Showing 9001 words to 12000 words out of 61405 words
shiga cikin labarin muji ya zata Kaya……
Comments nd Share please
Mrs A.M
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 7
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kara matse kafar nayi Ina fashewa da wani marayan kuka, kuka nake a hankali Ina jin wani irin mahaukacin feeling ni dai haka nayi ta juye juye, sai gab da asuba na samu wahallalen bacci ya dauke ni.
Umma ce ta tashe ni sallah, a nutse na mike kai na a kasa don bana son taga yadda idona yai, duk da ban kalli idona a mirror ba Ina jin yadda yayi luhu luhu nasan ya kumbura.
Dan shin da nake ji a pant dina yasa nayi tunanin mafarki nayi, kirjina sai bugawa yake don ynxu in nace zan yi wanka Umma tasan wankan me zan yi, karin abin ma ga Basma kuma da wayon ta tunda ta fara period har saurayi ne ma da ita duk da dai ba’a basa damar zuwa zance ba amma suna waya kuma iyayen sa sun je nema masa aure gurin Baban ta.
Toilet na nufa jikina duk a sanyeye, cikin ikon Allah ashe period ne wani ajiyar zuciya na sauke da karfi Ina murmushin da ban san yaushe yazo ba.
Fito wa nai rai na fess, dakin mu na shiga ina kara sunkuyar da kai na.
Umma dake zaune tana lazumi tace “har kin yi alwalar Aasmaa?”
Kai na a kasa Ina bude yar karamar wardrobe din mu, cikin nutsuwa nace “a’a Umma bakon wata nane yazo cikin dare wanka zanyi tukun”.
Gyada kai kawai tayi tana cigaba da jan carbin ta.
Pad na dauka da pant sai zanin wanka na fita zuwa toilet.
A nutse kamar yadda na saba nayi wanka na, sai da na wanke Kayan jiki na Ina fito wa na shanya akan igiyar mu ta shanya sannan na shiga daki.
Basma da ta gama shara tana goge ledar tsakar palon da tsumma dagowa tai ta kalle ni fuskar ta dauke da Murmushi tace “Ina kwana Aunty Aasmaa”
Nima murmushin na mayar mata nace “lafia qalau Basma ya ke war su Yaya”.
Dariya tai tace “tab ai bana kewar su Aunty Aasma Ina ganin ki da Umma”.
Murmushi nai cike da kaunar ta nace “toh masha Allah, anjima zaki raka ni gidan Maryam kinji”.
Cikin d’oki tayi dan tsalle cike da farin ciki tace “Allah ya kai mu Aunty”
A hankali nace “Ameen”.
Labulen daya raba daki da palon na daga ma shiga ciki.
Umma da har lokacin tana zaune akan sallaya kallona tai tace “yau zaki je gidan Maryam din”.
Daga mata kai nayi Ina shafa mai a jikina.
“Toh yau baki da aiki neh kar fa kiyi yamma kizo kije gidan nata sharp sharp ki fito”
Karamar dariya nai Ina daukar kayana zan fita nasa don bana iya sa kaya a gaban Umma nace “Umma yau aikin nawa mai sauki ne nasan kafin azahar ma na gama In Sha Allah”.
Daga Kai tayi tace “Allah ya taimaka toh”.
Kaya na sa na Ina fito wa na daura mana breakfast, kunu na dama kamar yadda yawancin lokaci nake yi tun da Umma tafi son kunu sai kosai dana soya mana, tun dare ba gyara waken da sassafe kuma Umar ya kai min markade.
Tare muka ci kosan a plate daya muna ci muna hira.
Hannu na wanko na zira hijab dina nayi wa su Umma Sallama na fita, bacci nake ji sosai amma baxan iya yi ba tun da nasan dole kafin 8 tayi min a restaurant don daura irin abincin da wasu zasu suyi breakfast da shi.
*******
Shi da Musbahu ne zaune a cikin jirgi zasu Abuja, flight din safe su ka yi booking don baya son ya kwana a can.
Sabon filin daya siya wanda zai gina babban estate zai je suyi magana da Wanda yake bawa contract din ginin.
Babban estate yake son yi sosai don wannan hadda katuwar Plaza zai bude a ciki, duk da sauran biyun ma ko wanne da Plaza a ciki amma wannan babba yake son yi.
Kallon sa Mushahu yai yaga yadda yayi shiru yana danna waya.
Murmushi Musbahu yai cikin tsokana don yasan abinda zai fada dole sai ran Abdallah din ya baci yace “baka manta ba dai koh, next week birthday party din Meena, kuma kasan yadda suke ta tsare tsare dole kai ma fa ka gayyaci friends dinka”.
Tabe baki yai bai ce komai ya Riga yasan tsokanar sa Musbahun yake tun da ai a gabansa ta kira tace masa next week ne party din nata yazo fa don in bashi ba party, a take a tym din yace mata baxai zo ba data nemi masa magiya kawai ya kashe wayar ya kuma yi blocking number ta sai da Mami ta masa magana sannan yayi unblocking.
Ganin bai ce komai ba Musbahu ya fashe da dariya yace “young billionaire dole fa sai kaje wannan party din haba kana mijin da zata aura”.
Manyan sexy eyes dinsa ya dago ya zubawa Musbahu, tabe baki kawai yayi yace “ban da tym dinka Man”.
Shima Musbahun ganin bai kule ba yasa kawai ya janyo wata hirar suka shiga yi akan school dinsu da ya rage musu saura semester daya in suka gama exam.
****
Faty da Meena ne zaune a dakin Faty din suna yin list din wadan da zasu gayyata.
Kallon Meena Faty tai tace “besty wai ya ake ciki neh, har ynxu Ya Abdallah bai ce zai je ba?”
Tabe baki Meena tai tana juya manyan idonta tace “bai fada ba amma zan san yadda zan yi gaskia, na fa gama fada wa friends dina zan gaba tar da su a gurin sa in bai je ba ai class dina zubewa zai yi”.
Shiru Faty tai tana kallon Meena ita dai a iya sanin ta ba’a yi macen da zata chanja wa Ya Abdallah tunani ba bayan Mami, ta sani farin sani Meena ba zata iya sa shi zuwa ba amma ba yadda za’a yi ta fada mata don tana fada mata sai sunyi fada.
Da sauri kuma Faty tace “ga shawara besty mai zai hana mu samu Mami mu fada mata kinga sai ta lallaba mana shi ya daure yaje koh”.
Ihun Murna Meena ta saki Tana rungume Faty din, sakin ta tayi tana dariya tace “gaskiya besty kin hadu, kin san wannan idea din bata zo min ba kwata kwata”.
Murmushi kawai Faty tai suka ci gaba da list din, sai da suka gama sannan aka dawo maganar abincin da za’a ci.
Cikin rashin damuwa Meena tace “wannan maganar yana hannun Dad, yace ya Riga na ya bawa wani restaurant order din zasu yi abinda ya kamata”.
Haka suka tashi ko waccen su ta dauki mayafi suka fita.
Gyran jiki ake wa Meena din, tun wancan week din aka fara mata sbd yadda take son ya kasance a wannan ranar ba Wanda yake haska wa irin ta….
*****
Tura dakin Yusrah Walida yayar ta tayi, a kwance ta same ta tayi rigingine tana kallon sama, fuskar ta jike d hawaye.
Zama tai a gefenta tana dafa kafadar ta, da sauri Yusrah ta mike tana share hawayen ta amma wasu sababbi suna kara zubowa.
Kallon ta kawai Walida take yi sai da taga ta dan nutsu sannan tace “Yusrah me yake damun ki, tun da Mummy ta kira ni tace nazo na tambaye ki abinda ne damun ki hankali na a tashe yake Yusrah wani abun ne yake faruwa?”.
Girgiza Kai tayi tana share hawayen ta kawai sai ta fada jikin Walidan tana tana sakin kuka.
Kuka take sosai zuciyar ta na mata zafi, ya zata yi da wannan soyayyar da take wa Ya Abdallah irin son sa da take yayi yawa sosai, hankalin ta ne ya kara tashi lokacin da taji Meena da Faty suna maganar cewa ai Ya Abdallah din zai je birthday party dinta, har tana cewa Yusrah gyaran jikin nan ma da take so take in zasu yan ka cake hankalin sa ya tashi sbd yadda zai ji kamshi da taushin jikin ta.
Rintse idon ta tayi da karfi tana Kara sakin kuka, tana matukar kaunar Ya Abdallah haka kuma take kishin sa, abinda yasa ma kishin nasa take iya controlling dinsa sbd shi wanda take yi domin sa bai sani ba, Karin abin kuma an riga an zaba masa matar aure.
Sai da tayi kuka ta koshi sannan ta d’ago ta kallo Walida, sunkuyar da kai tayi tace “Ya Walida abinda ke damuna ko na fada a banxa ne tun da baza a iya yi min Maganin sa ba”.
Zuba mata ido Walidan tayi tana sauke ajiyar zuciya tace “fada min dai Yusrah in kika fada wa wani zaki samu saukin abun in sha Allah”.
Kara sunkuyar da kai tayi sosai tace “Ya Abdallah…. naa… kee….. s…….o”.
Zaro ido Walida tai gaba tana Juyawa da sauri ta kalli kofa ko Mummy ta biyo ta, ganin ba kowa yasa ta janyo Yusrah jikin ta tace “kin san mai kike fada kuwa?”
Kuka Yusrah ta kara saki tana daga kan ta cikin kuka tace “Wallahi Ya Walida Ina matukar kaunar sa, gashi shi ko sani bai yi bama kuma an masa mata nasan baxan taba auren sa ba, kuma in ban aure saba baxan iya aure ba Allah shi kadai nake so da son sa na girma Ya Walida”.
Shafa bayan ta Walida take yi gaban ta yana faduwa, wannan abun da kyar ya faru amma sbd ta kwantar wa da Yusrah hankali sai tace “ki ta addua Yusrah in Allah yayi mijin kine shi sai kin aure sa”.
Da sauri ta d’ago daga jikin Ya Walidan tace “da gaske in Allah yayi shine miji na sai na aure sa?”
Daga mata kai Ya Walida tayi cikin tabbatar wa.
Dariya ta saki a lokaci daya hawaye na zubo mata tace “ko da fah Mami da Mummy da shi kan sa basa so fah”.
Nan ma daga mata kai tayi.
Sai kawai ta fada jikin Ya Walidan tana sakin ajiyar zuciya cikin kwarin gwiwar sake dagewa da addu’a.
*******
A nutse nake zuba abubuwan da muka yi a manyan flask.
Abubuwa kala 8 muka yi cutlet, croquette potato, cinnamon rolls, kenorkey fried chicken, vegetable white rice, shredded beef sai cowtail soup sai banana smoothie.
Ogan sune ya shigo tun da ya shigo yake ta Murmushi, shiyasa ya ke rike Aasmaa da kyau tun da ta fara musu girki restaurant dinsu yake cika don ta iya abubuwa da yawa daga na kwadayin har na gargajiya.
Kallon ta yai yana murmushi yace……
Comments nd share please
Mrs A.M
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 8
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kallon ta yai fuskar sa dauke da murmushi yace “ranar Monday za kuyi aikin wani birthday da aka bayar, kuma Ina son kije da kan ki gurin taron kisa ido akan yadda za’a yi rabon komai bana son a samu matsala ko kadan”.
Hade rai nayi kamar zan musa sai dai kuma tunanin yadda yake daga min kafa a duk lokacin da na ce baxan je rabon abincin ba yasa kawai na daga nasa Kai.
Kara washe baki yai yace “toh ai shikenan, kinga ranar dama zaki dawo daga hutun ki koh”.
Kara daga masa kai nayi don bana son wata magana kuma.
Shima ganin yadda nake Shan kunu yasa ya fita yana ya mutsa fuska yarinya ba wani shegen kyau ba amma sai girman kan masifa.
Ina gama abinda nake gida na koma nayi wanka nida Basma muka tafi gidan Maryam.
Mun dade sosai don sai bayan Isha’i muka dawo, naji dadin zuwan kuwa mun dade bamu hadu nida ita ba, mijin tane ya dawo damu a motar sa wanda da kyar na yadda ba shiga motar.
Ranar Thursday na samu Hutu, dama duk friday, Saturday nd Sunday din karshen wata nake hutu a restaurant din mu, a ranakun nake samu na shiga kasuwa tunda an yi mana salary na siyo abubuwan da nake bukata na kuma hadu Kayan jiki.
A ranakun ukun nan nake warewa nake gyaran jiki na, ko zan fita to sai na sa liqab.
Ynxun ma haka ce yau Friday dawowar mu daga kasuwa kenan nida Basma mun siyo kayan gyaran jikin.
Muna zaune a tsakar gida ina hada gyran Basma nayi min magiyar don Allah nayi mata itama.
Shiru nayi mata kawai sai da na gama hada komai sannan na kalle ta nace je ki rufe gidan kizo nayi miki.
Tsalle tai cike da murna tace Yauwa Auntyna.
Rufo gidan tayi tazo ta zauna, cire kayan ta tayi ta janyo under skirt kirjin ta na shiga murza mata hadin.
Sai da na gama mata sannan na shiga daki na rufo kofar bayan na dauko garwashin da zan sa dukkan a ciki na shiga shafa wa nima.
Sai da nayi 20 minutes akan dukkan din sannan na tashi Ina murje jikina a kan ledar dana shinfida.
Kwana uku na dauka ina yin wannan gyaran na kara wani kyau sosai, fatata ta kara sulbi da taushi kamshi mai sanyi da dadi kawai jikina yake.
Basma data zuba min ido bayan na shigo daki sanye da Kayan bacci tace “Gaskia Aunty Aasmaa kinyi kyau sosai kamar wata Amarya wallahi”
Murmushi nai nace “kema ai kinyi kyau din kamar amarya Basma”
Turo baki tai tace “aa Aunty Aasmaa kin fini yin kyau gaskia sai kamshi kike ba ruwanki da sa turare”.
Dariya nai Ina zama nace “kema ai kina kamshin Basma”.
Dan kwalin ta ta janyo ta rufe fuska tace “Aunty in aure na yazo ke zaki yimin gyaran jiki”.
Duka Umma ta kai mata tana cewa “ja’ira wato maganar auren ki kike koh”
Dariya nai nace “Toh Umma ai da gaskiyar ta, tunda Auntyn ta ta iya gyaran jiki ba amfanin zuwa gurin masu gyaran da kai na zan dirje diyata koh”.
Da sauri Basman ta mike ta shige daki tana dariya.
Ni da Umma din ma dariyar muka shiga yi mata muna hira.
*******
Zuba masa ido Mami tai tace “kana ji koh Abdallah, hakuri zaka yi ka je tun da take hada birthday party din ta baka taba zuwa ba, wannan kuwa kaga duk fa sbd Kai take wannan shirye shiryen”.
Ganin yayi shiru yasa ta kalli Musbahu da yake shan zobo tace “ka sa baki kaji Musbahu kayi ta lallaba sa har ya yadda”.
Cire cup din daga bakin sa Musbahu yai ya kalli Mami yace “Mami ni Kai na Ina ta fada masa Wallahi amma banxa ma yake min shiyasa kawai na kyale sa”.
Dauke idonta daga kam Musbahu tai ta mayar kan Abdallah wanda ya lumshe idonsa yana sauraren su.
Shi duk sun kasa fahimtar sa neh, mai zai je yi wai wani party sbd kawai ita yar kauye ce shine zata wani hada party ita bata san irin wannan abubuwan sam basa burge saba a haka kuma ake cewa ita zata aura bayan har ynxu ta kasa nutsuwa ta fahimci waye shi.
Kallon sa kawai Mami take yadda take son Abdallah baza taso ta tilasta mata ba, amma kuma Hajia Bilkisu tun dazu take damun ta da waya akan zuwan Abdallah din, a cewar ta Meena sai kuka take tace ita in har Abdallah baxai je party din ba to ta fasa.
Ita kuwa ko dan mutuncin Hajia Bilksi ai dole ta sa Abdallah ma yaje.
Ajiyar zuciya ta sauke tace “ynxu Abdallah baxa ka iya yimin wannan alfarmar ba, ba fa wai sbd wani zaka je ba ni zaka duba da kuma Auntyn ku”.
Bude idonsa yai da suke lumshe yana mikewa tsaye yace “Allah ya kaimu”.
Washe baki Mami tai tace “Allah yayi ma albarka son Ya tsare ka a duk inda kake ya jikin mahaifin ki”.
A hankali ya amsa da “Ameen” yana wucewa bangaren sa, ciwon mara yake damun sa sosai don haka yana shiga part din nasa dan karamin kitchen dinsa ya dora ruwan zafi a kettle.
Yana cikin matsa lemon tsami a cikin cup din daya hada tea Mushabu ya shigo, yana ganin shigo war sa ya hade rai sosai don baya cikin mood din da za’a masa iya shege.
Shima Musbahun duk da yadda yake son tsokanr sa amma kuma sai yayi shiru don yadda yga fuskar Abdallah tsab zai iya Kai masa duka.
*******
Iya gajiya na gaji sosai da aikin sa muke yi, tun 6 na fito sbd yadda Oga ya dinga kira na akan nayi sauri abubuwan suna da yawa.
Ai kuwa muna aikin Ina tsaki don abubuwa wajen 12 ne ake yi ko wanne kuma na mutum 50, sai 2 muka gama gaba daya na hada gumi.
Sallah na idar na dawo kitchen din Ina kara gyara abubuwan yadda zasu yi kyau sosai Oga Kona ya shigo.
Kallona yai yace “kin shirya dai koh, by 3 nake son ku tafi can tunda zaku fara serving mutane snacks da smoothie kafin a fara party din sosai”.
Fuska ba yabo ba fallasa nace “Oga Ina son zuwa gida ne nayi wanka duk na hada gumi”.
Zuba min ido yai yana lasar Baki yace “me zai hana kiyi anan, in ma Baki da Kayan ne ai sai nasa a siyo miki koh”.
Juyar da Kai gefe nayi nace “shikenan ma kawai”.
Da sauri yace “no ba Ina nufin wani abu ba fah, kije amma kiyi sauri kinga 4 za’a fara”.
Godiya nayi masa na fita Ina dan sauri.
Ina zuwa gida toilet na shiga nayi wanka sharp sharp, doguwar rigar material dina nasa sai dogon hijab light brown, har zan fito naga yadda fuska ta take maiko sai na tsaya na dan shafa powder da kwalli nasa lips balm
Ina fito wa Umma dake kallona tace “Inyee Allah yasa dai a samo min siriki acan”.
Zaro ido nai nace “Umma gurin party ne fah duk kananun yara neh a gun”.
Tabe baki Umma tai tana cewa “Allah ya kiyaye”.
Dariya nai Ina ma Basma bye na wuce nasan Umma haushi taji don nace duk yara ne a gun to ai ba karya nayi ba duk yaran ne, babban mutum zai je wani birthday party neh.
Ina zuwa na tarar har sun shiga motar ni suke jira, a baya na zauna nima muka wuce…….
Comments nd share please
Mrs A.M
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Dedicated to Aysha 2rawax❤️❤️
Page 9
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Madaidai cin hall