Showing 51001 words to 54000 words out of 61405 words
da skirt na lace Wanda ya kama ni sosai ya min kyau, rigar daga sama ta kama ni sosai har balloons din ana hango su, na saka siririyar sarki mai heart da dankunnen ta sai kamshi nake yi.
Zama nayi Ina jiran dawowar su don ya fita kai Yusrah asibiti da zasu fita yazo ya fada min bata Jin dadi zai kai ta shine nake jira in sun dawo naje na mata sannu.
Binta tana kitchen tana yanka min carrots don yau danderu nake sha’awar ci Ina so nasa carrots kuma a ciki.
Bude kofar da aka yi ne yasa ni kallon mai shigowar.
Shine ya shigo yana sanye da riga da wando farare kar wanda suka masa kyau matuka, lumshe ido na nayi wani wutar kaunar sa tana kara ruruwa a zuciya ta.
Ji nake kamar na tashi na fada jikin sa kawai ko na huta da azabar da nake ji.
Kamar wacce aka tsikara kuma na bude idona na zuba masa sai Murmushi yake yi, mike wa nayi tsaye cikin wani salo na kasa kasa da murya nace “barka da rana”.
Murmushi yayi yace “barka kadai Noorie”.
Juya ido nayi wanda ni kai na ban San lokacin da nayi sa ba sbd jin dadin sunan sa yake kira na dashi, kallon sa nayi kasa kasa nace “ya mai jikin?”.
Murmushi ya saki sosai ynxu yace “tana lafiya qalau ai abin murna ne ma Alhamdulillah Ya Rabb”.
Kallon sa nayi cikin rashin fahimta.
Murmushi yayi yace “kun kusa zama iyaye in sha Allah nan da 6 months”.
Ware ido nayi cikin murna nace “ciki ne da ita?”.
Dariya yayi yana daga min Kai.
Nima sai nayi karamar dariya nace “Allah ya raya ya kuma sauke ta lafiya”.
Murmushi ya Kara saki yace “Ameen Ya Rabbi bara na je gurin nata dama cewa nayi bara nazo na fada miki mun dawo”.
Gyada kai nayi nace “nima in sha Allah anjima zan shiga”
Murmushi kawai ya saki yana bin ta da kallo ta kasan ido, shi kadai yasan abinda yake ji ya fara tunanin karya alkawarin sa gaskiya don ya gama fahimtar Husna kashe sa take son yi kawai.
Ni kuwa ganin irin kallon da yake min yasa ni juyawa na nufi kitchen Ina wata tafiya dana tabbatar zata tayar masa da hankali, ta kuwa tayar din don baya yayi sbd wani jiri daya ji ya kwashe sa.
Lumshe ido yayi yana sauke wata wawuyar ajiyar zuciya, sai da ya dan nutsu sannan ya fita daga part din.
Dandarun ma tsaya nayi na dibar ma Yusrah sai lemon kankana dana mata na zuba mata a jug, sama na koma nayi wanka don duk kamshin spices nake yi na zira abaya maroon color wacce tayi min kyau sosai, bata da ado ko kadan sai jela da take da ita wacce ake daure wa, mayafin abayar na yafa ma dan fesa turare sama sama tun da gurin mai karamin ciki zami zai iya yuwa bata son kamshi sosai.
A basket na zira flask da jug din na dauka na nufi part din ta gaba na yana dan faduwa sbd tun haduwar mu da ita lokacin da Ina gyara part din mai gidan bamu sake haduwa ba.
Door bell na danna ban dade a tsaye ba mai aikin ta tazo ta bude min.
Sa kai na nayi a ciki a hankali Ina cire takalma na daga bakin kofa, a takaice na karewa Kayan palon kallo komai irin nawa ne banbancin color kawai da kuma wasu frames din.
Zama zanyi akan kujerar mai aikin tace min na hau sama suna palon sama, kamar dai kar na hau sai kuma na mike Ina tunanin ai tunda tace na hau maybe sun fada mata ne.
Hawa na shiga yi tun da kafata ba takalmi ba lallai suji takowa ta ba, sai da gabana ya fadi sbd yadda na gansu, suna zaune akan kujera daya ita ta kwantar da kan ta ne akan hannun kujerar hannun ta rike da goro tana ci shi kuma ya daura kafafun ta akan cinyar sa yana matsa mata a hankali.
A tare suka jiyo suka kalle ni da mugun sauri Yusrah ta janye kafafun ta daga kan cinyar Abdallah, saurin da tayi sai da Abdallah ya riko ta yace yi a hankali Wifey plz kar kiji ciwo.
Murmushi kawai tayi tana kallon Aasman da take takowa a hankali, Murmushi nima nake sakar mata duk kuwa da irin zafin da kirji na yake min.
Zama nayi akan kujerar dake kallon wacce suke nace “kuyi hakuri plz yarinyar data bude min ce tace na hawo so nayi tunanin ku kuka bata izinin haka”.
Murmushi Yusrah tayi tace “bkm Aunty Ina wuni kwana da yawa”.
Nima murmurshi na mata nace “lafiya qalau Yusrah ya jiki jiki Allah ya raba lafiya”.
Sunkuyar da Kai tayi cike da kunya sai shine ya kalle ni yana murmushi yace “Ameen Noorie”.
Dan satar kallon sa Yusrah tayi Jin sunan daya Kira Aasmaa da shi sai dai gudun shedan ya raya mata abu mara kyau tayi saurin addua a ran ta tana tuna wa kan wa matar sa ya fada wa haka fah ba wata ba.
Basket din na dan tura mata nace “ga shi kanwata danderu ne nayi sai na zubo miki da lemon kankana”.
Murmushi tayi tace “Ngd sosai Aunt Allah ya saka da alkhairi”.
Murmurshi nima nayi nace “Ameen ya Rabbi, duk abin da kike so dai plz ki fada min kin ji kinga muna kusa sai da dafa miki in sha Allah”.
Da sauri Yusrah ta girgiza Kai tace “haba Aunty bkm wallahi wannan ma na gode”.
Zungurin ta Abdallah yai cikin zolaye yace “kee kanwata waya fada miki ana kin abincin Noorie da kika ganin ta haka babbar chef ceh”.
Zaro manyan idon ta yusrah tayi tana tabe baki tace “Amma Yayana baka taba dan kafco min a leda ka kawo min ba”.
A tare muka sa dariya gaba dayan mu Ina jin wata nutsuwa wacce tun da na shigo ban ji irin ta ba.
Kallona Abdallahn yayi yana Langwabe Kai yace “ynxu Noorie shi wannan kayan dadin Wifey kawai kika kawo wa ni ban da ni kenan”.
Kallona Yusrah tayi cikin dariya tace “Aunty Kice nawa ne ki kadai plz muga yadda Yaya zai yi da bakin cin nama”.
Dariya nayi nace “na kanwata ne kadai gaskiya”.
Turo baki yayi kamar yaro ya juyar da kai gefe yace “dama ai bakya sona baxa ki bani ba”.
Wani irin faduwa gaba na yayi ban san lokacin da na ce masa “ni nace bana son ka”.
Kallon da ya min yasa ni gane baranbatamar da nayi sai na waske Ina Murmushi kawai.
Nayi wajen 30mins muna hira wanda karfin hirar Yusrah ce da Abdallahn ni sai dai nayi Murmushi kawai ko na ce eh ko a’a .
Mike wa nayi nace “bara na tafi Yusrah me kike so amma zuwa anjima sai nasa a kawo miki”.
Shiru tayi alamun tunani kafin ta dago ta kalle ni tace “wainar fulawa Aunty”.
Yar dariya nayi nace “yncu kike so ko kuwa zuwa anjima”.
Murmushi tayi tace “ko yaushe ne Aunty”.
Mike wa Abdallah yayi yace “wifey bara na dan taka mata”.
Daga masa Kai tayi tana kwantawa akan kujera.
A tare muka sauko mun jeru muna tafiya a hankali, sai da muka isa har kofar part dina sannan ya tsaya ya kalle ni yace “Ngd sosai Noorie”.
Tsayawa nayi na juyo na kalle sa Ina sarke hannu na nace “akan me kake min godiya”.
Murmushi yayi yace “yadda kika nuna kulawa akan wifey ban yi tunanin haka ba”.
Tsare sa nayi da ido cikin wani kallo nace “me yasa baka yi tunanin zan iya kula da ita ba?”
Langwabe kai yayi yace “sbd ni bakya nuna kin damu da ni Noorie, don Allah kiyi hakuri ki yafe min wallahi kin hora ni da yawa baki ga yadda na rame ba wai ki tausaya wa Kanin ki”.
Wata katuwar harara na sakar masa nace “kar ka kara cewa kai kanina ne Abdallah lokacin da ka min fata fata ai baka tuna cewa na girme ka ba”.
Kasa kasa da murya yace “ki bani wata damar Allah a hankali zan yi”.
Da sauri na kalle sa cikin mamaki nace “me zaka yi din….”
DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 34
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da sauri na kalle sa cikin mamaki nace “me zaka yi din”.
Kasa kasa da murya yayi yace “na sake shiga gurin Allah a nutse zan yi kin ji Noorie nah”.
Girgiza kai nayi da sauri na bude kofar Ina cewa “baka da kunya Allahu ya shirya ka”.
Murmushi yayi yana dafe saitin zuciyar sa a hankali yace “ina matukar kaunar ki fiye da yadda nake son Kai na Heartbeat..”
Ni kuwa Ina shiga ciki rufe kofar nayi da sauri Murmushi yana subuce min, a rai na Ina tunanin na fi sa son mu kasance tare amma kuma ban san yadda zan fada masa ba…..
HAJJO
Yau wata daya kenan da aka kawo mata amarya gaba daya ta rikice ne komai tana yin sa cikin rashin nutsu wa har ynxu ta kasa yadda cewa Kabeer ne ya Kara aure.
Ba wai yana rashin adalci a tsakanin su ba yana iya bakin kokarin sa amma kawai ita gani take yi duk ranar da ya kasance girkin amaryar rawar jiki yake yi.
Gashi amaryar ta zo ne da wani kissa na jan yaran ta a jiki, kullum suna gurin ta sbd in suka je sai abinda suke so take dafa musu gashi har homework ynxu ita take musu.
Ta dake su akan su dai na zuwa gurin amaryar amma sun ki ji kullum suna dawowa daga makaranta Kaya kawai suke chanja wa zasu tafi gurin amaryar in kaga basa gurin ta to tayi baki ne Ko kuma baban su yana nan.
Ita Ynxu babbar damuwar ta shine yadda zata yi kokari su shirya da Aasmaa don tana so taje ya bata hakuri, tayi ta kokarin kiran ta amma bata shiga wanke take tunanin ko blocking din ta tayi.
Bata bata lokaci ba taje har gidan Umma ta bata hakuri akan abinda suka zo suka musu ita da Ummu, Murmushi kawai Umma tayi mata tace mata ya wuce In sha Allah ita dama bata rike ta ba.
A gurin Umman ta karbi address din gidan Aasmaa ta tambayi Kabeer bai hana ta ba kuwa ya amince don shi kan sa ynxu zai so Aasmaa ta hakura ta cigaba da kula Hajjon ko dan yadda HAJJO ta zama ynxu duk ba nutsuwa ko yaushe a birkice take.
Washe gari kuwa karfe goma tayi wanka ta shirya Kabeer ya sauke ta a kofar gate din gidan ya tafi bayan ya bata kudin motar dawowa yana fatan komai yayi dai dai tsakanin ta da Aasmaan.
Tun da Hajjo ta shiga gidan take bin gidan da kallo da tsananin mamakin wai anan Aasmar tayi aure, part din Yusrah ya shiga mai aikin Yusrah ce tace mata ba nan ne part din Aasmaa din ba, tare suka fito da Hajjon ta kai ta har bakin part din Aasmaa sannan ya tafi.
Binta ce ta bude kofar tana kallon Hajjon tana mata Murmushi, shigowa ciki Hajjo tayi ta zauna akan kujera.
Ruwa da lemo Binta ta kawo wa Hajjo akan tray sannan tace “bara na Kira ta tana sama”.
Murmushi kawai Hajjo tayi tana gyada kai tana bin palon da kallo cike da mamakin wai nan duka na Aasmaa ne.
Ina kwance a daki ina chatting da Maryam Binta tayi knocking, mike wa nayi na bude mata kofar nace wani abunne Binta
Daga kai tayi tace “Aunty bakuwa kika yi tana kasa”.
Da mamaki nace “bakuwa kuma?”
Gyada Kai tayi, juya wa nayi cikin dakin nace “kice mata ina zuwa”
Ban yi wanka ba don haka na shiga toilet a gurguje nayi wanka na fito na shirya cikin Riga da zani, ban wani yi kwalliya ba powder kawai na shafa sai lip-balm mai danko.
Waya ta na dauka na fito, tun kan na karaso nake kallon Hajjo da mamaki sosai, tana sanye da Hijab kuma fuskar ta ba kwalliya shine abin da ya bani mamaki.
A sani na da Hajjo bata sa Hijab sai zata yi sallah kuma kullum fuskar ta bata rabuwa da kwalliya mai sauki har ta haihu kuwa, so tari muna shan fada da ita in zamu fita taga nasa Hijab dole nayi mamaki yau ita ce sanye da Hijab.
Hajjoo kuwa kallon Aasmaa take cike da sha’awa ganin yadda tayi bul bul tayi kyau sosai sai kamshi take yi.
Murmushi nayi Ina dafa kujerar da take gefen tata nace “wa nake gani kamar Hajjo”.
Dariya tayi cikin kunya tace 0nice Aminiyar”.
Dan kallon ta nayi jin sunan data kira ni da shi, sai nayi Murmushi kawai na zagayo na zauna, Binta na kira ta kawo mata kayan gara su dubulan a cikin wasu bowl masu kyau data dora akn tray.
Sai bayan Binta ta shige dakin ta sannan na kalle ta nace “sannu Hajjo ya gida da yarana”.
Tabe baki tayi tace “yaron ki suna nan lafiya qalau, gida kuwa sam ba dadi ko baki da labarin Abba ya kara aure ne”.
Murmushi nayi nace “to ke ynxu Hajjo don Kabeer ya kara aure sai ki wani daga hankalin ki, kalle ki fa don Allah kamar ba Hajjon dana sani ba”.
Girgiza kai tayi idon ta na ciko wa da kwalla tace “baxa ki gane bane wallahi Aasmaa amma ni kadai nasan abinda nake ji a zuciya ta gaba daya Kabeer hankalin sa baya kai na ynxu kar kiso kiga yadda yake rawar kafa duk ranar girkin ta”.
Murmushi nayi nace “Allah ya kiyaye”.
Kallona tayi galala tace “abinda zaki ce kenan Aasmaa”
Kallon ta nayi nace “to me zan ce Hajjo”.
Gyada Kai tayi tace “ni duk ba ma wannan ne ya kawo ni ba zuwa nayi na baki hakuri akan abinda na miki don Allah kiyi hakuri ki yafe min Aasmaa mu koma kama da don Allah”
Murmushi nayi nace “Hajjo kenan maganar na yafe miki ni tuni na Riga na yafe miki, amma batun mu koma kamar da baxai taba yiwu wa ba Hajjo don kin riga kin nuna min matsa yi na, na karashe fuskata dauke da Murmushi”.
Idol ta ne ya ciko da kwalla tace “don Allah ki yafe min Aminiyata wallahi ynxu na gane ba karamin hauka nayi ba da na miki abinda na miki, gaba daya Ynxu bana cikin nutsuwa ta amma na rasa wanda zan je gare sa ya bani shawara da kwarai ke kadai ce dama wacce take bani shawara kuma nayi amfani da ita naga dai dai ki yafe min”.
Girgiza kai nayi ina dan Murmushi nace “bkm wallahi Hajjo ai maganar ya wuce kawai batun mu koma kamar da ne har abada”.
Mike wa nayi nace “ina zuwa don Allah”.
So nake na aika Binta ta tambayo Yusrah me take so nayi mata na kwadayi ban taba jin haushin rashin numbern ta da bani da shi ba sai ynxu.
A dakin Binta na same ta nace taje ta tambayo Aunty me take zo nayi mata, na kuma bata waya ta nace tace ta samin numbern ta bani da ita.
Dawowa nayi gurin Hajjo na zauna tana min hira ina amsawa ba wai na saki jiki da ita bane don ni daga kan ta dan Adam ya kara bani tsoro a iya tunani na yau in Kabeer yace wa Hajjo yana son aure na zata iya danne kishi ta amince duk da kuwa zaman kishi yafi karfin wasa amma tayi biris taje har gidan mu ta zage ita da yayar ta, taya kuwa take tunanin zan amince na mu koma kamar da.
Binta ce ta shigo ta bani wayar tace “ta samun wai tama yi saving tace kuma don Allah in zata samu wainar fulawa irin ta jiya”.
Gyada mata kai nayi nace “je ki yanka albasa babba guda daya ki kuma jajjaga attaruhu guda uku, in kin gama ki min magana”.
“Toh” tace ta mike ta shige kitchen.
Wayar na kunna na shiga call log naga tayi saving da kanwata, Murmushi nayi ina girgiza Kai yarinyar tana burgeni kuma Ina ganin darajar ta, a ynxu Nima ina addu’a Allah ya bani ikon koyi da ita a wasu halayen nata, na kara ganin darajar ta da kimar ga a jiya da Abdallah yake yaba girki na a gabanta amma ko alamun sauyin fuska ban gani a tattare da ita ba sai ma biye masa da tayi wanda nayi imani da nice sai rai na ya sosu don kuwa ni ina da kishi matuka wanda nake Addu’a Allah ya sassauta min.
Wainar flour din na mata wadda nayi da manja, guda biyun da na fara yi na sa yaji na bawa Binta ta kai mata don kowa yasan wainar flour tafi dadi daga kasko sai kitchen.
Ina soya ta hudu suka shigo ita da Binta hannun ta rike da plate din tana dangwalar yaji.
Kallon Hajjo tayi ta gaishe ta ta nufi kitchen inda take jiyo kamshin wainar tana lumshe ido.
Ina tsaye naga ta shigo juyo wa nayi na kalle ta tana sanye da riga wacce ta sauko mata har gurin gwiwa sai wando palazzo ta yafa mayafi dan daidai tayi kyau sosai ta kara wani haske.
Dariya nayi nace “kika biyo ta kuma kanwata”.
Lumshe ido tayi tana hayewa kan table din dake tsakiyar kitchen tace “Aunty ina kwana, ai ina ci naji baxan iya jira ba Allah ni kamshin ma kawai nake son shaka”.
Murmushi nayi nace “lafiya qalau kawo plate din to na sa miki wannan”.
Miko min tayi na sa mata na cigaba da suyar tana min santin dole Yayanta ya rikice da girkina itama gaskiya a dinga hada kwano da ita, Murmushi kawai nayi ina cigaba da suyar.
Ina soya kaskon karshen muka ji shigowar sa, yana tsaye a bakin kitchen ya zuba hannayen sa duka a cikin aljihu yana kallon mu fuskar sa dauke da Murmushi a ran sa addu’a yake Allah ya dawwamar da wannan zaman lafiyar har abada a cikin gidan sa…….
DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 35
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yusrah ce tayi Murmushi tace “Yayana me kazo yi nan kuma”.
Hararar ta yayi da wasa yace “tambaya ta kike ma mai nazo yi koh, na shiga part dinki aka ce bakya nan kina nan ashe dadi kike ci son ran ki anan”.
Fari tayi da