Showing 57001 words to 60000 words out of 61405 words

Chapter 20 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3779

duk mai girki ita zata yi abincin shan ruwa zamu hadu a part din sa a ci.


Duk abinda nasan zan bukata sai da na dauka da wasu abubuwan na gida sannan muka fito.


Cikin amincin Allah an rasa azumi lafiya na dage sosai da ibada bama duk ranar da ya kasance bani da girki.


Tun da ko abincin da Binta zata ci Yusrah ce take aiko mata da shi haka ni ma in ranar girki nane ni nake bawa mai aikin Yusrah abinci.


A haka azumi yau har anyi kwana sha biyar, komai yana zuwa min da sauki tun da tun da daddare nake dama tsara abinda zan dafa don haka bama kwanciya sai mun rage aikin na feraya ayi, jajjage ko yanke yanke.




YUSRAH…


Wannan azumin da ake na hada abinci ake aiki baya mata dadi sam da farko itama hakan ya mata ko dan ganin hutun tane itama zata samu kwana biyu ta huta amma kuma sai ta fara fuskantar kalu bale tun da tana da ciki bata da taste wani lokacin sai da dan saki gishiri ko ta bawa mai aikin ta dandane tace mata komai yayi ita ji take kamar bai ji ba sai ta kara.


Don haka in zun zo cin abinci ita zata ci komai lafiya a gurin ta, amma shi Abdallah abu kadan yake ci in tace bai ci sauran ba yace gishiri yayi yawa ne.


Duk ranar girkin Aasmaa kuwa zage wa yake ya cika cikin sa duk abinda tayi sai ya ci, wannan abin yana matukar bata mata rai danne wa kawai take yi.


Iya kokari tana yi bama kuma tun lokacin da yake yawan mata korafi tana cika gishiri take kiyaye wa, sai ta zuba dan daidai koda ita Zata ji a bakin ta bai yi ba nan ma sai yace yau abincin magi bai ji ba kanwata, abinda yke kara bata mata rai a gaban Aasmaa yake fada mata irin haka ai da ko fadan zai yi sai ya bari sai sun kebe su biyu.


Duk wannan karamar matsala ce akan yadda yake wani kallon Aasmaa in suna tare sai yayi ta mata kallon kasa kasa yana murmushi, wannan abin ba karamin kona mata rai yke ba tana tunanin ko gani yake ita bata da kishi ne don kawai tana kawaici tana kawar da kai.


Wadannan abubuwan su suka sa taji zaman shan ruwan duka ya fita a kan ta bata son sa.


Yau ma girkin ta ne tayi iya kokarin ta na ganin tayi komai dai dai, mai aikin tace ta taya ta suka jera abincin a part din Abdallah.


Koma wa tayi tai wanka lokacin har an sha ruwa tana da tabbacin kuma Abdallah ya dawo ita yake jira tayi serving dinsa shiyasa take ta sauri.


A gurguje ta shirya ta nufo part din sai kamshi take yi, tana nufo palon cikin tayi birki ganin yadda Abdallah ya daura Aasmaa akan cinyar sa yana bata wani kiss.


Daure wa tayi ta hana hawayen dake don zubo mata sauko wa tayi Sallama.


Da sauri na dago duk sai naji kunya ta kamani da sauri na sauka akan cinyar sa Ina gyara riga ta data ya mutse, sai da na ce masa ya rabu da ni kar ta shigo amma ya kafe akan kiss kawai zai min dan kadan..


Shima duk kunyar ce ta Kama sa sai ya shiga sosa kai duk ya diririce.


Serving din su tayi ita kuma ta sawa kan ta kunnu don bakin ta duk ba taste.


Kiran ta da Abdallah yayi ne yasa ta dago ido cike da gajiya wa ta kalle sa.


Plate din sa na komai ya tura mata yace “kin dandana kuwa Wifey kin ji yau yafi na ko yaushe gishiri”.


Kallon sa take da idon ta da suka kada suka yi ja kawai ta mike ta dire cup din hannun ta tace “Allah ya baku hakuri ban san yayi gishiri ba daga haka ta bar palon”.


Baki sake Abdallah yake kallon ta cike da mamakin ta shi bai ga abinda zata tsaya tana yi wa fushi anan ba.


Kallon sa nayi nima a ko yaushe ni Ina mata uzuri don naga yadda wasu masu cikin suke girki sai ana ci da hakuri don ba kowa bace take da taste.


Cikin sanyin murya nace da baka mata magana na don Allah ai sai ka duba halin da take ciki..












DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 38




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






Shima kallona yayi yace “me nace mata Toh?”


Girgiza kai nayi nace “ba wacce zata ji dadi kullum in tayi abu miji y kushe kuma a gaban kishiyar ta sai ka duba ka gani ai da ba haka take ba yanayi ne yasa ta haka mace mai juna biyu sai ana mata hakuri Hub”.


Shiru yayi bai yi magana ba shi har ga Allah ya dauka an zama daya ne in ya fada cewa abinci yayi gishiri ba wani Abu bane.


Haka muka gama nice na tattare ragowar na ajiye a gefe, wanda muka bata kuma na wanke mata sannan nayi masa sai d safe ma bar masa part din.


Shiru Abdallah har karshe goma Yusrah bata shigo ba sai yaji hankalin sa ya fara tashi don yasan bata wuce 9:30 tun da da wuri suke bacci.


Mike wa yayi ya nufi part dinta.


Da Sallama ya tura kofar dakin ta ya shiga tana zaune akan kujera tana jan carbi idon ta a rufe, a saman lips din ta ta amsa masa kawai ba tare da ta bude ido ba.


Tako wa yayi a hankali har ya iso in da take, cikin sanyin murya yace “Wifey ki tashi mu tafi bacci nake ji”.


Banza ta masa kamar bada ita yake ba don wallahi a yadda take jin zuciyar ta zata iya zagin sa in har tayi magana, ita zai zo yana wani Kira da Wifey uban Wifey din karewar soyayya.


Kujerar da take zaune ya zauna shima ya dora hannun akan cinyar ta.


Da sauri ta tashi ta ture hannun ta zuba masa idanun ta suka yi jajir sbd kuka.


Da sauri ya mike shima yace “wifey kuka kika yi haka.”


Wata muguwar harara ta sakar masa murya a kausashe tace “fitar min daga daki don Allah tun kafin na fada ma maganar da zan zo Ina dana sani daga baya”.


Zaro ido yayi yace “Wifey me nayi miki”.


Kallon sa take hawaye yana zubo mata, cikin kuka tace “tambaya ta kake mai kayi min Yaya, ka manta ko kuma ture wa kayi sbd rashin adalci”.


Nuna kansa yayi cikin mamaki yace “nine mara adalci Yusrah”.


Cikin ido ta kalle sa tace “eh kai ne Mara adalcin Yaya, tun da aka fara azumin nan bana cikin nutsu wa duk ranar girki na fargaba nake yi kar nayi abinda zai sa ka kushe girki na amma duk kokari na sai ka kushe a gaban KISHIYA ta”.


Kuka ta kara fashe wa da shi tace “duk ranar girkina haka zaka tsakuri abinci kadan kaci amma ranar girkin ta farin cikin da kake baya boyuwa a fuskar ka, haka zaka zauna komai sai kaci kana santi amma ni kuwa ko sau daya da azumin nan ka taba sha ko cin wani abu nawa ka yaba min Yaya?”


Kallon ta yake jikin sa a sanyaye duk abinda ta fada gaskiya ne to me kuma zai ce.


Murmushin takaici tayi tace “bayan wannan haka Ina zaune a gurin zaka dinga kallon ta kana mata Murmushi cike da soyayya ni kana min irin kallon da kake mata ne Yaya ko a tunanin ka bani da zuciya a kirjina da zan ji zafi”.


Numfashi ta sauke tana share hawayen ta da mayafin data daura tace “kar ka manta wata na shida da aure ka kara aure Yaya, ba irin maganganun da ban ji ba na toshe kunne na, Ina iya kokari na don naga na boye kishi na duk kuwa da cewa ba wai bani da shi bane kawai son da nake ma ne yake sa ni danne kishin don a zauna lafiya”.


Kallon sa ta kara yi ganin yayi shiru ya zuba mata ido ta girgiza kai tace “Ina boye kishi nane don nasan ban kai matsayin da zan yi kishi da matar son ka na tun da ni ba sona kake ba dama taimakona kayi”.


Cikin tashin hankali yace “don Allah Yusrah ki dai na wannan maganar kamar ya taimakon ki nayi Wallahi Ina son ki”.


Girgiza masa kai tayi cikin kuka tace “baka so na Yaya duka alamu sun nuna haka kuma ni din matar cushe ce wacce ka taimaka ka aura sbd yadda na mace a son ka har na kwanta a gadon asibiti sbd kai, ynxu da ka auri matar so Ina ganin soyayya kala kala Yaya duk iya hakuri na ka kure ni”.


Nufo ta yayi hankalin sa a tashe don tun da yake da Yusrah bai taba ganin ta cikin bacin rai irin haka ba, baxai ce basa samun sabani ba amma ko yaushe ko shi ne ya mata laifi tana basa hakuri don kawai ya hakura komai ya wuce.


Cikin tsawa tace “kar ka sake kazo kusa dani Yaya Wallahi in ka sake ka taba ni zan baka mamaki kwarai da gaske”.


Tsayawa yayi cak cike da dunbin mamakin ta yace “Yusrah ni ne fah Yayanki”.


Girgiza Kai tayi tace “Hub din Noorie ne ba Yayana ba, a da kafin ka auro ta kana nuna min soyayyar data ke mantar da ni cewa auren taimako kaii ashe ban sani ba a lokavin sbd baka da muradin ran ka neh, duk abinda kuke yi Yaya kawar da kai nake sbd Ina fada wa zuciya ta kai din Mijin mu ne ba nawa ba ni kadai”.


Murmushin takaici ta sake saki tace “yau din ranar girki nane Yaya ban haka ka yiwa matar ka kiss ba amma da ka daure duk irin yadda ka zaku daka ji bakin ta da ka bari in ka shiga part din ta sai kuyi in abinda yafi kiss ne amma sbd baka dauke ni da daraja ba kamar yadda ka dauke ta sai gashi ka daura ta akan cinyar ka kana mata kiss, ni duk ranar girkin ta ko zama a kujera daya da kai bana yi kuma kai ma baka yi sbd ita matar so ce baka so ran ta ya baci amma ni ai bola ce ko wacce Shara aka zuba min dauka zan yi”.


A sanyaye tace “fitar min daga daki bana son ganin ka wallahi Allah ABDALLAH”.


Wani irin bugawa kirjin Abdallah yayi ciki da tashin hankalin da zai ce ya dade rabon da ya shiga irin sa yau shi Abdallah Yusrah take cewa ya fita bata son ganin sa shi Abdallah ne yafi Yusrah ya ambaci sunansa gatsal sunan da tun da suka yi aure bai kara ji ta fada ba sbd Yayana take ce masa.


Haka ya fita daga dakin jiri yana kwasar sa.


Ita kuwa Yusrah ba karamin kuka ta sha ba sbd tuno wa take da irin kallon da Abdallah yake yawan jifan Aasmaa da shi da kuma yanayin data same su dazu.


Kasa bacci tayi don haka tayo alwala kawai ta fara sallah.




Gidan dai yau gaba daya ba’a yin kwanan dadi ba don ni kai na duk juyin da zan yi yanayin da Yusrah take ciki kawai nake hango wa.


Mata da yawa suna cewa KISHIYA baxa ta taba kaunar kishiyar taba amma ni zan bugi kirji na karyata su, Ina ganin darajar Yusrah sosai kuma Ina son ta har rai na sbd yadda take girmama ni.


Nice amarya amma Aunty sama Aunty kasa ne kamar ba uwar gida bace ita wanda ina da yakinin a zamanin nan da wuya a samu irin haka.


Haka dai Washe gari ma na tashi jiki na a sanyaye da yake ni ce da girki da wuri na shiga kitchen kamar yadda na saba don nayi abinci.


Ko da aka sha ruwa Ina zaune a part din sa Ina gyara kayan abincin ya dawo daga masallaci sai wara ido yake.


Kallo daya na masa na karanto tarin damuwar da yake damun sa.


Murmushi na masa nace “sannu da shan ruwa”.


Daga mun kai kawai yayi yace “Yusrah bata zo ba”.


A nutse nace “eh bata zo ba”


Gyada Kai yayi ya juya ya fita ya nufi part din Yusrah cika da zumudin ganin ta don dazu daya zo tana daki kuma duk bugawar da tayi masa kin bude masa kofa tayi.


Ya kuwa ci sa’a tana zaune a kan kujera tana shan tea idon ta yana kan TV tana kallon Sunna Tv.


Ajiyar zuciya ya sauke da ganin ta da yayi cikin sanyin jiki ya kara so ya zauna a gefen ta.


Ko kallon sa bata yi ba duk kuwa da cewa tana jin yadda ya zuba mata ido








DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 39




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Tsoron mata magana yaji da kyar ya jawo jarumta yace “barka da shan ruwa Wifey”.


Akan lips din ta tace “barkan mu dai”.


Shiru yayi yana kallon ta a sanyaye yace “ki zo muje muci abinci ke kawai muke jira”.


Juyo wa tayi ta kalle sa fuskar ta dauke da Murmushi tace “ai kaga abinci nake ci Yaya bana jin Yunwa na baka space ne kuyi kallon love din ku kaga ba sai kana satar kallon taba bana gurin ynxu”.


Dafe kan sa yayi yace “don Allah kiyi hakuri Kanwata nasan nayi kuskure hakan baxai kara faruwa ba in sha Allah”.


Murmushi tayi tace “Yaya ai ni zan baka hakuri ni da kullum nake cika ma gishiri a abinci kuyi hakuri don Allah ni ynxu girkin nawa ma na bar wa Aunty kawai har na haihu sai na kar na in sha Allah kaga baxa ka dinga cin abincin da zaka dinga complain ba in sha Allah”.


Hannu yasa ya rufe baki cikin tashin hankalin yace “Innanillahi wa inna ilaihir raji’un”.


Murmushi ta kara sakar masa tace “Yaya nayi laifi ne”.


Hankalin sa a tashe yace “ynxu Yusrah ni kike cewa zaki bawa Noorie kwanan ki sbd na dai na complain”.


Girgiza kai tayi tace “Yaya kawai na taimake ka ne fah kaga bakin ka zai dai na ma ciwo”.


Daga haka ta dauki cup din ta ta wuce sama.


Bin ta da kallo yayi hankalin sa a mugun tashe sai ynxu yake hango girman laifukan da yke aikata wa Yusrah din.


Rintse idon sa yayi dake mugun sara masa da kyar ya tashi ya koma part din sa.


Abincin da yake ci kullum cikin farin ciki yau kunu kawai yasha rabin cup ya hau kan kujera ya zauna yayi tagumi.


Kallon sa nayi duk sai naji ba dadi a tunani na ko dan sbd abinda muka yi mata jiya ne take fushi.


Sai da na haka kwashe kayan abincin sannan na dawo kusa da shi ma shiga tambayar sa mai yake damun sa, bai min magana ba.


Nima dana fahimci baya son fada min sai kawai na shiga masa tausa a jiki.


Gaba daya ynxu zaman shan ruwan ba dadi duk ranar girkin ta baxa ta ki yin abinci ba kuma tana gyara masa part din sa amma sai taga baya nan.


Duk iya hakurin da zai bata tayi biris don a ynxu so take ta nuna masa tana da daraja ba komai bane in yayi zata dinga dauke ido akai don taga shirun ta shi ne yake sa wa ake kwarar ta ake tunanin ai kamar bata gani ne.


Abdallah kuwa gaba daya baya ma cikin nutsuwar sa, kullum haka zai sha kunu kadai sai in yaji yunwa ya tsakuri wani abu, a ynxu yake Kara tabbatar wa cewa Yusrah ita ce cikon farin cikin sa duk irin farin cikin da yake ciki in Yusrah bata tare da shi sai yaji tabbas da akwai babban gibi.


Ni kai na yncu zaman gidan duk gashi nan dai ne amma nasan hankalin Mijina a tashe yake bai fasa sauke hakkin sa dake kai na ba amma kallo daya zaka masa kasan cewa cikin farin cikin sa ya bata a tattare da shi.




*****
Yau ake gobe sallah Yusrah na zaune a dakin ta tana turara Kayan ya Abdallah ya shigo.


Kallo daya ta masa jikin ta yayi sanyi gaba daya kamar ba Abdallahn data sani ba ya rame kadan yayi zuru zuru.


Mike wa tayi ta ajiye mayafin abayar ta, nufo sa tayi taga yadda yayi tagumi yana kallon ta.


A hankali ta cire masa tagumin tace “Yaya mene?”


Cikin sauri ya riko hannayen ta sosai yace “don girman Allah ki yafe min Wifey Wallahi baxan sake ba rashin sani ne yasa nayi amma in sha Allaj hakan baxai Kara faru wa ba”.


Turo baki gaba tayi tace “ai ni tuni dama na yafe maka”.


Mike wa yayi ya sungume ta ya shiga zage ye dakin da ita yana fadin I love U Yar Aljanna tah.


Dariya Yusrah take sosai tace “Yaya sauke ni don Allah kar mu fadi”.


Sauke ta yayi ya zaunar da ita akan cinyar sa yace “kar ki Kara fadar cewa taimakon ki nayi Yusrah, Allah ne shai da ta ina matukar kaunar ki wallahi, fadar irin son da nake miki bata baki ne ni kadai nasan irin tashin hankalin dana shiga akan horon nan da kika min ki yafe min don Allah kuskure ne nayi miki baxan sake ba in sha Allah.”


Bata basa amsa ba sai hade bakin su da tayi.


Ranar a dakin suka kwana dama kuma ranar girkin ta ne.


Washe gari sallah da wuri ta tashi suka yi tuwo da masa da sinasir tare da wata Tsohuwa da Mummy ta kawo mata sbd harkar abinci tun da tayi wa Mummy complain ynxu bata taste.


Komai sai da aka dibar wa Aasmaa aka mai mata.


Ni ma yau na tashi cikin farin ciki kamar yadda ko wanne musulmi yake tsintar kan sa a irin wannan ranar.


Ni ma nayi abincin sallah na zuba wa Mami da Umma a flask na kuma zuba wa Yusrah ma na bayar aka aika mata.


Wanka nayi na shirya cikin shadda fara kal doguwar riga data ji aikin light blue zare har kasa sai na saka light blue din Hijab dogo wanda ya kara kawata kwalliyar tawa.


Na gama fesa turare ya shigo yana saba babbar rigar sa, fara’ar da na gani akan fuskar sa ce ta shaida min sun shirya kenan hankalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login