Showing 24001 words to 27000 words out of 61405 words

Chapter 9 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3787

aminiyar da ta gama sanin sirrin ta ko jiya jiya sai da ta kira ta tana mata complain cewa Abba yace ta bude gaskiya me ya kamata ta sha don ta hade ita kuma bayan ta gama mata fada akan ta rike sirrin ta sai ta fada mata abubuwan da zata hada don taji ta matse din tun da ita ta fita sanin abubuwan gyaran jiki.


Murmushin yake ta saki tana kallon sa wai ita ce yau Abba ya zauna a gabanta kamar mai neman gafara akan kawai ta amince ta shawo masa kan Aasmaa.


Hannun sa ta rike tace “ynxu dan wannan ne yake damun ka Abba shiyasa naga kwana biyu duk baka cikin walwala, ita Aasmaa din in ban da abin ta ai ba komai bane”.


Ajiyar zuciya ya sauke da karfi wacce har sai da ta sake zuba masa idanun ta, kara matse hannun ta dake cikin nasa yayi yace “Wallahi na fada mata haka nace mata nasan baki da matsala tun da ai kun san juna kin san baxa ta mallake miki ni ba amma taki yadda”.


Dan gajeran tsaki Hajjo tayi tace “gaskiya amma ta wahalar min da kai Allah ne kadai yasan tsawon lokacin daka dauka gurin shawo kan ta, wata kula ma da tuni ta haihu”.


Da sauri yace “tuni ma wallahi ai da tana da yara uku haka ma, kin San kusan shekara 6 fa kenan ba in da ban je ba gurin aikin ta kusan kullum sai naje da safe amma Wallahi ko kallo bata ishe ni ba, haka in naje gidan su ma kwata kwata bata fito wa tama yi blocking dina a wayar ta”.


Wani irin kuna Hajjo take ji a cikin zuciyar ta wani irin cin amana ne haka ace shekara 6 Mijin ta yana yawon neman soyayyar aminiyar ta lokacin shekarun su 2 da aure da haihuwar ta daya, amma ita ta kasa fada mata wannan maganar haka kullum bata da aiki sai na zama ta bude wa Aasmaa sirrin ta ita tana neman shawara ashe ma Mijin ta yana can yana fada mata kalaman soyayya.


Mike wa tayi daga zaunen da take fuska ba yabo ba fallasa tace “zan yi shawara zuwa da safe in sha Allah, in ta kama ma gobe sai naje gidan nasu muyi magana”.


Bin ta yayi da kallo har ta fita daga dakin yana so yace mata don Allah kar ta yi shawara da Ummu yayar ta amma kuma yana tsoron tunanin da zata yi.


Ajiyar zuciya ya sauke yana addu’a a ransa Allah yasa ba zata Kira Ummu ba don yasan matukar ta Kira Ummu lamari ya baci ya dade da sanin cewa Ummu bata son Aasmaa, da akwai lokacin daya gaba dawo wa daga aiki ya tarar da Ummun tana zuga Hajjo kan ta rabu da Aasmaa in ba haka ba sai ta aure mata miji, a lokacin Hajjo gwasale Ummun tayi ta nuna mata cewa tasan Aasmaa ko maza sun kare baza ta taba auren Mijin taba sannan kuma ta yadda da Abban ma tasan baxai auri Aasmaa ba.


Ynxu ya tabbata in har Hajjo ta fara kiran Ummu to fah lamari ya lalace..


Hajjo kuwa tana zuwa dakin ta kuka ta dinga yi sosai na bakin cikin wannan ranar data ke gani, kamar wacce aka zabura ta dauki waya ta kira Ya Ummu, fada mata komai tayi cikin kuka in da ya Ummun tace mata ta kwantar da hankalin ta gobe da sassafe ta nufi gida ita ma zata je can su hadu.




********


Idar da sallar Azahar nayi Ina zaune ina jan carbi a tsakar gida cikin nutsuwa umma tana kwance a gefe na akan tabarma don garin yayi luf luf alamun hadari sai iska mai dadi dake kada wa.


Da sassarfa Ummu da Hajjo suka shigo kai tsaye ko sallama babu, Kara Ummu tasa tayi ball da robar dana ajiye sbd ko ruwan sama zai sauko ya taru a ciki.


A razane na mike tsaye gaba na yana faduwa sbd mugun kallon dana ga Hajjo na min.


Cikin rawar baki nace “Hajjo lafiya kuwa”.


Kafin tayi magana Ummu ta riga ta da cewa “ai dole kice lafiya tsohuwar guzuma, wato kina nan kin nade a gida ana miki kallon saliha ashe mazajen mutane kike farauta, sbd abin kunya ma ki rasa mijin wa zaki dinga bibiya sai Mijin aminiyar ki”.


Hajjo dake kallon Aasmaa cike da tsana tana bin jikin ta da kallo tace “Allah y isa tsakanina da ke Aasmaa, ba dauki amanar duniya na baki duk sirrina ba wanda baki sani ba ashe kina nan kina mallake min miji a waje ban sani ba”.


Cikin rawar baki nace “Hajjo Ina kika ji wannan maganar don Allah Kar kiyi min mummunar fahimta ki tsaya ki saurare ni kiji”.


Cikin karaji tace “in saurare ki akan me Asma’u ai Wallahi kin bani mamaki, tsawon shekara 6 Abba(sunan da yaran su suke kiran Kabeer da shi shiyasa itama take ce masa haka)yana neman ki wai har kofar gida da gurin aiki yake zuwa don kawai ki amshi tayin soyayyar sa amma ki kasa fada min, wannan wani irin yaudara neh Asma’u Ashe bakin ciki kike min sbd nayi aure shiyasa kika shiga kika fita kika farauto zuciyar Mijina, Mijina fa Asma’u”.


Umma da bata fahimci abinda yake faruwa ba ta mike a hankali tana kallon su tace “lafiya kuwa Ummu meye yake faruwa neh”.


Da sauri Ummu ta daga mata hannu tace “don Allah Umma kar kisa baki bana so na fadi wata magana ne sbd kar kice nayi rashin kunya amma ai ba a banza Aasmaa tayi kokarin kwace wa aminiyar ta miji ba, kowa yasan ai da yadda kuke da Mama amma haka Liman yaso ya aure ki da kyar da addu’a ya dawo hayyacin sa ya bar maganar auren….”


Ynxu kuwa ji nayi rai na ya fara baci haka yasa na isa gaban su Ina duban su nace “Ummu bana son na zage ki ko ba komai Umma tayi min tarbiyyar girmama na gaba da ni, amma Wallahi kinji na rantse matukar kika ce zaki zagar min mahaifiya sai na sai ta miki baki”.


Tafa hannu Ummu ta shiga yi tana dariya tace “eh lallai abin na yi neh, wato sbd baki da kunya shine zaki zo ki tsaya a gabana kina cewa zaki sai ta min baki bayan kin aika ta cin amana”.


Tsaki Hajjo tayi tana kankance ido tace “Ya Ummu ban da abinki ai karuwa bata san wani abu wai shi kunya ba”.


A tsorace na juyo Ina kallon Hajjo cikin rawar murya nace “Hajjo ni kike cewa karuwa?”


Cikin idona Hajjo ta kalle ni tace “kwarai kuwa in ba karuwa ba wace zata dinga janyo attention din mazan mutane, ai duk mutumin da aka ce yayi aiki a hotel kawai a kalle sa ne a juya don an san kawai an gama farfarke sune, ai shiyasa kullum kike zama da hijab kamar saliha Allah ne kadai yasan abinda ke kasan Hijab din”.


Umma data yi shiru ce ta kalli Aasmaa da tayi sakato tana kallon Hajjo hawaye na zubo mata tace “Zo nan kin ji Aasmaa”.


Da kyar na iya daga kafata na nufi Umma Ina zuwa kawai na rungume ta Ina fashe wa da kuka.


Lumshe ido tayi tana shafa bayana cike da kulawa.


Ummu da Hajjo kuwa bakaken maganganu suka cigaba da gasa min son ran su sai da suka ga ba wanda yace musu komai sannan suka juya bayan Hajjo tace na bar mata miji in ba haka ba Wallahi sai ta halaka ni….


Sai da nayi kuka na mai isa na Umma bata hana ni ba sannan na d’ago na kalle ta nace “Umma ynxu kowa kallon karuwa yake min sbd nayi aiki a hotel, Umma girki fa kawai nake yi a kitchen Wallahi Allah Umma”.


Murmushi Umma tayi tana shafa kai na tace “ba wanda yake Miki wannan kallon sai mara tunani Aasmaa, Kar ki damu d abinda mutane zasu yi tunani matukar kin san ke dai baki sabawa Mahaliccin ki ba toh ki rabu da maganar mutane don su ba’a iya musu kin ji.”


A sanyaye na daga kai Ina share hawayen daya zubo min.


Dan hade rai Umma tayi tace “mene tsakanin ki da Kabeer Mijin Hajjo?”


A nutse na fada mata yadda ya dinga damuna a cewar shi sona yake, sosai Umma ta min fada kan rashin fada mata ba dan yi ba duk tsawon lokacin sannan kuma ta ce ko da ace son Kabir din ma nake bata amince na cigaba da kula saba, nima dama ba son sa nake ba ai ko son sa nake sbd darajar Hajjo ma zan hakura da shi.


Duka yinin ranar haka muka shi sa suku ku, da daddare Liman ya shigo ya bamu hakuri ni da Umma yace kanwar Hajjon ce data ji abubuwan da suka zo suka mana ta fada masa, suma kuma ya musu fada sannan ya kara da cemin in har na amince da Kabir din na fada masa zai kira sa ya turo magabatan sa.


Girgiza masa Kai nayi da sauri nace ni dai sam bana son sa, ba dan Liman yaso ba ya mana sallama ya tafi yaso lallai ace Aasmaa din tana son Kabir shi kuma ya aura mata shi yaga yadda zasu yi da haukan su daga ita har Maman tasu da suka daga hankalin su.






*******
A hankali rana ku suke tafiya har na koma aiki na, kuma tun daga ranar da su wannan Mara kunyar yazo da daddare bamu sake haduwa ba, sai biyu yana zuwa yana mai da Umma asibiti amma bana nan shiyasa bama haduwa ma.


A gajiya nake matuka akan aikin da nake yi yau, aiki ne na abincin gargajiya za’a kai gidan deputy governor da ake taro, sinasir ne da masa sai miyar taushe data ji naman talo talo, ga kunu aya da muka yi mun zuba a cikin jarkoki abin sai sam barka.


Mun gaji matuka sai dai kuma mun samu alkhairi don da muka kai abincin gidan 100k matar deputy governor din ta bamu.


Shiyasa abokan aiki na sai murna suke suna kasafa yadda zamu raba kudin tun da mu uku muka je ni da Salma sai Abubukar dayai driving din mu.


Nidai murmushi na musu kawai har muka koma restaurant din suka bawa Oga Kona kudin, 30k ya bamu kowa shi kuma ya dauki 10k, wannan na daya daga cikin halayen Oga Kona daya sa muke ganin girman sa bashi da mugun ta akan kudi in har aka baku zai baku abin ku ba tare daya zaftare muku ba.


Cikin farin ciki na isa gida Ina fadawa Umma kudin da muka samu, 10k na dauka na bawa Umar ya ajiye min a bank dinsa haka nake yi in har na samu kudi ko aka mana albashi Ina cire wani kaso ba basa ya ajiye min sbd aure na in ya tashi.


Kallona Umma tayi tace “Babana dai shiru kwana biyu baya zuwa ya dade bai zo ba gashi ban kar bi number din sa ba balle mu kira muji ko lafiya”.


Turo baki nayi a shagwabe nace “Umma don Allah kar ki wani damu ai gwanda ma da baya zuwa kwata kwata yaron bashi da kunya ni murna nake ma da baya zuwa wallah”.


Baki sake Umma take kallona tace “wai lafiyar ki kuwa Aasmaa mai yaron nan ya miki da kika tsane sa haka neh wai…”


Yar dariya nayi Ina mike wa nace “Umma bashi da kunya wallahi shiyasa ni kawai bana son sa…”






*******


Ihu take sosai tana watsi da kayan da suke jere akan tafkeken mirror din ta, tun da taga katin dinner din Abdallah da Yusrah hankalin ta ya tashi take kuka, abin da ya sake daga mata hankali ma hoton su da Teema ta dauka zuna zaune akan kujera da alama a palon Mami ne, Abdallah ya zuba mata idon nan nasa yana murmushi ita kuma ta sunkuyar da kai tana rufe fuska da mayafi.


Wannan hoton ya dugunzuma hankalin Meena har taji zata iya hauka akan Abdallah….


Da sauri Hajiya Bilkisu ta riko ta tana cewa “ki kula don Allah Meena mana kar Kiji ciwo”.


Cikin kuka tace “wallahi Mum Ina son sa Ina matukar kaunar sa, ynxu Mum aure zai yi Ina ji Ina gani ba yadda zan yi, Mum aure fa za’a daura masa ni shikenan baxai aure ni ba kenan Mum”.


Shafa kan ta take cikin damuwa tace “ki kwantar da hankalin ki bara Iya tazo ai ta kusa zuwa bikin zan same ta na mata magana nasan zata yadda kuma zata tursasa Abdallah din ya aure ki tun da dukkan ku ai jikokin ta neh”.


Da sauri Meena ta d’ago ta kalli Hajiya Bilkin tace “da gaske Mum iya zata iya sawa ya aure ni”


Daga mata kai tayi alamun tabbatar wa haka yasa ta koma ta kara lafewa a jikin Mum din tata tana jin tsanar Yusrah na kara kama ta, dama tun farko ba son ta take ba Ynxu kuma ai tana da hujjar kara tsanar ta tun da zata aure mata masoyin ta…….








DijahAM
09066728387








Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️










*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃




*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 17




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Tagumin da tayi ta cire tana goge hawayen daya zubo mata, ta rasa meye mafita akan wannan lamarin, tun ranar da suka je gidan su Aasmaa suka ci mata mutunci Kabeer ya dai na kula ta gaba daya.


A daran ranar taga tashin hankali ganin idon ta, ashe Liman ya kira sa y fada masa duk abinda suka aika ta.


Sosai ya nuna mata bacin ran sa kuma ya rantse mata neman soyyayar Aasmaa ynxu ma ya fara in har taga ya daina bibiyar ta to an daura mata aure da wani a masallaci, kuma ya taba tabbacin ana daura mata auren zai baxa ma neman Matar aure cikin wata biyu zai sake aure wallahi.


Hankalin ta gaba daya a tashe yake ta rasa me yake mata dadi a duniyar, data kira Ummu ma ce mata tayi ta yi dabaru ta janyo hankalin sa gare ta, to taya zata janyo hankalin nasa bayan ya kaurace mata baya mata magana da sassafe yake fita baxai shigo ba sai 12 na dare, baya cin abincin ta gaba daya kullum haka yake shigowa karshen magana ma ko ruwan gidan baya sha, da ruwan sa yake shigowa.


Bukatar ta kuwa in taje tana shafa sa zai biya mata bukata amma gaba daya ba alamun samun nasara, babban tashin hankalin ta ma jiya da tasha magungunan da Ummu ta kawo mata taje tace tana bukatar da yana sassakar ta amma kiran sunan Aasmaa yake, wannan abun ba karamin bakanta mata rai yayi ba da kara mata tsanar Aasmaa din.


Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon agogo karfe 1:30 amma bai shigo ba.


Alamun bude kofa da akai ne yasa ta dagowa ta zuba masa ido, a nutse ya shigo sai dai ko kallon ta bai yi ba ya shige dakin sa.


Da sauri ta mike ta bi bayan sa ta kuwa taki sa’a bai kulle kofar da key ba.


Durkusawa tayi tana fashe wa da kuka tace “don girman Allah Ya Kabeer ka yafe min, wallahi sharrin shaidan ne amma hakan baxai sake faruwa ba”.


Ko kallon ta bai yi ba sai kayan sa da ya cire ya daura towel zai shiga wanka, da tasan halin da zuciyar sa take ciki ba taba ce masa haka ba, kullum sai yayi wa Aasmaa message na ban hakuri bata taba masa reply ba sai yau tace duk abinda aka mata ai shine ya ka mata don haka ita bata ga lefin Hajjo ba tasan kishi ne amma ba wanda ya jawo mata sai shi, ta kuma kara da ce masa ko zata mutu bata yi aure ba baxa ta taba auren sa ba.


Wannan maganar tata ba karamin daga masa hankali yayi ba, shi kam yasan kaddarar sa ce kaunar Aasmaa amma yana mata wani irin so ne mara misaltuwa.


Ganin ya mata banxa zai shige toilet ta rungume kafafun sa tana basa hakuri.


A kufule ya fisge kafar tasa ya na nuna ta cikin rawar murya yace “da kin san irin son da nake mata da baki je kin zage ta ba har ki Kira ta da karuwa, a lokacin dana fara ganin ku ita nake so ba ke ba, amma sbd ta min kwarjini Ina ganin cewa tafi karfina yasa na koma gare ki Hajjo, bayan auren ki hankali na ya kasa kwanciya da ke sbd ke da gangar jikina kike rayuwa zuciya ta tana gare ta, shiyasa na fara neman soyayyar ta don ta amince min na aure ta amma taki sbd ke, duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login