Showing 78001 words to 81000 words out of 108352 words
Chapter 27 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt
dead mahaifiyarta ake cikawa akanta nima bari na kashe kaina maybe alokacin ne zakabi umarnina” kawai Ammi tadaga wukan da gaske zata chakama kanta dawani irin sauri Zayn yazo hannunta da wukan kekai yakama chak yana kallonta saiga hawaye sun zubo daga idanunshi sharrrrr murya chan kasa yace “Ammi basai kin dauki rayuwanki bane zan miki biyayya ba” ijiyan zuciya yasauke kana ganinshi kasan abin namai ciwo sosai hawaye yasake gangarowa daga idanunshi yana kallonta still. Ahankali yace “Ni Zayn nasaki Ummulkhairy” da dayan hannunta dabai rikeba Ammi tanunamai uku, wasu uban hawaye ne sukai gushing daga cikin idanunshi zuciyanshi namai ciwo ahankali yace “saki uku” sanan yakarbe wukan hannun Ammi ahankali kafin yajuya zai fice cikeda zafi tace “ina zaka sami paper ka rubuta kabama Mahaifinka nasan zaice nina saka amman na shiryamai kome zaimin yayi, dolenshi dai yaje ya nema maka Aisha ka aura” bude kofanta yayi yafice yana goge idanunshi yay side dinshi jiyayi yama tsani komi da komai bazaima iya kara 1 good minute anan Nigeria ba, flat dinshi yawuce koda yashiga Mamu na bathroom hakan yasa yadauki paper da buro yashiga rubutu yana share hawaye kafin ya linke yasa a envelope yadaura kan gadon sanan yadauki wani bag pack yadauki su international passport dinshi da other necessary abubuwa dayake bukata kafinma Mamu yafito yawuce kawai yafita yashiga mota straight to airport.
Wanan kenan!!!
Wuraren 4 Baba da Baffa suka dawo gidan bikin dudda akwai mutane cikeda gidan sama sukayi zuwa dakin Baba sanan suka tura Batool taje ta taho da Ummulkhairy.
Ummulkhairy na zaune adakinta abin duniya yamata yawa babu abinda kemata dadi aduniya, tai wani irin zuru zuru Batool yashigo dakin tace “tashi muje su Baba nakiranki zaa fara miki fadan Amarya” kallon Batool tayi tama kasa tashi ita kanta bazata iya explaining yanda takeji yau dinan ba kaman tamutu kawai takeji, kamata Batool tayi tana gyara mata lullubi sanan suka wuce zuwa falon Baba da ita suka bude kofa suka shiga, daga Anty Mariya sai Mom da Baba da Baffa zaune suka shigo zama sukai akasa Baba na kallonta yanda tai kyau sanan yay gyaran murya yace “Ummulkhairy nazo miki dawani sabon labari dudda nasan ba lallai bane kiso kijishi ba” Baba yadanyi shiru kafin ahankali yace “dazu muna wajen daurin Auren yayyinki babban amincin Zayn yakawo mana wata wasika daga Zayn” Baba yasakeyi shiru, ahankali Baffa yace “Ummulkhairy d’ana Zayn ya aiko da wasika dake dauke da saki, yace yasakeki saki uku!” Dawani irin sauri daga su Mom har Batool da ita kanta Khairy ke kallon Baffa, dan ijiyan zuciya Baffa yasauke anatse yace “I don’t want to go into details Ummulkhairy, nasan Auren Zayn burin mahaifiyar kine, amman wanann da tunkafin akai ko’ina Allah ya wargaza al’amarin inaga akwai wata aya da Allah ke kokarin nunamana Ummulkhairy dan haka kiyakuri” wani irin gyamboo taji zuciyanta namata tun dazu zuciyanta namata ba dadi amman na yanzu is like times 1000, Aliyu kawai take tunanowa da wulakanci datamai, ta wulakanta wanda ke sonta kaman zai haukace, tacimai mutunci, tamai gori da Zayn, tayi insulting pride na Ya Aliyu gashi yanzu wanda yasa tamai haka yasaketa tunkafin akai ko’ina kaico! Wani kalan kuskure tayi arayuwanta ne haka Ummulkhairy! Baffa ya katse mata tunani ta hanyar kiranta hakan yasa ta kalli Baffa, anatse Baffa yace “Ummulkhairy mun daura miki aure da Aliyu ga sadakin ki nan!” Wani irin zaro idanu tayi tanajin maganan kaman amafarki taga Baba yatashi ya ijiye mata wasu bandir na kudi akan cinyanta, ahankali Baffa yace “saidai mijin naki Aliyu baida lafiya sosai har yanzu yana gadon asibiti mahaifinshi yace ayanzu haka baimasan wanda ke kanshi ba, anjima dukanmu nan bayan sallan magrib zamubar kome mukeyi muje mu duboshi, kekuma nan bada jimawa ba dan mahaifinshi yariga yakiramu za’azo daukanki gidansu za’akaiki for now, idan yazo yaji sauki In Allah ya yarda sai ayi duk bikin dazasuyi akaiki gidanki ki tare kinsan yanzu babu wani shirye shiryen da akayi bikin yazo mutu bakatatan” Baffa yay shiru sanan Baba yace “Ummulkhairy inaso idan kinje gidan mijinki kiyi koyi da halin mahaifiyarki, nasan Aliyu baida mahaifiya tarasu, amman yanada Kaka da Matan Baba da kanne, nasanki da girmama mutane inaso kibisu sau da kafa karnaje complain akanki sai yabo, ki kasance mai tsoron Allah da biyayya ma mijinki dan yanzu aljannar ki na karkashin mijinki ne……..” Baba yashiga mata fada mai ratsa jiki dayasa tafara kuka, har cikin ranta dataji ance an aura mata Aliyu jitayi kaman an cire mata wani babban kaya azuciya amman kuma aliyu ya tsaneta, but ba matsala idan shine battling dinta agidan mijinta she is ready zatai fighting for her love back she will win Ya Aliyu back and taroki gafaranshi lokaci yayi yanzu dazata zama dat sensible and matured girl da Mama koda yaushe kEhso tazama.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
[7/3, 5:33 PM] +234 913 791 2752: 5️⃣9️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Daga Baffa, Anty Mariya, Baba da Mom babu wanda bai mata fada da wa’azi cikinsu ba, wajajen 6 Baba yace “wife kutafi da ita ta shirya motocin daukanta na hanya” gyadamai kai Anty Mariya tayi sanan suka dagata ahankali tana kuka sosai daki aka kaita wanka akasa tayi sanan aka bata ruwan turare tayi dashi sanan tafito shiryata sukayi cikin wani milk hadadden lafaya mai bala’in kyau, 6:40 hadaddun motoci sunyi layi gaban gidansu kowane mota dan sanda ne da full uniform keja dan duka boys sun Aliyu Dad yakira.
Tsaf aka shiryata bakaramin kyau tayiba aka lullubeta sanan aka fito da ita takasa daina kuka she can’t believe shikenan dagayau tabar gidan iyayenta rungume Baba tayi gam gam ana guda ana ayiriri sun dade ahaka shima Baba idanunshi sunyi ja sosai sanan yadagota yace “ya isa haka kukan kar kanki yayi ciwo” ahankali yakama hannunta yasaukar da ita kasa ana binsu suka fita tsakar gida har zuwa kofar gida da kanshi yabude kofar motan kafin ahankali yace “go in peace Ummulkhairy, ubangiji Allah yama aurenki albarka, ina rokon Allah to bless your new home yakuma haskaka rayuwan aurenki, go my daughter” yay maganan yana sata cikin motan ta zauna ahankali tana kuka, shiga motocin su Mom sukayi da kawayenta da Batool sanan aka tafi da ita.
Tsakanin gidansu Aliyu da nasu nada nisa sosai, dan sai wajajen 8 nadare sukakai, wowww Batool dake gaban motan tafadi ganin Babban gidansu Aliyu, an bude gate wato kudi nada kyau dudda su kansu basusan da bikin ba but they were able to pull something an zuba kujeru hadadun agidan ga DJ an kawo, yan uwa sun cika gidan ko’ina hayaniya ga girke girke abinci kala kala na yawo a tsakar gidan, kafin sufito daga mota Gwaggo da Mami dasukaci gayu na gani afada sukazo taransu idan kaga Gwaggo zaka dauka an mata bushara da Aljanna ne, fito da Khairy akayi daga mota kawai Gwaggo tafashe da kuka Dan she can’t believe Ummulkhairy ce aka kawomata amatsayin Matar Aliyu danta, taruwa akai kan Gwaggo dake kuka cikin kuka tace “ni kubani y’ata na rungume” murmushi su Mom sukayi sanan suka kawo mata Ummulkhairy dakenan alullube tawani irin rungumeta tana mata ruwan saman addu’a a godiya aka sanan tasaketa tace “kushigo” shigowa sukayi babban falon Mami aka fara kaita aka zaunar da ita atsakiyan dakin ana waka ana rawa Mami na murmushi ana cemata saita saya baki zata ganta, kudi Mami takawo da box na warwarayen zinare tadaura kan jikin Khairy ana ihu ana guda sanan aka bude mata fuskan Khairy kallon fuskan Khairy da idanunta ke kasa tayi sanan tamata addu’a kafin a dauketa akaita dakin Gwaggo, Gwaggo da dan kafafunta dababu lafiya rawa tahauyi Haba zokaga dariya sanan takawo turaman zani guda ashirin tabama Khairy da bandir na yan dubu dai dai guda uku, da zoben azurfa da warwaron azurfa da sarkan azurfa masu kyau sosai aka dinga guda, tashi Mom da Anty Mariya sukayi sukai sallama da su Baffa najiransu suzo aje aduba Aliyu, da Kyar Khairy tasakesu suka tafi sai kuka take sanan Kaka takaita dakinta dan fir tace “ita awajenta Khairy zata zaune har zuwa aliyu yaji sauki tanada dakuma daban daban dayawa a side nata, wani hadadden daki aka kai Khairy gadon ciki ma sabone fill dan dazu da rana Dad yasa wani furniture company suka kawo aka chanza komi na dakin aka fitarda nada zaunar da ita akai akan gado itada Batool da Amal kawarta sauran mutane duk suka tafi.
Wuraren 10 su Baba sukakai asibitin Dad, Dad dakanshi yazo yadauke su akasa yace “barkanku da zuwa” gaisawa sukayi suna sama Baba yace “yajikin nashi” ijiyan zuciya Dad yasauke yace “Alhamdulillah muje” sukai sama har zuwa wajen wani daki, bude kofan Dad yayi ahankali yashiga su Baba biyedashi Aliyu na kwance kan wani hadadden gado da kayan asibiti idanunshi akulle he’s attach to wani machine, salati su Baba sukayi, Baffa yace “what’s the plan yanzu” dan ijiyan zuciya Dad yasauke yace “wanan machine din shine taimakama heart dinshi to beat, beating na heart nashi is very slow, so yanzu dai gobe zamu fitardashi zuwa Oman akwai wani heart Dr achan he’s my very close friend tare mukai karatu a Ukraine yace nakawoshi Aliyu will be fine” dukansu ajiyan zuciya suka sauke Baba yace “In sha Allah zaiji sauki, please if u need anything we are here for you yanzu munzama family” murmushi Dad yamusu cikedajin dadin maganan su yace “Allah yabar zumunci nagode sosai” motsi da Aliyu yayi yasa dukansu suka kalleshi dasauri Baban yay wajen gado yana kama hannunshi yace “Aliyu, Hydar I am here can you hear me”? Wani irin bude idanunshi Aliyu yayi kadan da kana gani kasan baya cikin hayyacinshi sanan murya chan kasa yace “Um….mulk….hair” kafin yakara lumshe idanu kaman bashi ne yay motsi ba, sakinshi Dad yayi yadanyi murmushi yajuyo yakalli su Baba da jikinsu yay sanyi sosai yace “tun shekaran jiya haka yake saidai yadan bude idanu kadan yakira sunan Ummulkhairy yakoma” dan murmushi Dad yasakeyi sanan yakalli Aliyun yace “one thing I am sure of shine d’ana na bala’in son Ummulkhairy so thank you Alhaji dakuka auramai Ummulkhairy bazan taba mantawa da wanan kyautatawan dakukamin da d’ana ba” yay maganan yana juyowa yakalli su Baba daduk sukejin badadi suna addu’a Allah yabashi lpy, sun dade a asibitin sai wajajen 12 na dare sanan suka tafi, Baba da Baffa sun dade suna magana sanan kowa yawuce gidanshi.
Saida sukakai gida sanan Mom takalli Baffa kafin tafita daga cikin motan ahankali tace “one thing danasani cewa inaso gamedakai shine rashin yanke hukunci acikin fushi, nasan ba hurumina bane nan amman inaso na roki alfarma biyu daga wajenka” tai dan shiru tace “nafarko shine inaso kamaida Ammi and inaso kai kokari and look at her situation and understand her, batasan da Auren nan ba itace mahaifiyar Zayn, taci buri kan danta is understandable idan taki yarda da Auren nan kowa da kalan zuciyanshi, kuma yanda Zayn bai auri yarinyar nan ba barabonshi bace wlh inda rabonshi ne daba Ammi ba ko duk aduniyan nan ne basu isa suraba Auren nan ba, sai alfarma tabiyu shine ko’ina Zayn yaje ka kirashi danka ne, nasan yanachan cikeda damuwa yasa kazama karamin mutum da sauransu kanunamai bahaka bane yadawo gida, Auren Ummulkhairy ko rashin aurenta won’t change kai mahaifinshi ne yazo idan yanason wacce Ammi keso ya aura wato Aisha kaje ka nemamai Auren idan bayaso yakawo kowa yakeso ya aura, rayuwa batada tabbas kowa datashi kaddaran just look at Aliyu yanzu yanachan kwance rai hannun Allah yay giving up but Allah yaga zuciyanshi cikin sauki yabashi Ummulkhairy, komi yafaru nada dalili sometimes abinda mu iyaye kesoma yaranmu is not the best or Khair for them, I know u are hurt amman kayakuri and forget everything let this family continue to be in peace kaji”? Gyadamata kai Baffa yayi ahankali bude kofa tayi zata fita dasauri yakamo hannunta hakan yasa tajuyo takalleshi, ahankali yace “I am so lucky to marry a wife like you, Allah yamiki albarka” murmushi tayi tace “Ameen” sanan tawuce ta tafi shikuma yadan dade zaune a motan sanan yaciro wayanshi yakira number Zayn ringing yake yana gab da tsinkewa yadauka.
Ahankali Zayn yace “Abba kayafemin I am so sorry” murya chan kasa Baffa yace “shiiiiiii Zayn i understand you Allah yasa hakanne mafi alkhairi, kana ina”? Murya chan kasa tace “ina wani hotel ban sami flight ba yau saida safe” anatse Baffa yace “dare yayi yanzu dan haka forget about tafiyan nan gobe dasafe kadawo gida kajini, I am not angry with you one bit hakama Baffan ka shima he’s not, so kadawo gida kadauki komi amatsayin kaddara inda Ummulkhairy matarka ce da Ammi n ka bata isa taraba Auren nan ba, so it’s okay, kadawo gida inaso kafito dawata yarinyar ka aura idan wacce mahaifiyarka keso ne to idan ma ba ita bane duk daya kaji” gyadamai kai yayi ahankali yace “thank you Abba” murya chan kasa Abba yace “don’t cry again good night son” ya katse wayan.
[7/3, 5:34 PM] +234 913 791 2752: 6️⃣0️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Jirgin karfe 6 nasafe Dad da abokinshi sukabi aka wuce da Aliyu Oman.
****
Dukansu adakin sun makara sabida yanda akai bacci late jiyada daddare, Ummulkhairy tafara bude idanunta wuraren 8 nasafe, saman dakin tabida kallo komi nadawo mata sabo she can’t believe ita Amarya ce and tana gidan iyayen mijinta Aliyu anan ta kwana, tashi zaune tayi ahankali tana kallon Batool da Amal dake shargan bacci sanan ahankali tamike tsaye tawuce bayi, shiga tayi ta maida kofan tarufe sanan tabude tap wanke fuskanta tayi takalli madubi tai wani irin fresh fatarta tayi da sulbi sulbi yakeyi tsabagen dirzan gyaran jikin da aka mata tarame babu abinda yarage ajikinta banda boobs da hips, ijiyan zuciya tasauke ahankali sanan tadauki brush sabo dake dakin tadauro alwala tafito daga bayin ganin Batool zaune yasa tashimfida dadduman dake dakin tadauki hijabi tasaka tai salla.
Koda ta idar zama tayi tai shiru tana tunani, Aliyu kawai zuciyanta keso yagani tabashi hakuri, tsayawa akanta Batool data fito daga bayi tayi tace “tashi kije kiyi wanka ki shirya” gyadama Batool kai tayi sanan tamike tsaye ahankali tana kallon Amal dake bacci still sanin bata salla yasa tawuce bayi batare data tadata ba.
Wanka tayi tafito daure da towel set na akwatin da Baba yamata Batool tashigo da daya shigo daga cikinsui sanan ta ciro mata wani lafiyayyen lace ja, shiryawa tayi da taimakon Batool duk wanda yaganta saiya kara kallonta, mayafi Batool takawo mata tayafa mata aka sanan ta feffesa mata turare tace “fita kije ki gaida Gwaggo tana falo” Gyadamata kai Ummulkhairy tayi sanan tabude kofa ahankali tafice tanabin corridor dake kamshin turaren wuta sanan tadaga labule tafito falon, Gwaggo na zaune afalon kan daya daga cikin jerin kujerun dake falo 3sitter tana burga wani lafiyayyen fura a kwarya, Meena na zaune kusada ita itama tasaka atampanta mai kyau sosai, ganin Khairy yasa tawani irin ijiye wani empty kwaryan dake hannunta wanda tarike tana jiran Gwaggo tagama ta tsammata tadauke kai, kaman ance Gwaggo ta waigo sabida kamshin turaren da jikin Khairy keyi ganin Khairy gaban corridor kanta akasa kana ganinta kasan kunya takeji yasa tawani washe baki tana kallonta tace “jama’a kuzo ku kalli Matar jikana Ali Gadanga kusar yaki” dan gajeren tsaki Meena taja mara kara tana kara dauke kai kaman taga kashi, ahankali Khairy takaraso gabanta sanan ta tsugunna har kasa akunyace tace “Gwaggo ina kwana” dungure kan Meena Gwaggo tayi tsabagen dadi tace “dan gidanku kalli yanda ake gaida manya ba irinku ba da kullum kedamuna da kud moni daga tsaye kuna shanyemin jini masu bakin hali, tashi tashi kinji diyata Allah ya lullubeki da albarka, zauna kenake dama ma fura zo zauna nan kusadani ke Meena matsa mata” gyara zama Gwaggo tana kara matsa mata girgiza matakai Khairy tayi akunyace tana kokarin zama akasa dasauri Gwaggo tace “kul karki zauna akasa, sokike sanyi ya shigeki kina amarya, zauna nan kan kujera kusadani kiga, matsa mata Meena” tai maganan tana tunkude Meena wani mugun kallo Meena tama Gwaggo kaman ta maketa sanan ta tashi fuuuu tafice daga dakin Gwaggo tabita da harara tace “kinga bakin hali yan gidan nan ko dukansu haka suka gaji Wanan bakin halin daga wajen ubansu, zauna kiga” zama ahankali Khairy tayi kan kujeran Gwaggo itama ta gyara zama da kyau sanan takarasa kada furan tamika mata tace “ungo sha kena dama mawa” ahankali tasa hannayenta biyu takarba tana murmushi sanan takai bakinta takurba furan kadan dadi sosai tadade bataci abinci hakaba tass tashanye furan Gwaggo nawani irin murmushi sanan takarbi kwaryan tace “kawo nan kiga banson kiyi komi, ko sauro banson ya cijeki zan taya Aliyu kula dake harsu dawo daga kasan waje” kallon Gwaggo Khairy tayi dan batagane metake nufiba hakan yasa Gwaggo tace “yauda sassafe aka tafi dashi kasan waje sabida zuciyanshi ba lafiya Baban shi yakaishi wajen wani abokinshi likitan zuciya kidinga ma mijinki addu’a kinji In sha Allah zaiji sauki” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali tana kokarin rike hawayenta dan duk itane dalilin Wanan rashin lafiyan nashi.
Yan aikin Mami ne suka shigo da manya manyan kulolin abinci zasu ijiye a falo tace “tafin musu dashi chan dakin Amarya” wucewa cikin sukai sa abincin, ahankali Gwaggo tace “tashi kije kiyi Kari ki kwanta ki huta anjima kawayena zasuzo su ganinki kinji” gyadama Gwaggo kai tayi sanan ahankali tace “nagode Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “ohh Allah yabani mai mini godiya, gantalallun yaran gidan nan kome zan musu