Showing 27001 words to 30000 words out of 108352 words

Chapter 10 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt

24 Dec 2024

5621

yasa Mami tace “akawo abincin yanzu Alhaji” girgiza matakai yayi yay hanyar stairs yace “I am coming tukunna muje Aliyu” binshi Hydar yayi har zuwa sama wani babban falo suka shiga wanda kana gani kasan na Baban shine, zama yayi akan kujera Abba yazauna kusada shi yakai hannunshi yabude idanunshi yana haskawa dawani dan tocula dankarami yana dubashi, dan jim yayi sanan yace “you have typhoid Aliyu, I think zan saka on injections tunda bakason magani” yatsine fuska yayi ahankali yace “Abba wlh naji sauki, kainafa kadai ke ciwo kuma yadena” “yimin shiru my friend” Abba yay maganan yana tashi wani babban first aid box yadauko yabude sanan yahada wani allura Aliyu naji yana gani Abba yamai allura, sanan Abba yace “Aliyu this work is draining you, akan me u are a Barrister kawani kama kashiga aikin police with just mukamin ASP eh, why will you choose a police man job Son common talk to me” yay maganan yana kallon Aliyun cikeda damuwa, Aliyu ne kadai danshi namiji, yaranshi duka takwas aduniya, Aliyu ne nafarko he’s 32yrs sai kannenshi mata guda bakwai hudu sunyi aure dukansu baa Nigeria suke aure ba Saura 3 agida suna school, ganin yay shiru yakasa cewa komi yasa ahankali Abba yace “tashi katafi, but make sure kaci abinci kafin ka kwanta kaji” gyadamai kai yayi sanan yatashi yawuce yabude kofa shikuma Abba yashiga cire kaya dan yay wanka duk bayajin dadi.




Yana fitowa da Mami yaci karo anan falon sama tana zagaye, kallo daya yamata yadauke kai yashiga sauka kasa itakuma tawuce tashiga falon Abban da sauri tanabin ko’ina da kallo dan Abba yariga yashiga bayi, ganin allura da first aid box abude yasa tasauke ijiyan zuciya taje gaban wardrobe tana budewa dan samoma Abba kayan dazai sa….
**


Tana komawa gida kayan jikinta tacire tayo wanka sanan tai salla tasauko kasa gabaki dayansu duk suna zaune a falo suna dinner gaida kowa tayi sanan tazo kusada Mama tazauna tana kallon Mama dataga tasaka sweater turtleneck black daya rufe har wuyanta tasaka hulan sanyi shima baki kafanta da bakin safa, kallonta Mama tayi jin ajikinta ana kallonta hannu tasa taja hancin tace “ke abinci zakici ko kallona kikazo yi” dan dariya kadan tayi tace “Mama sanyi kikeji ne AC akashe” gyadamata kai Mama tayi batare data bata amsan tambayan ba tace “mezan zubamiki” kallon abincin tayi sanan takalli madaran da Baba kesha tace “Mama madara zansha banson naci abinci” Madaran da Baba Kesha a cup da zafinshi ma yamika mata da sauri ta karba tana murmushi tace “thank you Baba” hararanta Mama tayi tace “kwadayi Khairy, aikin ki kenan tun kina Yar kankanuwan ki sabida babban ki kullum yanashan dafaffen milk kema kikesha” mikewa tsaye Baba yayi yace “bagashi nan saisa she’s so bright ba ga kwanya, milk is good for children barin ma Wanan na Shanu damuke sha dababu mix, bari naje nai salla” yakalli su Manaf da duk suka tashi suma sukawuce suka tafi masallaci, madaran ta shanye tass sanan ta tashi ta tattara kayayyakin dasukaci abinci takai kitchen sanan tadawo tana kallon Mama dahar lokacin take zaune inda tabarta tace “Mama tashi mutafi sama” ahankali Mama tace “wuce kitafi akwai wani program na wa’azi dazan kalla yanzu za’a fara” sanin Mama da kallon tashoshin wa’azi yasa tawuce stairs abinta tace “Mama gobe zani saloon kitso good night” ahankali Mama tace “Allah yakaimu Khairy” saida taji bude kofanta tashiga daki sanan gently tasa hannunta tadaura kan kujeran dake gefenta tana kokarin tashi tsaye amman takasa idanunta sunyi jazur kana ganinta kasan tana wahala ita kadai tasan metakeji, komawa tayi tazauna ahankali sanan tasauke ijiyan zuciya, hawayen daya zubomata takai hannunta tashare tanajan hancinta jin majina ya tsinke mata kafin tasauko da hannun ta share majinan, sanan ahankali tasauke hannunta kasa tana kallon tafin hannayen nata dasukai jajir kaman wanda yaji ciwo, ajiyan zuciya tasauke majina na gangarowa daga hancinta sanan tadaura hannunta kan hannun rigan tajashi sama tana kallon fatan jikin hannunta dasukai jaaa wasu kalan kuraje dasuka fitomata sunyi dabbare dabbare sunyi chaaaaa wanda is not just hannu ko’ina ajiki suka fesomata har wuya saisa tasaka Riga turtle neck dankar Khairy tagani, hannu takai tashare majinan dataji yana gangaromata yakai mata baki sanan tadaura hannunta kan baki tana kuka mai bala’in tabarai, she don’t even know why she’s crying, tana zaune a inda take aka turo kofan falon aka shigo dago kanta tayi takalli kofan Baba ne yashigo, kallo daya yamata yagane kuka take maida kofan yayi yarufe sanan yakaraso ciki ahankali yazo gabanta tsugunnawa yayi sanan yakai hannunshi yakama nata yakai kan kafadarshi kafin ahankali yadagata tashi tsaye tayi da taimakonshi dan ayanzu sai an dagata an kuma kwantar she can’t really do anything da kanta sabida, har yakaita daki bai iya cemata uppan ba, zaunar da ita yayi akan gado sanan yashiga bayi yadauko baho da buta da kanshi yamata alwala sanan yasamata hijabi kwantar da ita kan gado yayi sanan yace “pray” gyadamai kai tayi da idanunta dasukai jajir sanan tashiga yin sallan isha’i yana zaune gefenta harta idar sanan yacire mata hijabin.
Kashe wutan dakin yayi sanan ya kwanta gefenta yarufa mata bargo kafin yadaura kanta kan kirjinshi yanajin yanda jikinta yay zafi sosai, murya chan kasa tana kara kankameshi tace “nagode Baban su Manaf” gyadamata kai yayi yakasa magana har lokacin, hannunshi takama takai kan kirjinta ta manna sabida yaji yanda zuciyanta ke bugawa ahankali tace “kaji yanda zuciyana ke bugawa ko, tunanin yarana yasa haka, dan Allah ka kara aure banso daidai da sakan daya yarana suyi maraici kaji Baban Manaf” wata kalan huci kai zafi Baba yasaki ahankali yace “Maryam at this junction danake in my life banma da natsuwan dazan iya neman aure, yarana bazasu taba maraici ba, I am here, Baffan su nada mata har biyu they are sounded with mata they can call mom, please tunane tunanin nan will keep on eating u harsai kin daina, please concentrate on your health kinji, gobe zan kira Dr” girgizamai kai tayi tace “please no kabarshi yaje yay saving those that still have chance not me nariga naji ajikina my end is nea…..” Kankameta sosai yayi ajikinshi yana huci mai zafi wasu thick tears na neman fitomai daga idanu ya hadiye su ahankali yana jijjigata ahaka bacci yay awon gaba da ita saida ya tabbatar tai baccin sanan yatashi ahankali gyaramata bargo yayi sanan yawuce yashiga bayi alwala yadauro yazo yahau kan dadduma shafai da wuturi yayi yamata addu’a sanan yakoma gado kusada ita ya kwDanta.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣1️⃣


Free page
Saida tai sallan isha’i sanan tacire hijabi kayan bacci taciro tasaka tana tunanin abinda yafaru dazu itada Aliyu, dan murmushi tayi sanan ta kashe wutan dakin ta kwanta.
Batasan mesaba tadade kwance rikeda wayanta tana kallon wayan every minute deep down she wish to hear his voice amman kuma bamataso tana tunanin what she wish for din akanshi abin is so so new for her she’s not just use to it, ahaka bacci yay awon gaba da ita wayan nakan kirjinta this is the first ever time in her life da waya ke bacci akan kirjinta.




Wuraren 12 nadare wayan nata yahau ringing afirgice tafarka tana daukan wayan daga kan kirjinta tana danna gefe dan yadena ringing yay silent, sanan takalli screen din da kyau ganin Aliyu Hydar batasan mesaba faduwa gabanta yayi, ahankali takai yatsanta dake dan rawa ta danna wayan na gab da katsewa takai kunnenta, murya chan kasa dake nuna alamun bacci tace “Hello” shiru yayi yana sauraron muryanta da bazaiyi karyaba tunda yake baitabajin macen da muryanta yamai dadi kaman nata ba, dan gyaran murya kadan yayi cikin wata kalan murya dashi kanshi baisan yanada itaba yace “Khairy” ahankali kaman wata Yar karaman baby tace “Uhm yajiki? Kasha magani?” dan murmushi yayi jikinshi namai wani iri jin muryanta like that so naked sabida baccin data fara, sanan har ranshi yaji dadin yanda ta tambayeshi yajiki koyasha magani, ahankali yace “yeah, Abba yamin allura” kaman zatai kuka dan ita harga Allah tanada tausayin mara lafiya tace “auuch that must have hurts, I hate niddles, sorry ko!” murmushi yayi ya gyadamata kai yace “thanks, you are sleepy”? Gyadamai kai tayi tace “Uhm” ahankali yace “alright good night, make sure you plug in your phone sabida yasami chaji, and say your prayer before sleeping okay” gyadamai kai tayi ahankali tanajin wani iri azuciyanta kaman tacemai sucigaba da magana karya tafi tadenajin baccin tace “okay night” tai maganan batare data cire wayan daga kunnenta ba shima bai katse wayanba sunkai kusan 10min ahaka sanan murya chan kasan kasan makoshi yace “I love you Ummulkhair okay” gyadamai kai tayi ahankali tanaji hawaye nazuwan mata dabama tasan na meyeba but ko Allah yasani she just feel damn connected to him and vulnerable around him kaman ba itaba, katse wayan yayi hakan yasa taciro wayan daga kunnenta tarungume wayan hawayen na gangaro mata daga idanu, karan message dataji yasa taciro wayan daga kirjinta dasauri tabude wayan ganin message from Aliyu Hydar, bude messege din tayi da sauri. “Maisa nake sonki Ummulkhair? Well who am I to question faith? All I feel right now is I wanna spend my eternity with you, gud night Khairy”
Takaranta message din kusan sau biyar sanan ta danna reply tai shiru tana kallon blank space din bamatasan mezata rubuta maiba, saikuma chan tashiga typing .
“I feel vulnerable and free around you, my heart beat whenever I hear your voice, duk sanda na rufe idanuna kai kadai nake gani, is that love?“
Yana ganin message din yay mata reply.
“time will tell Khairy na❤️”
Wani kalan murmushi tayi ganin yakirata da Khairy na sanan ta tashi zaune USB takamo dake jone da wall socket ta saka wayan nata kaman yanda yace tayi sanan takoma ta kwanta tadade kafin bacci yay awon gaba da ita.






Da asuba Baba yashigo yatadata saida yaga tashinta dan Khairy nada nauyin bacci sanan yawuce yatafi, bayi tashiga tadauro alawala tazo tai salla, koda tagama karatun Al Qur’ani tayi yau sosai wuraren 6 ta tashi, hijabi tacire yau ita keson yimusu breakfast tunda bazata school ba hakan yasa ta tashi tafice daga dakin tasauka kasa kitchen tashiga tana murmushi tace “idan matarchan tazo yau zataga na hutashe ta” lafiyayyen breakfsat tahada musu dan sinasir tayi da farfesu sai kunun Gyada dasu fried chips, saida tagama tsaf sanan tashiga fito da komi falo ganin Mama zaune afalo kusada Baba yauma sanye da kayan sanyi yasa ta ijiye kulan a tsakiyan falo ta tashi tana kallon Mama dataga tamata haske sosai Mama datake nan baka but tai wani irin haske, kafinma Mama tai magana Baba yace “ke wuce ki kawo mana abinci ga yayyinki nan zuwa” dasauri tajuya tana murmushi tace “Baba naga Mama tai haske ne takara kyau” kitchen tashiga takarasa fito dakomi takawo lokacin su Manaf sun shigo suma zama duk sukayi Baba da kanshi yadebo ma Mama Sinasir yana bata abaki, murmushi tayi tana kallonsu tana taba Ya Manaf, hararanta yayi yace “dalla kauyus” cigaba dacin abinci duk sukayi kowa yay shiru Baba da Mama ne suka fara gamawa sanan yakalli Khairy yace “Maman ki tace zaki saloon ko” gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba, gyadamata kai shima yayi yace “yau rabonki da gidan Baffan ki kwana nawa” dan ajiyan zuciya tayi ganin yanda Baba ke kallonta sanan ahankali tace “an dade Baba” jinjina kai yayi yace “kije ki shirya kitafi saloon yanzu ana gamawa kije gidan Baffan ki ki gaidasu sanan kije gaida Matar Hafiz” ahankali tace “to Baba” “tashi kije” tashi tayi tai sama Baba yacigaba dayima Mama hira yau yanaso yakaita asibiti kotaki kotaso dan kwata kwata this days bata iya baccin dare ga kurajen nan kara fesowa suke ajikinta bana wasaba.






Tana shiga dakinta zama tayi kan gado sanan tadauki wayanta dahar lokacin bata cire daga chaji ba tabude message din Aliyu tagani around 5 na asuba.
“it’s time for subhi, wake up”. Murmushi tayi sosai sanan ta ijiye wayan tawuce bayi wanka tayo tafito direct gaban wardrope dinta taje wani riga da skirt na wani paper lace dinta tafito dashi da akamata dinkin jumper rigan yakai mata har gwuiwa sai skirt shikuma straight skirt daidai jikinta, mustard color ne lace din sai aka ni kayan dawasu bakaken stone, murmushi tayi taje tadaurasu kan gado sanan tazauna gaban mirror tadauki manta tana shafawa tana kallon fuskanta amadubi tana tunanin Aliyu, saida tagama shafawa sanan ta saka kayan dasuka mata bala’in kyau sosai, murmushi tayi black veil tadauka ta feffesa turare sanan tadauki handbag dinta ta jefe wayanta aciki tasa flat slippers yau tafito, afalo taga Baba kan doguwan kujera yana duba jarida Mama kwance tayi filo da kafanshi tana bacci yarufamata bargo, ganin Khairy yasa yadaura hannunshi akan lips dinshi yace “karki tadamin da matata tana bacci” turo baki Khairy tayi ashagwabe tace “Baba yanzu kafisun Mama dani Yar Autan ka” dan dariya tayi yamika mata wasu kudade yace “gashi Adamu na jiranki kije saloon kina gamawa ki wuce gidan Baffa” gyadamai kai tayi ta karbi kudin sanan takalli fuskan Mama dake bacci tace “Baba natafi” adawo lpy.


Saloon suka wuce direct baa wani bata lokaci ba wanke mata kan akayi sanan aka mata kalaba yan manya manya within one hour tagama tafito tashiga mota Adamu yatada motan zuwa gidan Baffa, dan tsaki tayi ahankali kawai dan babu yanda zatayi ne dabataje ba bata wani don zuwa gidan Baffa dudda tana bala’in don Baffa da duka yaran gidan, da Mum amman Ammi kwata kwata jininsu bai hadu ba batasan mesaba, tana cikin yan tunane tunanen ta ta iso gidan, Babban gida ne katoto, gidansu Babba ne but Gidan Baffan su is X2 nasu, mai gadi na ganinsu yahau murmushi yace “oyoyooo Khairy” murmushi itama tayi Adamu na parking tabude tafito dasauri mai gadon yazo wanda yake bayaro ba yace “munyi fushi wlh” dariya tayi tace “Baba Bala wlh school yaboyeni” tai maganan tana ciro kudi a jaka tamikamai 5k cikin kudin da Baba yabata karba yayi yace “nagode Yar albarka, Khairy mutuniyan kirki” murmushi tayi tajuya tana kallon cikin gidan, dankara dankaran flat ne guda uku agidan haka ajere, na farko wanda shizaka fara isa kafin kaje sauran yafi sauran biyun girma saina biyun dana ukun girmansu daya, da sauri saurin ta gudu gudu take tafiya wuce flat na farkon tayi tayi na biyun bude kofa tayi tana ihu. “Mummmmmm Mum” bin falon tayi da kallo daya hadu sai kamshin turaren wuta yakeyi stairs tayi da gudu tai sama daidai wata mata dazata kai 45 kefitowa daga wani daki cikin shiga na alfarma ta harari Khairy tace “ai nayi fushi wlh Khairy” wani murmushi Khairy tayi batayi wata wata ba taje dagudu tafada jikin Mum tana juyida ita cikeda murna tace “Mum I am sorry kinji, wlh school yahanani zuwa, Mum kinyi kyau iyyeee, ina Batool” turata Mum tayi tana nishi tana dafa kujera dan jiri taji tanaji tace “jama’a na shiga uku yarinyar nan zata kassarani” dariya Khairy tayi tajuya tai hanyar wani daki tace “nasan yarinyar nan tana bacci to baki isaba nazo” binta da kallo Mom tayi ganin kullum kara girma Khairy keyi, tana bude dakin taga wata yarinya da atleast zasu iya zuwa mate kokuma yarinyar tabama Khairy 1 zuwa 2yrs haka ta tashi zaune sanye da kayan bacci tana hamma tana hararan Khairy, yarinyar kamansu daya da Mom, wani tsalle Khairy tayi tafada kanta akan gadon yarinyar ta kwasa ihu tace “Mum kinga Khairy ko ni dagani ai wlh fushi nake dake konai chatting naki up baki dubawa kuma baki daukan calls” sakinta Khairy tayi tace “wlh Batool ni taba waya ma wahala yakemin balle responding to calls or chat har gwarama kamin text message ina gani zan reply, but rabona ma dana shiga watsapp harna manta wlh” baki Batool tabude zatai magana Mom ta turo kofan dakin tashigo hakan yasa duk suka kalleta, Khairy takalla tace “kinje kin gaida Ammi Khairy”? Dan zaro idanu Khairy tayi sanan ta girgiza mata kai ahankali, daure fuska Mum tayi babu alamu kan fuskanta tace “Oya tashi kije ki gaidata, fast” tashi tayi kaman ruwan jikinta ya shanye, jakanta ta ijiye kan gadon Batool sanan tawuce tafito Mum tace “duk idan kin shigo gidan nan always ki shiga flat nata ki gaidata kafin kizo nan” gyadamata kai Khairy tayi sanan tawuce ta sauka kasa kafin tabude kofa tafice.




Ajiyan zuciya tasauke tana kallon kofan sanan gently tasa hannu tabude kofan wani lafiyayyen kamshin turare namata sallama ahanci, Babban falo ne sosai dayamafi na Mom girma, zaka dauka dakin wani president ne ko gwamna sunji kujeru da kayan gayu, wata Babbar mace ce mai kiba sosai a falon, kana ganinta you don’t even need to ask twice kaga Hajiya irin cash HajiyUoyin nan.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣2️⃣




Free page
Fara ce tass kana ganinta kaga bafulatana dan tanada mark na fulani a gefen fuskanta taci gayu na alfarma tana sanye dawani stone gown na exclusive mai pattern, kunenta zinare wuyanta ma haka yatsun hannunwanta guda biyu ne kawai babu zoben zinare ajiki manyan yatsun hannunta sune babu but sauran 4 4 fingers nata duka da zinare tana zaune akan kujera ta hakimce gawani iPad na Apple agabanta tadaura kan wani very very fine stool tana video call dabata iya ganin kowaye a screen din tunda ita daga waje take, hannunta matan rikeda wani white transparent bowl da ita kanta Khairy basuda irinshi agidansu an yanyanka strawberries da kiwi fruits kanana tanaci da fork, kokai waye kaga matan saika shiga taitayinka like duk rawan kanka irin matan nan ne da they don’t even needs to show u su waye kana ganinsu kasan they’re no nonsense powerful woman saisa haryau itadai Khairy bazata iya cewa ta tsani matan bane but kawai bata sonta, hasalima ita tsoronta ma takeji ko haukanta take agidan dazaran Ammi tazo wajen natsuwa take kaman ba itaba kodako da Baffa take magana, kuma agaban kowa ko agaban Baffa ne Ammi zata iya rufe kowa da fada baruwanta saidai in bakayi ba daidai ba.




Kallo daya tama Khairy ta dauke kai, ahankali Khairy tajawo kofan falon ta maida tarufe sanan takaraso cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login