Showing 18001 words to 21000 words out of 108352 words

Chapter 7 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt

24 Dec 2024

5622

Maryam yatashi muna asibiti Baffa” anatse daga dayan bangaren akace “Subhanallahi, turn d car Bala muje asibiti” kawai aka katse wayan.




Yana zaune awajen ko cikakken 10min ba’a dauka ba, wani Babban mutum da akalla shida Baba zasuyi sa’onni ya shigo cikin asibitin yana gyara Babban riganshi, farine mutumin sol yanada kiba dan yamafi Baba, shida wani dan saurayi dabazai wuce sa’an su Manaf ba dayay kama dashi dukansu fuskokinsu yanuna damuwa sosai, yana karasowa dafa kafadan Baba yayi yace “be strong my friend, Allah yabama Maryama lafiya, Allah yatashi kafadunta, Allah yasa kaffarane” tashi Baba yayi yanadan murmushi sanan yakalli yaron dake gaidashi yace “su Baban Baby girl Hafiz, Allah ya raya” ahankali yace “Ameen Baffa” sanan suka shiga ciki, har lokacin bacci take, da idanu Baffa yama Baba alamu su fito, suna fitowa yace “bazamu fitada ita wajeba ko har yanzu tanakan bakanta”.






I will talk to her idan ta farka, ahankali Baba yace “Allah yasa ta yarda” kara komawa sukayi wajen Dr ko akwai wani solution amman babu, dudda haka Baffa saida yakira some of the best Doctors dayasani a Abuja but is still same thing hakanan suka hakura.


Wajajen 3:00 na rana tafarka, dakin tabi da kallo kafin ahankali tafara yunkurin tashi dasauri Manaf da Mu’az suka dagota, ahankali Mu’az yace “kinajin yunwa Mama mezakici” dakin asibitin tabi da kallo kafin ahankali tasauke ijiyan zuciya tadanyi murmushi ganin duk sun damu tace “ya akayi bakuje aiki ba yau, laaaa is that Hafiz” tai maganan tana kallon Hafiz dake zaune kan kujeran gaban gadon yana kallonta cikeda tausayi, cikeda murna tace “zonan zoka nunamin hoton jikata nagani” dan murmushi yayi yataso yazo, wayanshi yaciro yafito da picture cute baby girl dinshi yabata karba tayi tace “Masha Allah tubarkallah, Allah ya rayamana kaga yarinya kaman Babanta Yan biyu” tai maganan tana nunamusu hoton kafin idanunta ya sauka kan time din wayan ganin karfe uku har da minti goma yasa dasauri tamikamai wayan takalli Mu’az tace “kiramin Dr yasallameni inkoma gida, Khairi takusan dawowa daga school” tana maganan saiga Baba da Baffa da Dr sun shigo tare, Baffa na ganinta yace “ya jiki Maryam” murmushi tayi tace “Alhamdulillah Baffa, ya ji kalle inasu Hajiya Asiya” kafinma taji amsanshi tace “Dr zokai discharging dina natafi gida” ahankali Dr yakaraso wajen yace “Hajiya kibari mu dubaki na kwanaki tukunna saimu sallameki” kallon Baba tayi sanan takalli Dr rai Adan bace tace “sallameni yarana banaso su dawo Bana gida Dan Allah” kallon Baba tayi sanan ahankali tace “daman Wanan ne shirinka idan ka kawomi asibitin arikeni” dasauri Baffa yazo wajen anatse yace “Maryam kalleni nan” ahankali tajanye idanunta dagakan Baba dake kallonta kuri takalli Baffa, anatse Baffa yace “Maryam kiyakuri ki zauna likitocin nan su cigaba da baki gudunmawa, zamanki agida zai karasa ciwon yazama worst ne, dan Allah maryam inhar kinajin magana ta” lumshe idanunta tayi sanan tabudesu ahankali tace “Baffa tun ina yarinya kasanni ban taba cemaka no ba, kome kacemin inayi dan haka yau Baffa dukanku anan zan rokeku alfarma, dagayau dan girman Allah kome zai sameni karku sake dawodani asibiti, Baffa nasan kalan chutan danake dashi, nasan metake nufi, da inzauna anan allurai da maganinsu yakarasa cinyeni gwara in koma dakina, I want to die adakina tareda yarana dakowa, I hate hospital and zaman asibiti shizaifi kasheni dawuri sama da komi, please Baffa dan Allah, idan baka yarda ba naji zan zauna, amman rokonka nake please Baffa” kowa na dakin saida jikinshi yay sanyi har Baffa, ahankali Manaf yakalli Baffa yace “Baffa please grant Mama wish, let’s just take her back home ko Hafiz” gyadamai kai Hafiz yayi da idanunshi sukai jajir, hakama Mu’az, ganin Baffa da Baba sunyi shiru dan su sunfiso tazauna a asibiti tasami lafiya yasa ahankali Dr yace “Alhaji kubarta takoma gida, idan anything come up ku kirani ni zandinga zuwa nadauki Wanan nauyin” ahankali Baffa yakalli Baba dakokadan baisoba, kallon kayakuri takoma gidan, hakan yasa ahankali Baba yace “shikenan” murmushi Mama tayi sosai nan da nan aka zaremata drop din sanan Dr yarubuta mata magunguna suka saya sanan suka dawo gida gabIaki dayansu.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫




✍🏻M SHAKUR






1️⃣4️⃣


Free page
Wuraren 8:50Am sukakai school. Adamu na parking wajen parking tafito da saurinta bama ta tsaya mai sai anjima ba tashiga sauri cus 9 dot mutumin nan ke shiga aji gashi baya wasa da attendance, tana cikin tafiya zuwa class saiga wasu yammata su hudu sun taho tunda suka ganta sukahau ihun murnan ganinta Khairy nada wani irin farin jini naban mamaki wajen mata, tareta sukayi. “Khairy how far”? Murmushi tayi dake karamata bala’in kyau tace “lpy lau wlh, yanaga zaku waje daban ba class garemu ba yanzu” yatsine fuska sukayi, daya daga cikinsu tace “wlh dabaki wani wahalar da kanki ba wajen class din Mr Okeme ba ba’a taba ganewa ba, ke saurayinki Ahmad celebrity yazo nemanki fa” hararanta Khairy tayi tace “Malama niba saurayina bane kidena hadani dashi, na wuce class nidai” tai gaba abinta ranta abace, daya daga cikinsu ne ta daga murya tace “idan yakadoki meet us a garden chan mukayi” daga murya itama tayi tace “that’s not gonna happen Ladies” tana tafiya wasu another set na yammata na tareta bamata tsaya sauraransu ba tace “I will see u later ladies inada class now” tahau tafiya gudu gudu sauri sauri, duk inda tabi ana kwalamata kira Khairy Khairy waving mutane kawai take tawuce benen dazai kaita ajinsu tana kaiwa yana shiga tana tsaye yana kallonta yaja kofanshi yarufe, ahankali ta yatsine fuska murya chan ciki tace “this wicked man cannot make heaven” sanan tajuya tana kallon kasa daganan bene yanda student kowa na takanshi sanan ta fuzar da iska ita dai ko itace allazi boko bazata taba tsayuwa jikin window har agama 2hrs class ba, tashi tayi abinta tafara tafiya tawuce tana sauka daga staircase abinta tanadan turo baki ita kadai tana kunkunai.
Sabida yanda ranta yake abace taji bamatason tabi normal hanya friends nata suyita tareta da magana hakan yasa tabi ta parking space dan taje garden daga wajen, ahankali take tafiya ita kadai a parking space din tana cikin tafiya a parking space din taji an kwala mata kira. “Khairy” dan tsayawa tayi jim batare data juyoba jin muryan namiji ne ke kiranta, tunani tafara acikin kanta muryan waye wanan sai chan taja wani kalan annoying tsaki tacigaba da tafiya abinta gani kawai tayi ansha gabanta wasu maza guda biyu sunshamata gaba suna sanye da kananun kaya sun bubbude hannuwa irin suna tareta dinan, wani kalan daure fuska tayi babu ko alamun wasa akai tace “me haka” dan dariya sukayi daya daga cikinsu yace “listen to Ahmed mana Khairy yasan bazaki tsayaba saisa yace mutareki” yay maganan suna nuna mata bayanta, juyawa tayi cikeda masifa wani black skin guy ne da dududu bazai wuce mate nata ba in age maybe 20 ko 22yrs haka yake, yana sanye cikin rugget kayan yan iska dinan, crazy baggy jeans da wata babbar baggy riga yayi dying gemunshi zuwa blond color kana ganinshi kaga irin yan iskan yaran nan gashinan very popular aciki school nasu, wani kalan mugun kallo tamai da manya manyan idanunta tace “kai da boys dinka Ahmad should get out of my way” wani kalan murmushi yamata tareda daura hannunshi akan kirjinshi yana shafawa yace “auuch! I love it when you look at me like that Khairy with those ur big big lulu white eyes, Baby my heart only beat for you” spitting miyau tayi agefenta sanan tajuyo takalleshi tace “you disgust me Ahmad, nagayamaka time without numbers stop wasting ur time on me, you are not my type of guy, idan maza irinkane suka cika duniyan nan I rather die banyi aure ba dana aureka, I don’t like you an taba soyayya dole ne” dan takowa sahu daya yayi zuwa gabanta, tsayawa chak tayi tareda kama waist dinta kirjinta na bugawa fat fat, wani mayen kallo yabita dashi barima kirjinta dayaga yacikamai idanu tunba yauba tunda ya lurada yanda Khairy keda boobs yaji yakara haukacewa akanta, dan hucin zafi Ahmad yayi yana kallonta still sanan yanuna kanshi yana bude kafafunshi da tsabagen effizy sun koma kaman boleg yace “look at me kinsan how many babes anan School namu ke kiyamun laili because of me eh? Look at me Khairy, I have money, I was born in wealth, banda haka I am a hip hop rapper number 1 a arewa, yaro mai zamani, har rap nayi da sunanki natura miki a watsapp u don’t even open my chat balle kiji how much I love you, Khairy tell me mezan miki dazaki soni eh, kinga we are the only ones here, just tell me babu kowa don’t be shy Khairy, baki sona don’t u wish to be mine, don’t u wanna make matan makarantan nan jealous ace Kece tawa, I want you to be my Choima while I become your Davido, lemme make you famous, lemme make u a star gurl, what will I do to make you mine baby na? Don’t u want all of this” all maganganun dayake mata jitake kaman tai amai bala’in kyaman Ahmad take bawai he’s dirty bane, kawai dai yanayinshi yanda yake dressing yana shiga kaman wani su wizkid yayi coloring gemunshi da halinshi na waka ita kawai he’s not her spec, yana mata magana yana wani wawware fingers kaman yana rapping yana kama tsakiyan baggy wandonshi, ko kiranshi amatsayin boyfriend nata ma bataso ta tsani taji anyi, bakin ciki da haushin shi yamasa tama kasamai reply kawai tajuya ta gefenshi zata wuce dan sometimes idan abu is really annoying agareki rasama abinda zakace kake, kawai ji tayi yariko hannunta “don’t go baby wait” wani irin juyowa tayi batai wata wata ba kawai ta daukeshi da mari jikake tass! Wani irin ihu abokanenshi sukayi suna waige waige ko there’s anyone there dayaga Marin datama Ahmad dan zai zama abin kunya ance wata tamari hiphop rapper. “Ke celebrity kika mara” fizge hannunta tayi tana kallon yanda yadaura hannunshi kan kuncinshi yana wani irin kallonta da idanunshi dasukai jajir dan marin ya shigeshi, rawa jikinta yafara da sauri tajuya Ahmad daya bala’in zuciya yace “ku bita” jin haka yasa ta kwasa da bala’in gudu acikin parking space din dababu kowa tana kalle kalle, kaman ance takalli right side dinta, hango wani dogon mutum tayi yabata baya Awani lane na motoci yana tsaye jikin wata suv waya a kunenshi da alamu waya yake, wani irin kwana tayi tana gudu tai lane din dayake batai wata wataba tana kaiwa daidai inda yake batai wata wataba tawani zaga ta gabanshi ta shige kirjinshi at once tana boye fuskanta akirjinshi jikinta ko’ina narawa sosai sabida tsoro yanda maza har biyu komatace uku suka biyota, cikin Yar siririyan muryanta that is trembling sosai tace “please save me…..plss…….I’m sca…….” tana maganan tana nishi da sauri da sauri dayake jinshi harcikin fatan kirjinshi don fuskanta gabaki daya na wajen ne, daidai lokacin daga boys din Ahmad din har Ahmad din dukansu sunzo wajen sun tsaya agabansu suna maida ijiyan zuciya sabida gudun dasukayi, One by one mutumin ke binsu da kallo batare daya furta ko a word ba har lokacin wayan nakan kunneshi bai cireba, faduwa gaban Ahmad yayi ganin fuskan mutumin dake kallonsu, ahankali yajuya sadaf sadaf daso samune ko takalmin shi da kasan wajen karma suyi motsin nuna alamun yana moving sanan ya yafito abokananshi da hannu yace “let’s go guys” dasauri sukace “marinka fa tayi Boss” da saurinshi kaman ana hankadashi yawuce yace “shikenan nidai natafi ku ku tsaya” ganin yanda yake tafiya da saurin bala’i tun bayan yaga fuskan mutumin yasa suma sukasha jinin jikinsu suka juyada sauri suka wuce.


“Eh Gwaggo ina jinki sorry ba shareki nayiba, Abban nake jira nariga nakawo shi…” ahankali tashiga dagoda kanta kaman wata mara gaskiya cikeda kunya jin mutum na wayanshi ta tsokano fada tazo tafada jikin shi, kanta akasa ahankali sadaf sadaf tashiga fitowa tana matsawa baya kafin gently kanta nakasa batare data kalleshi ba tace “thank you” sanan ahankali tajuya tashiga tafiya har lokacin gabanta nafaduwa sosai. “You!” Taji kaman daga sama mutumin yakirata chak ta tsaya batare data juyoba, “turn around” taji muryanshi anatse yet with authority batasan mesaba amman kasa ketare abinda yace tayi tayi hakan yasa gently tajuyo sanan ahankali tadaga fuskanta takalleshi, wani dogon saurayi ne fari sol dashi kaman balarabe yana sanye da jumper na farar shadda bugaggiya kanshi babu hula gashinshi akwance baki sidik sai kyalli yake hannunshi rikeda iPhone 13 yazubamata idanu dababu alamun wasa daidai da digi acikinsu, hakanan jitayi takasa jure kallon mutumin dataga kaman ta sanshi amman ta manta a ina ta sanshi ta sauke kanta kasa, anatse yace “the next time I will see you making trouble I will arrest you!” dasauri tadago kanta ta kalleshi saida yafidi kalman arrest sanan police din ranan yafado mata arai, dauke kai yayi daga kallonta sanan yabude kofar motan daya tsaya jikinta ya shiga ciki tareda rufe marfin motan da sauri dayadan firgitata sanan ahankali tajuya tacigaba da tafiya ahankali.






Samin kanshi yayi da binta da kallo ta madubin motan, yanda take tafiya ahankali har lokacin bata dawo daidai ba, sanan ahankali yadauke kanshi daga kallonta jin wayanshi na ringing again screen din yakalla ganin Grandma yasa yabude motan yafito yace “this woman will not allow me leave in peace”.


Garden din takarasa tun daga nesa kawayenta dasuka hangota suka kwalamata kira hakan yasa takarasa zuwa inda suke zama tayi sanan tadauki bottle na ruwan dake gaban Farida tabude takai bakinta ta kwalkwale duk kallo suka bita dashi, saida ta shanye goran ruwan tass sanan ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya, Farida tace “daga ina kike haka duk kinyi zufa kaman kin fito daga yaki” dan yatsine fuska tayi kaman bazatai magana ba ganin yanda suke kallonta yasa tace “Ahmad na mara shine yabiyoni and someone…..” tadanyi shiru kafin ahankali tace “wani mutumi yataimakeni” atare dukansu all the 5 friends sukace “wani mutumi” shiru tayi sai chan tace “oho nima ban sanshi ba” dukansu dariya sukahau yi dasauri takallesu tace “me” hada baki sukayi sukace bakomi, sharesu tayi kawai cus she doesn’t even feel okay batasan mesa ba, duk suna zaune wata kawarsu tashigo eatery dagudunta tana haki tace “kufito kugani yan sanda sun shigo school dinan anzo ana kwashe su Ahmad da Gang dinsu” dasauri Farida tace “ke haba let’s go video it musashi a internet” dukansu tashi sukayi itama ta tashi tabisu suka fice daga cikin garden din, van suka gani na police gaban wani eatry dake kusada garden din dasuke ciki, dasauri suka karasa gaban eatry din student sun cika wajen suna kallon Van din police, suna tsaye wajen dayay cha da mutane sukaga an fito da Ahmad da akasamai handcuff a hannu an sashi a van din sai abokanen shi na dazsu dasuka biyota guda biyu saikuma wasu guda biyu daban yan sandan sun fito dasu ana sakasu a van din saiga police man dinan shima yafito daga eatry har lokacin yana sanye da kayan dazu farin shadda waya a kunenshi still, hada idanu sukayi batasan mesaba jitayi gabanta yafadi dasauri ta sauke kanta kasa tareda juyawa ahankali tamabar wajen bata kara juyowa ba kawai tai hanyar class nasu, daidai lokacin ana shirin fara wani lecture kujera tasamu atsakiyan ajin ta zauna sanan tabude jakanta taciro note nata da pen aka fara lecture ko kadan takasa concentrating batasan mesa ba she just keep seeing police man face din da what happen today, gabaki daya all through da day har yamma ita kanta tasan yau ba school tazo ba takasa natsuwa tunanin shi da komi yacika mata kai, wuraren 5 na Yamma Adamu direba yazo daukan ta shiga motan tayi ahankali tace “Adamu please kafara kaini Coldstone nasayi ice cream nasha saimu wuce gida” cikeda girmamawa yace “to Miss Khairy” daura kanta tayi akan kujeran tajuyar da kanta tana kallon hanya tareda fuzar da ijiyan zuciya, she just hope tanashan ice cream dinan sanyin shi zaisa brain nata yay sanyi tadena all tunane tunanin datakeyi tun safe.




Agaban wani Babban joint na coldstone Adamu yay parking hakan yasa tabude motan tafito ta shiga ciki, daidai wani Babban Jeep na shigowa wajen parking yayi kusa da Benz da Adamu ke ciki, bude gaban motan yayi yafito ahankali wanan karan yana sanye da kayan yan sanda Rolex din dake daure a hannunshi yakalla shidda saura, sanan yazaga zuwa boot din jeep din yabude keken guragu yaciro ya ijiye ya maida boot din yarufe sanan yadawo bangaren baya yabude motan wata kyakkyawan tsohuwa ce fara sol kaman balarabiya zaune abayan tasaka Riga da zani irin na tsofaffi anmai dinkin Bubu kafafunta da hannayenta sunsha lalli, hannunshi yamikamata batare dayace mata uppan ba hararanshi tayi tana kama hannun nashi tamike tsaye da kyar tana masifa tace “idan kaga dama kai gaba dani dagayau har jibi Ice cream dai saika kaini nasaiwa jikoki na ja’irin yaro kawai” ko kala baice mata ba da taimakonshi ya daurata akan keken sanan yamaida kofan bayan yarufe da karfi tace “kama balla motan baban karfi, ubanka zai sayamin wata Alhamdulilah Allah yamai arziki rufin asiri danasha takaici” cikeda masifa yace “wlh Goggo in baki shiru ba anan zan barki na shiga ciki nasayo” wani kalan murmushi tayi tamaka bakinta tace “yo ai nadauka gaba kake dani to muje nadena” dan murmushi kadan kawai yayi sanan yashiga turata zuwa gaban entrace din dakenan divided into 3, staircase ne gefe da gefe sai tsakiya a bit sloppy floor dazaka haura ka shiga cikin shagon, daidai lokacin security na budewa Khairy kofa tana fitowa rikeda paper bag na ice cream din dakuma handbag dinta rataye a shoulder dinta, saiga wasu yara su biyu maza dabazasu wuce 8yrs ba suna guje guje kowanne rikeda ice cream dinshi dayan kawai ya mamayi brother shi ya fizge ice cream din hakan yasa brother yay ihu yabi dan uwanshi da gudu Khairy dabude mata kofa kenan tasa kafa tafito zata fara sauka daga staircase din kawai yaran suka fito suka mugun bangajeta dayasa ita kanta tasaki wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login