Showing 21001 words to 24000 words out of 108352 words

Chapter 8 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt

24 Dec 2024

5623

ihu kafanta ya gicce abunku da tiles kawai ta kifo zata fadi da mugun sauri Gwaggo tace “Subhanallahi” dawani irin sauri yasaki wheelchair Gwaggo daidai kanta zai daki dakaIUlin stairs din…
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫




✍🏻 M SHAKUR


Dan magana da M shakur
wa.me/+2347012181461




1️⃣5️⃣




Yasa hannunshi daya awajen kanta ya daki tafin hannunshi bayan hannunshi yadaki stairs din sanan yakai dayan hannunshi yakama waist dinta yajuyo da ita hakan yasa ta mirgino side tafado jikinshi.


Daga yaran, security, iyayensu dasuka biyosu da sauri, Gwoggo dakekan wheelchair duk sandarewa sukai danba karamin faduwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba, yanda yakeji yanda take nishi a hannunshi yasa ahankali yazare hannunshi daga waist dinta gently yakai hannun kan fuskanta yadago fuskanta yana kallon face dinta yanda ta kankame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples dinta na lotsawa tana nishi sama sama dayake jinshi akan hannunshi, murya chan kasan makoshi while looking into her face yace “are you okay”? Muryan dataji yadaki dodon kunnenta yasa kadan kadan tashiga bude idanunta danta gasgata abinda taji kafin tabude su tass tadaura white fararen idanun nan nata manya manya dasukenan kaman an wanke da madara tadaura su akan fuskanshi, jitayi numfashinta ya makale somewhere in her throat ganin fuskanta dab da nashi yana kallonta as if he’s trying to check something, yatsanshi yakai saitin nose nata jin bata numfashi kawai takafeshi da manyan white eyes nata yasa dasauri yakalli security man din yanunamai jakanta dake kasa chan yace “give me her bag” dasauri yakawo jakanta yamikamai juye jakan yayi kasa inhaler ta yafado dasauri ya dauka yacire marfin yakai bakinta ahankali yace “breathe in Ummulkhair!” Wani irin bugawa zuciyanta yayi jin yanda yakira sunanta kaman sunanta dayakira ne yay reviving nata batasan lokacin datawani saki numfashinta data rikeshi amakogoronta ba yafito mai kara sanan taja inhaler, zagayesu mutane sukayi barinma parent din yaran da jikinsu yay sanyi ganin Yarinyar da yaranta suka ture is even asmatic, ganin yanda mutane suka cika kansu duk ana kallonta yasa ahankali takai hannunta batare data kalle fuskanshi ba tana kokarin karban inhaler daya rikemata abaki, ganin haka yasa gently yasakin mata ahankali yaran dasuke tsaye sukace “Anty sorry” dan murmushi tayi tana cire inhaler daga bakinta duk dasauri tana kokarin tashi tsaye, tsugunnawa Maman yaran tayi tace “rest a bit please” tai maganan tana maida mata kayan jakanta back aciki tareda daukan mata jakan ice cream dinta da sauri ta mike tsaye tana karban abubuwan ta daga hannun matan tace “I am okay thank u” Gwaggo dake kallonta tace “sannu kinji inane gidanku mukaiki nida jikana” dasauri tace “direbana na nan nagode Ma” sanan tawuce da sauri hartana tuntube tai wajen motansu da Adamu ya kwantar da kujera yanata hira awaya abinshi batare dayamasan meke faruwaba, saida yaga tabude motan ta shiga sanan yakoma wajen Gwaggo yatura keken sukai ciki tace “ohh yara da rashin wayau Hydar, inda badadan kaiba da sunja Yar yarinyar nan tafasa goshi wlh, itama yarinyar uwa batacin abinci yoo nakema wanan maganan haka rainon indomie ce daga ganinta, ace daga yan yara sun bangaje budurwan yarinya haka kawai sai faduwa uwa lagwani, ace yara suci tuwo suki duk irinku ne ai gashinan kaga yara sun taso basu da karfi ko kadan, kai Allah dai ya wadaran naka subaci, Allah dai yasa kai aure ka haihu, wlh tun yaranka na wata biyu zan fara basu lafiyayyen tuwo da miyan kuka dataji daddawa” hararanta yayi baima cemata komiba ya sassayi ice cream din sanan suka fito tace “minene Wanan abin danaga kanata matsamata abaki” kin kulata yayi yasa ta amota ya maidata gida sanan yafito yatafi aiki.






Har suka shigo anguwan su badaidai takeba yau sau uku kenan tana ganin mutumin nan, saida suka shigo gida tukunna sanan taji wani kalan dadi, parking sukayi sanan tafito dasauri tana kwaso kayayyakin ta tana kwalama Mama kira. “Mamaaaa! Mama nadawo” daga Mama, Baba, Baffa da yayyinta da Hafiz duk suna zaune a falo dan basu dade da dawowa daga asibiti ba babu wanda yama iya wani kwakkwaran motsi, ita tsabagen murna batama lura da Karin mota kan tagidansu ba tai hanyar flat dinsu tana shouting Mama. “Mama nayomiki tsaraba yau nasayo miki ice cream kuma best flavor naki mint ban miki adding any thing ba ayanda kike sonshi plane” tai maganan tana bude kofan falo tana shiga tana kiran Mama. “Maaaam……” kasa karasa kiran Mama tayi ganin mutane a falon ga Mama zaune kusada Baba tana kallonta tana murmushi, hararanta Hafiz yayi yayi yace “inda ace ke kadai keda Mama aduniyan nan Khairy da munsha takaici” cikeda wasa Baffa yace “kagamin d’a kai kanama namiji ka more taka Maman balle ita mace kuma auta, ina tsaraban dakika kawoma Maman bazaki zo kibata ba kin wani tsaya awajen” akunyace takaraso cikin dakin wani irin rungume Mama tayi tana murmushi akunyace ganin duk ana kallonta yasa tadaurama Mama paper bag na ice cream din akan jikinta akunyace ta sauko dagakan jikinta tace “Baffa ina wuni” murmushi yayi yace “diyar Mamanta ya makaranta” ahankali tace “fine” sanan takalli Hafiz tace “Ya Hafiz ina yini ya baby kuma, dan Allah ya Hafiz kasa mata sunana” dasauri yazaro idanu yace “waaaa niii rufamin asiri Khairy sokike y’ata tazama fitinanna irinki” dariya aka hauyi adakin ahankali Khairy tace “Baffa kaga Ya Hafiz ko” kafin Baffa yay magana Baba yace “karya yayi to Khairiya” turo baki tayi kaman zatai kuka Baffa yace “sharesu Yar albarka, sun lashe basusan baiwan dake tattare da sunan ki bane saisa suke magana ahaka” wani kalan murmushi tayi tace “yauwa Baffa” sanan tajuyo takalli Mama tace “Mama kin sha maganin kan yadena miki ciwo muji” takai hannunta tana taba goshin Mama with so much care, gyadamata kai Mama tayi tace “yadena, cikani maza tashi kai ice cream din kisa a fridge kije kiyi wanka kiyi salla idan bakiyi a school ba saiki sauko kici abinshi” gyadama Mama kai tayi sanan ta tashi tana kallon yayyinta dataga sunyi wani iri harzata wuce tace “Ya Manaf kungaji ne haka naga kunyi wani iri, Ya Maheer idanunka sunyi ja kaman kayi kuka” hararanta yayi hakan yasa ta murgudamai baki tawuce abinta sama itama, dayake yana takanshi dayaji ciwon Mama yatashi yau baima biyemata ba!


[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣6️⃣


Free page
😉 enjoy


Kofan dakinta tabude ahankali ta shiga tanabin dakin da kallo yanda ko’ina tsaf tsaf an gyaramata sai kamshi dakin yake, shiga ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin awani irin gajiye cikeda sanyin jiki tasaki handbag dinta akasan dakin tafada kan gadon batare data cire takalmin kafanta ba tawani kalan kankame jikinta tanajin wani irin sanyi na shiga jikinta, she don’t even know why amman hakanan fuskan police man dinan take gani a idanunta muryan shi namata yawo a kunne da kanta gabaki daya yana kiran sunanta Ummulkhair breathe in, runtse idanunta tayi gam gam tana feeling yanda bones nata ke cringing to each other tana ganin fuskanshi namata yawo a idanu kafin idanunta suna hasko lips dinshi wani kalan ihu tayi. “Ahhhh stop!” dasauri ta tashi zaune tana wurwurga kafafunta cikeda damuwa tace “Stopppp noooo what’s wrong with me”? Wani irin zabura tayi ta tashi tsaye kawai tawuce dasauri tafada bathroom, wanka tayo sanan tafito daure da towel tana tunanin yaushe Mama zatasa amata Kitso dan gashin ya isheta daga tsifemata jiya, wani simple dogon Riga tasaka sanan tasaka hijabi tai salla tana idarwa tafito falo tawuce ganin duk basu tasan sun tafi masallaci sallan magrib, dinning tawuce zama tayi tana bubbude kula rice tazuba kadan sanan tasa nama tafaraci saida tacinye sanan takai plate din kitchen kafin tafito ahankali tai stairs, knocking dakin Mama tayi sanan tabude kofan ganin Mama akan gado ta lullube da bargo yasa tashigo da sauri tace “Mama menene” wani kalan kallo Mama tamata tace “bacci zanyi nagaji” hawa gadon tayi tana kallon fuskan Mama tace “Mama kibari ayi isha’i tukunna nima bacci nakeji” gyadamata kai Mama tayi tana kallon gashinta tace “weekend zakiyi kitso tunda ke kin dawo yarinya daga tsife miki kai kanki yadawo kaman na mahaukaciya” gyadama Mama kai tayi tana hamma, ganin haka yasa Mama tace “Oya tashi kije kiyi sallan to gashinan ana kira saiki kwanta tunda kin gaji, kinmasha ice cream din” girgizakai tayi agajiye tace “gobe zan sha Mama nagaji, gud night world best” night my baby girl, Mama tai maganan tana binta da kallo wucewa tayi tafice daga dakin tana salla ta kallabi tahau gado sai bacci.




Da asuba tana tashi salla tafarayi sanan takoma bacci dan yau batada lectures sai 10 and she wants to sleep sosai cus kanta yay clearing tadena all this banzayen tunanin nan datakeyi.
Karan wayanta yatadata by 9, da kyar ta iya bude idanunta ta kalli wayan rabon data danna wayanta hartama manta one thing dabai dameta aduniya kenan ba waya, she’s not just a phone person, itadai barta da physical surutu, yawo rawa haaba anan ake samin Khairy, hannunta tamika da kyar tadauko wayan ganin Besty yasa taji duk wani kalan bacci datakeji yafice daga idanunta dasauri tai picking call din tace “Iyye su Besty Amarya ai nadauka kin manta dani yar rainin hankali saisa na shareki banma nemekiba” kuka Besty tasaki awaya dayasa dasauri ta tashi zaune adan tsorace tace “ke menene Besty, what happen? Kinasa inajin tsoro why are u crying?” Cikin wani kalan muryan ban tausayi Besty tace “Khairy wlh nafasa auren mutumin nan kasheni zaiyi tun ranan da aka kawoni abu daya ake har yau nagaji” dan ware idanu Khairy tayi tanajin maganan wani banbaram itadai barta da rashin ji but duk wani harka na maganan banza da Iskanci bata aciki, adan kunyace cikedajin nauyin magannan tace “to ba ance ana sabawa ba” tai dan shiru saikuma ta turo baki tace “idan yaki kihadashi da Maman ku” wani gajeren tsaki Besty taja cikeda masifa kaman tabugama Khairy dundu tace “I don’t even know why I called u you are crazy Khairy, da zancen party ake da yanzu kingama tsara komi, lemme call Amal” tana maganan ta katse wayan, hararan wayan Khairy tayi ta ijiye saikuma chan kaman ta tuna wani abu wayan ta dauka dailing number Besty tayi back ringing daya tadaga, ahankali tace “sorry Besty kinji I seriously don’t know what to tell u or how to advice u” cikin muryan damuwa Besty tace “wai Khairy when will you learn all this stuff eh, u are just hella wired Umma, u are just leaving life kaman bamace ba gashi duk munata aure Khairy keko saurayi bakida shi sai wanan Wizzy dake binki” hararanta Khairy tayi tace “nacemiki kidena hadani da wanan yaron” dan dariya Besty tayi kaman ba itane mai kuka yanzun nan ba tace “naji nadena, yanzu dai kinyi wani saurayin”? Dan shiru tayi kaman mai tunani harta bude baki zatai magana saikuma tai shiru hakan yasa Besty tace “ohhh wowww, Khairy this is something new, tell me who is he? Dan tunda nake dake duk aka miki tambayan saurayi direct kike cema mutum baki dashi wanan dakika kasa magana tell me wayeshi” dan murmushi tayi tayi dan juyi akan gado tana dan lumshe ido saikuma ahankali tace “wlh Besty banda kowa kawaidai wani Police man ne naketa haduwa dashi this days amman ko magana bamayi kawai dai he always saves me from trouble ne I don’t know if that means anything amma dai ba soyayya muke ba ko magana ma bamayi” ahankali akuma natse Besty tace “ohh my Goddd! Khairy kinji yanda harwani natsuwa kikayi kina bani labarin police man dinnan kuwa, My world Khairy you love me! Wlh….” Dan yatsine fuska Khairy tayi dasauri tace “stop it! Mutumin dabanma sanshi ba, yaushe zaki dawo school nidai” dariya Besty tayi sosai tace “tunda u are avoiding maganan ai ba matsala, this weekend zai dawo dani but every weekend zai dinga zuwa” gyadamata kai Khairy tayi tace “sai kinzo bye” tai maganan tana katse wayan da sauri dan tasan Besty bazata taba hakura da topic dinan ba, ijiye wayan tayi ahankali sanan ta mirgina zuwa dayan gefen gadon tana tunani.




Ajiyan zuciya tasauke sanan ta tashi tasauka daga kan gadon zatai bathroom wayanta yashiga kuka cikeda masifa tadawo tace “mekuma kike sake kirana eh” wayan tadauka ganin Glory yasa tai picking wayan takai kunne kafinma tai magana Glory tace “hello fine girl, melanin goddest, pop skin with those sexy milky eyes” dan dariya tayi, Glory is her friend masters ita take a school nasu ta girmeta far far amman tana bala’in son kawance da Khairy, dan murmushi Khairy tayi tace “Hey! Where have u been i haven’t seen u in school this days” dan dariya tayi tace “I travel naje PH chan gida, Khairy u don’t know I am angry with u ba” dasauri Khairy tace “what happen? Why” kaman zatai kuka tace “today is my birthday Khairy” Adan kunyace Khairy tace “ohhh Glory, sorryy happy birthday darling” dasauri Glory tace “come to my party and wish me there, zamuyi a jabi lake mall a cikin jirgin ruwa, dress code is red 4pm sharp” wani kalan juya idanu Khairy tayi tace “ohh okay then bye see u later” ta katse wayan sanan tawuce bayi da gudu wanka tayi agurguje sanan tafito cikin wata doguwan rigan atampa ta shirya tafito tana tunanin yanda zatai planning zuwa party zata dawo gida by 2 wuraren 5 saita tafi tadawo 6.


Tea kawai tasha sanan tawuce school dan tayCi latti sosai.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 1️⃣7️⃣




Free page
Ahankali yake tuki ganin ya shigo cikin estate dinsu, saida yakarasa gaban wani dankareren gate sanan ya danna horn, budemai gate da akayi yasa yaja motan zuwa cikin gidan dakeda bala’in kyau kuma babban gaske ga flowers dasuka karama gidan kyau sosai, parking yayi abangaren parking sanan yakashe motan yana kallon cikin gidan dababu kowa sai gardener dinsu daketa yayyanke flowers yana gyara su, yakai kusan 1min cikakke zaune a motan yay shiru sanan ahankali yabude kofar motan yafito yamaida kofan yarufe sanan yafara tafiya dai dai yawuce zuwa babban flat dakenan shine first flat a gidan, bude kofa yayi ahankali tareda sallama chan ciki sanan yashiga babban falon da babu kowa ciki, falon ya bala’in hadu yaji furnitures, saikuma dan kara dayakeji a kitchen da alamu mai aikice ke wanke wanke, juyawa yayi zai fice kaman daga sama yaji ankirashi. “Aliyu” dan juyoda kanshi yayi ya waigo, wata matace doguwa mai jiki fara kal da ita taci gayu da sarkan gwal a wuyanta wacce bazata wuce 40 ba tana sanye da lace ja da baki ke saukowa daga benen, kallo daya yamata yadauke kai yace “barka da rana Mami” dan murmushi matan tayi sanan takalli agogo bangon falon ganin is just 11 yasa tace “Lafiya kadawo gida ware haka Aliyu”? Batare daya kalletaba ahankali yace “lpy lau Mami” gyadamai kai tayi tana kallonshi still tace “tom shikenan, mezakaci a aiko maka dashi”? Batare daya kalleta ba har lokacin yajuya yace “zanci abinci wajen Gwaggo” yana maganan yajuya yafice tareda rufo kofan binshi da kallo tayi ta jikin window falon har saida yay side din Kaka yabace mata daga gani sanan tasami kujera ta zauna tanadan karkada kafa tunda take bata taba ganin wanda uniform na police kemai kyau kaman Aliyu ba, haryau tarasa maisa Aliyu yawani zama police ba yaron dayay lafiyayyen karatu yakuma gama da good result, kwanciya ahankali tayi tana kwalama Yar aikinta kira dan tazo ta danne mata kafa.




Bangaren Gwaggo shima yanada girma sosai, da sallaman nan nashi chan kasan makoshi yadaga labule ya shiga dakin ko kadan Gwaggo dake zaune tana kada lagwani bataji alamun shigowan mutum ba kawai karan kwas kwas na takalmin dake kafanshi taji akan tile din dakinta afirgice takalleshi tana “Innailaihi wa innailaihi raji’un, waikai Aliyu wani irin murdadden yaro ne eh, bama wanan ba dan ubanka koma ka cire shegen takalmin nan naka dazaka shigomin dashi falo ina salla a ko’ina afalona dan tsarki ne dashi wlh” ko kallonta baiyiba saima hawa kan dogon kujeran ta dayayi yay kwanciya abinshi yanadan lumshe idanu, ijiye komi Gwaggo tayi tamike tana gyara zani tazo kanshi zatahau mai bala’in idanunshi daya lumshe tabi da kallo ganin sundanyi ja yasa tace “kai yaron nan zazzabi kake yine”? Dan bude idanunshi kadan yayi yakalleta dauke kanshi yayi yaki kulata, dasauri ta kalli agogo ganin ko shabiyu batayiba yaron da dazun nan dasafe yafita aiki yasa tace “wlh bakada lafiya Hydar zo meke damunka”? takai hannunta da duk audugan lagwani yake kai zata tabamai fuska dasauri yatashi zaune yace “karki tabani da hannun dattin nan Gwaggo” dan sassauta murya tayi kaman ba ita kemai ihu ba cikeda damuwa tace “meke damunka eh Hydar? Duk wanda yasanka yana ganin Wanan idanun naka yasan bakada lafiya, meke maka ciwo” tashi daga kan kujeran yayi yace “tunda bazaki barni nai bacci ba bari na barmiki dakinki” yay maganan yay hanyar fita tana kwalamai kira kaman badashi takeba, cikeda damuwa tace “ai idan bakaji nawa ba zakaji na ubanka, yaro sai bakin zurfin ciki da shegen share mutane sabida yaga nadamu dashi” duk yanajin ta tana surutunta bai amsata ba flat dinshi yawuce bude kofa yayi yashiga cikin dakin da babu abinda yakeyi sai kamshi ko’ina a gyare kaman babu wanda ke zama adakin, bedroom nashi yawuce yana shiga adaddafe yacire rigan yan sandan ya Yar anan kasan dakin sanan yazauna takalmin kafanshi yacire yazaro wayanshi yadaura saman side drawer sanan ahankali ya kwanta yanadan yatsine fuska bala’in ciwon kai yakeyi daya rasa na menene amman sai uban dauriya, har bacci yasoma daukanshi yaji wayanshi na ringing da kyar yadaga hannunshi yakai wajen wayan dauka yayi batare dayama kalli screen dinba yakai wayan kunne ahankali yace “Hello” daga tachan bangaren muryan wani magidanci ne yace “Aliyu meke damunka?” Dan yatsine fuska yayi yanaji kaman ya rufe Gwaggo da duka akan me zata fadiwa Abba dan gyara muryanshi yayi yace “Abba I am fine” cikin rashin gamsuwa Abba yace “Aliyuuu” dagashi sai Abba sukasan meaning din anytime yakirashi da Aliyuuu hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login