Showing 63001 words to 66000 words out of 108352 words
Chapter 22 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt
ta yarda dashi kaman Baffan ki tasan ko Bana duniya sai inda karfinshi yakare akan yarana sabida haka tanason ta aurar dake tun yanzu datake da ranta a inda ko yanzu yanzu tafadi tamutu zata tafi batada damuwa” Baba yakara yin shiru kowa na kallonshi, handkerchief yaciro daga aljihu yakai kan idanunshi dan ko kadan bai son yay kuka agaban yaran shi, kafadan shi Baffa ya matse sosai yakalli yaran yace “Baban ki yadauka awanan daren Maman ki zata rasu, bayan tamai maganan nan tasashi yakirani awaya, kunga acikin kuryan darenan haka nashiga mota nazo asibitin nan, cikin tsananin zazzabi tana rike dake a hannunta tace tanaso tabani amanarki sanan tana neman alfarma wajena…..” wani irin faduwa gaban Khairy dake kallon Baffa chass takeyi dabama tasan na miyeba, ahankali Baffa yace “Maman ki tace tanaso nahada Ummulkhair da Zayn babban dana wanda Mamanki takeso sosai sun shaku da mamanki sama da su Hafiz ma, tace tanaso nahada ku aure” Zayn da tunda aka fara maganan kanshi ke kasa sai alokacin yadago kanshi yakalle Babanshi dake Magana, Baffa yace “jikin Maman ki yay zafi yay tsanani duk mun zaci zata rasune, Gyadamata kai nayi na nuna amincewa na, tace mukaita masallaci adaura auren, I remember Baban ki yafita waje yadauko keken guragu muka daurata akai muka gungura keken har zuwa masallacin dake asibitin nan dayake nan kaman ba dare ba jama’a duk suna zazzaune some a kwance iri masu jinyan nanne, da sauransu limamun muka kira mukamai bayanin komi ya matukar tausayama Maman ki sanan aka gungurota aka shiga da ita masallaci tana rike dake a hannu limam yadauki microphone aka tada duka mutanen dake bacci” tsinkewa gaban Khairy yahauyi yana dawowa daidai hakama Batool, Ammi, Zayn dakuma Anty Mariya, kowa na kallon Baffa, murya chan kasa Baffa yace “all I had was 20k ajikina haka na bayar kudin sadaki dani da mahaifinki limamin masallacin mahaifiyar ki jama’an dake wajen suka shaida daurin aure tsakanin Ummulkhair Ahmad Muhammad da Zayn Abdullahi Gabas akan sadaki naira dubu ashirin!”
Khairy jitayi numfashinta zai dauke kunenta yay dummm kaman ta sume ne kaman tafice hayyacinta ne oho ita kanta bazata iya tantance wani yanayi take ciki ba, daga Baba har Baffa murmushi sukayi suka kalli juna, Baffa yace “inda ace Baffan nan naku nada yara mata dayawa zansa yarana maza duka su aurensu sabida inaso muhada zuru’a wanan amincin dake tsakanin mu na abota takoma na jini, saisa bayan mun daura auren muka yanke shawarana sai yaranmu sunyi girma sun mallaki hankalin junansu zamu sanar daku, yanzu ma bikin su Manaf ne sabida munaso muhada bikin su da kuma taron bikin su Zayn ayi atare saisu tare nan da wata daya lokacin Ummulkhairy itama tagama jarabawa tagama makaranta ko aminina” gyadamai kai Baba yayi yana wani irin murmushi, Ammi dajitayi komi na duniya ya tsaya mata chak takalli mijin nata, cikin wani irin masifa tace “Alhaji na dauki cikin Zayn na wata tara, na tsugunna na haifo dana dakaina batare da wata ko wani yatayani ba ninasan ciwon kan d’ana nasan wahalan danasha na tarbiyantan dazai ka kama shekaru kusan ashirin kenan kama d’ana aure baka sanar dani ba wlh wlh wlh kayi kadan!” Ammi tama Baffa magana babu ko shakkan shi guda akan idanunshi dayasa kowa yakalleta shima Zayn yakalleta uppan Baffa baice mata ba hakama Baba duk kallonta suke da Mom da Anty Mariya dasauran yaran.
Hannun kujera Ammi tadaka cikeda bala’in dakin na amsa masifanta jikinta na girgiza tacigaba da magana. “Idan zuri’a kukeso kuhada abotanku yadawo tajini inace nan nan nan ga Batool nan diyar kace maisa baka hadata da Manaf ko Mu’az ba koma Maheer sai akan d’ana Zayn dina, kasan plan din danake dashi , buri danaci akan yaron nan nawa dazaka hadashi da yar gwal dinku? Kasan wace yarinya nakeso Zayn ya aura kasan matsayin Baban ta anan Nigeria kuwa kaga kyan Aisha? Wlh bazaka maidani karaman mutum a idanun kawata ba” takalli Zayn cikeda ihu tace “Zayn kalli fuskan mahaifinka kacemai bakason auren nan yanda sukayi suka hada auren subi haka su warware” shiru Zayn yayi kanshi nakasa shi bazai iyama cewa farin ciki yake ba ko bakin ciki all he knows is yaji dadin wanan labarin dayajita bagatatan haka kaman daga sama.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Baki Ammi tabude zata kara magana Baffa yadaga mata hannu cikin fushi, anatse yace “kinsan maisa duka wanan ihun dakike yi danki tozartani bazai taba bani kunya ba”? Dan murmushi yayi yace “sabida agaban dan uwana da yarana kike ko zaginane zaki iyayi” Baffa yasake murmushi yace “auren nan ba marigayiya kadai tai tunanin shi ba har mu nan, duk duniyan nan babu wanda zai rike Khairy amana kaman dan uwanta kuma Yayanta Zayn! Bata fita daga family ba zamu riketa amana dan dan uwanta take aure, banda kwanciyan hankali daya wuce nasan d’ana ke auren Khairy da mahaifiyarta tabani amana, nasanki karki manta na zauna dake tsawon shekaru danmu na farko shekarun shi 36 so babu wanda zai iya bada labarin halinki kaman ni, nariga nasan bakison mahaifiyar Khairy hakan zaisa bazaki tabaso auren shi da yarta ba abu nafarko dayasa naji bazan taba fadamiki ba kenan sai ranan da zan hada yaran nan nafada musu kisani kema, dan haka kome zakiyi kiyi Zayn mijin Ummulkhair ne nan da wata daya za’ayi walima ta tare agidanshi, kutashi kutafi” cikin yaran babu wanda ya iya cewa uppan duk mikewa tsaye sukayi banda Khairy data kasa mikewa tsaye tana kallon Baba idanunta sunyi jazur Baba shima yana kallonta, hannunta Batool takamo zata dagata tace “tashi muje Khairy” ahankali Baba yace “barta Batool” tashi yayi ahankali sanan yadauki wata yar jakan dake kusada shi yabude wani littafi yaciro tana kallon littafin ta tunashi Dairy Mama ne, karasowa gabanta Baba yayi ahankali sanan ya tsugunna agabanta yana kallonta, ahankali cikeda so dakuma tsantsar kaunar yarshi yace “Khairy kingan mu nan we are not bad parents idanma abinda kike tunani kenan, all abinda kikeji azuciyanki yanzu nasani, kina tunani tayaya aka miki aure tun kina karama baa taba sanar dake ba, auren ma da Yayan ki Zayn, wanda baki taba kallo da fuskan so ba, wanda bakisan koshi yana sonki ba” dan murmushi yayi yace “kituna babu aure mai albarka kaman wanda iyayenka suka zaba sanan suka maka banda haka kiyi tunanin auren nan mahaifiyarki dakikafi komi so aduniyan nan tahada ita tama miki shi Ummulkhair, and lastly mahaifiyarki tace nabaki Wanan abin ki karanta idan rana irin tayau tazo gashi” Baba yasamata book din a hannu, wani irin kankame book din tayi gam gam sanan Batool tadagata bin Batool kawai take suka wuce mota suka shiga suka zauna itama ahankali Anty Mariya tashigo taxauna tana kallona Khairy da idanunta suka bushe babu hawaye ko digi bazama ka iya tantance metake going through ba, chan saiga Baba yafito tareda Baffa motansu yazo yashiga yaja suka tafi sanan Baffa yawuce yakoma ciki biyoshi Ammi tayi tafara surfafa bala’i amman tak bai cemata ba
[6/26, 12:39 PM] +234 701 275 3212: 4️⃣8️⃣
Koda sukakai gida kasama fitowa daga motan Khairy tayi duk Baba na kallonta da taimakon Anty Mariya da Batool suka fito da ita sanan suka shiga ciki Anty Mariya tace “tafi da ita dakinku Batool” wucewa da ita sama Batool tayi sanan tajuyo takalli Baba zatai magana Baba yadaga mata hannu anatse yace “Zayn shine best husband da Ummulkhairy will ever wish for, please karkimin wata magana aikin gama yariga yagama beside auren nan mahaifiyanta tamata shi” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Baba saikuma ahankali tace “ok” sanan tajuya tawuce sama abinta.
Suna shiga daki Batool tazaunar da ita abakin gado sanan tamaida kofansu tarufe tasa key sanan tazo gaban gadon da gudu tazauna akasa kanta tadaura kan kafan Khairy tace “Khairy why are you not crying Innalillahi wa innailaihi raji’un, yanzu Khairy kefa matan aure ce, matan Ya Zayn, Khairy what about Aliyu? Ya Aliyu yaya zakiyi dashi? Khairy I am so sad for you not because Ya Zayn is a bad person but because of soyayyan da kukeyi da yanda kike sonshi da yanda Ya Aliyu yake sonki, Khairy how are you going to tell him eh? How”? Sai alokacin wasu kalan hot hawaye suka zubomata, jikinta harwani tsuma yake tana kuka mara sauti itama Batool kasa hanata kukan tayi saima rungumeta datayi suna kuka sosai, sun dade ahaka ganin asma ta na neman tashi yasada sauri tasaki Khairy tawuce tadauko mata inhaler ta dake kan drawer takawo mata tace “shaka and stop crying” ahankali ta shaka but takasa daina kukan, wani kalan bakin ciki da damuwa ne taji ya lullube mata zuciya littafin Mama ma sai kallonshi take takasa karantawa, da kyar da daddare ta iya shan tea tana zaune kallon wayanta kawai take idanunta sunyi jazur sun kumbura, wuraren 10 Batool tai bacci ta barta, tana zaune awajen tana kallon wayan shadaya nayi wayanta yahau ringing wani irin lumshe idanu tayi batare data kalli screen dinba hawaye taji sun zubomata sharrrr ajiki, tunda tasan Ya Aliyu kullum doki take yakirata yaune rana na farko dataji tana tsoron tadauki wayanshi ma dan gani take dazaran yaji muryanta zan gane and tayaya zata iya fadamai Wanan bakin labarin da tasan halinshi yanda yakeda mugun kishi idan wani abu yasameshi this night fa, kozata fadamai labarin nan she needs to think it through sanan tasami hanyan dazata iya fadamai batare datai breaking heart nashi ba dan batason wani abu yasameshi.
Wani kiran nashine yashigo ahankali tadauki wayan, maida wayan silent tayi gabaki daya sanan tasauka daga kan gadon ahankali tadauki littafin Mama, gaban wardrope taje tazauna ahankali akasa tana rikeda book din tana kallo tsoron ma karantawa take hawaye ta share dasauri sanan tabude book din ahankali tafara ni tana karantawa.
Tunda aka haifeta Mama tafara rubuta mata book dinan, taushe bakinta tayi jin wani mugun kukan dayake zuwan mata, sanan tacigaba da karanta littafin page after page, Mama na bata labarin komi wahalan datasha rayuwa kafin tahadu da mahaifinta, da ranan da ciwonta zai tashi da ranan da ciwonta zai lapa haka takebin littafin nan word by word tana taushe bakinta hartakai pages na karshen dataga yanayin rubutun mama ma ya chanza.
“Ummulkhair bansan maisa ba but anytime nake rike da littafin nan dakuma alkalamin nan babu abinda bana iya fayyace miki, yanzun nan kika fita kika tafi makaranta, lokacina yakusa ni kaina inaji ajikina saisa nace bari namiki Wanan one final rubutun. Ummulkhairy inaso kisani cewa duk cikin yaran dana haifo duniya babu wanda nakeso kaman ke! Nasan ance babu kyau uwa tafadima yaranta tafison Wanan kan Wanan nafadamiki hakane sabida inaso ki natsu aduk lokacin da Littafin nan zai sameki. Khairy ni mahaifiyanki nine na zabamiki miji Zayn sanan umarnina ne agareki kiyi zaman aure dashi!” Wani irin sakin book din Khairy tai akasa kawai tashi tayi dagudu tafada bayi ta kunna ma kanta shower tana wani irin kuka tamai sosa zuciya ahankali tace “Mama whyyyyyyyy? Mama Ummulkhairy ki Ya Aliyu takeso, Mama whyyy” wani irin kukan datayi batajin koda Mama tarasu tayi irin kukan nan ba, takai kusan awa daya abayin karkashin ruwa kuka take sanan da kyar ta lallashi kanta tafito bayan ta tube kayan tadauki towel tadaura akirji tabude kofa Littafin taci karo dashi ahankali ta tsugunna tasa hannu tadauka sanan tabude tacigaba da karantawa.
“Nasan bama kiwani san Zayn da kyau ba amman tun kina yarinya Zayn na bala’in sonki kuma yanaji dake, Zayn nada tausayi, yanada Imani sanan yanada kirki ni mahaifiyar ki na yarda da Zayn, karki tunani babu soyayya a tsakaninku so yakanzo daga baya, Khairy kaman yanda nafadi miki abaya na zaba miki Zayn ne sabida inaso hankalina ya kwanta aduk inda nasami kaina nan gaba dan haka y’ata don’t reject Zayn! Accept him and accept the marriage do that for me Ummulkhairy, do it for world best Mom dinki! Karki tadama Baban ki hankali ko yayyinki trust me nasan Baban ki will be going through alot kinsan kuma farin cikin ki shine farin cikin mahaifinki da yayyinki karki basu damuwa kinji Khairy na” Awani irin hankali ta gyadama Mama kai wasu sansanyar hawaye nabin idanunta suna saukowa kasa sanan tasake kallon book din.
“Allah yamiki albarka, inhar kayi abu for the sake of iyayenka dan ka farantamusu rai Allah zai albarkace ki, sanan zai baki kome kikeso cikin sauki, Khairy don’t stress your heart kiyi tunanin anything kibi umarnina dana mahaifinki bazaki taba tabewa ba Allah yamiki albarka daga mahaifiyanki Maryama”
Ahankali ta maida littafin tarufe sanan ahankali ta tashi tamike tsaye jinta take kaman iska zai kadata tafadi wardrobe tabude tadaga karkashin kayanta ta tura littafin sanan tajawo wani dogon Riga tasaka na bacci kafin tazo gado ahankali ta zauna tana kallon wayanta, ahankali tasaka hannu tadauka sanan ta danna 5miss calls tagani na Aliyu saikuma messenge, message din ta danna ahankali.
“Pickle are you sleeping? Maisa kikai bacci dawuri haka? Wait are you fine are you okay? Wani abu namiki ciwo ne??? Umm I am worried”
Hawayen daya gangaronata ta share ahankali sanan gently tashiga scrolling tundaga farkon message din dasuka farama juna harzuwa na yau tana karantawa wani irin jefar da wayan tayi kan gado takifa kanta kan gadon tana kuka, idan ta tuna Aliyu ta tuna yanda yake sonta da yanda yake mugun kishinta saitaji she can’t hurt him, bazata iyaba bazata iyaba! Ganin tana nema ta shige yasa tashaki inhaler ta sanan ta tashi tashiga bayi tadauro alwala wato idan kaga bala’i rasa bacci kake hijabi tasaka kawai tahau kan dadduma tana kuka tana fadima Allah komi itadai tasan tanata salla wajajen asuba barawon bacci yasaceta anan kaHn dadduman.🥰
[6/26, 12:40 PM] +234 701 275 3212: 4️⃣9️⃣
Bayan sunyi sallan asuba tareda Baffa da Zayn suka fito daga masallaci, tun bayan hatsarin nan haryau Baffa fushi yake da Zayn bayama amsa gaisuwan shi sai sa’i sa’i suna shigowa gida hannun Baffa Zayn yakama ahankali yace “Abba listen to me please” chak Baffa ya tsaya sanan ahankali yakalli Zayn din yay shiru, hannu Zayn yakai yakama kunnenshi ahankali yace “Abba nasan namaka laifi amman dan Allah ka yafemin and listen to me” wuceshi Baffa yayi zuwa kujerun dake garden na tsakar gidan masu kyau yazauna sanan yanunama Zayn daya daga cikin kujerun alamun yazo yazauna, ahankali yataho wajen yazauna yana kallon Abba, anatse Abba yace “Zayn shaye shayen ka bani kama laifi ba ubangijin daya hallito mu kamawa” murya chan kasa yace “Abba I know! Tun bayan abin yafaru I couldn’t live up to myself, Abba anytime naji inaso nayi I remember cewa abin yasa kanwata dat I care for wacce mahaifiyanta tabani amanan ta tace na kula da ita takusan mutuwa kan shan shishana, Abba ba lallai ka yarda ba wlh tun ranan ban kara marmarin shan shisha ba I even hated myself for shan shishan, Abba I am sorry” shiru Abba yayi yana kallonshi dan ya yarda da maganan shi dari bisa dari dan idanun Zayn basatabamai karya, ahankali Zayn yasa hannunshi yakama hannun Abba murya chan kasa yace “Abba I love Ummulkhairy tun kafin namasan da zancen auren and I want to promise you abu daya” yadanyi shiru sanan yace “Abba nasan bakada yanda zakayi ne daka tana auren mu tunda kagano ina shan shisha, Abba listen to me I have amended my ways wlh, and Abba namaka alkawari zan rike Khairy amana, bazan bari any harm to fall upon her ba, and I promise you Abba I will forever cherish and care for her batare dana bari Ammi ko anybody yatakurata ba and I will talk to Ammi zata yarda all those drama zata daina kaji Abba” hannunshi ahankali Baffa yakai kan bakinshi ya sumbace shi ahankali yace “Allah maka albarka Zayn” murya chan kasa yace “Ameen” tashi katafi, tashi ahankali Zayn yayi yawuce Baffa na kallonshi jiyayi duk wani nauyi da zuciyanshi yamai ya saukar tunda har Zayn din dakanshi yazo yay accepting mistakes nashi and promise to work on kanshi Abba jiyayi hankalinshi ya kwanta yanzu Ammi kadai tarage yasan ko itama she will come around.
All through ranan akan gado tayishi takasa fita school, takasa daukan wayan Aliyu takasa cin abinci gatanan ne kawai, wuraren magrib Anty Mariya tashigo dakin tana kallon Khairy dake kan gado maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna agefen gadon tana kallon idanun Ummulkhairy dasuka kumbura har lokacin hannunta takai tadagota tazauna sanan ahankali tace “maisa baki fadima Baban ki Aliyu kikeso ba” shiru Khairy tayi tana kallonta dan batasan ya akayi tasan aliyu takeso ba, ahankali Anty Mariya tace “nasan kinason Aliyu shima yana sonki tun a asibiti na karanci all of that, maisa baki fadiwa mahaifinki ba eh Ummulkhairy?” Ahankali tace “Anty kona fadamai is too late bazasu iya komi akaiba” shiru Anty Mariya tayi tana kallon Khairy she just wish tanada wani karfi dazata iya magance this whole case but her hands are tight, ahankali tace “Yaya zakiyi da Aliyu”? Wani irin ajiyan zuciya tasauke dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sanan taja hancinta danji tayi majina zai gangaromata tace “zan gayamai gaskiya” ajiyan zuciya Anty Mariya tayi tace “to ki gaggauta fadamishi dan kinsan bai kamata kina magana da namijin daba naki ba ko” gyadama Anty Mariya kai tayi, ahankali Anty Mariya tashafa kumatunta tace “karki damu duk wanda yabi iyayenshi bayaci baya kinji” gyadama Anty Mariya kai tayi, Anty Mariya ta tashi tace “yanzu zan Aiko Batool da abinci yakawo miki kici” sanan tawuce tafice daga dakin, abinci Batool takawo mata kadan taci sanan tai sallan isha’i ta kwanta yau by 9 ma Aliyu yashiga kiranta, kallon wayan Batool tayi sanan ta tashi ahankali tafita daga dakin danta basu waje suyi magana, kasa daukan wayan Khairy tayi a third call dinne tadauka takai kunne.
Cikeda damuwa Aliyu yace “I am sick worried, Pickle what’s happening? Tun jiya I’ve been calling you baki dauka sokike ciwon zuciya yakamani” girgizamai kai tayi da sauri muryanta na rawa tace