Showing 30001 words to 33000 words out of 61405 words
yan matan suka saki cike da farin ciki….
*****
A wajen daurin auren kuwa sai bayan an daura sannan Umar ya samu damar hango Abdallah a cikin mutane ana musu hoto.
Kara sawa gurin sa yayi ya mika masa hannu sukai musabaha, 10k din da Umma ta basa ya bawa Abdallah din ya mika masa yace “gashi inji Umma tace gudummawar tace”.
Dan zaro ido Abdallah yayi yace “gaskiya baxan karba ba ka mayar mata da shi Ngd Allah”.
Hade rai Umar yayi yace “in baka karba bafa zata ce ka rai na ne”.
Ba don ran sa yaso ba ya karba yace “Kace Ngd sosai Allah ya saka da alkhairi, ai anjima zaku zo koh”.
Daga kai Umar yayi yace “in sha Allah hadda su Yaya ma duk Umma tace suzo muje”.
Murmushi Abdallah yayi yace “ita zata zo”.
Kallon sa Umar yayi yana boye murmushin sa yace “wace fah”.
Dan hade rai Abdallah yayi yana sosa girar sa yace “wannan mara kunyar mana”.
Dariya ce ta kwace wa Umar ba shiri cikin dariya yace “ai ba yadda ta iya Umma tace dole taje”.
Wani murmushi ya saki yace “Yauwa kar ka bari ta fito ba hijab kaji kaga gurin hadda maza ita kuwa yadda take bata son rai ni ka tuna mata kaji”.
Cikin dariya Umar daga kai yana masa sallama a ransa kuwa addu’a yake Allah yasa su daidaita kan su don fa shi bai ga wanda ya dace da Yayar sa ba sai Abdallah yaron data rai na da alama shi baxai yadda ya zama Mijin tace ba.
*******
A gajiye na dawo sbd aikin abincin bikin da muka yi, ban yi mamakin ganin su Yaya da Maryam ba tun da Umma tace musu suzo don Allah aje wa wannan mara kunyar bikin, ni kam ba dan naso ba zan je sai dai kawai sbd yadda Umma ta nuna tayi fushi dole na amsa zanje.
Mu hudu zamu ni da Yaya sai Maryam sai Umar sai Basma.
Karfe 7 muka shirya gaba dayan mu kowa yayi kyau nima cikin lace red color na shirya doguwar riga ce wacce ta kama ni ba sosai ba amma ta fito da dukkan diri da structure dina, light makeup nayi nasa red jambaki wanda ya min kyau sosai, Hijab na dauka coffee iya gwiwa nasa na fito tun da ni kadai ake jira duk suna tsakar gida.
Da mamaki gaba daya suke kallona ganin nasa hijab Yaya ce tace “ba dai da wannan zaki je gurin Dinner din ba Aasmaa”.
Cikin rashin damuwa nace “eh mana Yaya ai ba abinda yayi ko yayi datti ne”.
Dariya Umar yayi yace “wallahi Ya Aasmaa kamar Abdallah ya san za’a yi hka yace kar ba bari ki fito ba hijab ni dariya ma nayi tun da nasan da Hijab din zaki”.
Tsaii nayi Ina kallon sa fuskata a hade, a dakile nace “shi ne yace na kar ka yadda naje ba Hijab”.
Daga kai yayi yana dariya kawai na koma ciki na cire hijab din, farin mayafi na dauka amma babba na yafa bayan na gyara daurin dankwali na.
Fito wa nayi duka suka bini da kallo ba wanda yace komai dai muka yi wa Umma sallama muka fito.
Adaidaita biyu mukai zuwa wajen kafin mu isa har 8 tayi.
A tare muka shiga gaba daya idona dai yana kasa Ina tafiya a hankali don gurin ba dai girma ba kuma yadda muka shigo sai aka bimu da ido ana kallon mu.
Umar ne yayi mana jagora har zuwa wani table da ba kowa tun da yana daga baya baya ne, gaba dayan mu muka zauna a kai.
Abdallah da yake zaune cikin wani dark blue voile ya hade yayi kyau sosai har ya gaji abinka da farar fata ta hadu da abinda ya haskaka ta ya kara fito da hasken fatar sa, gefen sa Yusrah ce wacce ta yi kyau sosai itama tasa light blue gown.
Tun da suka shigo idon sa ya sauka akan ta dama kuma tun dazun idon sa na kallon kofa yana jiran shigowar su ai kuwa yayi nadamar kallon nata, yadda ta yafa mayafi ba karamin kona masa rai yayi ba, sai da yaga ta zauna sannan ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido.
Muna zaune muna hira a tsakanin mu ni dai kallo daya nayi wa bangaren da amarya da angon suke ban sake gigin kallon wajen ba don ni kai na ban fahimci dalilin daya sa rai na yake baci ba.
Muna zaune mu dai kawai naji sallama daga bayana, dan juya wa nayi idona ya sauka akan wani mutum kallo daya zaka masa kaga kamala a tattare da shi.
Murmushi ya sakar min y sake yin sallama, su Yaya ne suka amsa ni dai a saman lips dina na amsa masa.
Kujerar dake gefena wacce ba kowa a kai ya kalli Umar yace “zan iya zama kani na”.
Dan waro ido Umar yayi yana kallon Aasma data hade rai sosai yace “eh ka zauna”.
Murmushi yayi y zauna yana kallona.
Fuskar sa dauke da Murmushi yace “barka da hutawa Queen”.
Ko kallon sa ban ba sai idona dana mayar kan wayata Ina game.
Ya bude baki zai sake magana kawai muka ji daga bayan sa ance “tashi na mayar da ke gida…”
Da sauri na juya ganin waye wanna yake bani umarni.
Da tsananin mamaki nake kallon sa sai kuma na juya na kalli bangaren da amarya da ango suke, Lumshe ido na nayi na sake bude wa don tabbatar da cewa eh tabbas baya gurin amaryar sace kawai a gurin itama kuma hankalin ta yana kan mu.
Muryar sa data ke dauke da bacin ran d yake ji a zuciyar sa ta sake fito wa a kausashe yace tashi na mayar da ke gida tunda amanar ki Umma ta bani……
DijahAM
09066728387
Salamu alaikum💃💃💃💃
Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵
Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.
Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃
Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥
Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.
Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥
Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490
Bissalam❤️❤️
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 19
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Muryar sa da take dauke da bacin dan da yake ji a zuciyar sa ta fito a kausashe yace “tashi na mayar da ke gida tunda amanar ki Umma ta bani”.
Gaba dayan mu zuba masa ido mukai har ni kuwa, a yadda nake kallon sa so nake na gurza masa rashin mutunci ko dan na goge rainin da yaron nan ya min a kwanyar sa sai dai kuma sabanin hakan ne ya biyo baya don wani irin kwarjini naji yayi min wanda yasa baki na yin nauyi.
Ganin yadda muka zuba masa ido ne yasa shi juyawa gurin Umar fuska a hade yace “amma Umar ya muka yi da kai don Allah, ba nace kar ka bari ta fito ba Hijab ba ni da nasan irin shigar da zata yi tazo baxan ma fara tunanin bata card din ba Allah”.
Umar da yayi tsifi tsifi don shi kan sa yanayin daya ga Abdallah din ya basa tsoro don haka cikin sauri yace “hijab fa tasa da zamu tafi kawai don na ce mata ai kuwa kace kar tasa mayafi dama shine ta koma ciki ta sa gyale”.
Lumshe idonsa yai yana kokarin controlling fushin sa ya bude idon ya zuba wa Aasmaa din wacce ynxu take danna waya hankali kwance.
Samun kan sa kawai yayi da magana cikin sanyin da bai san yana da shi ba yace “so kike ki kashe ni ko *Husna*”
Wani irin bugawa kirji na yayi har sai da na rufe ido da karfi, salon yadda yayi maganar da sanyi da kuma yadda ya fadi Husna sunan da ba wanda ya taba kirana da shi ya dake ni sosai.
Duk kokari na ganin ban kalle sa ba kasa wa nayi sai da na juyo idona ya shiga cikin nasa, da idanun sa ya shiga hora ni don wani kallo yake min wanda yasa na masa janye nawa idon duk kuwa da yadda naso yin hakan amma yaki bani damar janyewar.
Kamar wacce aka mintsina kuma ba tuno da auren sa fa ake yi sai ba tabe baki Ina maka masa wata muguwar harara.
Dauke idon sa yai daga kan ta ya mai da shi kan mutumin da yake zaune yana kallon su kawai fuskar sa cike da mamaki, sarai ya gane sa Kanin Mummy ne wanda matar sa ta rasu wajen shekaru 5 kenan a gurin haihuwa ta rasu ta bar yaron.
Hade rai yayi sosai shi fa ba damuwar sa bace don wai Kanin Mummy ne ko ma waye kawai ya tashi ya daina shakar kamshin Husna ai amanar ta Umma ta basa tun da auren sa suka zo ai.
Kara tamke fuska yayi yace “zaka iya tashi daga kan kujerar Alhaji”.
Da mamaki Sadam yake kallon Abdallah din ganin kamar bai gane sa ba yace “Abdallah baka gane ni bane Sadam ne fah”.
Kankance ido yayi cike da tijara yace Sadam na gane ka mana ka tashi plz kana bata min lokaci.
Kafin Sadam yayi magana Musbahu yazo da sauri ya janyo sa, tun dazu yake hango yadda Abdallah din yake magana duk da baya kusa dai amma yasan cewa ai maganar gizo bata wuce koki kawai kishin da har lokacin bai san yana yi bane ya motsa.
Bai sake sa ba sai da ya kai sa tsakiyar filin inda Yusrah yake tsaye yan uwa sun zagaye ta suna mata liki, wannan ne dalilin daya sa bata kara neman inda Abdallah din yake ba a tunanin ta ya shiga gurin friends dinsa ne.
Mu dai ganin 9 muka tashi muka fito Sadam yana bayan mu, nace min yayi har sai da na basa number na sannan ya kuma yace zai sauke mu gida.
Anan kuwa sai da Yaya ta kusa mangare ni sannan na yadda na shiga motar ya ja muka tafi.
Da sauri Abdallah daya fito sbd ganin su sun fita kuma Sadam na bayansu yayi baya ganin ta shiga motar Sadam yaja.
Da sauri Musbahu ya riko sa yana fadin ka bi a hankali don Allah Abdallah da ka fadi mana.
Cire hular kan sa yayi yana fifita jin wani gumi yana keto masa, ganin zafin karuwa yake kawai ya sabe babbar rigar ya rataya a kafada ya shiga zirga zirga a gurin.
Shi dai Musbahu ido kawai ya zuba masa cike da tausayi, ynxu abin Abdallah din ya dai na basa dariya ya dawo basa tausayi zai iya cewa tun da yake tare da Abdallah bai taba ganin abinda yake daga masa hankali kamar lamarin Aunty Aasmaa din ba.
Ganin Abdallah ya nufi mota yasa shi saurin zuwa gare sa yana rike murfin motar.
Da sauri yace “Ina zaka Abdallah?”
Daga idonsa da sauka yi jajir yayi yace “gida zan je kai na ke ciwo”.
Bai bawa Musbahu damar magana ba ya ja motar a guje ya fice.
Shiru Musbahu yayi duk ran sa ba dadi yadda Abdallah din yake yasan ba karamin kaunar Aasmaa din bane ya Kama sa amma bai sani ba, Kai shi fa yadda yasan Abdallah ko ya gane yana son nata baxai yadda ya fada mata ba abin gaba daya a cukurkude yake Abdallah da Aasmaa wacce t girme sa.
Gyada Kai Musbahu yai kawai ya shige cikin hall din ko za’a nemi Abdallah zai fada musu cewa ya tai gida kan sa yana ciwo.
********
A hankali rayuwa take tafiya yau fari gobe baki, wata uku kenan da haduwar mu da Sadam a cikin watannin nan duk ranar Saturday sai yazo Umma sai murna take amma su Yaya da Umar basa yin Sadam din wanda ban san dalili ba.
Baxan ce bana son Sadam ba kuma baxan ce Ina kin sa ba, yana da faran faran da mutane da kyauta matsalar sa kawai iko tun kafin na shiga gidan sa ya fara dora min doka wai dole in zan fita sai na kira na tambaye sa, a take a lokacin na nuna masa baxan yadda ba don ba a karkashin ikon sa nake ba ya bari In na shiga gidan nasa sai yayi min wannan ikon.
Na biyu kuma yadda yake abu kamar yana zargina, ba dama ya kira ni yaji line busy ya dinga fada kenan wai da wa nake waya ko da kuwa da safe ne ko rana, kusan kullum in yazo yana yawan cewa na basa wayata ya buda sai dai kawai na kalle sa na gyada Kai.
Wannan halayan nasa yasa ba fara jan jiki da shi don a yadda nake ganin wannan in muka yi auren zan samu matsala dashi, gashi na taba masa maganar ina son in nayi aure ko Mijina baxai yadda ba cigaba da aikin restaurant ba toh zan dinga snacks da abincin biki a gida, a lokacin na nuna min cewa shi dai gaskiya baya bukatar Matar sa ta dinga sana’ar komai wai in mace na samun kudi bata girmama mijin ta sosai.
Wannan halayen nasa na fada wa Umma duk abinda yake fadawa ta kwantar min da hankali tace na cigaba da addu’a Allah ya zaba abinda yafi alkhairi.
Ba wai Alhaji Inuwa ko Kabeer sun dai na kira na bane kiran Alh Inuwa dai Ina dagawa time to time na Kabir ne gaba daya ban daga wa amma kamar maye kullum da message dinsa nake farkawa na good morning da kuma wanda yake min da daddare.
Ni kai na nasan Kabeer yana sona kuma Ina tausayin sa wallahi har rai na da ace ba Hajjo bace matar sa da zan iya auren sa don na shaida soyyaya yake min ta gaskiya amma kuma baxan iya auren nan ba ai ana barin halak ko dan kunya, tausayin sa da nake ji ne yasa nima in na bushi iska nake masa text akan yayi hakuri ya mai da hankalin sa kan matar sa don ni dai baxan iya auren sa ba, a kullum reply dinsa shine bkm yana jira in naga ya rabu da ni to aure aka daura min da wani.
******
HAJJO
Wata ukun nan sun zo mata cikin rashin walwala gaba daya lamarin gidan ta ya tabarbare ita da kan ta Ynxu ta fara tunanin zata je ta roki Aasmaa data auri Mijin ta ko zata samu nutsuwar zuciya.
Kabeer ya chanja mata gaba daya taba da labarin cewa aure yake nema tun da kanwar sa ta hannun daman tace kuma ta fada mata yarinyar bata da kunya wallahi amma haka kullum dare sai yaje zance gurin ta kuma shi ne yake kai ta unguwa.
Ranar data samu labarin nan ba karamin tashi hankalin ta yayi ba da tayi confronting din sa sai ce masa yayi eh zance yake kuma budurwar sace ya raba kafa ne don in Aasmaa bata amince ba ya auri yarinyar.
Hankalin Hajjo ya tashi sosai ta dinga basa hakuri akan ya bar yarinyar wallahi ta amince ya auri Aasmaa din zasu zauna lafiya amma ko uhm bai ce mata ba ya fice daga gidan.
Shi da kan sa yasan dama dole Hajjon Zata ji haka tun da tana son sa kuma tana kishin sa da ace ma shi tayi wa tiijarar zai dinga lallaba tane amma Aasmaa taje tayi wa diban albarka hadda kiran ta da karuwa wanna kalmar tafi komai bata masa rai.
Kuma shi tun farko dama yana da ra’ayin zama da mace biyu ko dan karfin sha’awar da yake da ita, yarinyar ma da yake zuwa gurin ta ba wai son ta yake ba sosai kawai sbd sunan Aasman sace da ita Asma’u kuma itama tana yawan sa Hijab shiyasa yaji ta kwanta masa.
Ya sauko ynxun tun da yana cin abincin ta in ta girka kuma suna kwana a daki daya amma kullum a darare Hajjo take tana dana sanin amincewa da maganar Ummu wai a haka don Aasmaa din bata fada masa kalar zagin da ta dinga tura mata ba a group dinsu na school ta shiga ta fada musu Aasmaa din tana nemar mata miji har yana mata barazanar rabuwa da ita akan Aasmaa din haka suka hadu da Hajjon da wasu mates dinsu suka dinga zagin Aasmaa suna ce mata karuwa shiyasa taki aure sbd tsaya karbe wa maza Jen mutane kudi, in ku da kuke karanta wa kun tanka musu Aasmaa ta tanka, banxa ta musu kuma bata fita daga group din ba har suka gaji suka gama ganin wacce suke na din ta bawa banza ajiyar su..
DijahAM
09066728387
Salamu alaikum💃💃💃💃
Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵
Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.
Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃
Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala