Showing 9001 words to 12000 words out of 108352 words

Chapter 4 - Alkawarin Zuciya by M Shakur Complet .txt

24 Dec 2024

5624

tarufe duka fuskanta da hannun yace “call your family to come and pick you up then” yay maganan yana mikamata wayanda daya cirosu daga jaka dazu, ahankali ta hadiye kukan sanan tasa hannunta ta share fuskan nata tass kafin ahankali tajuyo tasa hannunta takarbi wayan dayake bata, taba wayan tayi ganinshi amace yasa ahankali kaman mai tsoron magana tace “banida chaji tamutu wayan” shiru yayi yana kallonta, yanabin hannunta datake fidgeting da kallo, yadade ahaka sanan gently yakai hannunshi ya murza key ya kunna motan batare daya kalleta ba yace “where is your house”? Kallon hanya tayi dudda gabanta nafaduwa amman hakanan taji takasa kin fadamai, ahankali tace “Wuse” dan juyowa yayi yazubamata idanunshi dasauri tasauke kanta kasa tana kara kankame inhaler dake hannunta, murya chan kasan makoshi yace “where at wuse” ahankali tace “Ademola adetokunbo way, gidanmu nakan hanya” jan motan yayi da bala’in gudu dayasa taji wani kalan mugun tsoro yashigeta yana sharara uban gudu akan titi kaman babanshi ne mai hanyan, har sukakai wuse din, zuwa layin sanan tanunamai wani dankareren gate din wani gida, karasawa yayi yay horn, lekowa mai gadi yayi ganin wata rubabbiyar mota da duk gabanta tai dameji yasa yafito daga gate din yazo wajen motan ta side din direba daidai police man din na saukar da glass din motan kasa kafin ma yay magana hango Khairy yasa dawani irin sauri cikin farin ciki yace “Khairy!” Dawani irin gudu yakoma cikin gida daganan gate sukaji muryanshi yana ihu yace “Alhaji tadawo ga Ummulkhairy nan” yay maganan yana bude gate din da duka karfinshi tsabagen murna, wani irin mahaukacin lafiyayyen gida ne mai bala’in kyau, ga mutane wanda kallo daya yamusu yasan iyayenta ne duk a tsaitsaye, barinma matan wanda ya kyautata zaton itace mahaifiyar yarinyar ce idanunta sunyi ja, saiga yayyinta daduk yagani rikeda waya a hannunsu da alamu ita suke kira, yanayin yanda yaga damuwa tattare dasu kuma duk motan suke kallo yasa baimayi wajen parking space din dayaga an tanada a compound din gidan ba yayi gabansu inda duk suke tsaye sanan ya kashe motan, duk suna tsaye suna kallonsu kafin ya Manaf shiya fara motsi dasaurinshi yakaraso bangaren mazaunin direban yabude kofan yana kallonta, ahankali yabude motar yafito yana kallon su Baba, cikeda girmamawa yakaraso gaban Baba dake kallonshi kuri batare dayay motsi ba dagashi har Mama cikeda natsuwa yace “Barkanku da dare Alhaji, nadawo da yarku gida ne, she had an accident akan titin Apo itada keke napep, ina cikin mota ganin hold up I had to step out naga what’s happening nan naga hatsari akayi motanta yadaki na keke napep ga masu keken su uku about to beat her because she couldn’t apologize, I step in nahana su, I was about arresting them naji faduwanta akasa breathing somehow, I had to let go off the keke guy and reach out to her, at first nadauka ciwo taji kafi daga baya nagano she’s asmatic bayan naga inhaler ajakanta, bata dade da regaining senses nata ba, ganin she can’t drive, I try to make her call family ta but wayanta akashe I had to ensure her safety dan yarinya ce kuma is not safe for her tadawo gida dakanta, saisa nadawo da ita, here is the car key” tunda yake maganan daga Baba har Mama da yayyinta da ita kanta Khairy da Manaf yafito da ita daga mota kanta nakan kirjinshi tai lamo kallon police man dinan dako rufamata asiri baiyi ba take, like babu an atom of lie a maganan shi.
Kafin Baba yay magana cikin tsananin bacin rai da damuwa Mama tace “Alhaji kaga abinda Khairy keyi ko, wai Khairy kadai na haifa aduniyan nanne da ita kadai kebani ciwon kai, ga maza yayyinta har uku da sune yama kamata suyi rashin ji amman basuyi sai ya mace ce keyi, yanzu inda wanan bawan Allah this kind hearted officer ya ceceta ba da Allah kadai yasan mezai faru, Allah kadai ne zai sakamai da alkhairi, inda ace bai taimaka mata ba kunsan kalan dukan da masu keken nan zasuma Umma eh, wlh……” dasauri Manaf yace “Mama please we are not alone here” cikin fushi sosai Mama tace “abinda kukeyi kenan dagaku har mahaifinku saisa Khairy duk ta baci haka, zaki gamu dani Khairy” tama Khairy wani mugun kallo taredayin kwafa sanan tawuce ciki fuuuu cikeda bacin rai.


Dan murmushi Baba yayi sanan yasa hannu yakarbi car key dayake bashi anatse yakai hannunshi yakama na officer cikeda murmushi yace “thank you, nagode nagode, I can’t even thank you enough, Allah yamaka albarka for saving Ummulkhair, nagode officer, Allah yamaka Albarka” gyadamai kai ahankali yayi yace “saida safen ku bari natafi” dasauri Baba yace “bari Mu’az yakaika wajen motanka please is late” dasauri yace “a’a Alhaji, dare yayi, yazauna agida I can manage, saida safen ku” yay maganan yana juyawa zai wuce dasauri Baba yace “youngman, I mean officer” jin Baba yakirashi yasa ya tsaya tareda juyowa yakalli Baba, ahankali Baba yace “baka fadimin sunanka ba” dan jim yayi yana kallon Baba kaman bazaiyi magana ba sai chan yace “sunana ASP Aliyu Hydar Zango” gyadamai kai Baba yayi yace “Allah maka albarka Aliyu Hydar” murmushi kadan yayi tareda juyawa yana tafiya one one kaman Gwarzo yawuce yafita daga gidan.


[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫




✍🏻M SHAKUR




8️⃣




Ajiyan zuciya Baba yasauke sanan yajuyo da kanshi yazubama Khairy idanunshi da kallo daya tamai kawai tafashe da mugun kuka, duk duniya babu wanda take tsoro kaman mahaifinta, Baba is the best father amman not just her kowa tsoron fushi Baba yake agidan nan sai Mama dan idan Baba ya burkice ko ita bata iya taroshi, tsugunnawa tayi awajen tana kuka sosai tace “Baba dan Allah kayakuri wlh wlh bazan karaba please I am so sorr…..” baima jira sauran maganan ta ba yawuce ciki shima fuuuu, cikeda tashin hankali takalli yayanta tace “Ya Manaf na shiga uku daga Baba har Mama fushi suke dani” cikin fushi Mu’az yace “da murna kikeso suyi dake sabida bakida hankali do you know how worried they were, saida akasa direba yakoma gidan bikin nan amman baaa ganki ba wai kintafi, Khairy tunda kike arayuwan ki kintaba tuka mota ne dazaki fara yau inda kinje kin kashe kanki ko kinjima kanki ciwo da yaya kikeso muji eh, kawai gakinan ne girma kawai kike amman bakida hankali ko kwara daya stupid girl” yawuce yajuya yay flat dinsu, hararanta Maheer yayi dudda tabashi tausayi yace “babu abinda ta iya sai rashin kunya da tara kawaye, inda police man dinan bai ceceki ba dakin gane shayi ma ruwane, fitsararra kawai” shima yajuya yatafi, ahankali Ya Manaf yasa hannu yadagota yace “stop crying muje kije change this clothes shower kici abinci and sleep” yay maganan yana sakinta yakoma mota ya tattara kayan jakanta yahada mata ya rike sanan yazo yakama hannunta suka shigo falon, Baba kadaine zaune a falon yana rikeda jarida hakan yasa sukai hanyar stairs, cikin kakkausan murya Baba yace “kawomin wayan ki nan” wani irin fashewa da kuka tasakeyi sosai jikinta har rawa yake ta karbi jakanta daga hannun ya Manaf ba musu hannu tasa taciro wayan sanan ahankali tana sheshekan kuka takaraso wajen Baba tabashi wayan, karba yayi ya ijiye gefenshi, sanan yajuyo yakalleta yace “Ummulkhair” muryanta har shakewa tayi tace “Naam Baba” cikin kakkausan murya yace “I ban you from going outside this house for a whole week” zubewa tayi agabanshi tana girgizamai kai tace “Baba please I am sorry dan Allah” cikeda fada yace “nabata ki dayawa, nabaki freedom dayawa kullum your Mum is complaining yau nagani da idanu na, dan haka bazaki saka kafa kifita daga gidan nan ba dagayau har zuwa kwana bakwai, ba school ba islamiyya, sanan ko friend naki guda daya nazo nagani kokuma aka gayamin tazo saina kulleta, i will even tell the gateman koda wasa yabar kawayenki suka shigo cikin gidan nan abakin aikinshi dan haka duk wacce tazo yacemata ma bakinan kowani abun I don’t care” sosai take kuka tana girgizamai kai Baba baitaba mata Wanan kalan punishment dinba tsawa yadaka mata. “tashi daga gabana!” da sauri ta tashi tawuce sama da gudu tana kuka Ya Manaf yabita da kallo yay jim sanan ahankali yadawo falon zama yayi kusada Baba ahankali yace “Baba please kayakuri, punishment dinan yay tsauri dayawa, Khairy batada hankali har yanzu Baba, mudena kallonta kaman wata Babba sabida tana final year a school, Baba she is just 20, yanzu shine lokacin her growth, lokacin datake feeling she’s capable itama takai matsayin ahankali zamu nuna mata this and that, but Baba hanata fita, hanata zuwa school, karbe wayanta, dakuma Hana kawayenta zuwa wajenta I feel is too much Baba, she will be depress” wani mugun kallo Baba yamai yace “Manaf koyamin tarbiyan yara kake?” Cikeda girmamawa yace “a’a Baba” cikin kakkausan murya Baba yace “to tashi daga nan wajen” ahankali yatashi zaiyi sama Baba yace “barin flat din nace kayi katafi naku” ganin ran Baba abace yake sosai yasa baiyi gardama ba ya sauko yazo yajuya yafita daga falon.


Waya Baba yadauka yakira wata number, ko 10min baa daukaba wani doctor magidanci haka yazo, tashi Baba yayi sukai sama, afalon sama Baba yanunama Dr kujera ya zauna sanan yawuce dakin Khairy saida yafara knocking sanan yashiga tana zaune kan gado ta chanza doguwan rigan jikinta tasa wata na Atampa simple tasa hula akanta idanunta sunyi jajir sundan kumbura, tana ganin Baba dasauri ta kwanta, ba Yabo ba fallasa yace “fito adubaki” yay maganan ya tsaya yana kallonta tashi tayi ahankali sanan tasaka slippers juyawa Baba yayi tabishi abaya suka taho falon gaida Dr tayi sanan tazauna, dubata yayi yamata yan tattanbaya tana bashi amsa sanan yabata wasu magani guda biyu kafin yakalli Baba yace “shikenan Alhaji” kallonta Baba yayi yace “wuce kitchen kije kici abinci kisha magani” gyadamai kai tayi sanan yajuya shida Dr suka fice, saida sukakai waje wajen motanshi sanan Baba yace “are you sure Dr she’s okay?” Dan murmushi yayi yace “eh, ai Asmanta yaragu sosai bakaman da ba datake having constant attack, I am telling u abinda ma yatada nayau was mugun tsoratan datayi saisa numfashinta yafara mata wuyan kamawa, wlh she’s very lucky tasami wanda yataimaka mata she would’ve lost….” Dasauri Baba yace “Alhamdulillah she’s fine” gyadamai kai Dr yayi yace “yes, bari idan anything change call me, but for now let her relax and rest system dinta yahuta, magungunan dana bata zaisata bacci sosai” gyadamai kai Baba yayi suka gaisa yashiga motanshi yaja yawuce.
[6/16, 7:55 PM] +234 701 275 3212: 💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫




✍🏻M SHAKUR






9️⃣






Wuraren 5 Baba ya shigo da kanshi yatadata don sallan asuba, da kyar ta tashi saida yaga tashiga bayi sanan yajuya yafice, tana idar da salla da kyar ta iya lallabawa takoma gado sai wani baccin.


Wuraren 11:30 ta tashi daga bacci, ita kanta wani dadin jikinta taji taji, ahankali ta tashi zaune tasauke kafanta kasa tana kallon dakin, dakinta very clean and very fine kana ganin dakin kaga dakin wacce akeji da ita, tashi tayi ahankali dagakan gado tai wajen window dakinta bude window tayi haske yawani daki fuskanta lumshe idanu tayi kafin ahankali tabudesu starring into compound dinsu that is very fine idanunta suka sauka kan motar ta da ake pake agidan, faduwa gabanta yayi ganin yanda gaban motan yay completely baci, maida labulen tayi tarufe window feeling sad sai yanzu ta tuna abinda yafaru sanan tawuce tashiga bayi, wanka tayi tafito daure dawani pink towel, karasawa tayi gaban madubi takalli kanta kodan tayi bacci sosai ne gani tayi tana wani kalan sheki, fatarta nawani kalan glowing and sparkling, yatsine fuska tayi sanan tawuce tadauko kaya a wardrobe tasaka wani pink half gown na cotton, batama tsaya daura dan kwali ba tasaka slippers kawai tafito gabanta na dukan uku uku tsayawa tayi wajen bene taleka falo ganin Mama bata falo yasa ahankali tajuyo tai gaban dakinta, tsayawa tayi sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tasa hannunta tai knocking ahankali, jin baaa amsaba kuma ta tabbatar Mama naciki yasa ahankali tabude kofan dakin tadan leka tana shiga ciki, hada idanu tayi da Mama dake zaune kan couch na dakin tana karanta wani Littafin zikiri dake hannunta, babu ko alamun wasa akan fuskanta tace “fitan min daga daki Ummulkhair” dan rau rau tayida idanunta kaman zatai kuka murya chan kasa kaman na Yar baby amugun shagwabe tace “Mamaaa sorrry please, kinj….” “Get out of this room Khairy” gyadama Mama kai tayi ahankali sanan tajuya tana tafiya kaman wacce ke koyon tafiya tana tunanin abinda zatayi Mama tahakura kaman daga sama Mama kawai taji Khairy taja wani uban nishi tana bubbuga kirjinta tayi baya zata fadi, wani kalan salati Mama tasaki tawani ijiye Littafin kan kujera ta taso dasauri ta tareta da hannayenta tace “Subhanallahi Khairy, Khairy, ina inhaler ki”? wani kalan dadi taji ya lullube ta ganin yanda Mama harta tsorata ta taso, kawai Mama gani tayi yarinya ta kankameta tafashe dawani sangartaccen kuka ajikin Mama tace “Mama please kiyakuri wlh wlh bazan kara abinda nayi jiyaba I promise Mummy, kikai fushi dani ina zansa kaina eh kinaso in mutu ne da ciwo? U are my best friend Mama, u are my happiness kika shareni I will be shattered, Mama dan Allah kinji smile for me haba my world best, best of the best, bestest, the best Mama in the world, Mama dan Allah kiyafemin” tai maganan tana kara kankame Mama kaman wata yar yarinyar da baa dade da yayewa ba, dudda yanda ran Mama yake abace amman saida jikinta yay sanyi sosai, ahankali tadaga hannayenta taciro Khairy daga jikinta ta tsare fuskanta da idanu hardan rama tayi ga hawaye sun cika idanunta, Mama takai hannunta ta share mata idanu sanan takama hannunta tajata zuwa bakin gadonta zaunar da ita tayi sanan tazauna agefenta tana kallonta ahankali tace “Ummulkhair bakiji, ba fushi nake dake ba I am only trying na nuna miki kuskurenki, ke y’a mace ce bazaki dawwama agidan mahaifinki ba dole zakiyi aure kije gidan mijinki, i want to teach you not just life but how to live life Khairy, inaso nakoya miki rayuwa dakuma yanda ake zaman duniya lafiya, ke mace ce Baban ki da yayyinki cannot teach you abinda ni mahaifiyar ki mace zata iya koyamiki, akwai mutuwa, akwai ciwo, akwai kuma tsufa any of the two can happen to me Khairy yaya zaki kare eh? Kin taba tunanin, wanan kawayen yau baki bikin wanan gobe baki bikin wanchan kene aganki achan gidan bikin kina tika rawa ko achan birthday kina tika rawa ko Micheal Jackson yaganki kina rawa saiya baki fili yarinya saikace rainon dujal, what are all this behaviors Khairy? Sabida ana cewa ke yarinya ce kinsan yara nawa wanda ma kin girmesu sukai aure suka hayyayafa eh? Yanzu abin haryakai kija mota dakanki ki shiga titi da daddare Ummulkhairy idan da wani abu yasameki how do you want me to cope? Kasheni kikeso kiyi da damuwa?” Dasauri ta girgizama Mama kai ahankali tace “Mama bazan karaba wlh” Ijiyan zuciya Mama tasauke ahankali sanan tai murmushi tana kallon yanda idanunta sukai zuru zuru long kalaban kanta duksun barbaje sun sauko fuskanta, hannun Mama takai ta gyara mata gashin sanan ta shafa fuskanta tace “ke kadai ne y’a mace da Allah yabani aduniyan nan Ummulkhair, inaso ki natsu, wisen up, anything can happen to me, and I want you to be able to take care of yourself, su Manaf, Mu’az da Maheer, you will be their Mum, kindaiga banda kowa, I told dukanku labarin nan agidan marayu Baban ku yaganni ya auroni ina gidanshi nai karatu, bansan any family naba dazance yau idan bani inada wata danasan zata rikeminku tsakani ga Allah so I want you to take after me kinji, ki natsu and know what you are doing” fashewa da kuka tayi ahankali duk zuciyanta namata nauyi da duhu, bayan hannunta takai ahankali ta share idanunta sanan cikin sheshekan kuka tace “Mama maisa duk idan namiki laifi saikitamin magana kaman zaki mutu eh? Wlh Mama bazan karaba na rantse da Allah kinji, dan Allah kayakuri kuma kawayena zan ragesu, Mama I love you a lot please kidena fushi dani kuma kidena magana haka kinji, Mama you will leave long har yarana zaki goya” murmushi Mama tamata she just wish zata iya daina mata magana hakan, kumatunta taja cikeda so tace “oya stop crying inba hakaba I will snap your face natura a group dinku na nunama friends naki sugan cewa the famous Khairiry dinsu is a crying queen agida” dasauri tasa hannu tashare fuskanta ta washe jerin white teeth nata kananu dakeda bala’in kyau tace “Mama nadena” dan dariya Mama tayi tace “oya je bude drawer nan nawa ki kawo comb da kipiya ayi wanan tsifan” da sauri tasauka dagakan gadon tai wajen drawer dakin Mama tabi bayanta da kallo wani irin girma Khairy keyi da batasan ina zatada girma ba ga shape kaman ita tai kanta, daukowa comb da kifiyan tayi tajuyo Mama tabi damemmen cikinta da kallo tace “wuce kidebo breakfast kidawo” tai maganan tana karban comb din hannun nata, juyawa tayi tafita daga dakin koba komi ta lallashi Mama tahakura saura Baba shikuma da Baffa zata hadashi simple.




Dinning taje, plate tadauka tana bude kula, chips tadeba da sausage batare data taba kwan wajenba sanan takada tea tajera komi a tray tadawo dakin Mama, ganin Mama na rubutu da pen a dairy dinta wanda inda sabo tasaba ganinta tana yan rubuce rubuce aciki yasa tai murmushi ijiye abincin tayi anan kasan carpet sanan ta taso tazo inda Mama take tana kallon abinda take rubutawa da sauri Mama tarufe dairy tadago kanta tana hararanta tace “lpy” turo baki tayi ashagwabe tace “Mama handwriting dinki nake kallo fa, wlh Mama handwriting dinki yafi harna Baba kyau, inama nine nakeda fine handwriting haka, amman rubutuna kaman tafiyan tsutsa” hannu Mama takai ta dakamata duka a kafa tace “kincikani da surutu wuce kije kiyi breakfast kizo namiki tsifan” wucewa tayi tana dan dariya sanan tazauna tanacin abincin tana wasadashi kaman wata yar yarinya Mama kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login