Showing 3001 words to 6000 words out of 61405 words

Chapter 2 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3797

Ina da kallo yai so yake ya bude baki ya tambaye su ina Mami amma bakin ya masa nauyi kawai sai ya nufi hanyar dakin nata.


Ajiyar zuciya Yusrah ta sauke da karfi bayan wucewar sa, tun da ya shigo gabanta yake faduwa don har sai data matse remote din dake hannun ta da karfi sbd yadda zuciyar ta take bugawa.


Allah ya dasa mata son Yayan nasu har bata san yadda zata yi ba gashi ita dai ba zata iya fadawa Mummy ba don tasan kashe ta ne kawai baxa ta yi ba.


Yadda Mummy din suke zaman kishi da Mami tasan abu ne mai wuya su amince wa auren su da yayan nasu, bama wannan ba in har sun amince shi zai yadda kuwa?


Wannan tunanin ne yasa taji wani hawaye mai zafi ya zubo mata da sauri ta mike ya fita daga palon, garden dinsu taje ta zauna ta hada kai da gwiwa tana kuka mai tsuma zuciya..




**
Kallon sa Mami take tana Murmushi, yaron nata kullum girma yake sake yi yana zama cikakken saurayi, a yadda yake dinnan ba wanda zai yi tunanin shekarun sa 24 sbd girman jikin sa tsaf sai kace ya kai 30.


Yar dariya ta saki tace “toh Abdallah na zama sirikar kane, kana zaune amma kayi shiru tun dazu kan ka a kasa”


Idonsa dake lumshe ya bude yana bude baki da kyar yace …….










Comments nd share please🥹








Mrs A.M🥰
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj


🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa


🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
Mrs A.M


Free book neh 🥰




Page 3




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Idonsa dake lumshe ya bude yana bude baki da kyar yace “Mami na dawo daga school neh”


Cire tagumin da tai tayi tana kallon sa yadda yake maganar da kyar kamar wanda yake ciwon baki, ita da take mahaifiyar sa har yau baya iya zama da ita yayi hira sosai, dama in kaji maganar sa toh yana tare da Musbahu neh aminin sa ko kuma Iya kakar sa wacce ta haifi Baban sa itama don dole take sa shi magana ba wai don yana so ba.


Gyada kai tayi tace “ina ta zuba ido tun safe ai kazo kayi breakfast sai ce min akai ka fita”.


A hankali yace “uhmm test mukai neh kuma Ina son na sake karatu a school”.


Murmushi tai tace “Allah ya taimaka toh ya bada sa’a”.


A kan lips dinsa taga ya amsa ba tare da sautin muryar sa ta fito ba.


Ita dai kallon sa kawai take miskilancin sa yana damun ta.


Mikewa yai tsam ya dawo kusa da ita, kwanciya yai ya dora kan sa akan cinyar ta idonsa rufe .


Itama bata sake masa magana ba sai hannu data sa tana sosa masa gashin kan sa.


Sun fi 10 minutes ba Wanda yayi magana har ta cire rai da maganar tasa taji yace “Na siya estate a Abuja Mami, Ina son zuwa ko weekend ne na duba”.


Shiru yai yana mar mar da bakin sa kafin yace “uhmm in yana bukatar gyara sai ayi mutane sun fara neman sa koh”


Fara’ar tace ta dadu sosai cikin murna tace “Masha Allah, Allah ya kara dauka ka yasa kafi haka”.


A hankali yace “Ameen Mami”


Bude kofar dakin akai wata matashitar budurwa ta shigo hannun ta rike wayar ta tana dannawa, birki taja ganin Yayan nasu kwance ya daura Kansa akan cinyar Mami.


Juyawa tai zata fita taji yace “kee”.


Sai da Kayan cikinta suka juya sbd tashin hankali, ita wallahi sam bata san yana cikin gidan ba da abinda zai sata fito wa sai ya fita.


Kamar zatayi kuka ta juyo tana takowa a hankali, tsugunna wa tai kanta a kasa tana jiran mai zai ce mata.


Mikewa yai daga cinyar Mami din ya tsaya yana zura hannayen sa a aljuhun wandon sa, sexy eyes dinsa ya zuba mata yana karantar ta.


Tsaki yai yana girgiza kai wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne dannen sa.


Kofar dakin ya nufa sai da ya bude zai fita yace “ki duba wayar ki” daga haka ya fice.


Nannuyan ajiyar zuciya ta saki tana mike wa, kallon Mami tai a tare suka fashe da dariya, miskilancin Abdallah yawa gare sa.


Cikin dariya Faty tace “wai Mami da ya bude baki yayi min magana gwanda ya turo min message tab lallai besty tana da aiki a gaban ta wallahi”.


Wayar ta bude tana zama a gefen Mami, message ya turo matan kuwa kamar haka


“Kar ki kara jawo min wannan yarinyar kuzo dakina, in ba haka sai na karya ku”.


Baki ta rufe da sauri tana zaro ido, kallon Mami tai tace “Mami wai ni da besty zai karya sbd jiya data zo tace sun dade basu hadu ba muje dakin sa su gaisa fah kuma Wallahi a bakin kofa kuma tsaya muka yi knocking”.


Tabe baki Mami tai tana mikewa tace “ke kika so ni dama ai na fada muku bana son ku dinga yawan zuwa dakin sa, amma bakya ji”.


Turo baki tai a shagwabe tace “amma Mami itace fa wacce zai aura meye a ciki don taje ganin sa”.


Hararar ta tayi tana wucewa toilet tace “in aka yi auren ai sai tayi ta shiga dakin nasa amma ynxu ba”


Bin bayan Mami da kallo tai tana Gyada kai, ajiyar zuciya ta sauke tana cewa lallai besty ta hadu da aiki wallahi.




Shi kuwa Abdallah daya fito garden ya nufa kasancewar gurin yana matukar burge sa yasa yake yawan zuwa gurin yana zama.


Sheshekar kuka yake ji a hankali wanda yana hankalin sa ya shiga ciki sosai don ganin wace take kuka haka.


Bayan ta kawai ya kalla ya gane ita ce, dazu daya shigo ya dan kalle ta hakan yasa ya shaida Kayan ta, kafe ta da ido yai yana kallon ta kawai, yarinyar tana da hankali sosai shiyasa suke dan shiri don wani lokacin har murmushin saman lips dinsa tana gani.


Shi dai kuma haka kurin jinin sa ya hada dana yarinyar ko hantarar ta baya shi don tausayi ma take basa yadda take shiru shiru dinnan ko yaushe zaka ganta cikin nutsuwa.


Gyaran murya yai da dan karfi wanda ya janyo hankalin Yusrah ta juyo gare sa.


Saurin mikewa tai tana goge hawayen idon ta, sai da ta gama goge wa tsaf sannan ta sunkuyar da kai cikin rawar jiki tace “ina wuni Ya Abdallah”


Daga kai yai kawai yana tsare ta da ido, cikin taushin muryar sa yace “ke mene kike kuka?”


Da sauri ta dago ta kalle sa zuciyar ta na tsalle sabon son sa yana mamaye zuciyar ta, cikin inda inda tace “umm physics test ne na fadi shine nake kuka”.


Karamin tsaki yai kawai yana kallon ciyayin da suke koraye shar mamaye da garden din, murya a dakile yace “dauko na koya miki”.


Zaro ido tai tana bude baki da mamaki tace “Ya Abdallah zaka koya min da…..” kallon daya mata ne yasa ta rufe Baki da sauri ta fyalle a guje zuwa part dinsu don dauko book din nata




Mummy dake zaune taga Yusrah ta shigo a guje ta shige dakin ta.


Ganin ta fito hannun ta rike da books tace “keh lafia Ina zaki”.


Tsayawa tai tana sosa gashin girar ta, cikin murya kasa kasa tace “Ya Abdallah ne yace nazo ya koya min physics”


Tsaki Mummy tai tace “ban hana ki wai shige ma wancan yaron ba, bana son tarayyar ki da shi Ina sake maimaita miki ki shiga hankalin ki wallahi”.


Kan ta a kasa idonta na kawo ruwan hawaye tace “Mummy karatu fah zai koya min kawai”


Tsaki Mummyn tai tana juyar da kan ta, ita dai tasan koma meye in ma wani abu Yusran taje sakawa a ranta Toh wallahi baxai sabu ba.


Ganin Mummyn ta juyar da kanta yasa yusrah fitaa a guje tana sakin Murmushi yau Abin kaunar ta zai koya mata karatu..






******


Aiki muka sha sosai, duk na hada gumi ga shi nice shugabar su a kitchen din.


Kafin azahar mun gama komai an ajiye a gefe, tsaftace kitchen din da yar barandar dake bayan kitchen wacce muke wanke wanke a gurin.


Sallah muka yi sannan muka dawo kitchen, tuwon shinkafa da miyar taushe na daura sai sakwara da miyar agushi.


Har na gama na zuba a inda muke zubawa ake ajiye wa in kazo siya a ma a microwave ba’a zo daukar abincin ba.


Fita nai na wanke fuskata na gyara hijab dina duk na hada gumi.


Ina zaune Ogan mu yazo yasa aka fara fita da abincin ana sawa a mota.


Sai da aka gama sakawa wadan da zasu je suyi rabo suka shiga motar, Ina daga zaune Ina kallon su so nake kawai 5 tayi na tafi tunda na gama abinda zanyi da wuri nake son tafiya Gida yau.


Ogan namu ne yazo ya tsaya a kai na yana bina da wani kallo irin kallon dana tsana kenan.


Murmushi yai yace “Aasmaa yau ma baxa ki taimaka kije ayi rabon da ke bah”.


Hade rai nai Ina juya Kai na gefe nace “bana son zuwa kaga ni aiki na a kitchen yake bare acee”




Murmushi yai yace “da kin taimaka dai kin je kin sa ido tunda kinga kece babbar su koh”


Mikewa nai Ina rike jakata a hannu na da kyau nace “maybe next time Ynxu kam bana ra’ayi Gaskia”


Wuce wa nai gate don nama fasa jiran 5 din tayi.


Bin bayan ta da kallo yai yana lasar baki, shafa gemun sa yai yana fadin Allah ya kai damo ga harawa








Comments nd share please🥹






09066728387




Mrs A.M🥰
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj


🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa


🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
Mrs A.M


Free book neh 🥰




Page 4




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






Sallama nayi daga bakin kofa na shiga cikin gidan, Umma bata tsakar gida nasan wata kila tana daki ko toilet.


Dakin na shiga sai dai bata ciki haka yasa nayi sauri na chanja kaya, fito wa nai na dora mana abincin dare.


Ina zaune Ina Candy crush Umman ta fito daga toilet.


Dago Kai nai na kalle ta Ina murmushi nace “Ina wuni Umma”.


Murmushi tai tana zama a gefen tabarmar tace “lafia qalau, ai Ina Jin sallamar ki nace yau da wuri kika dawo kenan”.


Dariya nai Ina gyara zama na don na dan jingina da bango nace “Umma mun gama duk abinda zamuyi shine kawai naga me zan tsaya ai gwara na taho koh”.


Daga Kai tayi tace “tabbas kuwa, tunda kin gama dama mai zaki jira neh”.


Muna hira jefi jefi har na gama mana dan waken da nayi, namu na zubo mana Wanda zamu ci nida Umma ynxu ragowar kuma na zuba a flask.


Sallamar Yaya da naji yasa na dago da dan sauri Ina bude manyan idona.


Yaya ce kuwa sai babbar yar ta Basma wacce har ta zama budurwa ma don shekarar ta 15, sai autan ta wanda take goyen sa Walid.


Murmushi kwance a fuskata nace “wa nake gani kamar mutuniyar”.


A guje Basma ta taho ta rungume ni, nima rungume tan nai tsam cike da kaunar ta, Ina son yarinyar sosai kamar yacce take sona don ni na yaye ta.


Tabe baki yaya tai tace “toh sai me don an rungume wata mu an bar mu a shanye”.


Dariya nai Ina Kama baki nace “Yaya abin kuma hadda haka”.


Zama tai akan tabarmar da Umma take zaune tai tana cewa “oho dai kuma Ina kallo dan wake ne dole a zubo min naci”.


Murmushi nai ina juyo ragowar dan waken, tare muka hadu duka muka ci walid na kan cinya ta Ina basa yana ci.


Da muka gama ci Basma ce ta dauki plates din taje ta wanko su, daukar Walid dake kan cinyata tai ganin ya fara bacci ta shiga daki da shi.


Kallon Yaya nai nace “ai da nasan zaki zo dana fadawa Maryam itama tazo ai”.


Dariya tai tace “na fada mata sai ce min tai ita baxa ta zo ba don tasan in har tazo baxa ki yadda kije gidan ta ba”.


Kallon Umma nai dake sauraren mu nace “Umma kina ji dai koh”.


Itama Umman dariya tai tace “ai da gaskiyar ta Aasmaa ayi mutum shi sam baya son zuwa gidan yan uwan sa”.


Shiru kawai nayi don nasan duk yadda zan yiwa Umma baya ni baxa ta fahimce ni ba.


Hira muka sha sosai sai bayan isha’i sannan ta tafi ita da Walid, Basma kuma hutu zata mana.






*******
Kara hade ran sa yai tam yana yatsina fuska, baya son takura amma ya lura yarinyar nan bata da hankali sam.


Musbahu da yake kallon sa dariya ya kara kyalkyalewa da ita hadda faduwa kasa.


Tsaki Abdallah yai yana kifa wayar akan hannun kujerar don ma kar ya ga yadda take haske


Fuska a hade ya kalli Musbahu da yake ta zanga dariya, Kara tamke fuskar nan yai sosai har sai da ta fara ja-ja.


Kokarin sai ta kansa Musbahu yai amma duk da haka murmushi ne kwance a fuskar sa, cikin tsokana yace haba angon Meena, ka daga wayar mana tana ta kira amma ka wani share ta.


Irin kallon da yake wa Musbahu kadai zaka gani kasan cewa lallai ransa a bace yake sosai, girgiza Kai kawai yayi yana dan saussauta fuskar sa a nutse yace “ni sa’an kane Musbahu”.


Dariya Musbahu yai yace “kwarai kuwa har na ma baka wata 5 sai dai kuma in a harkar kudi ne kasan ance Yaro da kudi abokin tafiyar manya”






Kuyi min uzuri yau plz da kyar na samu nayi wannan




Comments nd share plz






Mrs A.M🥰
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj


🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa


🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
Mrs A.M


Free book neh 🥰




Page 5




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Tsaki Abdallah yai yana mikewa kawai ya shiga dakin sa tare da banko kofar.


Dariya sosai Musbahu yake yi hadda kwanciya, yasan ya gama kule abokin nasa shiyasa ya mike kawai ya dauki wayar sa ya fita.




WAYE ABDALLAH




Asalin su yan Mambila neh, Iya kakarsu ce wacce ta haifi babansu, su biyu ne a wajen Iya da Ahmad sai Bilkisu.


Allah yayi ma mahaifin su rasuwa tun bayan haihuwar Bilki, iya bata sake aure ba ta zauna tana kula da yaran ta, kuma Alhamdulillah basu sha wuya ba kasancewar mijinta ya rasu ya bar musu dukiyar shanu da gonaki.


Lokacin da Ahmad ya gama diploma dinsa a jalingo sai ya ke fitar da albarkacin gonar su gari gari, ganin yafi kasuwan cin ya dan fi karbuwa a kano sai ya kasance in yaje can bayan ya siyar da Kayan gonar sai ya sari atampopi ya dawo dasu jalingo din ya siyar, a haka har ya koma harkar dillanci.


Shima daya lura da irin albarkar da kasa take da shi sai kawai ya koma Mambila sukai shawara da Iya aka raba musu gadon su, Gonar sa daya kawai ya bari amma ya siyar da komai ya taho da kudin kano.


A lokacin barayi sun yi kokarin sace masa kudin sa don har sun ritsa shi Allah ya kawo Sani gurin wanda yake dan taba rashin ji a zamanin.


Sun san ko waye shi sai suna tsere, tun daga nan abota ta kullu tsakanin Ahmad da Sani har dai Ahmad ya fada masa abinda yake son yi na siyar filaye da gidaje.


Da yake harkar Baban Sani kenan sai abin bai zowa Ahmad da wuya ba, Baban sani kuwa ya tsaya Akan gaskiyar sa ya koya wa Ahmad yadda zai gudanar da kasuwan cin sbd shima yaji dadin yadda sanadiyyar Ahmad din Sani ya shiryu.


Ai kuwa Allah ya sawa abin albarka cikin lokaci kankani kudi sun fara zamar masa, har ya gina gidan sa. Da shawara Baban Sani din ya bude shaguna a kwari ya bayan da haya.


A kuma lokacin Allah ya hada sa da Mami wato Maimuna, da farko ya ji tsoro don Baban Maimuna babban likita ne a AKTH.


Zuwan sa na farko gidan su Maimuna din hankalin sa ya kwanta don Baban nata karbar mutunci yayi musu shida Sani daya raka sa, ya tambaye shi game da asalin sa bai boye masa komai ba ya fada masa.


Shima kuma cikin dattako ya fada ma Ahmad yaje garin su ya fada wa iyayen sa suzo ayi maganar aure don tun kan ya basa izinin zuwa zancen sai da yayi bincike a kansa.


Da murnar da yaje ya fadawa Iya itama taji dadi sosai, ba bata lokaci manya suka sa shiga maganar har suka yi aure.


Zama suke mai kyau da tsafta don ba karamin son junan su suke ba, zuwan su Mambila na farko tare ya taho da Bilkisu wacce Iya tace da bata yadda ba sam bazai tafi da Bilkin ba, yadda ita bata zauna da Kanwar miji ba itama Maimuna din bata zauna da su ba gudun matsala.


Da kyar dai Maimuna ta samu ta shawo kan Iyan bayan ta nuna mana ba wani matsala wallahi, ba dai a san ran iya ba suka dawo da biki din, don itama da ya so dauketa ta murzawa idonta toka tace ita da barin Mambila sai dai in ziyara zata kai musu amma In sha Allah kabarin ta a Mambila yake.


Zaman Maimuna da Bilki abun sai sam barka, don cikin lokaci kan kani suka yi wata iriyar shakuwa.


Bilki tana zuwa B.U.K don yin degree dinta, kuma tana da kokari sosai, bata da fara’a sosai kuma mace ce ita mai son komai ace ita ce a gaba kuma ta iya.


Zaman su da Maimuna ba matsala don ita Maimunan ta iya zama da mutane shiyasa ta San yadda zata zauna da Bilkin ba tare da sun dinga samun matsala ba.


Arzikin Ahmad sai dai ace Alhamdulillah don kuwa kudi kullum zuwa suke, haka kuma kullum cikin sadaka yake, duk ranar juma’a haka mutane suke taruwa a kofar gidan sa yana muku sadakar kudi inda Maimuna kuma take fitar da jallof din shinkafa d wake a hade a cikin takeaway ake sawa ana rabawa, wannan dabi’a tasu ta janyo musu soyayyar al’umma sosai.


Shekarar su biyu da aure Maimuna ta samu ciki, fadar irin murnar da suka shiga bata baki ne, sai dai kuma tunda cikin ya shiga wata tara suka rasa gane kan Ahmad, yawan walwalar sa ta ragu kullum cikin tunani yake.


Wannan abin ya daga hankalin Maimuna da Bilki, sunyi juyin duniya ya fada musu abinda yake damunsa yace bkm kawai yaka yake jin jiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login