Showing 12001 words to 15000 words out of 61405 words
ne wanda aka kawata shi da decoration sosai, daga farkon shigo wa a bangaren dama gurin mu yake.
Jera abubuwan mu mukai tunda ba wai zamu yi serving dinsu bane sit by sit, kowa zuwa zai yi ya dibi abinda yake so, mu aikin mu kawai kula da yadda zasu diba da kuma Kai musu ruwa da drinks.
Zama nai akan kujeran Ina kallon yadda mutane suke shigowa mata da maza kowa yaci kwalliya, daga yanayin shigar su zaka gane wannan partyn na masu abun ne.
Muna zaune aka fara party din, ni dai kallo daya nayi wa birthday girl din na dauke Kai na Ina tabe baki, ta sanya wata farar gown wacce ta mugun matse ta ko Ina nata ya fito gashi daga wuya net ne ana hango saman na shanun ta.
Babban cake din dana yi na bawa Salma abokiyar aiki na kuma tare muke girki, duk abokan aiki nama mun fi shiri da ita don ita Ina dan zama muyi hira da ita sbd zamu yi sa’anni, tana da aure har da yara biyu.
Salma ce ta tura abin da aka d’ora cake din ta kai sa tsakiyar gurin da aka tana da don rawa..
Dawo wa tai ta zauna tace “Tabdijan Aasmaa abu kamar ba musulmai ba”.
Murmushi nai Ina dan muskutawa nace “musulmai ne mana Salma kawai sbd sun fi fifita nasara akan addinin su ne amma abin sam ba tsari”.
Tsaki tai tace “Ina fa tsari anan sam yaron ynxu kunya tayi musu karanci Wallahi”.
Shiru mukai kowa yana danna wayar sa.
Muna zaune mudai muna kallon yadda mutane kowa yake zuwa yana diban abinda yake so.
Ni dai nawa lura da yadda al’amuran suke gudana amma fuska ta a hade take.
Dafa sa Musbahu yai yace “ka tashi muje mu dibi abinci don Allah ni yunwa nake ji fah”.
Kara hade rai yayi, shi Musbahu ya kasa fahimtar sa, ran sa a bace yake sosai na ganin yadda Meena take ti kar rawa a cikin maza, ko wani namiji zai zo ya rikota ita kuma ta wani langwabe kai tana dariya suna hoto.
Ba wai kishin ta yake sbd yana son ta ba shi ko kadan baya son ta kawai dole yayi kishi mana tunda ita zai aura, ko bama zancen aure a tsakanin su ai kanwar sa ce.
Ganin yaki magana kawai sai ya tashi shi yaje ya zubo abinda yake so, ya kuma zubo tandori chicken da KFC a wani plate din, yafi kowa sanin yadda Abdallah yake kaunar kaza, abinci bai dame sa ba amma da in har kaza ce baya wuce tayi.
Ai kuwa yana zama idon Abdallah ya sauka akan plate din kazar, hadiyar yawu yayi yana lumshe idonsa yadda yake jin kamshin kazar nan ya tabbatar ba karamin dadi zata yi ba.
Zuba wa Musbahu ido yai yaga wai ko zai ce masa yaci amma yaji shiru bai ce komai ba sai ma cin abin sa da yake yi yana lumshe ido tare da gyada kai.
Tsaki yayi ya mike kawai ya nufi gurin da yaga masu abincin suna zaune.
Ina zaune ni kadai su Salma duk sun tafi kai Chapman, naji mutum a tsaye a kai na.
D’ago ido nai idona ga fada cikin nasa, a tare zuciyoyin mu sukai wani irin bugawa da karfi.
Shi ya fara janye idonsa yana wani hade rai, Nima sai na janye nawa idon Ina tabe baki.
Shiru yai yana jiran yaga ta dauki plate ta zuba masa yaji shiru sai danne danne take a wayar ta, tsaki yaja da dan karfi wai ko zata d’ago amma yadda take ko motsi batai ba balle yaga alamar taji tsakin da yai.
Kara buga tsakin yai da karfi amma yadda tayi shiru haka tai don haka a dan zafafe yace “baza ki zuba min abincin ba?”
Sai a lokacin na d’ago manyan idona na sauke a cikin nasa idon da suke a lumshe, tabe baki nai kawai na rausaya kai na Ina maida shi kan wayata.
Zaro ido yai yana kallon ta, yau shi Abdallah yake wa wata magana take masa banxa kamar ba magana yake da mutum ba.
Tsaki ya buga da karfi yace “ke wata iriyar mara kunya ce ana miki magana kin yi banxa”.
D’ago wa nai da sauri na kalle sa, ni wannan yaron yake cewa Mara kunya, yaron da nake masa kallon zai yi sa’a da Maryam in ya girmi Maryam da kadan ne ni yake cewa Mara kunya.
Irin kallon da nake masa shima irin sa yake min.
Girgiza kai nayi Ina hade rai sosai nace “waye sa’an ka anan gurin da zaka zo kana min rashin kunya, nayi kama da sa’ar wasan ka? Ku yaran nan daga kunga kun fara balaga sai rai na na gaba da ku koh”
Kara bude idonsa Abdallah yai yana kallon ta
Musbahu da ya taho yana hango su daga gefe hannu ya dora a kai yana zare ido, Addu’a kawai yake Allah ya sa kar Abdallah yayi wani abu da zai hargitsa gurin party din.
Tsaki nai Ina cigaba da danna wayata, wannan yaron lallai bashi da kunya kk hmm.
Abdallah ji yayi hankalin sa y tashi, yau shi ne ake kira da yaro tashin hankali.
Kara zuba mata ido yai yana son karanto shekarun ta amma cute innocent baby face dinta kawai yake gani ta hade rai.
Ya bude baki zai yi magana Musbahu yai saurin kara sowa yana kallona Aasmaa yace Aunty don Allah kiyi hakuri.
Dan kallon sa nai kawai ba gyada kai na Ina mayar da idona kan waya ta.
Jan hannun Abdallah Musbahu yai suka fita daga hall din gaba daya.
Kallon Musbahu yake yana Jin kamar ya rufe sa da duka, zai yi magana Musbahu yai saurin cewa don Allah kayi hakuri Abdallah ba girman ka bane ka tsaya kana sa’in sa a cikin gurin can, kuma fa Kai ne mara gaskia kowa yazo da kan sa yake zuba abincin taya zaka je ka tsaya kana zabga mata tsaki.
Shi dai kallon Musbahun yake kenan shi laifin sama yake gani koh……
Comments nd share plz
Mrs A.M
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 10
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yana tsaye yana tunanin irin yadda yarinyar ta raina masa hankali har bai san lokacin da Musbahu ya tafi ba.
Mota y shiga ya zauna yana huci ya ma rasa ta Ina zai huce wannan takaicin, yana zaune yaga ta fito tana tafiya a hankali kan ta a kasa.
Zuba mata ido yai yana kallon ta kafin wani idea ta zo masa yayi wani mugun Murmushi ya fice da motar da sauri.
Ni kuwa jin da nayi gaba daya mood dina ya chanja yasa na cewa Salma kai na ciwo yake min zan je gida na huta tun da an kusa tashi a party din.
A hankali nake tafiya kai na a kasa na dan yi nisa da hall din Ina so na tafi babban titi yadda zan samu adaidaita da sauri kawai naji an watso min wani abu mai sanyi a fuskata ya gangaro har light brown din Hijab dina.
Da sauri na d’ago don ganin wane mara mutuncin ne ya aikata min haka, ido na ne ya fada cikin idon wannan tsageran yaron da yake ce min bani da kunya.
Irin kallon da yake min na dage girar sama yana min kallon kyama ya tsaya min a rai, Kara kallon jikina nayi yadda nonon ya zubo min da alama nonon saniya ne da aka dama da fura.
Kallon jikina kawai nake kamar zanyi kuka don takaici, in na bude baki da niyyar magana ba abinda zai hana hawaye zubo min don haka kawai na gyada kai na yi gaba da sauri Ina goge fuska ta da hijab din nawa.
Bin bayan ta da kallo yai ran sa fess don yasan ya gama bata mata rai.
Wani murmushi ya saki ya juya kan motar ya nufi gida hankalin sa kwance.
Da kyar na samu adaidaita na shiga, ban da ajiyar zuciya ba abinda nake sauke wa.
A bakin layin mu na sauka na basa kudin sa, ko tsayawa kar bar chanji ban yi ba na shige ciki
Tun daga kofar gidan nake jin muryar Kawu Laminu yana fada, rintse idona nayi gaba na yana faduwa.
Da sallama na shiga ciki, da sauri Kawu y juyo yana bina da mugun kallo yace “an dawo daga yawon barikin kenan ko”.
Lumshe ido nayi ina sunkuyar da kai na kasa, tsugunna wa nai nace “Ina wuni kawu”.
Tsaki yai yana kankance ido yace “rike gaisuwar ki bana bukata, ni Yaya ya cuci Inna Wallahi daya sa maki sunan ta kowa yasan innar mu mace ce mai kamun kai amma ke kuwa lokacin da ake raba kamun kai kina daki kina baccin asara”.
Kara sunkuyar da kai na nayi hawaye yana zubo min, bakin cikin abinda yaron can ya mun da wanda kawu yake min ynxu yasa naji baxan iya daure wa ba.
A hankali nake kuka na Ina goge wa da hijab yadda Umma baxa ta fahimta ba sai dai na makaro tini ta fahimci kuka nake.
Shiru tai kawai bata musa wa Kawun ba don bata son tashin hankali, tana magana zai harzuka tun da haushin ta yake ji dama tun bayan rasuwar Baban su Aasmaa din daya so ya aure ta tace ita sam ba maganar aure ynxu a gun ta zama za tayi ta kula da yaran ta.
Kallon sa Umma tai tana hade rai tace “laminu Ina fada maka tun ba yau ba ka daina jefar min y’a da wannan muguwar kalmar ni nasan wace diya ta kuma na yadda da ita”.
Tsaki yai yana duban Umman ran sa na kara baci, nuna ta yai yace “tun da yau ba dama nasan cewa ke kike goyawa yarinyar nan baya take duk abinda yake so, ta Ina ma baxa ki goya mata baya ba tun da duk abinda ya samo ke take kawo wa kuke ci tare, ni dai na fada muku wallahi wata 6 na baku ta fito da Miji in ba haka ba zan bawa Alhaji Inuwa auren ta tunda ai shi kadai ne yace ya ji ya gani duk da muguwar dabi’ar ta”.
Juya wa yai cikin fushi ya fita daga gidan ran sa na kara baci, har shi Zainabu(Umma) zata wulakanta ai ya riga ya rantse tun da ta murza wa idon ta kwalli tace baxa ta aure sa ba shi kuma baxai gaji d kuntata masu ba, ya san cikin wata 6 ba Wanda zai zo gurin Aasmaa din tun da dama ba wani farin jini gare ta ba, shi kuma zai yi amfani sa matsayin sa na kanin uban ta ya aura mata Alhaji Inuwa.
Dafa ni da Mama tai yasa na mike Ina share hawaye na.
A nutse Umma tace ki fawwalawa Allah komai Aasmaa, nasan kin karbi kaddarar ki da hannu biyu ki cigaba da addu’a in sha Allah wata ran sai labari kinji.
Daga mata kai nayi kawai na shige daki, Basma na makure a jikin kofa da alama ta ji komai.
Sassanyan murmushi na sakar mata Ina shige wa cikin dakin, kaya na cire na shiga wanka.
Haka muka wuni dukan mu suku suku yau din, a haka har akai sati muka koma yadda muke Basma kuma ta koma gida sbd hutun su ya kare.
******
Ina jingine a jikin kitchen cabinet Ina candy crush a waya ta Oga Kona ya shigo.
Kallona yake yana tande baki kamar tsohon maye, shi dai kullum yana mamakin wannan yarinyar tun da ta fara aiki tare da su shekara 3 kenan bai taba ganin ta ba Hijab ba, yana fatan wata ran ya ganta ba hijab shiyasa yake yawan fado wa kitchens din a mafi yawon lokaci a nasa tunanin ko tana aiki zata cire hijab din amma kullum cikin sa take bata cire wa.
Sauke wayar nai daga fuskata na kalle sa nace “Oga wani abu kake soh?”
Murmushi yai yace “yess shawarma zaki hada guda biyu ynxu da banana smoothie ki kai table din vip zaki ga mutane biyu kiyi sauri plz sabin customers neh”.
Daga masa kai kawai nayi na shiga aikin hada musu abubuwan, cikin 20mins na gama komai na d’ora akan tray madaidai ci ba riko na tafi gurin VIP din.
A saman restaurant din yake guri ne da yake a rufe ba wanda zai gan ka kuma ba hayaniya ko kadan.
A nutse nake tafiya a hankali Ina Jin yadda zuciya ta take wani irin bugu da karfi.
Table din da mutum biyu suke kai na nufa, ba tare da na yadda na kalle su ba na ajiye tray din.
Bude idon sa da yake lumshe yai cike da gajiya sbd jin kamar kamshin ta yake ji fah, a nutse ya sauke lumsassun sexy eyes dinsa akan ta kuma akai sa’a ita ma ta d’ago cikin tsautsayi idon su suka sarke dana juna.
Ido na zaro da mamakin ganin wannan mara kunyar yaron, sai dai kuma nayi kokarin dai dai ta kai na Ina danne bacin rai na na juya a nutse na sauka zuciya ta na bugawa.
Mai da idonsa yai ya lumshe cike da wani irin yanayi da baxai ce gashi ba.
Kallon sa Mushabu yai yana murmushi yace uhmm abokina kaga kawar ka koh?
Bude idon yai ya zubawa Musbahu yana yamutsa fuska kamar yaga kashi, gajeran tsaki yai kawai ya janyo shawarma ya fara ci a hankali.
Lumshe idon sa yai yana sakin wani siririn murmushin daya tsaya iya lips dinsa, in yace tun da yake a rayuwar sa bai taba cin shawarma mai dadin wannan ba bai yi karya ba.
Shi da yake fushin Mushabu ya janyo sa restaurant sai gashi ya cinye nasa ya kuma dau na Musbahu da bai ci ba yana danna waya ya cinye.
Banana smoothie din ya dauka ya kora yana lumshe idonsa cikin nutsuwa, amma sai yaji shawarmar bata ishe sa ba sam kuma.
D’ago war da Musbahu zai yi yaga tray din wayam sai paper din da akai wrapping shawarma kawai.
Zaro ido yai yana kallon Abdallah da mamaki yace “Ina kayan suka tafi?”
Tabe baki yai kawai yana goge bakin sa da tissue.
Ashar Mushabun ya danna masa cike da takaici, yunwa suke ji gaba dayan su tun safe ko breakfast basu yi ba Abdallah din yaja shi suka shiga zagye supermarket dinsa don lura da komai yana tafiya dai dai, sai da kyar Mushabun ya roke sa suka zo nan din su dan ci wani abu kafin su karasa gida su ci abinci kuma sai yaga wayam.
Ya bude baki zai yi magana Abdallah yai saurin tarar numfashin sa da cewa plz gaya musu su karo wani.
Tsaki kawai Musbabun yai kafin yaje ya fada aka wo guda uku, suna zaune aka kawo da sauri Abdallah din ya dauki daya ya fara ci sai dai gutsira daya yai ya cire yana yamutsa fuksa.
Kallon Oga Kona yai daya zo don yana farin cikin yadda sabbin customers din suka ce a karo musu shawarma din sai Murmushi yake yai.
A dakile yace “wannan ba irin wancan bane”.
Dan sosa kai Oga Kona yai yace “uhmm eh ai da yake ita wacce ta kawo muku na dazun ita ce tayi kuma ynxu lokacin tashin ta yayi ta tafi gida sai gobe”.
Kara hade rai yai sosai yana kicin kicin da fuska yace “ka kira ta Kace ta dawo ynxu Ina bukatar shawarma din”.
Zaro ido Oga Kona yai yace “ita Aasmaa din zan cewa ta dawo ynxu”.
Tsaki Abdallah din yai yana zira hannu a aljihun sa ya fito da bandir din 500 sabbabi ya ajiye akan table din.
Da sauri Musbabu yace “kana da hankali kuwa Abdallah, akan shawarmar 1500 zaka bada 50k”.
Juyar da kan sa yai gefe yana tsotsar harshen sa, abinci sam bai dame sa ba yafi cin abubuwan kwadayi kuma kowa ya san sa yasan soyayyar sa da shawarma da Kaza baya iya fushi da su a rayuwar sa.
Da rawar jiki Oga Kona ya danna wa Aasmaa kira, sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka.
Kasa da murya yai yace “kina Ina Aasmaa kin tashi bayan baki fada min ba, kiyi maza maza ki dawo customers na bukatar shawarmar ki alkhairi ne yake kiran ki”.
Yamutsa fuska nai nace “Oga gaskia nayi nisa bana jin zan iya dawo wa ai Salma na nan kasa tayi musu mana itama ai ta iya”.
Kara marairaice murya yai yace “ai Salma din ta musu amma suka ce batai musu ba, kinga Aasmaa ki dawo plz in kika musu 15k zan Baki wallahi kuma ba’a salary din ki be”.
Tabe baki nai ai in har ni zan yi wa wannan mara kunyar yaron shawarma ya dade shi Oga Kona din bai bani 15k ba, wata tsanar yaron ce kawai ta shige ni tun wulakancin daya min wancan satin kuma na kasa manta wa kullum na tuno abin sai idona ya ciko da kwallar takaici.
Jin batai magana ba yasa cikin sarewa Oga Kona ya kalli Abdallah daya tsare sa da ido yace “sir taki yadda kuyi hakuri ko zuwa gobe kawai”.
Hannu ya mika masa alamar ya basa wayar.
Ba musu ya basa ya sa wayar a speaker
Cikin husky voice dinsa yace keeee baki da kunya koooohhh……..
Jama’a ku jawa wannan yaron kunne da naga alama ya rai na mu da yawa🤨
Comments nd share please
Mrs A.M🥰
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 11
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Zaro ido nai da mamaki nace “wane yaron ne kuma haka da bai iya magana da manya ba…”
Bude manyan idonsa yai yana wani munafikin murmushi yace “uhmm yaro manya keee waye tsa’anki wai…”
Tsaki na naja da karfi nace “naga alama kan ka na hayakin balaga bani da tym din ka karami” na kashe wayar Ina kara jan tsaki.
Shiru yai fuskar sa na soma ja sbd bacin rai, shi wannan yarinyar zata dinga cewa tashar balaga, bama wannan ne yafi damun sa ba illa kalmar yaro da take dangan tasa da ita.
D’ago idonsa da suka rine zuwa ja sbd bacin rai yai ya zubawa Musbabu su wanda yayi tagumi yana kallon ikon Allah.
Ganin kallon sa ma kawai Mushabu yake bashi da niyyar rarrashin sa akan wannan cin mutuncin da aka gama masa yasa shi kawai mike wa a fusa ce ya sauka.
Da sauri Oga kona ya bi sa da