Showing 27001 words to 30000 words out of 61405 words
amintar sai gashi kina kiran ta da Karuwa”.
Zama yai a bakin gadon hawaye na zubo masa, cikin kuka yace “da kin san irin son da nake mata da kin amince min kin taya ni neman soyayyar ta, sbd Ina mata son da zan iya mutuwa sbd ita Hajjo….”
Baki sake Hajjo take kallon sa ganin yadda yake kuka yana ambatan son da yake wa aminiyar ta, itama ji tayi hawaye na taruwa a idon ta cikin sanyin jiki tace “don Allah ka dai na kuka Abba”.
Girgiza kai yayi yace “kuka ai ynxu na fara tun da har ta budi baki tace baxa ta taba aure na ba ko zata dawwama ba aure, abu daya na sani wallahi in har ta auri wani ba ni ba toh ki shirya bayan wata biyu kema zaki tarbi taki kishiyar….”
Daga haka ya mike ya shige toilet yana goge hawayen sa.
Mike wa tayi cikin sanyin jiki ta fita daga dakin zuwa nata zuciyar ta tana bugawa, ynxu in Aasmaa tayi aure kenan Mijin ta zai auro mata wata kishiyar ce dai sai ya mata kenan…
Zama tayi a kasa yana fashe wa da kukan bakin ciki……
********
Kallon Yusrah yake wacce take ta sunkuyar da kan ta kasa cike da kunyar irin kallon da yake mata.
Kankance ido yayi yace “wifey wani turare kike amfani da shi ne uhmm…”
Lumshe idon ta tayi cikin shaukin soyayyar sa tace “bkm Yayana..”
Ware mata ido yayi yana kallon ta, shi kadai yasa irin abinda kamshin nan yake masa, daure wa kawai yake yana magana amma gaba daya ya shiga wani yanayi ne, yana son kamshi sosai balle wannan kamshin da yake ji yana shiga dukkan wata kofofin jikin sa.
Ita dai Yusrah rufe fuskar ta kawai taka tana murmushi, gyaran jikin da ake mata ne ya kama jikin ta sosai, Mami ce da kan ta take mata tun da ta iya, da kyar ta yadda Mamin ta fara mata sbd kunya amma ita Mamin ko a jikin sa dage wa take tana gyara Yusrah, a cewar ta ai ko ba Abdallah bane zai aure ta ita mai gyara Yusrahn ce tun da yar ta ceh.
Tun da aka fara gyaran basu taba hadu wa da Abdallah ba 3 weeks kenan, boye ta ake sai yau da ya rage saura kwana 6 daurin aure kuma ta tare a gidan sa shine ya kira ta akan yana bukatar katin dinner guda biyar, shima Mummy bata san ta fito ba satar hanya tayi ta kitchen ta fito.
Mika masa katin tayi tace “gashi Yayana, wasu friends dinka zaka bawa koh, Teemah ta bawa Yaya Musbabu bai isa bane kenan koh”.
Lumshe idon sa yayi yace “no ya isa wata zan kai wa”.
Da sauri ta d’ago ta kalle sa haka kurin taji gaban ta yana faduwa, cikin rawar murya tace “yaya wata zaka kai wa cards din har 5 friend din ka ceh”.
Zuba ma idon ta kallo yayi yana hango kishin sa dake kwance a ciki, murmushi ya saki yace “uhm zan basu ne ita da maman ta sai sisters dinta”.
Turo baki tayi tana juyar da kai gefe duk ran ta a jagule.
Murmushi ya Kara saki yace “wifey haushi na kike ji neh…”
Turo baki tayi a shagwabe tace “Yaya ba kai bane wai zaka bawa wata cards din bikin mu har 5”.
Shiru yayi don bai san kuma mai zai ce ba, ajiyar zuciya ya sauke yace “bara na tafi ki koma ciki kar sanyi ya dake ki”.
Bin sa da kallo tayi kwalla na tarar mata, tasan baya son ta ita kadai ce take son sa amma tsoron ta shine kar yaje ya samu wacce yake so tasan sai ya fifitata akan ta.
Hawayen daya zubo mata ta goge ta shige ciki.
A nutse yake driving din sa yana tunanin sabuwar rayuwar sa zai fara in aka kai masa mace gidan sa, yasan ba wai son ta yake ba amma yana ganin girman ta sosai a idon sa, shi kan sa a ynxu ya shaida cewa tana son sa soyyaya ta gaske na kuwa.
Duk abinda yace yana so nan da tan take yi wanda kuwa ya nuna baya so barin sa take duk irin son da take ma abin kuwa.
Sai da ya tsaya ya siya tsire da yawa sannan ya nufi unguwar su mara kunyar sa yana murmushi.
Da sallama a bakin sa ya shigo kan sa a kasa yana haska wa da wayar sa tun da ba wuta sai hasken farin wata.
Umma da Umar da sauke zaune ne suka amsa masa fuskar su Washe da murmushi.
Shima murmushin yayi yana zama akan kujerar da ke tsakar gidan.
Cikin girmama wa yace “Umma Ina wuni”.
Murmushi tayi tace “lafiya qalau babana kwana da yawa Ina ta cigiyar ka gashi ban da number ka balle Umar ya kira ka”.
Shi fa Wallahi haka kurin yake jin kunyar mata ya rasa dalili kawai kunyar ta yake ji, dan sosa girar sa yayi yace “na shiga hidima ne yau saura kwana 6 bikina”.
Ina zaune a daki ban san lokacin da na mike da sauri ba ina dafe kirjina da yayi wani mugun bugawa.
DijahAM
09066728387
Salamu alaikum💃💃💃💃
Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵
Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.
Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃
Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥
Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.
Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥
Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490
Bissalam❤️❤️
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 18
Dedicated to Abubakar Musa Sulaiman Ina godia sosai Allah ya bar zumunci ya baka mata ta gari mu sha biki💃
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Mike wa nayi daga zaunan da nake Ina dafe kirjina jin yadda yake bugawa da karfi, lumshe ido nayi Ina jingina da bango don ban san wani abu ke damu na haka ba da nake jin zafi a kirjina.
Daga waje kuwa Umma ce ta kalli Abdallah cikin murna tace “Maa sha Allah babana, ashe ango ne a zaune a gabana ban sani ba”.
Sunkuyar da kai yayi yana sosa kan sa don kunya yaji kawai yana ji.
Umar ne ya mika masa hannu yace “congratulations bro zan so daurin auren kuwa in sha Allah”.
Mika masa yar karamar jakar daya sa cards din yayi yace “gashi na daurin aure ne sai na dinner”.
Umma ce tayi murmushi tace “dinner din dai sai dai su Yaya dasu Aasmaa amma ni tsohuwa kawai sai naje wani dinner”.
Marairaice mata yayi yace “plz Umma ai dinner din har da manya ba ta yara bace kadai”.
Girgiza kai tayi tace “Aa babana kaga ban gama warke wa bama da saura su Yaya zasu je in sha Allah”.
Ba don ran sa yaso ba ya bar maganar suka shiga wata hirar yana bata amsa a nutse, kasan zuciyar sa so yake ta fito amma bai ganta ba kuma yana jin nauyin ya budi baki ya tambayi inda take.
Ledar tsiren ya mikawa Umma yace a hanya ya gani shine ya siyo mata, sosai ta masa godia cike da farin ciki tana ajiye ledar a gefe.
Sai goma ya mike zai tafi Umma ta kira Aasmaa akan ta fito su gaisa da Abdallah ta masa murnar auren da zai yi.
Hijab na saka na fito ina turo baki, tun da na fito yake kallon ta zuciyar sa na bugawa duk da ba haske a gidan amma yana iya hango baby face dinta d take a hade kamar wacce aka ai kowa sakon mutuwa.
A hankali na kalli Umma nace “Umma gani”.
Dan hade rai Umma tayi tace “baki ji shigowa babana bane baki leko kun gaisa ba gashi ashe aure zai yi kinga katin bikin ya kawo nace ni dai baxan iya zuwa ba sai dai ku”.
Waro ido nayi irin ban san abinda ya faru ba nace “Umma ynxu wannan yaron za’a ma aure”.
Tafa hannu na shiga yi na d’ago Ina kallon sa cike da mamaki nace “ynxu wata yarinyar ce ta yadda zata aure ka don Allah, dan yaro da kai har wani iya rike aure zaka yi”.
Tsawa Umma ta daka min tace “meye haka Aasmaa taya mutum zai zo ya kawo mana katin sa kawai ki fara maganar shirme, ynxu baban nawa ne baxai iya rike aure ba”.
Turo baki nayi Ina langwabe kai a shagwabe nace “Umma to gani nayi fa don Allah yayi yarinta da yawa kawai sai a masa aure duka duka nawa yake ma”.
Abdallah daya zuba mata ido ran sa yana baci sbd yadda take kiran sa da yaro yace ma Umma bara na dan wanke hannu nah Umma kafin na wuce.
Daga masa kai Umma tayi tana watsawa Aasmaa harara.
A nutse yake tafiya sai da ya maso kusa da ita ya tabbatar hankalin Umma da Umar basa kansu kawai yasa hannu ya fisgo ta jikin sa, dan matsawa yayi baya kadan don yadda ta taho din saura kadan kirjin su ya hade.
A fusace na bude baki zanyi magana sai dai ban kai ga cewa komai ba na tsinkayi muryar sa a dai dai kunne na yana fadin “ki kula da kira na yaro bar ganin ki kin fini shekaru in na damke ki a hannu na sai na farka ki tsab don daga ganin kugun kima na miki yawa….”
A razane na daka tsalle nayi baya da sauri Ina fadin “A’uzubillahi”
Umar ne ya mike ya taho guri na da dan sauri yace “lafiya Ya Aasmaa”.
Ban basa amsa ba sai kallon Abdallah kawai da nake Wanda ya gama wanko hannun sa yazo ya wuce kamar bai san abinda ya aika ta ba.
Sallama yayi ma Umma ya wuce Umar ya mara basa baya don masa rakiya.
Umma fada ta kama min bayan sun tafi akan na dai na wannan tsanar da nake nuna ma babanta, ni dai ban yi magana ba sai idona dana lumshe kawai duk lokacin dana tuna kalaman sa sai tsigar jikina ta tashi kafin na ankara kawai sai ji nayi na jika pant.
Nidai haka na kwanta gaba daya sukuku a rai na kuwa ban da Allah ya isa ba abinda nake ja masa, wannan maganar da yayi min ta taso min da mugun feeling din da nake danne wa, a wahalce bacci ya dauke ni cike da mafarkai.
Karfe biyar na farka a lokacin da aka yi kiran farko, lumshe ido na nayi kawai hawayen takaici yana zubo min Ina kara jawa wannan yaron Allah ya isa.
Da sauri na bude idon kuma sbd mafarkin sa da nayi ni da shi muna duniyar ma’aurata muna tsotse wa juna man Kai yasa na tashi da sauri Ina share hawaye na.
A rai na kuwa Allah ya kiyaye kawai nake har na shiga toilet, a gurguje nayi wanka don kar Umma ga farka taji ina wanka da sanyin safiyar nan, kayan jikina na mayar tun da ba yadda zanyi na chanja kaya Umma sai ta fahimta.
A toilet din na wanke pant dina na fito na shanya akan igiyar dake bayan dakin mu na koma ciki da sauri.
Sai da nayi sallah sannan na tashi Umma ita ma tayi sallah…
Bani da aiki yau don haka kwanciya ta nayi na koma bacci.
******
Ranar Daurin Aure💃
Shirye shirye ake ta ko wani bangare da safiyar yau juma’a data kama daurin aure, jiya sukai mother’s eve/kamu bai je ba shi dai su kadai sukai kayan su sai yau da za’a yi dinner karfe 7 gobe asabar suyi yini a kai amarya kuma da daddare.
Yana kwance a daki har 12 tayi ana ta shirye shiryen tafiya masallaci tun da sai 2 daurin auren amma shi ya kasa tashi haka kurin yake jin jikin sa yayi masa weak sosai.
Musbahu ne ya dala masa duka a cinya yace “baka da kirki wallahi Abdallah ynxu har 12 amma baka yi wanka ba.”
Bude idon sa yai da suka masa ja yace “bana jin dadi sosai ne”.
Dariya Musbahu yai yana zama a gefen sa yace “ko dai tunanin sabuwar rayuwar da zaka shiga kake, kai ni ban ma yadda da kai ba tunanin Aunty Aasmaa kake koh”.
Wani mugun kallo ya jefe wa Musbahun wanda yasa Musbahu mike wa yana kyalkyala dariya.
Da kyar ya tashi ya shiga toilet yayi wanka, shiryawa yayi cikin wata farar dakakkiyar shadda maikon da take ne zai fada ma cewa ba karamar shadda bace, yayi kyau sosai sai dai bai sa babbar rigar ba ya rike ta a hannu ne kawai.
Shi da Musbahu da sauran friends dinsu ne suka tafi masallacin Umar bin kattap anan za’a daura auren…
A cikin gida kuwa fada ne ya kaure tsakanin Meena da Teemah, sbd Teemah din tana wakar bikin su Abdallah da Ali jita yayi musu shine Meena ta mike daga zaunen da take ta sha gaban Teemah tana ce mata da take wakar bikin Abdallah din an fada mata zata damu ne, kuma ta rubuta ta ajiye auren Abdallah ne dole tayi sa ko ba dade ko ba jima.
Ita ma Teemah din dama tana Jin haushin Meena sbd lokacin da tayi wa Mami rashin kunya bata zage ta ba tun da Mami ta ha mata kunne don haka tayi dariya cike da tura wa mutun haushi tace a Ina din zaki auri Yayan nawa, ai auren Yaya na sai mace kamila mai daraja ba wacce take raba wa gayu ba.
Wannan maganar ta bata wa Meena rai sosai ai kuwa ta shako wuyan Teemah suka kacame da fada, da kyar aka raba su Teemah ta fita zuwa part din Mummy ita kuwa Meena zama tayi a gaban iya tana kuka.
Hjy Bilkisu da tayi tagumi tana kallon yadda tilon yar ta take kuka ce tace “don Allah iya ki sa baki Abdallah ya auri Amina, mu ynxu mun amince ma zata je a ta biyun wallahi kuma In sha Allah zasu zauna lafiya”.
Iya mace mai daraja da sanin ciwon kai da take zaune cikin shiga ta alfarma tana jan carbi a nutse ba birkicewa irin ta tsoffi ce ta kalli Bilkisu tace “ynxu ke Bilki baki ji kunya ba, duk irin zagi da dibar albarkar da kuka gama wa Uwar yaron nan amma ynxu kice dan ta ya auri yar ki, ba kun ce baxa ku aure sa ba Ina har cewa kika yi dama ke ai rufa masa asiri kikai ynxu kuwa yar ki tafi karfin sa kinga sai kuje ki bawa wadanda basu fi karfin nata ba”.
Ihun kuka Meena ta saki tana riko hannun Iya tace “don Allah iya ki tausaya min ki taimake ni ki fada wa Ya Abdallah ya aure ni Wallahi Ina son sa, kishi ne ya rufe min ido a lokacin amma baxan sake ba na yadda zan zauna da Yusrah din Allah ki taimaka iya”.
Hade rai iya tayi ta kalli Hajiya Bilkisu data sunkuyar da kai kawai tace “dauke min yar ki daga gabana Bilki tun kafin rai na yayi mugun baci, kin san halina bana daukar rai ni koh don haka ki gode ma Allah ma da ban miki fada ba a cikin jama’a akan abinda kika aikata, ba wai kyale ki nayi ba kawai na miki shiru ne sbd taro ana gama wa kuwa In sha Allah har gida zan zo na same ki mara kunyar banxa da wofi wannan ba tarbiyya ta bace sam”.
Daga Meena Hajiya Bilkin tayi tana bawa Iya hakuri suka fita don fa tafi kowa sanin wace mahaifiyar ta bata daukar raini, ita ma data zo bikin tayi mamaki da taji mahaifiyar tata bata maganar abinda sukai ba har ta fara murna cewar maganar bata je kunnen ta ba ashe shiru tayi mata kawai.
Ajiyar zuciya ta sauke tana addu’a Allah ya sassauta zuciyar iya ta huce kafin a gama bikin.
A dakin Yusrah kuwa suna zaune yan mata da kawayen ta suna tsokanar ta, ita dai tana zaune a gefen gadon cikin wata farar shadda anko Abdallah ya musu ita da shi tayi kyau sosai don dinkin da aka ma shaddar ha haskata sosai, fuskar ta yayi kyau da make-up din da Teema tayi mata tayi kyau sosai kamar ka sace.
Zuciyar ta kawai bugawa take tana addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi don ji take kamar za’a ce an fasa auren shiyasa duk ta rasa nutsuwar ta.
Karar shigowar message a wayar ta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, da sauri ta kunna wayar ganin sunan My King❤️💍👑 daya fito, da sauri ta bude message din ta karanta sakon kamar haka “Allah ya bamu zaman lafiya Wife Alhamdulillah”
Lumshe ido tayi kawai sai ta janyo mayafinta ta kara yafa wa sosai ta dauki sallayar da take ajiye a gefen ta ta shinfida ta tayar da sallah, raka’a biyu tayi ta dade tana addu’a a sujjada kafin ta d’ago tana kuka.
Sai da ta sallame sannan ta juya gurin Ya Walida data shigo ynxu kawai ta sai ta mike da sauri ta fada jikin ta ta saki kuka, cikin kuka tace “an daura Ya Waleeda shikenan na zama Matar Yaya Abdallah..”
Guda