarasa falon Abba.
Su kawu Bello ta samu da wasu a dangin Abban. Sai hajiya mama. Bayan ta gaishesu ta nema waje ta zauna duk da ba dukansu suka amsa ba.
A gadarance Kawu Ayuba ya fara bayani. “Hasiya basai mun sake ɓata lokacin tisa magana ba. Nasan kema tunda kika ganmu anan kinsan zancen. Kamar yanda su Yaya Ballo sukazo kwanaki akan maganar auren ƴaƴanki da yaran wajen Alhaji Halilu yanzu batun saka rana ne ya tashi. Saboda tsabar halacci da hangen nesa irin nasa yace kawai tunda munzo dubasa a saka. Shi baya wani bukatar ƴan kunji-kunji tunda batun tuwona maina akeyi. To a yanzu haka dai ga kayan saka rana nan ma duk ya saya dan yace shine uban anguna shine na amare, kuma koma bai faɗa ba dama shine, tunda tun suna kananunsu shiketa wahala akansu. Koda kuwa mahaifinsu na raye shine mai bada auren nasu ai dama. Basai na jaki da nisa ba. Yanzu haka dai an yanke ranar aure wata biyu kacal. Batun kayan aure na akwati da kukeyi anan binni duk yace zaiyi baya buƙatar komai da ga yaran nan. Ita kuma Muhibbatu tunda kun saka yarinya ta nuna bata bukatar wannan haɗin, da azo ta bijire bayan auren kota illata yaro kawai za'a fasa. Za'a bata shi wanda ta kawo ɗin ALLAH ya basu zaman lafiya.....”
A firgice Ummi ta dago ta dubi Abba. Wani shegen murmushi ya sakar mata tare da kashe mata ido ɗaya. Zatai magana yay saurin katseta cikin marairaicewa. “Hakan ai shine yafi kwanciyar hankali Kawu Ayuba. Kaga da alalata zuminci gara dai abi komai a sannu zaifi. Kuma ita mace ce. Banason a cuta mata akan abinda bataso. Dan yarinyace mai hankali da nutsuwa. Duk da damuwar da Junaid ɗin ya shiga nace ya haƙura kawai tunda tana da zaɓinta. Kuma zaɓin nata ma naga mutumin kirkine sunansa Muhammad Shuraim. Ɗan gidan Alhaji Aliyu ne mutumin kirki. Inajin kunyar ma nace bazan bashi jinina ba”.
Harga ALLAH Ummi ta shiga ruɗani, ta kuma ji ɗan sanyi ta wani fannin. Dan tana mamakin ta yaya shi Abban yasan da zancen zuwan Iyayen Muhammad Shuraim ɗin? Kodai su masu kawo kuɗinne sukai mistake ɗin zuwa nan kawo kuɗin maimakon gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina? Lallai akwai abinda bata sani ba. Dan akwai manufa da dalilin yin hakan ga Abba, saboda halin makircinsa da ta sani. Hakanan salin alin bazai hana ɗansa ba ya bama wani.........
“Wannan shaiɗancin dai nasan ita ta kitsashi. Duka yarinyar nawa take da tasan wani bijirema zaɓin iyaye. Ni wlhy dan Halilun yace a barta ne da baza'a bari ba. Sai dai idan an aura mata Junaidun ta mutu”. Sababin Kawu Bello ya katse ma Ummi tunaninta.
Cikin makirci Abba ya amshe da faɗin, “A'a kawu bello ba'ayi hakaba ai. shima wnanan ɗin mutumin kirki ne wlhy. Dan yamafi Junaid nagarta. Muyi fatan ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.
A take duk ƴan falon suka shiga yabon Abbah da jinjinama ƙoƙarin sa, Ummi kam anata zaginta wai bata da godiyar ALLAH akan ƙoƙarin da Abban keyi tun bayan rasuwar mahaifin su Ammar. Tare da yi mata gugar zana na habaicin asalinta.
Ita dai uffan batace da su ba. Hasalima hankalinta ya rabune gida biyu. Duk sauran bayanan da suka cigaba dayi sai tama koma bata fahimtar komai. Jinsu kawai dai take da kunne da binsu da ido har aka tashi a taron ko nace suka sallameta.
Koda ta fito a sashen taso zuwa gidan malam sai dai gudun abinda zaije ya dawo da fitar tata yasa ta haƙura. Dan haka tai kiran numbar wayar matarsa da yake ƙawarta ce suna zuminci sosai duka biyun. Sai dai tasan uwargidan Maimunatu yanzu haka tana Oman da autan gidan dake karatu acan.
Bugu biyu Malama Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa da ɗan barkwancin ƙawaye Ummi take tambayarta ko Malam na nan kuwa?.
Malama Jiddah tace, “Eh yana nan, sai dai yana tare da kamar baƙin da naji kunyi magana ranar zasuzo yau ɗin. Lafiya dai ko?”.
“Tofa, kaji wani kuma ruɗanin. Umm Muhammad! Lafiya dai ba lafiya ba. Akan baƙin dama na kirasa ban samu ba......” (Komai Ummi ta zayyane mata da ya faru yanzun anan gidansu).
“Bara muga baƙin su wuce to sai na sanar masa. Duk da dai inaji a raina ko duk shine ya tsara hakan dan mijin nan naki sai da siyasa ake iya kamasa a hannu. Ya riga ya zama mai fuska biyu inba ka saniba babu mai cewa zai iya sheɗancin da yake zubawa shi da uwarsa Umm Abubakar. Amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ALLAH yana tare damu”.
“Shikenan Umm Muhammad ALLAH yay mana jagora. A gaishe da yaran sai na jiki”.
Sallama sukai da ga haka zuciyar Ummi fal waswasi da saƙe-saƙe.
*__________________*
Ido Hibbah ta buɗe a ɗan yanayin razana saboda barcin da ya figeta. Gabanta ya faɗi lokacin da idanunta ke kaiwa waje ta windown motar da aka sauke gilashi baki ɗaya. Mazaunin direban ta kalla tana haɗiyar yawu da ƙarfi saboda bushewar da maƙoshinta yayi lokaci guda. Tai saurin ɓalle murfin motar ta fito domin tabbatar ma kanta inda ya kawotan fa ba anguwarsu bane...............✍
*_Tofa. Ina mai taxi ya kai Hibbah?. Wane ruɗanine ya shiga kan Ummi game da kawo kuɗin auren Hibbah da ga gidan su Shuraim? da alama ta nuna tasan da zancen. Shin malam Aliyu Abdul-Ra'uff Maina ne ya fara aika iyayen Shuraim ga Abba kokuwa yaya abin yake ne? Wane shiri Ummi keyi akan yaranta da takejin ƙarfin gwiwar nasarar kubutar dasu ne haka? Minene shirin Abba shima game da fasa bama Junaid ɗansa auren Hibbah ya yarda ya bama Muhammad Shuraim? Shin kodai dama shine ya turosa batare da ita Ummin ta farga ba?. 🤔tambayoyinfa da yawa. Yayinda ni kaina amsarsu nake nema🚶🏻😩._*
________________________
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI......_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*
*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
.........Da sauri ta dafe kanta da ya sara mata da ƙarfi. Cikin ɗacin murya da zafin da takeji a zuciyarta tace, “Wai nikam mina muku ne na laifi? Dan ALLAH kubar rayuwata ta cigaba da tafiya a yanda take karku sakamin ahali a masifa. Wancan karon kunce dan na bibiyi wanine. Wannan karon kuma mina aikata zaku kawoni nan?”.
“Duk bani da amsoshin tambayoyin nan naki. Aikina kawai shine ɗakkoki na kawoki nan wajen. Gashi kuma na cika. Amma idan muka shiga da ga ciki harma abinda baki tambaya ba za'a baki amsarsa na sani”.
A fusace Hibbah ta dubesa zatai magana aka katseta......
“Gaskiya ya faɗa miki, bashi da amsar da zai baki. Dan haka bismilla ɗiya ta”. Dattijon wancan karon da aka kaita office ɗinsa ya faɗa dai-dai yana ƙarasowa inda suke. Dan tun shigowar taxi ɗin cikin station ɗin yake kallonsu ta window. A fahimtar da yay mata na tsiwa da rashin tsoro da kafiya ya sashi yanke shawarar sakkowa da kansa ƙila tafi jin shakkarsa ta shiga.
Sai dai kuma ina. Shima a fusace ta kallesa wasu hawaye masu zafi suna sakko mata. Ganin tana motsa laɓɓanta alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. “Nan ba muhallin da ya dace ki cigaba da cewa komai bane ɗiyata. Ina mai tabbatar miki wannan kiran yasha ban-ban dana farko. Dan kai tsaye ke zai taimaka bamuba Muhibbat. Bakomai yasa nace hakaba sai ƴan uwanki dake gab da shiga haɗari”.
“Ƴan uwa na?!”.
Hibbah ta faɗa ƙirjinta na wani harbawa. Uffan jami'in dattijo A.G baice ba ya juya zuwa office ɗinsa. Da sauri tabi bayansa har tana haɗawa da ɗan gudu. Dan ba ƙaramin hargitsa tunaninta maganarsa ta ƙarshe tayi ba. Duk da yanajin tana binsa da gudu bai tsaya ba sai da ya isa har office ɗinsa. Kusan a tare suka shiga da Hibbah. Tai saurin zuwa gabansa ta durƙusa.
“Uncle dan ALLAH karku cutarmin da ƴan uwa. Ku daina tursasani yi muku abu ta hanyar yimin barazana da su. Kunsan kuwa mi kuka nema haddasama rayuwata a wancan karon? Saura kaɗan na rasa Ummi na, gatana ni da yayuna. Farin cikinmu madubin rayuwarmu. Miyasa kuke son saka alkairi da sharri? Miyasa kuke son yin amfani da ni saboda ku haskaka kanku ma duniya? Miyasa ku ke........”
“Ya isa ɗiyata. Duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba a wannan gaɓar. Yanda kiɗan ya sauya itama rawar zata sauya ne dole. Inason ki nutsu ki bani dukkan hankalinki nan, domin haɗa hannu wajen tabbatar ma mutanenmu abinda suke ganin bazai yuwu ba saboda rauni da ƙarancin shekaru da suke kallo kai tsaye”.
“Ni bazan nutsu ba, bazan taɓa nutsuwa ba dan ku taurarine masu wutsiya. Dan ALLAH ku daina saka rayuwata data ahalina cikin *_TAKUN SAƘAR KU_* da bawan ALLAHn nan. Bani da alaƙa da komai nasa kamar yanda kuma bani da alaƙa da ku. Indai harkar computer ce na barta har abada duk da kuwa itace burina, itace mafarki na, itace zummata, itace kaifina. Amma saboda cigaba da rayuwar ahalina cikin salama na tattarata na ajiye. Na manta kaina cikin waɗanda suka iya koda kunnata. Please na roƙeku ku barmin rayuwa data ahali su huta. Ku barni naji da damuwar cikin gidanmu ita kaɗai ta isheni”.
Yanda ta haɗe hannaye tana roƙonsa hawaye na kwarara a kumatunta duk sai tausayinta mai tsanani ya kamashi. Idanunsa suka kaɗa sukai jajur. Kansa ya shiga girgiza mata yana ƙoƙarin kamo hannayenta dake haɗe har yanzu waje guda alamar rokonsa🙏🏻. Sai dai yana kawo hannu ita tai azamar jan nata baya.
Da sauri yace, “Shike nan naji zan barki ki tafi. Amma ki tabbatar Tabbas kinada alaƙa da Master Muhibbat, saboda wannnan ɗin kasarki ce, kuma a ƙasar taki yake aikata dukkan ɓarnarsa. Sannan rayuwar yayunki da mamanki na cikin haɗari a hannun ƙanin mahaifinku da shi wanda kike ganin baki da alaƙar komi da shi. 1Mu kaɗai ne kawai kuma zamu iya cetosu tare da ke kanki. Zakuma muyi hakanne kawai idan kin amince kin yarda zaki cigaba da mana aiki akan mutumin nan Master. Idan kuma bazakiyi ba zaki iya tafiya kawai”.
Shiru Hibbah tai tana kallonsa. Kallo mai cike da ma'anoni da yawa da ita kanta ko ca'akai ta fassarasu bazata iya ba. Kansa ya jinjina mata alamar tabbatarwa.
Sosai zuciyar Hibbah ke ƙara wani irin lugude, babu abinda ke mata kai kawo a zuciya sai batun auren yayunta da ƴaƴan Abba. Dama har cikin ranta tanaji akwai manufa, amma batasan miyasa Ummi ta amince ba bayan kuma ta sanar mata yayun nata nada waɗanda suke so. Wani tunani da yazo mata daban a cikin rai ya sakata kai hannu kawai taja kujera ta zauna tana share hawayenta da suka kasa tsayawa. Shima sai ya sauke ajiyar zuciya da takawa wajen kujerar zamansa ta office ɗin ya zauna yana fiskantarta.
“Miyasa sai ni kaɗai ce zan muku aikin? Bayan nasan akwai mutane da yawa masana kuma jajirtattu akan wannan harkar, waɗanda idan a gabansu nake ni ɗin bakomai bace, bansan kuma komaiba?”.
“Tunani mai ƙyau Muhibbat. Tambayarki na da matuƙar muhummanci kuma ta birgeni. Har cikin raina na sake yarda zaki iya domin kina da kaifin ƙwaƙwalwa. Kafin kiyi mana wancan aikin tunanina irin nasune, ina kallon raunin mace matuƙa nima. Ko a cikin hukumar nan aka bama mace aiki raina kan ɓaci naga babu abinda zata iya. Amma sai ke kika ruguza dukan wannan tunanin nawa a waccan ranar, dan kinyi abinda ƙwararru da yawa suka kasa matsayinki na mace mai ƙarancin shekaru kuma ɗaliba da iya ƙasarta kawai ta samu ilimin kimiya da fasaha. Na zauna nayi dogon nazarin da yasa na fahimci irinku ba'a sakaci da al'amarinku, dan da irinku ƙasashen turawa suka cigaba a nasu ƙasashen da suke birgemu a yau. Muhibbat na miki alƙawarin wannan aikin ƙashin kanki zakiyi. wanda dole duniya tasan da zamanki bayan kammaluwar komai insha ALLAHU. Inason barinma bayana alkairi bayan na ajiye aiki, kuma kece wanan alkairin da nake fatan bari insha ALLAH. Da kuma wanan damar zakiyi amfani kema wajen ceto ahalinki da sake darajasu cikinƴan uwanku, ki wanke baƙin fentin da ƙanin mahaifinku da kakarku sukai muku wanka da shi. Da wanan damar zaki canja masu irin tunanina game da ɗiya mace”
Murmushi Hibbah ta saki wanda ita kaɗai tasan ma'anar kayanta. Ta ɗan muskuta zamanta da faɗin, “Na amince zan muku aiki, sai dai ku sani hakan ba yana nufin idan baku sami nasarar kamashi ba zan cigaba da dawowa nan wajen. Zan muku abinda kuke buƙata ko ba'a sami nasara ba nima zaku kuɓutarmin da ahalina”.
“Tabbas mun amince, harma da wata gagarumar ƙyauta da zaki samu inhar yazo hannun namu.”
“Yallaɓai na bar muku ƙyautar basai kun bani ba. abinda kawai nakeso shine ranar auren yayuna ana gab da halartar ɗaurin aure ku kama Abba ku ɓoye min har sai an kammala ɗaura auren yayuna da matan da suke so da kwanaki biyu. Abu na ƙarshe kuma inason amin cikakken bincike akan Muhammad Shuraim da Abba ya iya hana ɗansa ya yarda na auresa duk da zaɓin Ummi na ne shi”.
“Duk mun amince da sharaɗinki”.
Murmushi Hibbah ta saki a karo na biyu. “Inhar ya kasance Muhammad Shuraim bashi da wani aibu a rayuwarsa zan auresa na rayu da shi matsayin miji kodan son da Ummi na da Yayuna ke masa. Zanbi duk hanyar da zanbi na ganin ya ɗaukeni zuwa ƙasar China yin karatuna akan ilimin kimiya da fasaha. Ni kuma a wannan lokacin zan muku aiki. Ko wanene wanan master ɗin nayi alkawarin insha ALLAH sai na zama sanadin da zaku kamashi a tafin hannunku. Dan haka na baku dama kafin kwanakin aurenmu 60 da aka saka nasan wanene Muhammad Shuraim ciki da bai. A samama ahalina waje na musamman da zasu rayu a lokacin da zan fara farautar MASTER. Dan ko ƙwarzane bana son ya samu koda farcinan hannunsu”.
Wani irin tattausan murmushi dattijo A.G ya saki, yayma Hibbah jinjina. “Tun a ranar farko da kikazo nan na tabbatar zaki iya a cikin idanunki, tabbas zaki iya. Kuma insha ALLAH dukkanin bukatunki zasu biya Muhibbat, daga ƙarshe ƙyautar dana ambata zata kasance biya miki kuɗaɗen tafiya