Showing 93001 words to 96000 words out of 165076 words

Chapter 32 - TAKUN SAKA COMPLETE DOCUMENT Romantic Book.txt

05 Nov 2024

74046

yake dan shikam jin wata sabuwar ƙaunar shi yake har cikin jini da ɓargo duk da har yanzu bai faɗi dalilinsa na wawasar kuɗaɗen ba bayan dalilin kama Master daya kasance mai laifi a garesa.
Master ya cigaba da faɗin, “Na shigo rayuwarku ne a dalilin Muhibbat, sai dai labarin ya sauya adalilin karamcin Ummi da ku kanku. Sai kuma randa na jima Halilu ciwo saboda ranar na fara ganinsa a gidanku, na kuma sansa a matsayin yaron su Alhajin Mande. Wannan dalilin ne ya sani yin bincike akanku sosai harna gano mummunar manufar da yake da ita a kanku. Cikin sa'a kuma abinda yake shiryawa a kankun sai aikinsa ya faɗo hannuna duk da dai nina saka A.G yay hakan batare da shima ya sani ba. Shiyyasa na koma ta bayan fage nazo ma Muhibbat matsayin Muhammad Shuraim. A lokacin da naita bibiyarta nine da kaina. Sai dai kuma ƙanina Musbahu shine yake zuwa gareku da fuskar Shuraim. Yayinda shima kansa baisan niɗin nine Isma'il ba, na kuma cigaba da ɓoye musu zahirina saboda wani dalili nawa daban. Dan basu taɓa sanin ainahin fuskata ba duk da kuwa tun suna ƙanana suke tare dani. Sannan basu taɓa sanin aikin dana tsundumasu a ciki munayi tare ni miye dalilinsa ba. Tsabar biyayya da soyayyar da sukemin ce kawai tasa basu taɓa min musu ba akan komai da nace suyi. Domin gaba ɗayansu na horar da su akan harkar Computer.”
“Kune mutane na uku da kuka san ainahin fuskar Isma'il bayan iyayena da baba. Wanda da farko naje asibiti da wata fuska ne daban, a dalilin Ummi naji bazan iya zuwa mata a baɗinina ba shiyyasa na sake komawa na biya kaso ɗaya bisa ukun kuɗin aikinta bayan na biya duka a farko. A yau kuma na zaɓi bayyana muku zahirin gaskiya ne a dalilin Ummi. Banason ta shiga wani hali akan rashin Muhibbat, sannan ya kamata kusan wane ƙudirine a zuciyar Halilu kar yabi ta wata hanyar ya cutar da ku idan yaga ban masa aikinsa yanda yake so ba. Dan na tabbata zai binciko gidan nan yanzu hakama dan a rikice yake kuma shi mutum ne kamar sauna idan ya ƙwallafa rai akan abu.”
“Na ɗauke Muhibbat ne saboda bin bayan Halilu da tai ranar ɗaurin aure batare da kun sani ba, yayinda ta jiyo sirrikansa masu yawa. A ranar ɗaurin aure yawan mutane yasa bazaku fahimci bana tare da ku ba. Amma kuma nazo, sai dai ganin fitowar Muhibbat da duk da ta saka hijjab da Niƙab na ganeta ya sani fasa bin ƴan ɗaurin aure nabi bayanta. Sai da na tabbatar da inda ta nufa sannan na koma gida a hanzarce, amma tunkan na ƙarasa na kira Habib ya sameta a wajen, hakama maigadin gidan halilun, saboda duk gidajensu na sirri da suke aikata tsiyatakunsu akwai yarana a ciki, amma ba cikin su Habib ba. wasu masu gadi, wasu masu musu aikin gidan batare da sun sani ba. Aurenku kuwa da yaransa dama can na shirya wargazashi tsaf. Dama na tsara sai an kai Muhibbat gidana zaku san nine master, a gefe kuma na cigaba da kasancewa daku matsayin Isma'il. To sai akai rashin sa'a autar Ummi ta buɗemin aiki saboda rashin jinta”.
Murmushi Ummi tayi da kai hannu ta share hawayenta. Suma su yaya Muhammad duk murmushin suke da sauke ajiyar zuciyoyi.
“Kuyi haƙuri da fuskokin yaudara dana zo muku daban-daban. Ni kaina inaji haushin yaudarar Ummi, shiyyasa na zaɓi zuwa na bayyana muku kaina dan ku kanku ku sami nutsuwar shiga sabuwar rayuwa a yau. Hakama Ummi hankalinta ya kwanta kar garin neman gira a rasa ido dan bazan yafema kaina ba idan wani abu ya sameta adalilina. Auta na tare dani tana zubamin tsiwa da tsaurin ido Ummi, sai dai banason ta san niɗin wanene yanzu har sai nan gaba. Aiki akan Halilu kuwa ita daya raina itace zatayi komai da kanta insha ALLAH”.
Dariya duk sukayi, Yaya Abubakar da gaba ɗaya ya tsunduma tunani da nazartar labarin Isma'il Master yay ɗan murmushi, “Ai ni auta kamar ba'a gasa mata baki wajen wankan jego ba. Dan wannan bakin natane ya jefata a tarkon jami'an tsaro su A.G sukaso yin amfani da ita. To ashe wanda suke bulayin neman shi tuni ya gama neme su”.
Nanma dariyar suka sanya. Yaya Umar ya karɓe da faɗin, “Ai bakin auta ya mana rana. Tunda gashi ya jawo mana Master har cikin gida batare da mun saniba. Sai dai muna son sanin ƙyaƙyƙyawar manufarsa kodan mu cirema ranmu zarginsa a jerin na ɗan ta'adda ɓarawo da kowa ke kallonsa da shi.”
“Wannan gaskiya ne yaya Umar. ALLAH ya jikan su Mamy yay musu rahama ya saka musu, amma ya kamata musani kam”.
Cewar Yaya Usman da hawaye suka ziraro masa na tausayin Master ɗin. Gaba ɗaya suka amsa da amin, sannan suka shiga ƙara jero sabuwar addu'a ga mahaifansa. Ummi kam tama gaza cewa komai. Dan zuciyarta a matuƙar raunane take da tausayinsa. Yayinda a gefe takejin matuƙar nutsuwa da kasancewar sa miji ga ɗiyarta ɗaya mace tilo marainiya duk da yaƙi faɗar dalilin nasa na shiga wannan harkar, sai dai tana masa ƙyaƙyƙyawan zato. Sai ɗunbin al'ajab na son zuciya da shahara a zalunci na Halilu wanda suma su Yaya Muhammad ɗin duk yake cin zukatansu......
Master ya katse tunanin Ummi da faɗin, “Ƴan uwana kuyi haƙuri wannan sirri ne mai matuƙar daraja a gareni, badan ban yarda daku ba kuma na ɓoyesa. Insha ALLAH zaku san dalilina wataran. Na yarda ku san niɗin wanene saboda kuma kun sanar dani sirrinku a lokacin da baku gama sanin niɗin wanene ba. Kun kuma yarda dani duk banzo muku a yanda kukai tsammanina ba. Dan ALLAH ina roƙonku ku bizne wannan sirrin a wannan falon har sai ranar da ya kamata gaskiya ta bayyana kanta ga kowa”.
“Tabbas ita amana abuce mai nauyi Isma'il. Kuma ka cancanci muriƙe maka ita dan kaima ka riƙe tamu, yayinda kaketa hidima da gwagwarmaya a kanmu batare da mun sani ba. ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya akan ayyukanka. Ya kuma baka ikon sanar mana dalilin naka wataran. Bani da haufi game da sauran ƴan uwana akan riƙe maka wannan sirrin, dan nasan mahaifiyarmu ta mana horo akan hakan tunba yanzuba. Ballema wannan sirin riƙesa a garemu tamkar rike namu sirrine. Fita da shi kuwa tamkar tozarta kammune.”
Yaya Abubakar ya amshe da faɗin, “Wannan gaskiyane Yaya Muhammad. Insha ALLAHU bazakai baƙin ciki akanmu ba Isma'il. A matsayina na jimi'in tsaro kuma zan cigaba da baka gudunmawa insha ALLAH a duk sanda kake buƙata, sai dai ina roƙonka ka tabbatar duk abinda kake aikatawar nan kanada hujja ta gaskiya aranar kare kai, dan idan naci karo da saɓanin hakan komai zai iya faruwa”.
Murmushi yayi na ƙasaita yana jinjina kansa, “Nagode matuka yan uwana da Ummin mu. Abubakar karka damu kaima insha ALLAH, dan na jima da saninka da kuma gaskiyarka da ƙwazon aiki.
“Shiyyasa kazo kaketa min ƙafar angulu akan auta ko?”. Yaya Abubakar ya faɗa cikin barkwanci.
Dariya suka sanya baki ɗaya. Banda Master da murmushi ne kawai nasa dan dama can yawan fara'a ba ɗabi'arsa bace. Sunema yake sakewa da su matuƙa fiye da zato da hasashe. Duk da dai lokacin baya yana zuwa musu ne da fuskar mutane masu sanyin hali saboda salon acting daya ƙware akai like wani ɗan film. Miƙewa yay yana duban agogo ganin dare yaja. “Kai kai bara na barku kuje ga amare fa Yaya Muhammad kar mu take shari'a. Ummi samin albarka na gudu nima”.
Kansa Ummi ta dafa tana murmushi dan ita kallon ɗa take masa bawai suruki ba. Tai masa addu'a da sanya albarka saboda har yanzu zuciyarta bata gama dai-daita da sheɗancin da Halilu ke shiri akansu ba. Dan ma bataji yana aikata ƙazantar luwaɗi ba kenan. Sallama yay musu ya fita akan zai dawo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai zama busy a satin nan.
Har ƙofar gida su Yaya Umar suka rakoshi zukatansu sakayau bakamar yini da kwanan jiya ba da suka kasance a damuwar rasa Hibbah. Yana tafiya suka rufe gidan suka dawo ciki, zukatansu kuma fal tunanin miyasa yake aikata yahoo? Dan suna buƙatar sanin hakan kodan ƙanwarsu da ke a hannunsa matsayin mata. Bazasu so ta kasance a gararin rayuwa ba, ba kuma zasu so ta kasance da mijin da zai ciyar da ita ta hanyar haram ba.
Sun so zama su tattauna maganar Ummi ta korasu suje ga matansu da safe zatai magana da su.



★★★★


Tunda yabar gidan su Ummi ajiyar zuciya yaketa faman saukewa da dafe kai saboda ciwon da yake masa na rashin sabon dogon surutun daya zuba a yau. Sai dai kuma yanajin zuciyarsa sakayau tamkar ya sauke wasu kaya masu azabar nauyi dake a kansa ne. Sai da ya biya ta gidan A.G ya amshi takardun aikin Abba sannan ya wuce gida.


Koda ya isa gidan a falo ya samu su Habib sun baje kowa da hidimar da yakeyi, ga kayan ciye-ciye sun baje tamkar wata sabuwar bola. Shigowar tasa ce ta saka falon ɗaukar shiru kowa ya nutsu. Cike da girmamawa a garesa tamkar yanda suka saba suka shiga masa barka da zuwa. Hannu ya ɗan ɗaga musu yana bin falon da kallo fuska a tamke da binsu da harara. Sun san laifinsu dan haka suka shiga sosa ƙeya kowa na kai hannu a sace yana ɗauke ledar gabansa da su gwangwanaye.
Komai baice musu ba ya nufi upstairs ɗin yana hawa steps ɗin a kasalance da izzar data zamewa gaɓansa jiki. A dai-dai nan Hibbah da yunwa da damuwa ke neman halakawa ta fito daga cikin ɗaki itama cikin ɗan layin barcin data fara tun bayan idar da salar isha'i. Abincin data hanga a shirye a dining ɗin falon saman ya sata nufar can duk da ta fahimci mai faɗa ajin gidan aka shirya mawa. Kujera taja ta zauna a fili take faɗin, “Daga gani shegen ci ne da wannan mutumin, tunda kuwa ya sakani kuka ɗazun na rantse da yunwa zai kwana shima mugu dangin su Halilu mtsoww ”.
Karaf kuwa wannan zance a kunnen Master da ke hauro step ɗin ƙarshe. Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da kai dubansa gareta da lumsassun idanunsa da tsantsar gajiya da ciwon kai ya kanainaye. Ya ɗan sake tsuke fuska da nufar inda take batare da ita kuma tasan da shigowar tasa ba. Hidimar ma zuba lafiyayyen abincinsa da baba saude ta haɗa masa na musamman takeyi cike da mugunta. Ta ɗiba gasashen hantar da yaji kayan haɗin salad zata kai baki ya riƙe hannun..............✍






*_Gashi nan harda na gobe idan ALLAH ya kaimu😌🚶🏻_*






TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*


*_NAJI DADI SHINE GARI......_*


*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*


_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*


*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*


*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*


*SABBIN LABARAI*


*SABUWAR SHEKARA*


*SABON NISHADI*


*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*


*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*


*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.


*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_


*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_


*_ƊABI'AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_


*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_


*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*


6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank


Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number


08184017082


*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*


09134848107


Littafi daya


1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).


*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽


#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*








*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*




*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*


https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share


*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb




_________________________




*_Chapter Thirty_*


...........Saurin kallon hannun tayi, ƙamshin mayen turarensa dake daɗewa jikinsa yana rige-rigen shigaa hancinta, hannunta tai ƙoƙarin fisgewa ya ƙara damkewa. Zafin daya ratsata saboda yanda ya matse tafin hannunta da spoon ɗin ne ya tilastata ɗago idanunta dole ta dubesa fuska a kumbure. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tai azamar janye nata dan harga ALLAH ƙwayar idanunsa mai kama data gawurtaccen bajimin zaki tsoto take bata. Ɗan luuu yay da idanun tare da dafa makarin kujerar da take zaune ya ranƙwafo kanta har yanzu hannunsa na riƙe da nata.
Gaba ɗaya ta dabirce, ta matse jikinta tana sake ƙoƙarin fisge hannunta amma ta kasa.
“Bayan satan waya ashe har na abinci kin iya kandala?”.
Ya faɗa a saitin kunneta cikin wani irin slow voice daya saka Hibba ɗan zabura ta matsar da kanta saboda wani irin harbawa da zuciyarta tayi, yayinda gaba ɗaya tsigar jikinta ya miƙe. “Ni wlhy bana sata, kuma ba sunana kandala ba”. Tai maganar da saurin yunƙurawa zata tashi ya sake tsare ko ina har tana jin fita da saukar numfashinsa.
Wani ɗan lalataccen Murmushin gefen baki ya saki tare da ɗago hannun nata ya kai spoon ɗin bakinsa batare da ya saki hannunba ya sake faɗin, “Tunda na sameki akan abincin da ba naki ba ai sata ne. Sai shegen handama kin cinye naki zaki haɗa da nawa. Da kin sake ko spoon ɗaya ya shiga wannan bakin mai kama dana akku sai kinyi amansa”. Yay maganar yana sake ranƙwafota da ƙyau cikin alamar tabbatar da zancensa. Sai kuma ya saki hannun nata.
Da sauri ta yarfar da cokalin tamkar wadda ta riƙe maciji. Shima ɗagawa yay da ga ranƙwafawar da yay kanta ya miƙe tsaye sosai akan kafafunsa. Kujerar kusa da ita yaja ya zauna duk da bai ra'ayin cin abincin ba da farko. Plate ɗin data zubama abincin yaja gabansa, tare da sake ɗaukar wani cokalin ya fara ɗiba ya kai bakinsa. Miƙewa tai cikin fushi ta ture kujerar baya tabar gurin hawaye na sakko mata.
Yi yay kamar baisan da tashin nata ba. Sai da ta kai ƙofar ɗakinta ya ɗan ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi da kai abincin bakinsa. (Burum!!!) ta rufo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ƙasaitaccen Murmushin ya sake saki yana miƙewa. Ya ja tissue ya goge bakinsa sannan ya janye idonsa daga ƙofar ɗakin nata. Ɗakinsa ya nufa dan babu abinda yake bukata sama da son jin ruwan ɗumi a jikinsa. Tun kafin ya shige ya zame facemask ɗin fuskarsa ya bayyana a Isma'il ɗinsa.


Hibba na shiga ta faɗa saman gado ta riƙe ciki, dan da gaske yunwar takeji sosai. Babu yanda Baba saude batai da ita ba taci abinci bayan fitarsa gidan amma taƙi. Har tea tace ta haɗo mata tace ta ƙoshi. Hawayen da suka ciko mata ido ta share tana matuƙar jin kewar Umminta da su yaya Muhammad. Ga kayan jikinta sun isheta matuƙar har ƙyanƙyaminsu takeji. Miƙewa tai da tunanin bara ta ɗanyi wanka ko zata rage halin da take ciki ma ta samu damar yin tunanin mafita akan azzalumin nan ɗan homo.
Kusan mintuna sha biyar sai gata ta fito ɗaure da ɗankwalin kayan nata da dudu iyakarsa cinyarta, cinyar ma ko rabi bai rufeba. Da ace zata duka babu abinda zai hana a ga jikinta. Bakin ɗan kwalin ta ɗan sa tana goge gefen kunnenta zuwa goshinta da ƙananun gashi suka kwanta sosai. Dan masha ALLAH hibbah nada gashi yalwatacce. Ga cika ga tsaho gwargwado.
A dai-dai lokacin ne kuma Master da har yay shirin barci bayan ya watsa ruwa ya iso bakin ƙofar riƙe da plate daya zuba abincin kaɗan sai tab.. Da kaya kala ɗaya. Hannu ya ɗaura bisa handle ɗin yana sake tsuƙe fuska dan kansa ciwo yake masa matuƙa. A firgice Hibba ta juyo jin an buɗe ƙofar. Ta zazzaro idanunta saboda daburcewa ma ta gagara neman mafita.
A kanta ya sauke mayatattun idanunsa da barci da gajiya suka maidasu fici-fici. Janyewa yay cike da basarwa yana cigaba da takowa cikin ɗakin tamkar ma bai fahimci dalilin ruɗewar tata ba. Hibba da ta samu nasarar jan hijjab ta saka ta haɗe fuska sosai tana hararsa. “Shi dai musulinci ya bada dokar yanda ya kamata mutum ya shiga waje ai. Amma ba'a dinga faɗoma mutane kamar wata kirsimeti (Christmas) ba”.
Banza yay mata kamar bai jita ba. Sai ma ajiye tarkacen hannunsa da yay saman mirror ɗin ɗakin. Batare da ya sake dubanta ba ya fara magana a daƙile. “Kiyi shopping na duk abinda kike buƙata ta online, idan kika cimin data bayan haka kuma....humm”. Ya ƙare maganar yana watsa mata hararar data hanata sake magana.
Harya fara tafiya tunanin da tayi yanzu-yanzu yasata azamar zabura tai saurin zuwa tasha gabansa. Wani irin shegen kallon da ya saka hantar cikinta kaɗawa yay mata, amma itama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login