Showing 66001 words to 69000 words out of 108352 words
Chapter 23 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt
“n…..o” shiru Aliyu yayi hakan yasa dasauri ta taushe bakinta tana kokarin hana kanta kukan datakeji, yakai kusan 1min yay shiru kawai, kaman daga sama yace “waya saki kuka”? At this point zare hannun kawai tayi daga bakinta tafashe dawani irin kuka Aliyu knows her so well, if she’s happy yasani, if she’s sad yasani, if she cried yanajin muryanta yasani, shiru yayi yana sauraron kukan ta kaman yashiga wayan yazo inda take yakeji, almost good 2min yabarta tai kuka yanda takeso sanan ahankali cikeda iya lallashi yace “I always tell you I am here for you, why will you be crying haaa? Oya yishiru kinji” gyadamai kai tayi tana kokarin Hana kanta kukan, murya chan kasa ahankali yace “maiya sameki why are you crying”? Jitayi wani kukan yazomata tasake saki, cikeda damuwa sosai Aliyu yace “Pickle wai kasheni kikeso kiyi? U want my life eh? Kinsan yanda kukan ki ketabamin zuciya kuwa? Did you have any idea wlh idan kikaji ance I slump and die kece” rage sautin kukan tayi ahankali dan tasan ko karya daya baiyiba, cikeda lallashi yace “tell me menene, nazo gidanku naganki” dasauri ta girgizamai kai dan tasan wlh zai iya tace “a’a” ahankali yace “to what’s the matter”? Batasan yaya ma akayiba jitayi tace “cikina ke ciwo” tasake taushe bakinta jin takasa fadamai gaskiya for the first time yau tama Aliyu karya, shiru yadanyi sanan ahankali yace “sorry, is it MP? All this menstrual cramps shi?” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” murya chan kasa yace “sorry, sannu, stop crying, kinsha magani kona siyo nakawo miki” ahankali tace “nasha” murya chan kasa yace “then it will stop soon, hey you this MP cramps I command you to leave my Pickle alone or I arrest you, nayi arresting nashi”? gyadamai kai tayi tana dan murmushi tace “eh” murmushi yayi jin tadanmai murmushi yace “okay MP u are under arrest for disturbing the peace and harmony na Miss Khairy, for taking away her smile and bringing her kukan banza back” dan dariya tayi, hakan yasa yace “yes koba kukan banza bane kikemin ba, idan kika ganni saiki kara wani narkewa kina kuka just to worry my heart Khairy angayamiki ban sani bane” at this point wlh tama manta itane mai kuka dariya tafara sosai, ganin haka yasa yace “haka ranan nazo asibiti u were very fine fa hira ma kike, kina ganina kika kokkobe fuska ashagwabe zaki faramin kuka sabida kawai ki rudani this girl keko don’t worry eventually zan saki kukan mai dalili” dariya tayi dan ita bamata gane last maganan ba, ahankali yace “kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tace “but small baran iyaci dayawa ba” murya chan kasa yace “tom anjima idan yalafa sai ki karaci ko” tom, murya chan kasa yace “if it persist tell Batool tasa towel a warm water tamiki massaging abdomen it will stop” gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” ahankali yace “gobe zaki school” girgizamai kai tayi tace “no sainaji sauki” Gyadamata kai yayi yace “okay, bari na barki kihuta idan pain din yadawo call me but don’t cry for me again” murmushi tayi tace “saina maka bye” dan dariya yayi ahankali yace “I love you Ummukhairi” katse wayan yayi dip, ahankali tajanye wayan daga kunnenta takasa koda kwakkwaraZn motsi.🥰
5️⃣0️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Ranan ma bacci barawo yasace ta da kyar ta tashi dasafe tai salla, tana zaune da safe ita kadai akasa taji an bude kofanta hakan yasa takalli kofan Baba ne, shigowa dakin yayi hakan yasa ahankali tace “Baba ina kwana” zama yayi akasa kusada ita shima ahankali yana kallonta yace “yauma bazaki school ba” gyadamai kai tayi ahankali tace “bama komi sai ranan exam zanje” shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta saukarda kanta kasa, ahankali yakai hannunshi yatallabo fuskanta yana kallon kwayan idanunta yace “have you been crying Ummulkhairy”? Dan murmushi takakalo sanan ta girgiza mai kai, baki Baba yabude zaiyi magana dasauri ta girgiza mai kai tana hadiye miyau sanan tasa hannunta ta goge hawayen daya zubomata da sauri sanan takalli Baba murya chan kasa tace “Baba nariga na karanta Littafin Mama na karanta komi naciki” shiru tadanyi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali, murya chan kasa tace “Baba babu abinda bazan iyama mahaifiyata aduniyan nan ba she’s my number one dan haka karkaji komi” tasakeyin shiru tana saukar da ijiyan zuciya ahankali tace “I accept Ya Zayn amatsayin mijina wanda kuka auramin Baba” tai maganan tana danne hawayen ta, wani irin farin ciki dataga ya lullube fuskan Baba yasa tasakinmai murmushi ahankali, rungume ta yayi yana mata addu’a sanan yacirota yace “kome kikeso nasaya miki Ummulkhair kifadamin ko yaushe I will buy it for you, I know Maman ki is very very happy dake, Allah miki albarka, bari naje nafadima Anty ki dan ta shirya tafiya Dubai yomiki shopping zaki bita kutafi tare” girgixamai kai tayi tace “zanyi karatu for final exam Baba” “ohhh hakane nama manta tsabagen farin ciki bari naje” Baba yay maganan yana fita daga dakin cikeda farinciki datama dade bata ganshi da irinshi ba tun Mama nada rai, hannu tasa tashare fuskanta ahankali tace “Ya Aliyu I am sorry” ko kadan batasan tayaya zata fadima Ya Aliyu ba ita batamajin zata iya fadamai ba bama tasan tayaya zatai avoiding nashi ba tana zaune tana tunanin Batool tashigo dakin ganin idanunta sunyi jajir yasa Batool tamaida kofan tarufe tazo inda take zaune akasa tazauna tace “Khairy zakije kisawa kanki wani ciwo ne wai, kin fadama Ya Aliyu”? Girgizamata kai tayi cikin muryan kuka tace “Batool I don’t know Tayaya zan fadamai, I can’t hurt Ya Aliyu, I can’t hurt him, I don’t even want to imagine what he will go through Idan yaji wanan zancen, banson wani abu yasameshi” ta karashe maganan tana goge kwalla duk Batool na kallonta tace “to tayaya zakiyi avoiding nashi yanzu I am sure sabida shine kika kasa zuwa school, Khairy you need to think of something” hawaye tadan share sanan takalli Batool tace “na chanza SIM card”? Dasauri Batool tace “ko kin chanza SIM card ai yasan gidan nan, saidai” tai shiru dasauri Khairy ta kalleta tace “saidai me”? Ahankali Batool tace “call him up kifadamai zakuyi tafiya kauyen su Mama garin kuma babu service gobe zaku tafi ba lallai idan yakira yasameki ba saiki kashe wayanki kawai, karki kara zuwa school din saikun fara exam baduk idan kina exam baya zuwa school wajen kiba” gyadamata kai Khairy tayi tace “to kingani dazaran an gama exam din karki kara fita kawai nasan idan aka kaiki gidan Zayn zai chanza miki layin waya shikenan, idan bai ganki ba daga baya yaji kinyi aure zai hakura” shiru Khairy tayi tana kallon Batool Wanan shine simplest thing datasan zata iya dan she can never ever hurt Ya Aliyu, hannu Batool tasa akan fuskanta ta sharemata hawayen tace “kirashi yanzu” ahankali tadauki wayanta tai dialing number Aliyu, saida wayan ya katse sanan yakirata back, ahankali yace “good morning Miss Khairy yaya jikin I was about calling you Boss dina yarikeni a office annoying man kawai, cikin yadena ciwo”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” sanan tai shiru dukan cinyanta Batool tayi hakan yasa dasauri tace “Ya Aliyu zamuyi tafiya yau” dan shiru yadanyi kafin ahankali yace “ina zakuje”? “Kauyen su Mama zamu” ahankali yace “ina ne kauyen”? Dan shiru tayi tana kallon Batool data Balla mata harara dan tana jin maganan Aliyun daga inda take, ahankali tace “uhmmm namanta sunan kauyen, nataba zuwa sau daya da ita secondary school” ahankali yace “ok yaushe zaku dawo”? Murya chan kasa tace “sai Baba yafada I don’t know” hararanta Batool tayi hakan yasa tace “Ya Aliyu kauyen babu network” danjim yayi kafin ahankali yace “Tayaya zan dingajin muryan ki to” hawaye taji yazo mata ahankali tace “nima bansani ba” jin yanda muryanta yayi zatamai kuka yasa yace “to shine zakiyi kuka? Ki tambayi Baba sunan kauyen saiki fadamin kafin kutafi duk randa naji nagaji da rashin jin muryanki I will just enter road and come cus I can’t survive this life banganki ba kuma banji muryanki ba, so don’t cry okay” ita kanta jikin Batool wani sanyi taji yayi ko itane she can’t hurt a guy kaman Aliyu haka with pure heart gashinan so cool and calm. Ahankali Khairy tace “okay” murmushi yadan mata yace “mai kukan banza, lemme get back to office kafin boss dina yay firing nawa in the middle of minute nadauki excuse nafito, bye I love you Miss Khairy” ya katse wayan da alamu sauri yake ajiye wayan zatayi taga kiranshi yashigo ahankali tadauka gudu taji yanayi yace “I forgot to tell you Allah kiyaye hanya, kidauki mosquito cream, insecticide and mosquitoe net kauye akwai sauro I don’t want them biting you, and go with indomie da some cereal incase bazaki iyacin abincin kauye ba, and again go with some bottle water karkisha ruwan rafi kinji, take care of yourself for me kinji Ummulkhair” gyadamaikai tayi ahankali tace “naji Ya Aliyu thank you” dan murmushi taji yayi sai chan taji ya tsaya dagudun yace “shitt! Pickle my heart kinda feel sad, I guess I am missing you already, zanyi missing Khairy na very very so so sooo much” murmushi tayi tace “me too” sanan tace “Ya Aliyu ka koma meeting bye bye” takatse wayan dasauri sanan tafada jikin Batool tace “Batool na shiga uku ina cikin tsaka mai wuya yaya zanyi da ALKAWARIN ZUCIYA NA?” Bubbuga bayanta Batool tayi tace “kaddaranki kenan kiyakuri Khairy” da kyar ta lallashi Khairy, sanan tadauki wayan Khairy tacire SIM card dinta tawuce bayi amasai ta Kefa SIM card din tai flushing dan that’s the only thing dazata iyama Khairy dan yasan yanda so yake lokacin dazata kunna wayan nan takira Aliyu bazata sani ba and she needs to let him go dan tanada mijinta, dawowa dakin tayi kawai ta rungume Khairy suna kuka sosai.
Wasa wasa 2weeks kenan bataji muryan Aliyu ba, gidansu sai gyare gyare ake na bikin da za’ayi nata dana yayyinta, Anty Mariya was just like a mother to Khairy dan mai gyara ta dauko daga Sudan aka bata daki daya tana gyara Khairy in and out, Khairy tarame tun tana kuka da hawaye yanzu tasoma mara hawaye kawai gatanan ne, yau zasu fara exam duka duka 1 week zasuyi sugama, shiryawa tayi cikin hijabi har kasa da nikabi duk wani abu datasan Aliyu zai iya ganinta yaganeta dashi ta chanza sanan tafito tama Anty Mariya sallama, amotan da Baba yasiyawa Anty Mariya da direbanta tadauka suka tafi bayan ta sanar da mai gadi idan wani namiji yazo nemanta ace batanan, har gaban department dinsu tasa direban Anty Mariya yayi parking sanan tawuce tashiga exam hall wanda yake zasuyi 2hrs aciki tana gama paper ta bama tajira kawayenta ba tafito tana tafiya ahankali kamshin Aliyu taji kaman daga sama amman tadaure taki dago kanta saima sauri data kara zuwa motan, baya taje zama amman saitaje gaba tabude ta zauna suka wuce saida suka sanyi nisa sanan tajuyo Aliyu ta hango tsaye yana sanye da kananun kaya yana kallon exam hall din tasan ya tsaya ne yana jira afara fitowa kozai ganta jitayi kuka yazo mata nikabin takama afuskanta tana kuka sosai.
Wasa wasa yau Friday yau tagama last paper ta yauma still saida taga Aliyu a school dinsu yarame sosai yay duhu yau kukan datayi yafi na kullum dan tasan yaune last day dazata ganshi dagayau bazata kara fita ba ahaka suka tafi.
Parking sukayi a compund dinsu da ake fentin tsakar gidan, ahankali ta sauko nikabin kanta tacire sanan tawuce flat dinsu, ahankali tabude kofa tashiga Zayn tagani zaune afalon su taci gayu yay wani irin bala’in kyau tana magana da Anty Mariya ganinta yasa yadago kai ya kalleta dawani irin sauri ta sauke kanta kasa ahankali tace “ina yini” sanan tawuce dasauri tai stairs. “Ummulkhairy” yakira sunanta ahankali chak ta tsaya batare data juyoba, tashi Anty Mariya tayi tace “bari kaga naje na dudduba aikin da akeyi Zayn” tai maganan tawuce ta gefen Khairy tai sama abinta, ahankali Zayn yace “Khairy” juyowa tayi ahankali kanta nakasa sanan ahankali ta taho yana binta dawani irin kallo ganin yanda takara kyau fatarta harwani sheki take, zama tayi akan kujera kanta akasa, dan murmushi Zayn yayi sanan yadauki wani Leda da flowers red keciki dake gefenshi sanan yataso yazo har gabanta tsugunnawa yayi agabanta sanan ahankali yadaura hannunshi kan nata wani irin rawa jikinta yafara dasauri takalleshi wani cute smile yasakin mata sanan ahankali yakama hannun nata yana kallon fuskanta yasamata flowers don aciki yace “congratulations u are now a graduate wife” wani sarawa taji kanta yayi dawani irin sauri ta lumshe idanunta sanan tabudesu ahankali takalli flowers din Aliyu kawai taji yafado aranta, sharrrr hawaye yazubo daga idanunta dasauri Zayn yace “why are you crying” hannunshi yakai kan fuskanta zai sharemata dasauri ta kauda fuskanta tace “kaina keciwo I want to sleep thank you” sanan tabi ta gefenshi ta tashi dasauri zata wuce karaf taji yakamo hannunta, dawani irin sauri tajuyo takalleshi tashi yayi ahankali yana kallonta sanan yazo ta gabanta Ya tsaya yay folding hannunshi akirji ahankali yace “I love you Ummulkhair! And I wanna spend the rest of my life with you! I accept you as my wife cus ina bala’in sonki! Allah yajikan Mama data bani ke, and I will forever be greatful to her data zabeni a matsayin soulmate na yarta, Ummulkhairy Zayn love you alot” wani irin fizge hannunta tayi dawani irin gudu tai stairs zuwa dakinta maida kofa tayi tarufe tasa kwado sanan tawani cillar da flowers nashi gefe jikinta na kyarma sabida kalamanshi Aliyu kawai suka dinga tunamata fadawa gado tayi tana kuka ahaka bacci yay awon gaba da ita.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
5️⃣1️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️
Yau tun safe yama kasa tashi yakai kanshi bayi yay alwala yay salla sabida mugun zazzabin dayake, Abba dabaiganshi a masallaci ba daman jiya Gwaggo tacemai baida lpy amman da Aliyun yazo wajen ya tambayeshi yacemai lafiyanshi kalau yasa yana shigowa gidan daga masallaci straight side din Aliyun yayi ahankali yabude kofan dakinshi yashiga dakin tsaf babu kowa a falo bwdroom nashi yayi yana budewa kakarin aman Aliyu yaji abayi, Aliyu tun yana yaro ciwon shi always comes da amai dawani irin sauri yashiga bayin ganinshi a duke yasa Dad yace “Subhanallahi Aliyu” ruwa yatare Awani bowl yakawo mai da kyar ta kuskure bakinshi sanan Dad ya wankemai fuska sanan yadaukeshi yafito dashi yanajin yanda jikinshi yay zafi, bargo yasa ya lullube shi sanan yajuya zai fita dawani irin sauri Aliyu yakama hannun Dad ahankali yace “Dady” dasauri Dad yazo gaban gadon zama yayi yace “Aliyu menene” ahankali yace “Dad last 3weeks dasuka wuce Ummulkhair called me cewa zasu village, and a village nasu basuda network, Dad I’ve been going to school masu all through last week sabida zasuyi final exam amman batazo ba, Dad I am so worried did something happen to Khairy?” Shiru Dad yayi yana kallon Aliyu duk cikin yaranshi babu wanda yadauko zuciya da hali irin nashi kaman Aliyu, Aliyu bai iyason abu ba, bai kuma iya kin abuba, Aliyu loves da zuciya daya, and he loves completely without rage space, Aliyu is very cool, baida hayaniya da rigima amman akwai zuciya na masifa. Ahankali Dad yace “sabida bakaga Khairy bane yasa kake neman kashe kanka Aliyu? When was the last time kaci abinci” murya araunane yace “I can’t remember Dad” shiru Baban shi yayi yana kallonshi sanan anatse yace “yanzun nan zan taho maka da magani da abinci write down address na gidan su Ummulkhairy for me zanje gidansu, I will go and check her up for you daganan zan nema maka aurenta wajen mahaifinta kafin kaje ka kashe kanka sabida soyayya” Dad yay maganan cikeda tausayinshi dakuma jin haushin shi duka atare sanan ya tashi yafice, yana fita daga dakin sukaci karo da Gwaggo datasa Meena ta turata akeke ganin danta yasa tace “haba nakasa bacci lafiya tun tsakar dare Nike damun ja’irar nan takawoni naduba takadirin yaron nan dan jikina yabani baida lafiya amman taki wai nabarta tai bacci yanzu ma saida nahada mata da kuka tafito dani, wlh Abdul bakai dacen yara ba ko kadan, shikuma ina yake yana cikin ne”? Ganin yanda Maman shi tadamu dan shi kanshi baisan iyakacin irin son da tsohuwar nan kema Aliyu ba yace “muje Gwaggo baida lpy amman yanzu zan bashi magani yayi bacci” kirji Gwaggo tafara tace “hala yanata amai dan cutan Aliyu kenan duk ciwo yay ta uban amai na shiga uku, meke damu shi eh gayamin” shiru Dad yayi ganin yanda tadamu ihu tamai tace “nace kagayamin Abdul” kallon Meena yayi yace “wuce kitafi” wucewa ahankali tayi ta tafi tsugunnawa Dad yayi yace “Gwaggo sabida yarinyar nan dayakeso yake rashin lafiya wai tunda tai tafiya zuwa kauye bai kara samunta awaya ba ko ganinta” fashewa da kuka Gwaggo tayi tace “to laifin wa inba nakaba, tuntuni nike damunka muje mu newama yaron nan Ummulkhairy amman kaki wai abari tagama makaranta yanzu idan wani aka bamawa fa iyye, kaini daki na shirya yau kafata kafanka gidan su Khairiya zamu billahillazi kuwa” kaita dakinta yayi sanan yawuce yahado magani yabawa Aliyu da shayi dakanshi sanan yamai allura kafin mene bacci yakamashi fitowa yayi yakoma nashi dakin shiryawa yayi cikin manyan kaya yana fitowa tsakar gida yaga Gwaggo itama ta shirya cikin lafiyayen atampan ta jajir dashi da aka mata dinkin bubu kan kekenta tai kyau sosai fesfes da ita duk