Showing 72001 words to 75000 words out of 108352 words

Chapter 25 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt

24 Dec 2024

5626

tace “menene Alhaji lpy” hannu yadaga mata alamun tayi shiru yana sauraron maganan da Baba ke gayamai kafin ahankali yace “Innalillahi wa innailaihi raji’un, Innalillahi wa innailaihi raji’un” yama kasa fadin wani magana sama da haka kafin ahankali yace “Alhaji dan girman Allah kuyakuri, I am so ashame of myself, banmasan fitan Aliyu ba, da Izinin Allah duk inda Aliyu yashiga saina nemoshi zakaji daga gareni, assha wanan labari baimin dadi ba” zare wayan yayi ahankali daga kunnenshi Mami data damu sosai tace “wai Meya faru ne”? Cikeda damuwa yace “yarinyar da Aliyu keso Ummulkhairy daya nuna muku amma yarinyar aure tun tana karama ita kanta bata sani ba yau damukaje nemama Aliyu aurenta…….” Gabaki daya abinda ke faruwa Dad ya sanar da Mami cikeda tashin hankali tace “ina Aliyu yakai Yar mutane yanzu, ohhh Allah kayayema Aliyu Wanan zuciya tashi jama’a, ina yakai yarinyar mutane” fita daga dakin Dad yayi dasauri zuwa dakin Gwaggo cikin fushi yakalli Gwaggo dahar lokacin kuka take idanunta sun kumbura yace “Gwaggo ke kika fadama Aliyu yarinyar nan anmata aure” wani kalan zaro idanu Gwaggo tayi tace “nikuma nida tun dazu nike nan wajen kuka nike inagayawa Allah kome zakama magana haka, yanaganka haka menene wai”? Gwaggo tai maganan ganin damuwa karara a idanun dan nata, cikeda damuwa yashiga bama Gwaggo labarin abinda Aliyu yayi firgita tayi tamike tsaye tace “mun shiga uku jama’a wani irin bala’i Aliyu ke neman jefamu ciki, yo a ina yasan da maganan nan”? “Ninagaya mishi Gwaggo” kaman daga sama sukaji muryan Meena data fito daga uwardaka ta tsaya idanubta sunyi jazur, ahankali takaraso gabansu murya chan kasa tace “Dad I am sorry nina fadamai, Ya Aliyu is suffering abanza, gwara yasani and get over her yaden……” wani mugun mari da Dad ya kwasa mata ita kanta Gwaggo daba ita akamawa ba saida ta kwasa uban ihu, cikin balain fushi tace “kai Abdul kashe min jika zakayi ne” ta riko Meena data fashe da mugun kuka, cikeda zuciya Dad yace “angayamiki I don’t know abinda nakeyi ne danai deciding to hid the truth from Aliyu eh Aminatu? Nine ubanku I know halayyanku daya bayan daya, nasan waye Aliyu, nasan kalan zuciyan d’ana idan yanzu yaje yay abinda zaiyita nadama daganan har karshen rayuwanshi fa? How do u want me to handle this case? He kidnapped this girl kinsan idan suka kaima hukuma kara yayanki da kikeso kike gani abin arziki kikamai by telling him will spend the rest of his life agidan yari kinsan dahaka, hauka kikeyi ne Aminatu” yasake daga hannu zai daketa Dasauri Gwaggo tashiga gabanshi tafashe da kuka tace “dokanni Abdul ai abinda nake fadi kenan halinka sak Aliyu yadauko ko abu guda bai rage ba” takalli Mami dake tsaye awajen kofa tace “kawomin ruwa” takama Dad da jikinshi kerawa tsabagen bacin rai yana kallon Meena dake kuka sosai ta durkusa tazaunar dashi daidai Mami takawo ruwan karba Gwaggo tayi tace “yi bisimillah kasha Abdul yanzu ba lokacin fushi bane, sha dan Allah yi bisimillah” ahankali yay bismillah sanan yakafa bakinshi yasha, dan dama dama yaji, janye ruwan Gwaggo tayi daga bakinshi tace “yanzu ina kakega Aliiyu zai kai diyar mutane”? Ahankali yace “bansani ba Gwaggo but zansa all properties nashi da gidajen shi adubamin su daya bayan daya hopefully he will be in one” ahankali Gwaggo tace “to tashi kaje kayi abinda yakamata kadaina fushi Allah zai daidaita mana komi ka gwara kiranshi?” Gyadama Gwaggo kai yayi yana mikewa tsaye still dialing number Aliyu yace “all his lines are not going, duka layikanshi Gwaggo basa zuwa bari naje” yay maganan yana fita Mami tabishi da sauri zama dirshan Gwaggo tayi akasa tace “Ya Allah kashigo Wanan lamarin oh ni Tani, wani irin bala’i Aliyu ke neman jefamu, yaro yaje yasace Yar mWutane Amarya na shiga uku na lalace”.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.


wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp


This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
[6/29, 8:41 PM] +234 816 788 8825: 5️⃣4️⃣






Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.


wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp


This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️




Juyawa Zayn da zuciyanshi ke tafarfasa yayi stool dake gefenshi yay wani irin ball dashi dayaki kofa dayasa kowa ya kalleshi cikeda damuwa Manaf yadafashi yace “calm down Zayn” cikin tsananin bacin rai dababu wanda yanashan Zayn nada irinshi yace “don’t tell me to calm down Manaf! Wayeshi? Meyake takama dashi? What gives him d right yashigo har gidan nan yadaukan mun mata eh, wlh wlh saina kashesh…..” dasauri Baffa yatashi dakuwa yamai rai abace yace “kaci gidanku Zayn, lafiyan ka kalau dazaka faracin alwashin kisa? Awanan rayuwan anything u are doing try not to be selfish, bawai ina justify abinda Aliyu yayi bane is totally wrong but we all are humans, all of us have flaws, put yourself in his shoes for once and just imagine kanka idan kaine yaya zakayi? How will u handle new din wacce kakeso kuma kuke soyayya jibi ne aurenta how???? Kowa have his own way of handling emotions Zayn, now is not time for fada or hauka is two choice komubi komi ahankali musamu yadawo da Ummulkhairy kokuma mukabi ta karfi kota hayaniya muga akasin haka so just calm down kabarmu mu manya muyi handling abin” fuuuuu Zayn yawuce yafita, goshi Baba yadafa yana salati ahankali, dafashi Baffa yayi yace “don’t worry Allah zai magance mana Wanan matsalan” ahankali Manaf yace “Baffa ko za’a daga bikin mune” girgizamai kai yayi yace “a’a Manaf babu abinda za’a chanza kucigaba da shirye shiryen biki, Aliyu yarone mai hankali da natsuwa Khairy zata dawo gida kunji, nasan duk inda yake mahaifinshi zai nemoshi kutashi kuje” fita su Manaf sukai daga dakin zuwa flat dinsu da Zayn yayi.
******




Wani irin gudu da Aliyu keyida mota yasa tama fashe da kuka tana jijjiga marfin kofan motan kozai bude amman akulle tafita ganin yana neman kashesu, tunda take bata tabajin tana tsoron Aliyu ba sai yau sabida yanda taga yanayinshi, wani daji taga suna shiga arude takalleshi tace “Ya Aliyu ina zaka kaini dan Allah kamaidani gida, dan Allah kayakuri” kaman baimasan tana magana ba gani tayi sun bullo gaban wani container mai kyau, parking motan yayi motan na dukan jikin wata bishiya dayasa ta runtse idanunta jikinta narawa yawani irin bude mota yafito yazagayo ta inda take yabude kofan komawa baya tayida sauri tana kallonshi tana girgizamai kai tana kuka. “Ya Aliyu ina ka kawoni dan Allah kamaidani gida, bazan bikaba” wani irin fizgota yayi daga motan tashiga kokarin kwace kanta tana ihu chak yadauketa yana zuwa gaban container yasa password agaban kofan sanan yabude kofan yashiga lafiyayen daki ne ga kujeru harda tv akwai aciki da AC aciki, wani irin jefar da ita yayi akan kujera dawani irin sauri ta tashi dagakan kujeran tana kallonshi tana komawa baya kaman yanda yake kallonta yana kulle kofan yana dannamai password, saida yagama sanan yadago da kanshi yana kallonta dawasu irin idanu da sukai kaman jini tsabagen jan dasukayi, ko’ina najikin Khairy rawa yake kirjinta nabugawa fas fas tana kallonshi tana komawa baya, ahankali yadaga kafa yataho yana biyota yana kallonta tana komawa baya, jin bayanta abango yasa dasauri tajuya takalli wajan ashema takai karshen dakin, dawani irin sauri tajuyo zata gudu taganshi tsaye gabanta dab da ita dan tanajin saukan numfashin shi akan fuskanta, faduwa gabanta yasakeyi tazo tagefenshi zata wuce yatareta ta hanyar saka hannunshi daya abango sanan dayan hannun nashi yawani irin dakan bangon dasaida ya lotse azuciye yace “why did you lie to me!” Yamata wani irin ihu dasaida tajishi har cikin brain dinta, tunda take bata tabajin tarude takuma tsorata irin wanda takeji yauba kasa kallonshi tayi dan jitake idan takalli idanuwanshi zata iya fitsari ajiki, sake mata ihu yayi yasake dukan bangon. “Maisa kikamin karya Ummulkhair” wani irin fashewa tayi da kuka dake tsuma rai har lokacin takasa kallonshi tace “Ya Aliyu I don’t want to hurt you, nima bansan anmin Auren ba tun ina yarinya akamin, Ya Aliyu I know you nasan kishinka, banson inyi hurting naka, dan Allah kayakuri kabarni natafi kaga gida xa’a damu jibi bikina” Wayyoo Allah na Aliyu jiyayi kaman ta watsamai gishiri aciwo wani irin fizgo gaban riganta yayi gabaki daya tafada jikinshi yawani irin matseta yana kallonta da idanunshi kaman na wanda yay shaye shaye yace “nikike gayama jibi bikinki Ummulkhair”? Girgizamai kai tayi tana wani irin kuka mai sosarai ahankali tace “Ya Aliyu ina sonka this thing is hurting me sama da yanda yake hurting naka, Ya Aliyu kayakuri ka manta dani Allah zai baka wata wacce tafini” wani irin wurgata yayi bayanta yabugu da bango yanuna zuciyan shi kaman wanda yazare yace “what about PROMISE OF OUR HEART? Ina ALKAWARIN ZUCIYAN mu yaje? Who told you I want any woman in this world samada ke? I gave you my heart gabaki daya batare danarage space ko kadan aciki ba, maisa baki fadamusu bakison Auren ba?Maisa baki fada musu kinada wanda kikeso ba? Maisa bakice araba Auren ba? Maisa kika yaudareni kikaci amanata kikamin karya eh? Why did you toil with my feelings”? Ahankali Ummulkhairy ta tsugunna danji tayi kafafunta can not hold her any longer, kafafunta sunyi sanyi kaman yanda jikinta dakowani gaba dake ciki yay sanyi, murya chan kasa that sounds very very weak tace “Mama tahada auren Ya Aliyu, is my mother’s dying wish, bazan iya rabuwa da Ya Zayn ba! Ya Aliyu I’ve already accepted this marriage! I am ready nai rayuwa da Ya Zayn sabida mahaifiya…….” Kasa karasa maganan tayi sabida hawayen datagani sun sauko daga idanun Aliyu duka biyun masu bala’in dumi yana wani irin kallonta, kallon dake kunce da maganganu dayawa, da kunci dayawa, da bakin ciki dayawa. Jitayi zuciyanta yawani irin tsinke takasa karasa maganan datake, wani kalan kunci takeji aranta seeing Ya Aliyunta cry, Aliyu is hurt because of her jitayi babu abinda kemata dadi azuciya, murya chan kasa dake rawa sosai tace “Ya Aliyu I am so sorry, I am sorryyyyyy babu abinda zan iyayi dazai gyara komi, yanda nadauki abin amatsayin kaddara kaima ka daukeshi ahaka, alokacin da mumini zaiyi accepting whichever kaddara da yazo way dinshi saikaga for that imani dayayi Allah yasakamai da wani kyakkyawan abu dabai taba tunanin zai samu ba, Ya Aliyu kayakuri dan Allah” yadade ahaka yana share hawayen dasuka kasa daina zubomai yakai hannunshi yana sharewa sanan ahankali yajuyo da fuskanshi yakalleta da jajayen idanunshi saikuma yajuya yay wajen wani kujera dayake ijiye daban adakin, daga foam na kujeran yayi saiga wata Yar karaman bindiga daukan bindigan yayi yajuyo yana budeta ganin bindigan is fully loaded yasa yataho inda take a tsugunne tana share hawaye, hannu yasa yadagata tsaye dasauri takalleshi ganin bindiga a hannunshi yasa tawani irin zaro idanu jikinta ya shiga kyarma tace “Ya Aliyu mekakeyi” hannunta yachapke cikin zafin zuciya yasaita hannun nata kan bindigan tana kokarin fizge hannun nata amman yasaita kan bindigar da karfi dayaji yakama hannunta gam kan bindigan sanan yakai gun din daidai saitin heart nashi yakalleta kaman yanda tawani zaro idanu tana kallonshi birkicewan datayi yafi na dazu tace “Ya Aliyu mehaka? What are you doing Innalillahi” damke hannunta yayi da kyau ta yanda bazata iya zare hannunta ba ahankali yana kallon hawaye na zaro idanunshi yace “Pickle kince kinyi accepting Zayn amatsayin mijin ki ko sabida wish din Mama ne, kinyi accepting Auren zaki zauna dashi” yadanyi shiru sabida hawayen dasuka sake zubomai kafin yay wani irin huci yace “instead of kalaman nan naki sudinga kasheni slowly I have a better idea miki, just shoot me lemme die in peace, shoot me!” Yay wani mahaukacin ihu yana gyara yatsanta akan trigger dayasa ahaukace dan duka ta daburce tafashe dawani irin kuka tana girgizamai kai tama kasa magana, ihu yamata yace “kill me Ummulkhair, ki kasheni saiki huta kiyi rayuwan Auren ki in peace I will never be a problem for you in this life, wlh the only way dazaki iya rayuwa da Zayn shine kawai ki kasheni I am giving u the best option now, kill me and enjoy marriage dinki matan Zayn, shoot me Ummulkhair!” At this point numfashinta ma neman daukewa yake kawai girgizamai kai tayi hawaye kaman kogi takasa ma magana kawai girgixamai kai takeyi, gyara hannunta yayi jin yana kokarin pulling trigger da yatsanta and the only way she can save Aliyu from kashe kanshi yadawo hayyacin shi is just one way.






Cikin wani kalan karfi karfi ta tureshi da dayan hannunshi sanan ta fizge hannunta dagakan bindigan taredayin wani irin sound ihu da sunanshi kai tsaye. “Aliyu!!!!” Gabaki dayan dakin saida yadauki yanda takira sunanshi yana echo adakin dayasa ya tsaya chak da jajayen idanunshi yakalleta, jitayi duk wani tsoronshi ya tsaya tadake dan she needs to help him and set him right tariga tai aure, tai aure, itada Aliyu can never work so she just have to help him yay getting over her, or even hate her. Cikin wani kalan kakkausan murya dako ita batasan tanada shi ba takalleshi right in the eye kaman yanda yake kallonta tace “why are u selfish maisa kacika son kanka dayawa Aliyu?” Tai maganan bitterly, tace “kataba gayamin sabida Maman ka dudda u were a barrister kaje kazama police from a scratch ma you fulfill wish na mahaifiyarka then who are you to try to meddle in the business of fulfilling my own mother’s wish bayan kai u are doing the same thing who do you think you are Aliyu!” Tai maganan tana kallonshi, kafin Awani irin zuciye tanunashi da yatsanta tace “uwa batafi uwa ba Aliyu! Soyayya is nothing compare to abinda mahaifiyata keso, zan zabi Ya Zayn so dubu akanka dan yafimin kai sau dubu cus shine zabin iyayena! Aurena dashi zai fimin albarka kan Auren ka dan u are nobody Aliyu pace a policeman, Ya Zayn is an Auditor, Business Auditor sorry I mean International Business Auditor unlike kai da u are nothing but a Divisional Police officer!” Aliyu jiyayi yayi baya zai fadi tsabagen yanda yaji karfin jikinshi yakare dasauri yakama bayan kujera yajuyo yana wani irin kallon Ummulkhairy dat was pointing finger at him tana kallonshi tsap jiyayi idanunshi na juyawa, cikin wata irin murya dabata fita sosai yace “Ummulkhair!” Yana kokarin yakara gasgata abinda take fadi, gyadamai kai tayi tana danne kukan datakeji ganin how she’s hurting him adake tace “yes Aliyu after zama danayi nayi all those analysis tsakanin kaida Ya Zayn, waye kai who know you, sainaji gwara Zayn, Zayn is better than you in each and every way na rayuwa! Zayn yafika komi! Gata, aji, kudi, ilimi duka yafika, Zayn is a PHd holder kaiko wani kwali kakeda? Saisa na yanke shawara namayi flushing SIM card dina sabida banson mutum irinka nakira na, listen attentively da wanan maganan dazanyi Aliyu, ni UMMULKHAIR MUHAMMAD I love mijina! I so sooo much love my husband, Ya Zay………” kawai gani tayi idanun Aliyu sun juya sama kafafunshi dake kasa sun daga sama yay wani irin suma ta saman kujera kanshi yay kan kujera zuwa kasa yaWwani irin mummunan faduwa daFyasa tai wani gagarumin ihu. “Ya Aliyuuuuu”.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.


wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp


This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️






[7/1, 10:33 AM] +234 701 275 3212: 5️⃣5️⃣


Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.


wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp


This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️




Dawani irin gudu tai kanshi tana kuka sosai, hannunta takai tadaura akan fuskanshi tana bubbugawa ahankali tace “Ya Aliyu dan Allah katashi, Innalillahi mena maka haka, Ya Allah kaduba zuciyata I don’t want wani abu yasami Ya Aliyu” jin baya numfashi yaki farkawa yasa tamike tsaye tashiga kalle kalle adakin kozata ga ruwa amman ko alamun ruwa batagani ba wajen kofa tayi ta murda ina yaki budewa saitasa password kuma batasan mene ba, dawowa tayi hankalinta ya bala’in tashi tazo jijigashi tashigayi tana kuka. “Ya Aliyu katashi dan Allah katashi kaji Ya Aliyu” mikewa tsaye tayi tama rude tana juye juye tarasa maizatayi hannu tasa tazare dan kwalin kanta ta warware dasauri sanan tashigamai fifita dashi da sauri da sauri tanamai addu’a.




Almost 5min tadauka tanamai fifita sanan ahankali taga idanunshi na motsi hakan yasa ta tsayar da fifitan datakemai tana kallon fuskanshi daga tsaye datake akanshi gently yabude jajayen idanunshi yadaurasu akanta all kalaman data gama fadamai suna dawowa kanshi zuciyanshi da kirjinshi namai wani irin ciwo kaman ana kona garwashi acikin kirjinshi wasu zafafan hawaye ne suka fito daga idanunshi suka gangara gefen idanunshi yana kallonta motsi datagani yayi da bakinshi dan yanda kirjin kemai zafi baijin zai iya wani ihu ba dawani irin sauri tai kneeling kusada shi takai kunnenta saitin bakinshi tana sauraron meyake fadi, cikin wata kalan raunanniyan murya yace “I hate you Ummulkhair! Na tsaneki with every bone and flesh na jikina, I regret the day I ever told you ina sanki! Nayi daman saninki arayuwana, I regret knowing you and even spending time with you, Ummulkhair Muhammad I Aliyu Hydar Abdullahi Abdulwahab hate you with every drop of blood na jikina!” wasu kalan hawaye taji sunzo mata amman tadaure ahankali tadago da kanta tajuyo takalleshi gani tayi yadauke kanshi yakalli gefe yana cijan lips dinshi kana ganinshi kasan wani abu kemai ciwo, ahankali yace “the door password is Pickle open and go back home” jitayi jikinta kaman yay kankara takasa ma wani kyakkwaran motsi daga inda take takai hannunta kan bakinta ta taushe sabida kukan datakeji tana kallonshi ganin yanda Aliyu ya tsaneta duk wani soyayya dayake mata ya rikida yakoma kiyayya bamayason yakalli fuskanta kaman ba Aliyun taba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login