Showing 54001 words to 57000 words out of 61405 words

Chapter 19 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3781

ido tace “Auntyna tana so na shine take min wainar flour”.


Dan hade rai yayi yace “ni bata so na kenan koh”.


Da sauri ta waro ido tana rufe baki ta kalle ni tace “Aunty ba ruwana wannan maganar ke zaki bada amsar ta”.


Satar kallon sa nayi naga yadda ya zuba min ido yana murmushi kawai nima sai na saki Murmushi ina kallon sa, shaf mun manta yusrah tana gurin kallon juna kawai muke muna Murmushi.


Yusrah kallon su take tana jin wani irin zafi a zuciyar ta, tabbas kishi gaskiya ne duk irin yadda take kokarin rike kishin ta ashe don basu cika haduwa su uku bane a guri daya, daga kallon da suke wa juna zaka fahimci tabbas ba karamin soyayya suke wa junan su ba.


Hawayen daya zubo mata tayi saurin goge wa tana karanta addu’a a zuciyar ta har lokacin kuma kallon juna suke yi cike da kaunar da bakunan su baxai fadu ba.


A nutse ta sauko tayi dan tafi tana Murmushin yake, cikin tsokana tace “kaga masoya irin wannan kallo haka gaskiya bara na baku waje” ta fada tana yar dariya kawai ta sa kai ta fice daga kitchen din.


Ajiyar zuciya na sauke duk sai naji ba dadi kallon sa nayi Ina dan langwabe kai nace “kaga ni koh, ka tsattsare ni da ido bayan tana zaune baxa taji dadi ba, bana son na zama sillar motsawar kishin ta don Allah”.


Ajiyar zuciya ya sauke yace “baxan taba yin abinda zai sosa zuciyar kanwata Ina sane ba sbd tana da matukar daraja da kima a idona bara na bi bayan ta sa min wainar flour din na tafar mata da shi”.


Saka masa nayi na zuba yaji a gefe na basa ya tafi duk rai na ba dadi muna zaman mu cikin farin ciki, dan Murmushi nayi sbd ni ma rai na ya dan sosu da yadda ya fadi matsayin ta a gabana lallai kishi bala’i neh.


Koma wa nayi gurin Hajjo muka cigaba da hira ban bata fuskar da zata min maganar Yusrah ko Abdallah ba ita ma ganin ba fuska sai tayi shiru bata ce ba.


A dakin ta ya same ta ta fito daga toilet tana goge fuskar ta da towel idon ta yayi ja alamun kuka tayi.


Kallo daya ta masa ta dauke kai kamar bata gan sa ta zauna a gefen gado tana shafa aboniki a kafafun ta da suke dan mata zafi.


Durkusa wa yayi a gabanta ya karbi man zafin yana shafa mata, bai ce mata komai ba sai da yaga ya shiga toilet ya wanko hannun sa sannan ya kawo wainar ya Mika mata.


Murmushi tayi tace “na koshi”.


Zama yayi a gefen ta yace “plz kanwata kar ki ce fushi zaki yi da yayanki uhm”.


Zaro ido tayi tace “akan me zanyi fushi da kai Yaya me kayi min”.


Girgiza kai kawai yayi yana kallon ta, cikin sigar lallashi ya shiga fada mata maganganu dake nuni da yadda yake daraja ta da ganin kimar ta ya karasa da fada mata matsayin sa a zuciyar ta da wadannanan kalamun nasa ta sake har tana murmushi.


Sai azahar Hajjo ta tafi bayan taci abinci.


Ina sallah na shiga kitchen ni da Binta muka shiga aiki, tuwon semo nayi da miyar alayyahu sai Zogale da na hada na kuma yi kunun aya, dukkan abin da na dafa sai da na zuba wa Yusrah na ba wa Binta ta kai mata.


Karfe 6 na shiga part dinsa yau special gyara nayi masa don yau fa karshen hakuri na ya kare gaskiya ko romance ne sai anyi.


Kayan abincin na dauka na kai na jera a part din sa a gurguje na dawo nayi wanka na shirya cikin Riga da wando na Pakistan, nayi kyau sosai Kai na da yake tsefe na taje na shafa masa mai sai kamshi yake.


Sai da nayi wa jikina barin turare sannan na dauki wayata na fito na nufi part din sa gabana yana dan faduwa.


Yana zaune akan dining da alama serving kansa zai yi.


Murmushi na sakar masa na dan durkusa nace “Barka da yamma an dawo lafiya”.


Ware ido yayi da mamaki ganin wai yau shi Husna take durkusawa ta gaishe sa, kasa gasgatawa yayi sai da yace “wai ni kika durkusawa da gaske?”


Wani kallo na masa Ina mike wa na shiga serving din sa abincin.


Ya zage ciki kuwa yaci sosai kwadan zogalen ne dai yace na bar sa in ya dawo daga sallar isha’i sai muci tare.


Kunun ayar dai sai da ya kusa shanye sa sannan ya ajiye ya nufi palo.


Kwashe plates din daya bata nayi na shiga kitchen na wanke komai sannan na dawo na zauna a palon nima ina kallon TV duk a matse nake ji nake kamar na tashi na koma kusa da shi amma Ina daure wa.


Zaman kurame muke yi kowa da abinda yake saka wa a ran sa, sallar isha ne ya tashe ni na koma part dina.


Kankana na dauko a fridge na yayyanka ta na zuba madara da zuma sai dabino da na bare, sai da na cika cikina dam da shi sannan na mike na nufi sama yau nayi alkawarin a part din sa zan kwana in sha Allah.


Wanka nayi na musamman na shafa mai, jikina nabi da humra masu kamshi sosai sannan na dauki rigar bacci ta iya cinya ce mai siraran hannu, kunya ce ta kamani dana tuno wai duk wannan abin da nake yi sbd Wanda ya ke sa’an autar mu ne sai nayi saurin kawar da tunanin na zira rigar ban sa bra ba don dama bani iya kwanciya da ita.


Powder na sa da kwalli nasa lipstick fari na kara bin jikina da turare.


Hijab na sa na dauki swt na sa a baki na ban dauki waya ta ba tun da dama a cike take sai na ajiye ta kawai na dauki karamar na fito bayan na rufe dakina da key na boye a dayan dakin.


Sai da safe nayi wa Binta na dauki flask din dana dafa masa tea na nufi part din sa.


Yana zaune yana kallon ball na shigo baki na dauke da Sallama, a hankali ya amsa yana bina da wani kallo cike da mamakin ta.


Zama nayi a gefen kujerar da yke zaune nace “sannu da hutawa”.


Lumshe idonsa yayi yace “yauwa Noorie”.


Nima lumshe nawa idon nayi nace “na zubo ma tea din ne”.


Da sauri ya tashi ya kashe TV yace “no bacci nake ji sai da safe” ya shige daki ya bar kofa a bude, zagaye ya shiga yi a dakin yana addua Allah yasa ta shigo sai leke yake yaga ta taho amma tana xaune.


Ni kuwa shiru nayi Ina tunanin na bisa dakin ne ko kar na bisa amma azahar da nake ji a kasa na na tabbatar yau in ba an sosa min ba baxan iya bacci ba.


Ajiyar zuciya na sauke gabana yana faduwa ina tsoron azabar dana ci wancan lokacin haka dai na daure na nufi dakin gabana yana faduwa.












DijahAM
09066728387
I You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 36




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






Yana ganin tahowar ta yayi tsalle ya tafi gado a sukwane ko jallabiyar jikin sa bai cire ba ya kwanta yaja bargo ya rufe jikin sa shi ala dole bacci yake yi.


A sanyaye na shigo dakin ina tuno abinda ya faru da ni wancan karan, rufe kofar nayi na lumshe idona.


Na dan jima a tsayen kafin na sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya na shiga tako wa zuwa gurin gadon.


Sai da na hau sannan na cire Hijab dina na ajiye akan bed side drower.


Da sauri Abdallah ya mike yana rintse ido da karfi don wallahi yadda yaga surar ta ba abinda zai hana shi danne ta.


Cikin rawar baki yace plz Noorie ki fita don Allah kar na saba alkawarin dana daukar miki baxan iya jurar ganin ki a haka ba don Allah ki taimaka min ki fita.


Duk sai naji ba dadi ganin cewa hakkin sa ne amma yake nisanta kansa da karba kawai don ya nuna min cewa da gaske yana sona ba wai jikina yake so ba.


Mike wa nima nayi cikin nutsuwa na shiga tako wa har na iso gare sa, ban yi wata wata ba kawai na fada jikan sa.


Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke yana rungume ni tsam a jikan sa ji yake kamar ya fashe da kuka ko zata tausaya masa ta fahimci irin son da take masa.


Cikin rawar murya yace “Allah ne shaida ta NOORUL HAYAT ina matukar kaunar ki wallahi ba sha’awar ki nake ji ba tun ranar dana fara ganin ki nake matukar son ki ina boye wa ne kawai sbd a da ban san yadda zan nuna ina son ki ba duba da cewa….”


Hannu nasa na rufe bakin sa n dago ina kallon idon sa, lumshe masa ido nayi nace “ba sai ka fada min ba iya abinda nake ganin a idon ka ma kawai ya ishe ni hujja”.


Manne bakin mu yayi yana bata wani kalar kiss mai zautar da mutun, ban san lokacin dana shiga mayar masa da martani ba cike da wani salo da ya kusa zautar da shi.


Soyayya muke gwadawa juna a aikace gaba daya bama hayyacin mu baki baxai iya buduwa ya fadi abinda muke ji akan juna ba amma aikin mu ya nuna.


Kalar soyayyar da yake gwada min ta tsaya min a rai sosai ta kuma Kara min wata zazzafar kaunar sa da kishin sa a rai na.


Lokacin da yake karanto addu’a sai da na kusa ture sa amma na daure na bar sa ko dan ya samu cikakkiyar nutsuwa, ba karamar wahala nasha a hannun sa ba wai a haka ma don yana sassauta min ce a cewar sa amma ni kuwa na ji jiki.


Da kansa ya gasa ni yau ban hana sa ba sai kukan shagwaba nake yi yana biye min yana jera mun sannu, rungume da juna bacci ya dauke mu.


Shi ne ya tashe mu sallar asuba, sai da na gasa jikina sannan na kuskure baki na mouthwash tun da bani da brush a dakin duk kuwa da ina gani wasu sababbi a cikin drower ban dauka ba.


Salla nayi kafin ya dawo na gyara gado amma yana dawo wa ya dauke ni cak muka koma kan gadon yana kara laluba ta.


Ynxu kuwa kuka na masa sosai sannan ya rabu da ni sai hakuri yake bani ni.


Wanka muka yi ya kwanta bacci ni kam ban koma ba duk da yadda nake jin jiki haka a daddafe na gyara masa part din sama sama na koma part dina.


Breakfast na mana na koma sama nayi wanka na shirya na sauko na dauki breakfast din na Kai masa part din sa.


Yinin ranar tare muka yi sa duk inda nasa kafa ta yana biye da ni ko fita bai yi ba duk kuwa da yadda Musbahu ke danna masa kira.


Kwana biyun na nayi na girki na mun yi sane cike da bawa juna wata soyayya mai zafi, a kwanakin nan da nayi da shi na fara karantar sa na jinjinawa Yusrah yadda bata tayar da hankalin ta ba da ya auro ni.


Ni yau da zan fita daga girki wani irin kishin sa nake ji bana in na tuno duk abinda yake min shi zai yiwa Yusrah da kyar na samu bacci ma ya dauke ni bayan nayi sallah don dana kwanta tuno sa kawai nake yi Ina hasaso haka yake kashe Yusrah ma da wannan kalar soyayyar.


Soyayya muke gudanar wa mai kyau da tsafta, ya siya min mota iri daya ce da wacce ya siya wa Yusrah color ce kawai ta banbantasu, ya chanja min waya mai tsada komai dai sai dai nace Alhamdulillah.


Na kara cika na yi kyau sosai kowa y ganin yasan Ina cikin kwanciyar hankali, duk ranar weekend ya yamma muke fita ni da shi yana koya min mota, Yusrah yace ta bari ta haihu sbd cikin ta da ynxu ya shiga wata biyar.


Shirye shiryen azumi ake wanda muke fatan gobe ne za’a dauki azumin, ban taba fita ba tsawon wata biyar dinnan sai yau da yace mu shirya anjima zai zo ya dauke mu zamu je gidan su.


Tun da ya fada min haka ban zauna ba na fito da naman da yake freezer na shiga aikin dambun nama, ban taba haduwa da Sirika nawa ba duk da nasan baxan taba kamo matsayin Yusrah ba tun da ita yar su ce amma zan so nima ace na samu fada dai, sau daya kannan sa suka taba zuwa Sultan da Sultana sai Auta kanin Yusrah.


Kafin 2 na gama lafiyyar fried rice da potato salad sai kunun aya da na yi ga dambun nawa, sai kayan snacks.


Duk na dibar wa Yusrah na bawa Binta ta kai ma don tun da cikin ta ya shiga wata biyar ba abinda bata ci kuma cikin yazo mata da ci sosai.


Wanka nayi na shirya cikin lifaya yellow mai tsada da taushi a lefena take duk da ban san kudin ta ba amma nasan zata yi tsada.


Ina cikin fesa turare ya shigo yasha manyan kaya sai kamshi yake.


Murmushi na sakar cikin wani salo na shiga tafiya Ina zuwa daidai shi na fada jikinsa a hankali yadda nasan cewa balloons din zasu taba sa yaji su sosoi.


Ya kuwa ji sun don Lumshe ido yayi ya riko waist dina sosai, sunkuyo da fuskar sa yayi dai dai fuskata yana shinshinar kamshin dake tashi a jikina.


Dariya nayi na raba jikina da nasa nace “ba ruwana Hub kar ka bata min kwalliya ta”.


Lumshe idon sa yayi yace “Noorie ko kiss ne plz ki bani mana”.


Dariya nayi nace “sannun ka Hub da ban san ka bane dai”.


Shima dariya yayi, a tare muka sauko flasks din na dauki wasu na basa wasu ma sannan Binta ta rike wasu muka fito tare.


Baya na bude na shiga don yau girkin Yusrah ne kuma shine fitar da zamu fara yi mu uku a tare.


Ina zaune na hango su sun taho yana rike da ita tasha kwalliya cikin doguwar riga ta kara kiba wacce ta mata kyau, sai Murmushi take da alama wata maganar yake fada mata da ta mata dadi sosai.


Lumshe ido nayi kishin sa yana taso min ina addu’a don na danne sa.


Bude mata yayi ta shigo muka gaisa tana min godiyar abincin da Binta ta Kai mata.


Hira muke yi jefi jefi gabana yana faduwa ina Jin tsoron tarbar da zan samu daga sirikata..












DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 37




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






Tun da muka shiga cikin gidan gaba na yake faduwa a hankali, addu’a kawai nake yi.


Yusrah cikin farin ciki ta fito don tayi kewar gida sosai duk da dai bayan sake auren Yayan nata tazo har sai biyu amma ynxu kusan wata biyu kenan.


Cikin sanyin jiki na fito su Sultana da suke zaune a compound din gidan suna ganin mu suka taso a guje suka zo suka rungumw ni, Nima rungume su nayi Ina tambayar su ya school.


Su ne suka dauko kayan abincin da nayi suna min hira har muka isa part din Mami.


Da Sallama na shiga idona ya sauka cikin nata tana zaune cikin shiga ta alfarka sai Murmushi take mana.


Da sauri na sunkuyar da Kai na kasa har muka karasa cikin palon, cikin girmamawa muka gaishe ta ta amsa mana kuwa ba tare data nuna banbanci ba.


Kallon Yusrah Mami tayi tace “sannu Yusrah Allah ya raba lafiya”.


Sunkuyar da Kai tayi sai mune muka amsa da Ameen.


Kallona tayi tace “sannu Aasma ya gida”.


Kara sunkuyar da kai na nayi nace “lafiya qalau Mami”.


Murmushi tayi tace “Allah yayi muku albarka Toh”.


Gaba dayan mu muka amsa wannan karon, mun dan jima tana mana nasiha sannan tace na mike nabi Yusrah mu gaisa da Mummy.


Tare da Yusrah muka je part din Mummy nan ma ta karbe mu cikin fara’a sosai, na dan zauna kusan 30mins sannan nayi mata Sallama na koma part din Mami.


A nan na tarar da Teema a zaune tana cin mat pie din da nayi.


Gaisawa mukai yau dai bata min rashin kunya ba ko kunkuni ba yabo ba fallasa muka gaisa.


Godiya sosai Mami tayi min da abincin dana kawo masu, ni dai Murmushi kawai nake.


Tun ina shiru tana ja na da hira akan girki har na ware nake fada mata ai abinda na karanta kenan, da yake itama Mamin tana da baiwar girki sai gamu muna hirar abubuwa da yawa har na ware.


Sai wajen la’asar Yusrah ta shigo muka cigaba da hirar da ita sai gashi shima.


Mun dade muna hira har aka Kira sallah yace mu shirya ana idar da sallah a masallaci zamu tafi.


Bayan mun shirya tafiya Mami ta bamu leda mai dan girma nida Yusrah kowa daya daya.


Kallon Yusrah tayi tace mu tafi gurin Abba tare yncu Abdallah din shima zai zo.


Bayan fitar su ta kalle sa tayi masa nasiha sosai akan adalci sannan tace “kayi kokari kana iya boye soyayyar da kake yiwa Aasma a gaban Yusrah don Allah Abdallah, ina lura da kai a zaman ku gaba daya sai kallon ta kake kana Murmushi amma zan iya irga sau nawa ka kalli Yusrah shima sai in tayi magana ne”.


Cikin sanyin jiki yace “In sha Allah Mami zan cigaba da kiyaye wa ki taya ni da addu’a”.


Addu’ar ta masa sosai sanna ya fita lokacin har mun fito daga gurin Abban shima ya mana nasiha.


Shima shiga yayi gurin nasa bai dade ba ya dawo muka tafi, tun da muka shigo unguwar mu nake kallon sa ban tabbatar da unguwar mu bane dai da yayi parking a bakin layin mu.


Kallon sa nayi ta mirror nace “Hub da gaske gidan mu ka kawo ni”.


Lumshe ido yayi yace “ku zo muje mu gaishe da Umma zamu biya ne muyi siyayyar azumi”.


Sosai Umma taji dadin zuwan mu don ta rasa inda zata samu, bamu dade sosai ba muka fito ta bamu Kuka da daddawa nida Yusrah da yawa har da hawaye na da zamu fita.


Daga nan supermarket din sa muka je kowa ya dauki abinda yake so don ya fada mana dama tun ranar farko ta ramadan har karshe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login