Showing 39001 words to 42000 words out of 61405 words

Chapter 14 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3792

basu ne kuma tabbas wasu zasu iya kiran ta su fada mata, kasan mata kafin kai ka zaunar da ita za’a iya hure mata kunne shiyasa nake baka shawara ka zaunar da ita ka fada mata da bakin ka ace daga kai ta fara ji”.


Kan sa a kasa yace “baxan iya ba Abba tsoro da kunyar ta nake ji nace mata zan kara aure bana son na bata mata rai Abba”.


Wani sassanyar murmushi Alhaji ya yi yana sauke ajiyar zuciya, lallaba Abdallah yayi da yan dabaru da yadda zai tunkari Yusrah din sannan yace masa kar ya shiga gurin Mami ya wuce gidan sa kawai zai fada masa lokacin daya kamata ya je gurin ta amma a ynxu dai yayi wa gidan kaura.




Fita yai daga gidan sai da ya tsaya gidan su Musbahu ya fada masa auren da zai kara kuma Aasmaa ce amma ya boye masa yarjeje niyar da sukai, sosai Musbahu yayi mamakin yadda Aasmaa ta yadda har suke soyayya gashi zasu yi aure, daga baya kuma suka gangaro kan Yusrah, shima kwarin gwiwa ya basa sukai Sallama ya wuce gida.




*******


Ni kuwa yinin ranar su Yaya saka ni a gaba sukai suna min tsiya sai murna suke yi, in na kalli yadda suke murna sai naji kamar na yaudare su tun da basu san yadda auren zai kasance ba.


Umma kuwa sai nan nan take da ni tana lissafa kudin shanun ta da zata siyar da filin ta don a samu ayi wa Aasmaa din Kayan daki, ita kadai ce ta rage mata don haka take son komai tayi sa yadda zai burge Aasmaa din.


Murmushi kawai Yaya take yi tace “Umma ai Kayan kitchen ki cire su a lissafi don mun gama siyan Kayan kitchen komai an siya, suna ajiye a gida na fa a store a kudin albashin ta take ciro wa tana kawo min, kuma ni ma in naga wani abu ya burge ni siya mata nake, zannuwan gado ma duk mun gama da wadannan ai dama, ynxu kawai Kayan furnitures zamu mayar da hankali koh Umma tun da bikin cikin lokaci kankani ne”.


Murmushi Umma tayi tace “Allah yayi miki albarka dai ya zaunar da ku lafiya a gidajen ku, ya kara muku zaman lafiya da mazajen ku”.


A tare suka amsa da “Ameen”.


A hankali Umma tace “Allah ya jikan mahaifin ku da yana raye sai ya fi kowa murna Aasmaa din sa zata yi aure”.


Duka muka amsa da Ameen nan hira ta balle aka cigaba da lissafin abubuwan da ya rage a siya, ni dai Ina zaune a gefe Ina kallon su.


Muna zaune ya kira Umar yace masa gobe manyan sa zasu zo amma please yana so ayi komai a gaban Kawun su na gurin Umma ko kuma Liman tun da Umar din ya fada masa yadda suke da shi, kuma ya fada masa dalilin sa na son a yi komai a gaban Liman ko Kawun su don a damkawa Liman kudin zancen kar a bar su a gurin kawu.


Godiya sosai Umar ya masa don shima dama yana ta tunanin haka.


Da suka gama wayar Umma ya fada wa abinda Abdallahn yace, murmushi kawai tayi tace ya leka yace ma Liman din don Allah ya shigo zasu yi magana.


Liman daya ji dalilin kiran hadda hawayen sa don murna, kuma yayi mata alkawrin in sha Allah dashi za’a tun da sai sun fara biyo wa ta gidan sun dauki Umar sai Liman din ya bisu.


Ni dai nawa ido don tun ynxu jikina ya fara sanyi ji nake kamar nayi babban kuskure dana amince da auren nan yaushe ma nasan wannan yaron duk rashin kunyar daya ke min na manta har na amince da auren sa…..






*******


Shafa kirjin sa Yusrah tayi tace “Yayana ka fada min don Allah wata magana ce kake so muyi duk na kagu naji ta Allah…”


Kallon fuskar ta tayi yana d’ago kanta daga kirjin sa, hannayen ta ya riko gam yana kallon cikin idon ta yace “kafin na fada miki ki yafe mun Wifey nasan dole ran ki ya baci”


Ita dai Yusrah da ido kawai ta ke binsa ya tabbatar duk maganar da yake son fada mata mai muhimmanci ce sosai tun da ya dawo ya lura baya cikin walwalar sa komai cikin sanyin jiki yake yin sa shiyasa taji duk hankalin ta a tashe.


Kara damke hannun ta yayi yace “Yusra aure zan kara nan da sati biyar”










DijahAM
09066728387








Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️










*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃




*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰


Dedicated to Mufeeda tah💗 Uwar Amani kuma aminiyar Maman Amani❤️💗


Page 25




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Da sauri tayi A’uziyya tayi Murmushi tace mun gode sosai Yayana Allah ya cigaba da baka ikon yin adalici a tsakanin mu.


Cikin jin dadin addu’ar ta yace Ameen Ya Rabbi Matata.




******


Shirye shirye biki kawai ake yi a dukkan bangaren, ta bangaren Abdallah dama ba abinda zai yi in ba lefe da kuma kayan furnitures ba, suma already ya riga ya gama da su lefe kanwar Mami ya kai wa ya hada masa komai don baxai ma iya gigin fara zuwa gun Mami ba.


Da kyar ma ya lallaba ta ta fara masa magana amma da dogon fushi ta dauka sosai har sai da ya hada da Mama(Kakarsa) sannan ta sauko.


A gida kuwa yana bakin kokarin sa ganin yana kyautata wa Yusrah kuma baya sa tana feeling jealous, kullum cikin nuna mata yadda take muhimmanci yake yi wanda haka yake kara kwantar wa da hankali.




Yusrah..


A bangaren Yusrah kuwa tana iya bakin kokarin ta ganin tana boye kishin ta kar hakan ya dinga bayyana, ta dage da addu’a sosai kuma ta toshe kunnen ta daga jin maganganun mutane.


Yau ma zaune take a dakin Abdallah tana kwashe kayan ta daga wardrobe din Abdallah, hira suke yi da shi wanda yake taya ta kwashe kayan tun da yau saura 1week bikin.


Dagowa tayi ta kalle sa fuskar ta dauke da Murmushi tace “Yayana wai ni baka fada mun kayan a zan sa a dinner ba”.


Kira mata ido yayi yana dan hararar ta cikin wasa kafin yace “ba dinner din da zanyi sai kace wani saurayi”.


Juya manyan idon ta tayi tace “ai saurayin ne Yayana wa zai kalle ka ma yace kana da mata a gida”.


Tabe baki yayi cikin son ya faranta mata yace “ba wani dinner da zanyi ko auren fari ma nayi ne kawai don na faranta miki amma ynxu baxan yi ba gaskiya ai na girma kuma”.


Dariya kawai Yusrah tayi tana zuge akwatin data gama hada kayan, in tace kalamansa basu faranta mata ba tayi karya, tana alfahari da mijin nata tun da akai maganar auren nan bai taba chanja mata ba ita wani lokacin ma manta wa take yi cewa wai aure zai yi sai dai in ta fito taga part din dake gefen ta.


Kiran ta yayi ganin zata fita daga dakin yace mata gobe dangin amaryar zasu zo suyi gyara.


Sai da gabanta yayi mummunan faduwa amma kawai ta gyada masa Kai ta wuce tana Allah ya kawo su lafiya.




*****


Ajiyar zuciya na sauke lokacin da Maryam ta zuge akwatin karshen, yau aka kawo lefe maza ne suka karba kuma Liman ne ya amsa.


Tun da aka kawo ban kalla ba Ina daki sai ynxu da Umma ta sani dole na zauna na kalla, akwatina guda 16 ne saiti 4 wanda aka zubo kaya masu kyau na gani na fada, kusan rabin su a dinke suke da English wears masu kyau da tsari.


Ni dai kallon su Yaya kawai nake yadda suke zuzuta lefen da sarkunan gold din da aka zubo masu kyau.


Tun da bikin nan ya matso jikina a sanyaye yake gaba daya komai cikin sanyin jiki nake, ranar da aka kawo kudin zance ban Kara fita ba Umma ta hanani da kan ta take yi min gyaran jiki kullum sai biyu ake min.


Nayi wani mugun fresh jikina ya Kara laushi sosai, ga maganin sanyin da na sha masu kyau wanda Umma ta hada min da kan ta, Ynxu kuwa tsumi kawai take bani da hadin kaza.


Ni dai ba bakin magana amma wannan gyaran da ake min nasan kawai suna bata kudin su ne kuma ana wahalar da ni tun da kullum cikin matse matsen kafa nake.


Washe gari su Yaya suke je suka kara gyara gidan suka tafi kuma da lefen gaba daya, kayan kitchen ne kawai dama suka je da shi sai frames da wasu abubuwan dai da na siya.


Da suka dawo nan suka shiga santin gidan suna bawa Umma labari, gida ne mai hawa biyu a kasa babban palo ne mai dauke da dinning area sai kitchen babba da akwai daki a kusa da stairs mai dauke da toilet, hawa na farko shima kana hawa zaka ga palo bai Kai na kasa girma ba dan madaidai ci ne sai kofofi guda biyu suna kallon juna suna dakunan ne sai hawa na biyun shi kuma kana hawa kujeru ne guda biyu da table a tsakanin su sai dakuna biyu suma suna kallon juna, kuma duka dakunan ba wanda bai sa Turkish beds ba masu mugun kyau bama dakunan dake hawan karshen.


Ni dai kallon su kawai nake Ina ganin abun kamar a mafarki, shirye shirye ake sosai biki ya kankama.


Ranar Wednesday Yaya da Maryam suka dauke ni muka je salon din baby beauty aka min gyaran Kai sosai ta kuma tsantsara min Lalle ja da baki.


Kallon hannun kawai nake ganin komai nake kamar a mafarki wai yau ni Aasmaa ce dauke da Lalle kuma na aure na wai amma ba wani farin ciki da nake ji kamar yadda nayi tsammanin in na tashi aure.


Sai bayan isha’i muka koma gida wanda ya cika sosai da yan uwa na nesa dana kusa, mu dama a dakin Umar muka ajiye kayan mu don shi tun ana saura kwana uku ya koma gidan Liman sbd mata.


Washe gari Thursday kamu aka yi a wani fili dake bayan gidan mu, ni farko ma cewa nayi bana son kamun sai da Umma tayi min fada sosai sannan na yi shiru.


Gaba daya jikina a sanyaye yake, Ina tunanin gobe a irin wanna lokacin Ina da aure igiyoyin aure a Kai na duk sai naji hankali na ya tashi gashi dama Umma tace goben za’a kai ni baxa a tsaya sai Saturday ba.


Haka aka yi kamu aka tashi sai san barka mutane an yi min kara sosai yan restaurant din mu duk sun zo matan hadda gudunmawar su suka hada aka bani.




*******


Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya yau Juma’a aka daura auren Abdallah Ahmad da Asma’u Muhammad akan sadaki dubu hamsin.


Ina zaune a dakin Umar sanye da shaida fara wacce aka mata aiki brown a jiki tayi mun kyau sosai ta kwanta a jikina, Kai na farin mayafi ne na yafa a kai na hawaye ne kawai yake zubo min daga idona.


Tun da Liman ya dankamun sadakina na fashe da kuka, kukan dana rasa na meye farin ciki ne ko bakin ciki.


Umma ma dake palon ta hada Kai suka yi da Yaya suna kukan farin ciki, Allah ya amsa Aasmaa tayi aure cikin mutunci wannan abin farin cikin in basu godewa Allah ba mai zai suyi.


Salma ta gurin aikin mu ce ke aikin lallashina tana bani baki nidai gyada kai kawai nake ba wai don Ina fahimtar abinda take fada ba, ni kadai nasan abinda nake ji a rai na game da wannan auren shekara daya da muka yi.


Bana salla wanka Yaya ta sani na sake yi ta taya ni shirya wa cikin wata red atampa riga da zani sai farar lafaya mai adon ja kadan da na nada.


Lafayer tayi mun kyau sosai bama yadda ta kwanta a jikina kana kallon nadin kasan wacce ta nada ta iya dama.


A gaban Umma Yaya ta zaunar da ni Umma ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki, kuka kawai nake yi Ina rike hannun Umma lokacin da Aunty Murja kanwar Umma ta dago ni zamu fita.


Kuka nake sosai har aka sani a motar, tun da nayi wayo ban taba kwana a wani gidan ba in ba namu ba, yadda na tashi Ina da kwalafacin uwa shiyasa bana zuwa ko Ina ko Yaya In ta haihu duk yadda zata yi da ni naje na kwanar mata ko ana gobe suna ne bana zuwa dole haka take kyale ni sai Ynxu gani an baro ni da gidan mu za’a sadani da gidan da zan rayu na tsawon shekara.


Har muka iso gidan kuka nake yi sai dai a hankali nake kukan Yaya dake gefena tana kara min nasiha mai ratsa jiki.


Riko ni suka yi muka nufi bangaren matar sa kamar yadda yake a al’ada.


Yusrah tana zaune gefenta Teema ce sai Walida, su kadai tace su zo bata son mutane kuma Mummy da Abba ma sun goya bayan ta, su ma din tace suzo ne don tarbar amaryar amma amaryar na zuwa su tafi su bar ta, daga baya ne ma Abba yace a tura mata manya guda uku dai kar dangin amaryar suga kamar an rai na su yara ne suka tarbe su.


Tun da suka shigo da amaryar ta damke hannun Walida jikin ta yana rawa rawa amma fuskar ta kokari take tayi Murmushi, addu’a kawai take yi a zuciyar ta ita kadai tasan abinda take ji a zuciyar ta(I’m sorry Yusrah🥹)


Jarumta ta aro ta mike tana Murmushi ta nufo su Aunty Murja cikin fara’a ta tsugunna har kasa ta gaishe su tana riko hannun Aasmaa din fuskar ta dauke da Murmushi.


Kusan a tare kirjin mu yayi wani irin bugawa muka dago muna kallon juna, ni dai ta cikin lafayar Ina hango fuskar ta tar da hasken fitulu suka haska, tana da kyau sosai don kuwa ta fini kyaun fuska da hasken fata ga kuruciya sosai kana hango wa.


Ita kuwa Yusrah bata ganin fuskar ta amma laushin hannun Aasmaa din da kuma kamshin da take ji yana tashi daga jikin ta shi yaso tayar mata da kishin ta.


Zaunar da ita tayi a gefen kujera ita ma ta zauna a gefenta, nasiha aka musu sosai da addu’oin zaman lafiya sannan Yaya Murja ta kara riko ni muka fito.


Ajiyar zuciya na sauke lokacin da Yaya ta zaunar da ni a kan gadona bayan nayi addu’a, Lumshe ido nayi wasu hawaye suka sake zubo min, wai yau ni ce aka kawo gidan miji amma bana farin ciki don auren ba irin ko wani aure bane auren yarjeje niya ne.


A rai na nace dama Sadam na aura nasan ko banxa sai na fi jin sassauci, da sauri nayi istigfari tuno wa da nayi da auren wani a Kai na.


Ina ji Ina gani su Yaya suka tafi amma kafin su tafi sai da suka Kara gyara min gidan suka kunna Turaren wuta.


Ina zaune shiru a gefen gadon har na gaji na koma tsakiyar gadon na kwantar da kai na a cinyoyina.






******


Da sallama ya shiga dakin Yusrah, dagowa tayi tana kallon sa wani mugun haushin sa yana turnike ta.


Yana sanye da jallabiya fara kal sai kamshi yake hannun sa rike da leda babba ya shigo, ajiye ledar yayi a gefen kujerar dake dakin ya nufo ta yana sakar mata Murmushi.


Riko hannun ta yayi ta tayar da ita yace “barka da wannan lokacin Uwargidan Abdallah”.


Lumshe ido tayi wasu hawaye nasu dumi suka zubo mata, shikenan ynxu ta daina amsa sunan Uwargida kuma amarya kamar yadda yake kiran ta a da.


Rungume ta kawai yayi yana shafa bayan ta yace “na sani Kanwata nayi miki laifi, Yayanki kuma mijin ki mai laifi ne tabbas ke din Haruna ce Matata, Allah yayi miki albarka ya saka maki da mafificin Aljanna, ba ko wace mace bace zata iya dauriyar da kika yi wata 6 da aure ace mijin ki ya sake aure kuma ki hakura ki danne Ina alfahari da ke Matata”.


Kuka ta fashe da shi wanda take rike wa tun tuni, kuka take sosai tana dan dukan kirjin sa a hankali.


Sai da ya tabbatar ta amayar da abin da ke damun ta sannan ya ja ta suka shiga toilet tayi alwala, kwantar da ita tayi ya kunna mata karatu a Mp din ta ya ajiye a kan bed side drower, addu’a yayi mata ya shafa mata ya mike zai fita.


Riko hannun sa da tayi ne yasa shi juyo wa, Murmushi ta sakar masa cikin dauriya tace “Yayana ka kwantar da hankalin ka in sha Allah bacci zan yi ynxu ma baxan damu Kai na ba nasan kana so na bani da wata matsalar kawai dai dan kishi ne kadan yke mintsina na a nan”.


Ta karashe tana nuna sai tun zuciyar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login