Showing 6001 words to 9000 words out of 61405 words
sa wani iri wannan abin ya rage musu walwala sosai.
A wani dare wanda yana daya daga cikin dararen da Maimuna baxa ta taba manta wa dashi ba.
Tsakiyar dare ne cikin bacci taji kamar ana mata waiwayi a ciki, a hankali ga bude idonta.
Sai da gabanta ya fadi ganin Ahmad zaune yana shafa cikin cike da kulawa da tsantsar soyyaya.
Da sauri tayi kokarin mikewa sai dai yadda cikin ya mata nauyi sai ta kasa, shi ne ya taimaka mata ta mike zaune tana dan bude kafafun ta yadda zata ji dadin zaman.
Kallo fuskar sa tai cikin damuwa tace lafia kuwa Yaya har ynxu baka yi bacci ba gashi wajen 3.
Murmushi kwance a fuskar ta yana shafa cikin ta yace kawai bana jin baccin ne, yau ji na nake cikin wani irin farin ciki Maimoon(sunan da yake kiran ta in har yana cikin farin ciki)
Itama samun kanta tai da Murmushi cike da Jin dadin yadda yace mana yana cikin farin ciki.
Hira sukai sosai kamar ba dare bane in da yake ce mata in mace ta haifa ta sa mata Maimuna in kuma Namiji ne Abdullahi sunan Baban sa, sai turo baki take tana ce masa da kansa zai sawa dan sa suna In Sha Allah.
Kallon ta yai ganin 4 tayi ya umarce ta da tayi alwala suyi sallah, shi y jasu suka yi yayi musu addua sosai, suna hawa gado ya janyo ta jikin sa duk da yadda yake jin tsinkewar zuciya amma haka ya daure suka raya sunna.
Bayan sun samu nutsuwa wanka sukai a tare suka zo, kwanta da ita yai yana shafa kanta a nutse yana karanta mata Suratul Baqara har sai da yaga tayi bacci sannan shima ya kwanta yana mai sauke ajiyar zuciya.
Zuba mata ido yai hawaye masu zafi suna zubo masa, a jikin sa yake jin mutuwa zai yi shiyasa yake matukar tausayin Maimoon din da kuma dan da zasu Haifa, sai kuma Iyar sa wacce bata da koya sai shi da Bilki.
Lumshe idonsa yai yana maimaita kalmar shahada a hankali har bacci ya dauke sa.
A hankali ta shiga bude idon ta tana dan yamutsa fuska ganin haske daya shigo ta jikin window, da sauri ta mike duk da nauyin da jikin ta yai, tasan waye mijin ta baya son ya makara sallar asuba, kuma tunda taga bai tashe ta ba alamun cewa shima ya makara kenan.
Zagayawa tai ta bangaren sa ta shiga tashin sa sai dai shiru, tsoro ne ya fara shigar ta a hankali ganin yadda ya sandare ya kara wani irin haske sosai akan wanda yake da shi fuskar sa dauke da Murmushi.
Da mugun gudun da batayi tunanin zata iya ba ta kirawo Bilki, itama ta rude sosai da kyar dai Bilki din ga fita ta kirawo gate man.
Shine ya lullube fuskar Ahmad yana share hawaye ya fada musu Ahmad ya cika(Allah kasa mu cika da Imani Ameen).
Wannan maganar tasa ta tayar wa da Maimuna hankali don labour ne yazo gadan gadan, da taimakon Bilki aka fitar da ita zuwa mota amma ta kasa cewa komai sai ajiyar zuciya take saukewa.
Baza ta iya haihuwa ba dole CS aka mata aka ciro mata baby boy dinta.
Lokacin data farko tayi arba da son din nata rungume sa tayi tsam tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kamanin sa gaba daya na Ahmad ne don duka kyaun Ahmad ya dauka har ma ya dara sa.
Da aka sallame su ma gidan ta ta koma acan Iya ta zage take kula da ita da jaririn daya ci suna Abdallah.
Sai da tayi arba’in sannan iya ta koma Mambila, taso tafiya da Bilki amma suka hade kai ita da Maimuna suna kuka akan su fa anan gidan zasu zauna tare dole Iya ta kyale su, sai dai daga bangaren Maimunan an turo mata kakar ta suna zama tare.
Shekarar Abdallah biyu Sani ya fito da muradin sa na auren Maimuna, tashin farko ta ki amincewa a cewar ta wannan kamar cin amana ne ga marigayi.
Da kyar dai aka samu ta amince aka yi auren ta tare gidan Alh Sani.
Matar sa ta farko itace Hafsa suna kiran ta da Mummy tun farkon basa shiri da Mummy don tana mata hassada na yadda mijin ta ya fi nata mijin arziki.
Ba karamin hauka tayi ba da Alh Sani wanda suke Kira da Alhaji y fada mata zai auri Mami, har yaji tayi sai da ta tabbatar da an daura auren ba yadda zatayi sannan ta dawo lokacin tana da yarinyar ta Waleeda wacce ta girmi Abdallah da shekara daya.
A ynxu Mami (Maimuna) yaran ta uku da Alhaji sani Fatima wacce suke kira Faty mai shekaru 22, sai twins sultan da Sultana masu 13 years.
Mummy kuma tana da Yara uku itama, Waleeda wacce ynxu tayi aure hadda yaron ta sai Yusrah mai 18 years sai auta Aryan mai 10 years shi sunan masa ma ya bata don kowa Auta yake ce masa.
Zaman su ba yabo ba fallasa ita dai Mami bata shiga harkar Mummy sai ta kama taja mutuncin ta sosai, hakan da Mummy ta gani ne yasa itama ta share Mamin.
Abdallah
Matashin saurayi mai shekaru 24 a duniya, dogo ne sosai mai faffadan kirji wanda ya wadatu da kwantacciyar gashi mai laushi bakikirin.
Yana da jiki dai dai mitsali wanda ya taimaka gurin dai-dai ta tsayin nasa, fari ne sosai amma mai ja yana da fuska mai kyau wacce take dauke da manyan sexy eyes masu zaiba zaiba, sai dogon hancin sa wanda y dace sosai d fuskar tasa, yana da karamin baki masu siraran lips jajaye kamar wanda yake sa musu jambaki.
Yana da suma irin ta Fulani mai kyau da sajen da ya kara kawata fuskar sa, yadda yake kashe wa sumar da sajen nasa kudi ne yasa kullum kaga gashin zaka ga yana kyalli da daukar ido.
Miskili ne na karshe don zaku iya zama da shi tun safe har dare ba tare daya ce miki ko kalma daya ba, son girma ne dashi kamar gembo shiyasa bai cika zama a cikin kannen sa ba a hausar sa kar su raina shi.
Yana da kirki kuma yana da kyauta sosai sai dai mutuncin nasa ba kowa ne ya san da shi ba ko dan yadda yake mara son magana sai mutane da dama suke masa kallon mai girman kai.
A Ynxu yana level 4 a university inda yake karantar Computer Science.
Tun da ya gama secondary school Alhaji Sani ya saka shi a harkar kasuwancin babansa, don an dade da raba gadon yana juya masa ne kawai, kuma da y lura yaron yana da hazaka da kuma fahimt gashi duk abinda ya taba sai Allah yasa masa albarka sai kawai ya tattara dukiyar sa gaba daya ya damka masa tare da basa shawarwarin yadda zai gudanar da kasuwancin nasa.
Da taimakon Alhaji Sani da kuma Uncle Usman lawyer din babansa ya shiga kara bunkasa kudin, manyan supermarkets guda biyu ya bude a kano, bisa shawara ale Alhaji ya siya katon fili a Abuja ya gina wani a Garki Area 1.
Manyan mutanen daya fara kasuwanci dasu ne suka tallata masa siyan Estate a Abujan tare da fada masa yadda ake samun kudi a harkar.
Sai da yayi shawara da Alhaji da Mami da kuma Uncle Usman duk suka basa goyon baya sannan ya siya manyan estate har biyu, daya a Maitama daya a Apo.
Dabarar da yayi sai yasa kudi masu dan dama nan da nan kuwa aka Kama haya wasu kuma suka siya, bai tsaya harkar filaye da gidaje ba har gidan Mai ya bude ya kuma siya Manyan shaguna a kwari ya zuba kaya a ciki.
Kudi ne na fitar hankali sai dai ba kowa ne yasan haka ba don boye kan sa yake, a school dinsu ma bai san ya akai suka sani ba shi dai kawai ji yai ana ce masa young billionaire.
Yan mata da suke son sa yawa gare su, wasu ma iyayen su ne suke takowa takanas har gidan su samu Alhaji ko Mami sai dai ita Mami kai tsaye take ce musu yana da Mata already ai MEENA.
Comments nd share 🙏
Mrs A.M
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 6
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Meena yarinyar Bilki ce Kanwar Baban Abdallah kuma aminiyar Mami, ita kadai ce yar Bilki wacce tare sukai aure ita da Mamin.
Baban ta mai kudi ne shima don Custom ne kuma babba ne, yar gata ce ta gaban kwatance a wajen uwar ta, bata hada farin cikin Meena dana kowa.
Meena farar bafullata na ce wacce take Kama da Abdallah don itama kyakkyawa ce sosai tana da kyaun fuska mai daukar hankali, budurwa ce mai shekaru 22 a duniya wacce take amfani da kyaun ta gurin gara kan samari.
Meena budurwa ce mai iyayi da mugun jiji da kai, ta dauko halayen mahaifiyar ta gurin son ganin cewa tafi kowa, sai dai abinda yake damunta duk wannan kyau nata bata da structure mai kyau, tsayi kawai yake da shi amma duk wani abu na cikar mace ita komai nata karami ne don siririya ce sosai, shiyasa Bilki wacce suke cewa Aunty take siyo mata abubuwan ciko tana sawa, wannan ya taimaka gurin kara iyayen Meena don Jin kanta take dai dai da kowa.
Tun bayan rasuwar Ahmad Mami da Aunty sukai alkawarin in har Bilkin ta haifi mace zasu hada su aure kuma sai Allah ya amsa musu ta haifi macen, dukan su sun san da zancen auren nasu daga Meena har Abdallah.
Meena wannan auren da zata yi da Abdallah yasa kanta yake kara girma zata auri young billionaire, ko ac cikin friends ta dinga hura hanci kenan tana fadin Abdallah nata ne ita kadai.
Shi dai Abdallah kawai ya karbi zabin Mamin ne ba wai don yana son Meena din ba ko kuma ta masa kawai ya yadda ne don baya son Mami ran ta ya baci, amma shi sam bata masa ba bata cikin tsarin macen da yake so sannan shi baya son ma farar mace yafi son baka.
A yadda su Mami din suke so shine in Abdallah din yayi masters dinsa lokacin Meena din itama ta gama Uni sai ayi musu aure.
Meena bata ji don tana taba soyayyar shan minti da samarin ta, duk da maganar auren Abdallah kowa ya sani amma haka take samarin ta sai dai tana boye wa Faty kanwar Abdallah kuma bestyn ta.
Yusrah
Yusrah yarinyar Mummy ce ta biyu kamar yadda kuka sani, shekarun ta 18 yarinya ce mai kyau fara tana da kyau, kyaun bahaushe farar fatar da take da ita ta taimaka sosai gurin kara fito da kyaun ta kuma duk gidan ita kadai ce fara don su Faty duk chocolate colour ne sai kuma Abdallah da yake fari.
Yarinya ce mai hankali da nutsuwa mara son hayaniya, bata dauko bakin halin Mummy ba don ita tana son yan uwanta sai dai ita Faty bata wani cika shiga harkar Yusrah din ba don basa shiri da Mummy.
Tun da ta tashi take kaunar Abdallah, son ta ya shiga cikin jinin ta kuma bata san lokacin da hakan ta faru ba, kawai dai ita ta ga tana son sa ne da kaunar sa ta girma a zuciyar ta sai dai tasan samun nasa abu ne mai wuya duk da kuwa nata cire rai ba kullum cikin addu’a take Allah ya bata Abdallah in alkhairi ne shi in kuma ba alkhairi bane Allah ya c cire mata son sa amma kuma kullum kara son sa take haka yasa ta dage da addu’a.
Musbahu
Aminin Abdallah ne gidan su yana jikin gidan Alhaji sani, makaran tar su daya daga boko har Islamiyya hakan yasa suka shaku sosai, tun Abdallah yana share sa sbd miskilancin sa har ya sake ya dawo yana kula sa duk da yawancin hirar tasu Musbahu ne karfin ta.
Aminin kwarai ne Musbahu sun shaku da yan gidan sosai har ba wanda bai san gidan Musbahu ba mutuncin da ke tsakanin Abdallah da Musbahu yasa gidajen biyu suma suke zumunci sosai.
*Cigaban Labari*
Sai da Musbahu ya leka dakin yaga Abdallah na bacci sannan ya shiga toilet yayi wanka, Kayan sa da suke wardrobe din Abdallah yasa ya kwanta shima a gefen Abdallah yana chatting a wayar sa yau a gidan yake son kwana kuma ya fadawa Ummin sa dama ya saba kwana a gidan shiyasa ma yake da kaya a wardrobe din Abdallah din.
Abdallah din ne dai bai cika zuwa gidan su Musbahun ba har sai yayi fushi sannan yake zuwa.
*******
A palo nake kwance idona yana lumshe Ina tunanin rayuwar mu, Basma da Umma na bari a daki su kwana a kan katifar ni kuma na dawo palon na kwanta.
Idona a lumshe nake tunanin rayuwar mu, mu hudu ne a gurin Umma, Yaya, ni, Umar sai Maryam.
Mun tashi cikin rufin asiri don Baban mu kayan masarufi yake siyar wa a kasuwan singa yana da Sharon sa dan karami da yake siyar da Kayan sa.
Da akwai soyayya sosai tsakanin mu bama ni da naci sunan Maman sa.
Shekarar sa 16 da rasuwa Ynxu don a shekarar da aka yi bikin Yaya ya rasu.
A lokacin abubuwa da dama sun zo mana da wuya kuma munsha wuya sosai, tym din Ina Ss 2.
Shagon Baba wanda shi ne kawai mallakin mu sai gidan da muke ciki Kawu laminu Kanin baba yaso ya karbe, Umma bata tsaya kunya ko wani abu ba fa fadawa Liman din unguwar mu wanda yake Aminin Baba kuma mahaifin Hajjo.
Shine ya karbe shagon daga hannun kawo Laminu ya bayan hawa duk karshen wata ana kawo mana kudin, da kudin muke rayuwa Umma kuma tana da siyar da kosai da safe tayi shinkafa d wake da yamma sai awara da daddare.
Aikin baya mata wahala don kusan komai ni nake yi, Maryam tayi yanke yanke Umar kuma yayi wanke wanke shi.
Tym din data gama secondary school taso matuka ta shiga university sai dai kuma kudin mota da abubuwan da za’a kashe yasa kawai ta shiga catering school.
Tana gama wa kuma Allah ya taimaka ta ta samu aiki a wani hotel, duk da albashin ta bashi da wani yawa amma kuma yana taimaka musu sosai shima.
Wannan aikin data fara Kawu ba karamin zagi tasha a kai ba lokacin shekarun ta 22 yace taki aure ta tsaya karuwanci an fake da aiki.
Tasha kuka sosai sai dai Umma ta kwantar mata da hankali akan kar t daga hankalin ta ita ta yadda da ita tasan kuma In sha Allah baxa ta bata kunya ba.
Maryam na da 19years aka kawo kudin ta, kudin da sai da Aasmaa ta yi kamar zata zane ta sannan ta yadda aka kawo amma kullum cikin kuka take zata yi aure ta bar Yayar ta wacce lokacin take da 24years.
Auren Maryam ya sa Aasmaa cikin kadai ci sosai, duk da kasancewar ta miskila amma Maryam din taka rawa gurin rage masa wasu damuwar da take da ita tunda Umar namiji ne kuma shima miskilin ne.
A lokacin kuma ta kara shiga wani catering school din, da ta gama ne ta samu aiki a restaurant din da take ynxu da taimakon wata class mate dinsu.
A ynxu Aasmaa tana da shekaru 29 a duniya, tun da take kuma saurayi bai taba tsayar da ita wai da maganar so ba, duk wanda zai zo gare ta toh fa Jan zuwaira ke kawo sa, ita kuma bata kasa a gwiwa take korar su wannan yasa Kawu kullum yake cewa ta tsaya zaban mai kudi shiyasa take koran samarin ta.
Kabir mijin Hajjo ne kawai yazo da maganar aure da gaske, ita kuwa yadda take ji ai ko maza sun kare a duniya baxa ta auri Kabir ba.
Ita fa ko ba Mijin Hajjo bane to yayi mata karami don Hajjon ta taba fada mata shekarar sa 34 shekara 5 kenan kawai ya bata, toh ta aure sa tace ta auri sa’an ta sam baxai yi ba, tafi son babba kamar 45 zuwa 50 haka sune dai dai ita a ganin ta don bata son rai ni gwanda ta auri Wanda ya girme mata sosai….
Aasmaa chocolate color ce wacce take da wani irin daukar ido da sheki, don tana kula da fatar ta sosai tunda basu da arzikin da zata siya mayukan gyaran fata masu tsada sai take siyan kayan gyaran jiki yake yin abinda duk karshen wata kamar so biyu.
Tana da manyan ido masu dauke da black eye ball, bata da dogon hanci can sai dai kuma ba gajere bane dai dai yake wanda ya dace da round face dinta sai karamin bakin ta mai kala biyu, lip din kasan light pink ne sai na saman kuma yayi dan duhu kadan.
Tana da cikar suma sosai don tun daga cikar gashin girar ta zaka gane haka, kanta yana da tsayi sosai har tsakiyar bayan ta kuma yana da cika sai dai ba wai laushi ne dashi ba yana da dan tauri bata sa masa relaxer.
Bata da tsayi sosai kuma baza a kirata da gajeriya ba, tana da dan jiki a cike take sosai tana da wasu irin manyan boobs masu daukar hankali da tsokale idon mai kallon su, sai kasanta daya baje sosai hips dinsa suka fito ras da mazaunan ta da suka kara kawata surar tata, shafaffen cikin ta ya taimaka kwarai gurin barin shape din ta fito wa sosai, shiyasa kullum zata fita cikin Hijab take ko Ina zata kuwa don ita bata ma siyan mayafi sai Hijab.
Aasmaa miskila ce kuma mara son rai ni yadda take da shekarun nan yasa bata sakin fuska don kar a rai na ta.
Ynxu Yaya nada 34 years sai Aasmaa mai 29, Umar 27 sai Auta Maryam mai shekaru 24(Ashe ma sa’ar Abdallah ceh🤫)
Lumshe idonta tai bayan ta gama wannan tunanin tana dan matse kafafun ta, yana daga cikin dalilan da yasa bata son yana yin sanyi da d’anima tana matukar wahala da sha’awar dake damun ta.
Kara matse kafar tana jin kamar zatayi hauka, lumshe idonta tai kuma a karo na farko da inhar tana cikin wannan yanayin hawaye mai zafi suka shiga zubo mata……
Tohhh Alhamdulillah munji Asalin Abdallah da Aasmaa ynxu sai mu