Showing 21001 words to 24000 words out of 61405 words

Chapter 8 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3790

da akwai wadan da zan sa suyi ohk..”


Siririyar dariya tayi tace “Jazakallah bil Jannah Yayana, Allah ya tsare mun kai aduk inda kake i love u……”


Girgiza kai yayi jin ta katse wayar yasan kunya taji shiyasa.


Yana tsayawa a kofar layin namu na sauka da sauri Ina banko kofar nayi cikin layin, haka kurin nake jin haushin wayar da ya gama yi da dukkan alamu aure zai yi wannan yaron wai shi za’a bawa mata to yayi mata uban me, tsaki na saki da karfi Ina gyada kai.


Daga Umma har Abdallah din da kallo suka bi ta, ita dai Umma tunani take Allah yasa ba abinda take hange bane don in har shine akwai kura.




A tare suka fito da Umman, har suka isa gidan.


Dan tsayawa yai yana bin gidan da kallo sbd mutanen ciki, juyawa yayi da niyyar tafiya Umma tace “shigo mana babana”.


Ba yadda ya iya dole ya shigo kan sa a kasa zama akan kujerar da Maryam ta basa.


Gaisar da Yaya yayi sbd daga ganin ta ma ai yasan babba ce shi kuma Maryam ta gaishe sa.


Kallon su Yaya Umma tayi tace “shine Baban nawa da nake fada muku”.


Godiya suka shiga masa shi dai kan sa a kasa bai ce komai ba sai dan Murmushi daya ke kokarin yi.


Umma ce ta nuna Yaya tace “wannan itace Yayar su, yaran ta biyar sai Aasmaa sai Umar ai kasan sa shi sai auta Maryam ita kuma diyar ta daya Iyman gata nan sai kuma wanda ke hanya”.


“Ita Aasmaa din har ynxu Allah bai kawo ba muna ta addu’a dai Allah ya kawo na gari.”


Su Yaya da Maryam suka amsa da Ameen banda ni dana hade rai Ina juyar da kai na gefe.


Shi kuwa shiru yai yana tunanin shiyasa ashe take wani hade rai ita a dole babba, Ashe Yayar Umar ce shi da yace masa shekarun sa 27 kenan ita sai 29 ko 30, dan tabe bakin sa yayi kuma irin Ina ruwan sa din nan, yarinyar da in ta tsaya a gabansa yake ganin ta yar cukul.


Waleed yaron Yaya ne ya boyo abu a hannun sa yana mul mul da baki ya nufi Abdallah yana bangara dariya.


Da sauri Basma data lura da Bra ce kuma ta tabbata ta Aunty Aasmaa ce tun da Kayan ta ne daya wanke bata shanya ba, don har zata shanya da suka zo sai kawai ya bari zuwa dare sbd mutane.


Da sauri Basma ta nufo sa tana cewa Waleed zo nan kaji, ai kuwa yaron daya lura abun hannun sa take son kwacewa kawai yayi wulli da shi bai sauka ko Ina ba sai a fuskar Abdallah…………






Mrs Elhajj😘😘
09066728387






Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰

Na Chanja Mrs Elhajj din😂😂😂 na fison DijahAM sunan da nake amfani dashi a wattpad…


Page 15




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





Dan yamutsa fuska yayi jin wani abu mai dan danshi danshi ya sauka akan fuskar sa, hannun sa ya mika ya ciro yana shakar sansayyan kamshin da abin yake.


Dan ware idon sa yayi yana sake bin red bra din da aka mata adon flower da kallo, bai san lokacin daya ware idon sa gaba daya ba ganin size 42.


Da sauri kuma ya dago ya kalli Basma da ta tsaya tana kallon sa ita ma sai sosa keya take.


Yaya ce tace “ke Basma karbi mana kije ki ajiye mata abin ta”.


Juya wa tai ta kalli Aasmaa wacce ta sunkuyar da kan ta idon ta taf da kwalla tace “kema dai ban da abinki Aasmaa ai da kin shanya ynxu sai kin sake wanke wa don nasan Waleed duk ya zuba miki miyar hannun sa a jiki”.


Dagowa nai idona cike taf da kwalla nace “ynxu Yaya dole sai kin fada a bainar nasi cewa tawa ce salon a rai na ni bayan duk ga yara a gurin”.


Da sauri Abdallah ya dago ya zuba mata ido yana kallon ta, ynxu ita ce take sa wannan babbar bra din dama haka take da cika ko dai ciko ne.


D’ago wa nayi na kalle sa ganin yana kallona yasa na hade rai nace “lafiya Malam”.


Kasa kasa yayi da idon sa kafin ya tabe baki yana mike wa fuskar sa a dan hade.


Umma yayi wa sallama ya ciro kudi a aljihun sa ba dai san nawa bane ya bawa Waleed ya fita.


Yaba halayen sa su Yaya suka shiga yi wanda hakan ya bata mun rai na mike kawai na shige ciki.


Sai da naji sun dauko wata hirar sannan na fito muka shiga yi….




******
A hankali yake kara kallon tym ganin 9pm, tsaki yayi shaf ya manta da maganin da doctor ya ce ya siyo na Umma wanda zata dinga shafawa a hannun.


Mushabu ne ya kalle sa yace “wai lafiya kuwa kake ta tsaki tun dazu”.


Tabe baki yayi yace “pharmacy zan je zan siyo wani magani”.


Kallon sa Mushabu yai yace “wane magani ne haka zaka siya”.


Juyar da kan sa yayi titi yace “Matar dana kai asibiti wacce ta karye, dazu mun koma toh ban siyo ba kuma nasan suma basu san da shi ba da wannan Mara kunyar zata siyo…”


Da mamaki Mushabu yace wace “kuma mara kunya….”


Shiru Abdallah yai yana bude motar kawai y fita don baya son maganar wannan mai manyan abubuwan kuma.


Maganin ya siyo a pharmacy din har zai wuce yaga inda ake siyar da gasassun kaji, tsayawa yayi ta siya guda 8 ko wanne biyu biyu a leda daya, biyu nasa biyu na Mami biyu na Mummy biyu kuma zai kai wa Umma haka yake duk abinda zai siya wa Mami sai ya siya wa Mummy.


Ajiye ledojin yayi a baya ya shiga yaja motar suka nufi gidan su Aasmaa.


Tun da suka shigo layin Mushabu yake bin layin da kallo, a ran sa yana kara ganin mutuncin Abdallah, kwata kwata shi baya kyamar masu karamin karfi ynxu da wani ne yake da dukiyar Abdallah Allah ne kadai yasan abinda zai yi.


Abdallah kuwa ban da bugawa ba abinda kirjin sa yake yi, wata yake gani kamar wannan mara kunyar a tsaye tana murmushi har ana ganin fararen hakoran ta kuma kamar tayi kwalliya don yana iya ganin yadda bakin ta yake kyalli sbd wutar nepa da ta haska layin.


Shi ba ma wannan ne damuwar sa ba yadda yaga kamar mayafi ne a jikin ta kuma ta yafa sa a kafada ana hango wuyan ta yafi komai daga masa hankali.


Gaba daya ran sa yaji yana mugun baci har wani yaji yaji yake ji a idon sa.


Har suka karaso kusa dasu ya tabbatar da cewa ita ce, kallon wanda suke tare yayi yaga babban mutum sosai don har yar furfura ce a gemun sa, yana da kiba sosai ga katon ciki.


Tabe baki yayi yana kallon ta kawai ya shige cikin gidan Musbahu ya mara masa baya.


Sallama sukai Umar ya fito ya musu iso zuwa cikin palon tun da Umma na ciki.


Shiga sukai suka gaisa ya bawa Umma ledar maganin da kuma ledar kazar, godiya sosai Umma ta masa shi dai ce komai ba sai Murmushi kawai da yake yi.


Hankalin sa gaba daya yana waje ganin har 10mins da shigo war su amma bata dawo ba, mike wa yai kawai yana kallon Musbahu yace “bara naje na dawo”.


Bai ma jira amsar sa ba ya fice da sauri.


Har lokacin suna tsaye suna magana wacce bai san mai ake cewa ba don ita tana magana a hankali ne shi kuma Alh Inuwa sai kasa kasa yake da murya a dole yana tsara ta ta amince ta aure sa.


Daga bayan ta ya tsaya yace kije “Umma tana kiran ki”.


Da sauri na juyo na kalle sa har ga Allah sai da gaba na ya fadi ganin yadda ya mugun hade rai amma nima sai na hade rai Ina kau da kai nace “gani nan zuwa”.


Ganin alamar zata iya cigaba da magana a harzuke yace “tace kiyi sauri ne fah plz haba Umma fa nace miki…..”


Kallon Alh Inuwa tayi tace kayi hakuri Alh ko a waya sai mu karasa maganar kaga Umma na kira na.


Murmushin yake Alh Inuwa yayi yace bakomai sarauniya ta ki kula da kanki kinji.


Gyada kai nayi Ina sakar masa Murmushi, fata na shine ya fahimta ya rabu da ni don nidai Allah ya sani bana son auren sa sbd zan cutu sosai a wani fannin.


A gaba ya sani muka shiga cikin gidan shi dai Abdallah bai san me ya hau kan sa ba kawai yaga dai ya zubawa bayan ta ido yana ganin yadda suke juyawa a cikin mayafin suna rawa.


Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da suka shiga cikin palon.


Zama nayi ina mayafina nace “gani Umma”.


Cikin rashin fahimta Umma tace “ban gane ba”.


Kallon sa nayi yadda yake tsaye a bakin kofa nace “ce min yayi wai kin ce nazo ynxu ynxu”.


Kallon sa Umma tayi jiran karin bayani don haka yace “gani nayi ta dade kuma dare yayi”.


A zafafe nace “wai kai Ina ruwan ka dani neh, haka kurin Ina zance zaka zo ka wani ce dare yayi nazo Umma na kira na bana son hauka fah”.


Yamutsa fuska yy yace “ki dai na ihu mana”.


Fararen idona na zaro nace “ni ce mahaukaciya ma kenan koh, wai meye damuwar ka dani ne ynxu da na dawo gida mai zaka min”.


Dan hade fuska yayi yace “toh meye zaki wani fita gurin wancan mai katon cikin da mayafi kina wani masa murmushi wai ke son sa ma kike yi neh”.


Tsaki kawai nayi Ina kallon Umma data zuba mana ido tana murmushi nace “Umma don Allah ki jawa wancan yaron kunne ba ruwan sa dani, Ina ruwan sa da saurayi na kuma ko ba mayafi naje meye damuwar sa”.


Da sauri yace “kee yarinya ba dai kin dauka son ki nake ba koh”.


Watsa masa wani mugun kallo nayi nace “kaso wa din ni Aasma ai abun kunya ne na nayi tunanin sa’ar autar mu yana so na wallahi”.


Tabe baki yayi yace “better don ni ba wai son ki nake ba kawai dai sbd Umma ne, ni bana ma son gajerar mace….”


Mikewa nai Ina buga tsaki nace “banxa kawai….”


Zaro ido yai y kalli Umma yace “wai ni take zagi Umma”


A fusace na juyo zanyi magana Umma ta zunguri kafa ta dole nayi shiru na shige cikin dakin ina kwafa..


Musbahu da yayi tagumi yana binsu da kwallo murmushi kawai yake, a ran sa kuwa mamaki yake dama akwai wacce zata iya sa Abdallah magana haka ta fada ya fada, bama wannan ba wai Abdallah son ta yake ne don ga kishin ta nan karara a idonsa dama tun da suka hango su dazu ya lura da yadda gaba data fuskar sa ta sauya, haka kuma da suka shigo ya kasa nutsuwa sai da yaje ya taso keyar ta, murmushi yai yana addu’ar Allah yasa aminin nasa soyayy ya fada sai dai kuma yana hango kura duba da yadda ga lura ita din tana da zafi gashi daga yanayin maganar ta ya nuna cewa ta girme musu kenan…


Sallama sukai wa Umma da Umar suka fito.


A mota Musbahu ya saki Murmushi yana kallon Abdallah yace “gaskiya amma wannan Aasmaa din ta hadu ga sunan ta na yan gayu gata kuma da kyaun fuska dana jiki”.


Hade rai sosai Abdallah yayi yana tsaki yace “ina ruwana to ni”.


Langwabe fuska Musbahu yayi yace “da zaka amince ni ai da kamun jagora inje gareta don ni dai ta gama birge ni a rayuwar nan komai yaj……”


Bai kara sa ba sbd wani wannan birki daya ji Abdallah yayi a tsakiyar titi.


Kallon sa Abdallah yayi da idon sa da sukai mugun ja yace “don uban ka saukar min a mota”.


Zaro ido Musbahu yayi yace “na sauka akan titi Abdallah, me nayi ma”.


A fusace yace “sbd kai dan iska ne zaka zo kana ce min wani wai wannan yarinyar tana da kyaun jiki, Musbahu yaushe ka zama dan iska ido ya zuba mata kenan kana kallon halittar ta”.


Cikin son sake tado kishin Abdallah din da yake danne wa Musbahu ya Lumshe ido yace “wallahi tayi ne Abdallah kaga yadda take magana kawai nifa zuba wa lips dinta ido nai do….”


A mugun haukace Abdallah ya fito daga motar ya zagaya inda Musbahu yake ya bude ya fisgo sa waje da karfi ya rufe motar ya koma side dinsa ya bude yaja a guje zuciyar sa na wani irin dokawa …..


Musbahu kuwa mai zai yi in ba dariya ba, shi ko hauka yake sai ya tunkari Aasma da maganar soyyaya, shi fa Wallahi tsoro ta ma yake ji don haka kurin take masa mugun kwarjini irin su ai sai su Abdallah din….






*******

Shigowa tayi dakin Mijin nata bayan bayan ta gama yiwa yaran ta addu’a ta sunyi bacci.


Tana sanye da doguwar rigar bacci wacce ta kai mata har kusa da kafar ta mai siririn hannu sai kamshi take mai nutsuwa.


Ta matsu taji wani magana ne wannan mijin nata yake son fada mata wanda yace magana ce mai muhimmanci, irin yadda yayi serious dinnan yasa ta kagara data ji ko meye.


A zaune ta same sa a bakin gadon yayi tagumi da alama ita yace jira.


Yar dariya tayi tace “Abba irin wannan tagumi haka kamar Wanda aka aiko wa da wani mummunan sako”.


Yake yayi yana janyo hannun ta ya zaunar da ita a kan kujera shi kuma ya zauna a kasa.


Taso kwarai ta hana sa zaman a kasa amma ya hana ta yace yafi son ya zauna a kasa din dai.


A hankali yace “Hajjo kin San Ina son ki, kuma baki gaza a ko Ina ba kina iya bakin kokarin ki don faran ta min bani da abinda zan ce miki sai dai Allah yayi miki albarka kawai.”


Ajiyar zuciya ya sauke yace “nasan abinda zan fada miki dole zai bata miki rai kuma zai hautsina tunanin ki amma ba yadda na iya ya zama dole na fada miki Hajjo, Aure nake son kara wa”.


Wani irin bugawa kirjin ta yayi da karfi har sai da ta d’ora hannun ta akan kirjin, tun da ya fara magana dama gaban ta yake faduwa don tasan za’a zo wannan gabar.


Bata ce komai ba ya riko hannun ta yace “wacce nake so taki amincewa da ni Hajjo, Ina kaunar ta sosai amma ita nuna wa take data aure ni gwanda ta dawwana a zaune ba aure, ki taimaka min Hajjo ke kadai ce zata iya shawo kanta domin ta amince Wallahi zanyi adalci a tsakanin ku don duk Ina son ku……”


Cikin rawar murya tace “wace haka Abba da baza ta amince da auren ka ba sai na sa baki kuma”.


Lumshe idon sa yai cike da shaukin sunan ta ma kawai da zai fada yace “Aasmaa taaa….”








DijahAM
09066728387






Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 16




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM






Wani irin mugun duka da zuciyar ta tayi sai da taji kamar zata faso kirjin ta.


A zabure ta mike tace “ban gane ba Abba kana nufin aminiya ta wai Aasmaa dai tawa…”


Gyada kai yayi yana riko hannun ta yace “don Allah Hajjo ki fahimta Wallahi tun farko dama Ina son ta, kawai a lokacin na dauka ba son ta nake ba ke nake so shiyasa ban ma wai waye ta ba sai bayan munyi aure”.


“Duk yadda zan yi da ita don ta gane wallahi taki bani hadin kai don Allah ki taimaka min ki roke ta nasan zata yadda tun da dama sbd ke taki amincewa”.


Jiri ne taji yana diban ta so take ta gaya masa bakar magana wacce har ta mutu baxai taba manta wa ba amma kuma taji gwanda tayi shiru da dukkan alamu ba iya gaskiyar ya fada mata ba yana boye mata wani abun ita kuma tafi son taji komai.


Ajiyar zuciya ta sauke tana koma wa ta zaune ta zuba masa ido, mijin ta wanda take cika baki akan ba wata mace a gabansa bayan ita ashe yana can yana bibiyar aminiyar ta akan ta amince ta karbi soyayyar sa ta aure sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login