Showing 15001 words to 18000 words out of 61405 words
gudu yana cewa kudin sa gashi ya bar su fah.
Musbahu ne yace masa ya rike kawai, tun da Abdallah ya fitar dasu daga aljihun sa baxai karba ba, Allah yayi rabon sane.
Godia Kona ya dinga yi yana juya kudin a hannun sa, lallai dole gobe da wurwuri yasa Aasmaa yi musu shawarma biyar kyauta ya bawa mai delivery ya kai musu tun da ya karfi number din Musbahu.
Ni kuwa Ina adaidaita sai zabga tsaki nake, tsabar rai nin wayo wai ni wannan karamin yaron zai dinga cewa kee yana kira na mara kunya, girgiza kai nai cike da takaici ni dai ban san me nayi wa wannan yaron ba gaba daya ya rai na ni.
*******
Dafe kan sa yai da ke barazaranar fashe wa sbd tashin hankalin da yake ciki, shi kadai yasan yadda zuciyar sa take mugun bagawa a duk lokacin da ya tuno kalaman Aasmaa a gare sa.
Dafa sa Ibrahim aminin sa yai yace “ka kwantar da hankalin ka don Allah Kabir, nutsuwa zaka yi mu samo mafita akan wannan lamarin”.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke yana zubawa Ibrahim idanun sa da suka chanja launi.
A nutse Ibrahim yace “ni dai abinda zan ce shine anjima ka dauke ni muje ni da kai gurin ta in duhu yayi sbd munafukai, in har muka je bamu shawo kan ta ba zan baka shawarar da nake gani ita kadai ta rage mana”.
Ba dan ya aminta da cewa da akwai shawarar da zata bulle masa ya amince da zuwan nasu gurin Aasmaa ko ba komai yayi missing din ganin wannan kamillaliyar fuskar tata.
******
Muna zaune a daki ni da Umma da Umar muna hira waya ta ta shiga ringing, kallo daya nayi mata na dauke idona akan ta ganin sunan Kabir.
Tun Ina blocking din number dinsa har na gaji na dai na, sbd in nayi blocking da safe zuwa rana yayi yawa ya sake kira na da wata number din, dole na hakura da blocking din number din sa kawai nake kin daga wayar.
Kallona Umma tai tace ba kiran ki ake ba Aasmaa.
Ba tare da na kalli Umma ba nace kiran bashi da amfani ne Umma.
Daga kai tayi kawai tana mayar da hankalin ta gurin Umar da yake fada mata yadda cinikin da yai a satin nan da ya gaba ta.
Sallamar wani almajiri ne yaja hankalin mu, Umar ne ya mike ya fita tsakar gidan don jin abinda ya kawo Almajirin.
Bai dade ba ya dawo fuskar sa washe da murmushi yace “Ya Aasmaa gurin ki aka zo kina da baki a waje.”
Kau da kai na gefe nai ina tabe baki don tun da naga yadda Kabir yake kira na dama jikina ya bani zuwa zai yi ko kuma yazo din.
Umma data zuba min ido tace “baki ji abinda aka ce bane bako kike da shi ki tashi ki fita”.
Na bude baki zan yi magana ta hade rai dole na mike kamar zanyi kuka na shiga daki.
Hijab dina na zura ban sa turare ba amma kamshi yake mai dadi sbd yadda nake turara su da kabbasa.
A bangon gidan mu na same su a tsaye suna hira, suna ganin zuwa na suka juyo suna kallona fuskar su dauke da murmushi.
Fuska a hade na musu sallama daga nan naja bakina nayi shiru sai Ibrahim ne yake ta zuba kan yadda Kabir din ya susuce a Kai na.
Ganin naki cewa komai Ibrahim ya marairaice murya yace “kiyi magana kinji don Allah gimbiyar mata”.
Kallon sa nai Ina tabe baki nace “uhm…”
Daga haka na juya na shige cikin gida abu na…
Dukan su bina da kallo sukai kafin kabir ya kalli Ibrahim kamar zai yi kuka yace “kaga abin da nake fada ma koh..”
Dafa sa Ibrahim din yai yana sauke ajiyar zuciya yace “shawara daya ce ynxu kuma ita kadai ce mafita kawai ka samu Hajjo ka fada mata, in Allah ya taimake ka ta fahimce ka kaga shikenan sai ta sa baki nasan in tasa baki da kyar Aasmaa din ta ki amince wa tun da ita na girma take kuma tana bukatar namiji a kusa da ita”.
Girgiza kai Kabir yai yace “anya kuwa zan yi haka Ibrahim duk da fa cewa nasan Hajjo bata da hayaniya amma wallahi ina tsoron tunkarar ta da wannan maganar, dama da ace ita Aasmaa din ta amince da abun yazo min da sauki”.
Murmushi Ibrahim yai yace “abokina wannan ita kadai ce mafita daga ita kuma gaskiya bani da wata dabarar”.
Haka suka wuce kowa yai shiru har ya sauke Ibarhim a gidan sa ya wuce gidan sa zuciyar sa na bugawa.
*****
A hankali rayuwar take tafiya wata ran farin ciki wata ran aka sin haka.
A gajiya nake matuka amma na tsaya hada wa wannan dan rainin hankalin Shawarma, kullum sai yazo yaci safe da yamma, in bai zo ba ma za’a bawa mai delivery ya kai masa.
Ynxu haka ma guda 12 yace yana so, duk da gajiyar da nayi amma haka Oga Kona ya lallaba ni nake nasa Ina yi Ina tsaki, baya cin ta kowa sai tawa da farko zame wa nai a tunani na ai baxai gane ba amma ana Kai masa yace a dawo dashi.
Dole ni na yi masa, tun Ina korafi don har Umma na bawa labarin wulakancin da yake min tace nayi hakuri har na ma dai na mata korafin.
Sai dai ban taba kai masa da kai na ba, tun lokacin da yazo na farko bamu sake haduwa ba, duk hanyar da na san zata sa mu hadu na toshe ta, Ina jin Oga ya leko yace na hada masa shawarma bana fita har sai Salma tace min ya fita.
Na gama sa masa a leda amma ban san wanda zan bawa ya Kai ba tun da ba kowa a kitchen duk suna cikin restaurant din suna goge goge da kimtsa gurin.
Zama na nayi Ina game, Oga ya leko.
Da alama sauri yake sbd yadda yake ta duba tym yace “Abdallah yana waje a parking space ki Kai masa plz sauri nake yi kuma yana jira neh”.
Kafin ma nayi magana ya juya da dan sauri ya fice.
Na dade a tsaye Ina tunani kafin nayi tsaki na rataya jaka ta na dauki ledar na fito.
Ina a tsaye Ina dube dube ido na ya sauka akan fuskar sa dake kwalli sbd hasken rana.
Zuba mata ido yai yana kallon ta a ran sa kuwa gulmar ta yake yadda kullum take sa Hijab ita ko zafi bata ji.
Tabe baki yai yana kallon ta fuska a hade yana sauraren karasowar ta.
Nima hade fuska ta nai ina yamutsa fuska don yadda ya tsaya dinnan nasan jira yake kawai na kawo masa.
Girgiza kai nayi Ina dan murmushi kadan, don wannan yaran bai san ko wace ni ba.
Ganin yaki taho wa kuma lokaci na kawai yake ci yasa na buga tsaki na yi bakin gate, gate man na bawa nace ya Kai masa ni kuma na wuce.
Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi yana lumshe idon sa, bai san me yake damun sa ba, tun ranar da ya fara ganin ta duk lokacin daya lumshe idon sa ita yake gani tana watso masa harara da wadannan manyan idanun nata.
Gaba daya ta hana sa sukuni ko motsi yayi sai ta fado masa a rai, kullum yana zuwa ne kuma don ko zai gan ta tayi masa wannan kallon rai nin amma baya samun ganin ta sai yau.
Murmushi ne ya subuce masa yana shige wa motar sa yayi mata key ya tafi…….
*******
Lokacin da na Isa gida Umma bata nan kuma dama ban yi tsammanin samun taba tun da tace zata je gidan kanwar ta.
Girki na daura don shinkafa sa wake nake sha’awar ci, salad na yanka na wanke na ajiye a gefe.
Kafin 6 na gama komai na juye a flask, a gurguje nayi wanka na zira doguwar riga mai hannun vest don garin yau ana zafi sosai.
Ina zaune a kan kujera a tsakar gida Umar ya shigo, kallon sa nai fuska ta dauke da murmushi nace “Sannu da zuwa mutanen kasuwa”.
Dariya yai yana zama a kan dakalin dake kofar dakin sa bayan ya dan kade kurar yace “Sannu Aunty Aasmaa mutanen restaurant”.
A tare muka yi dariya, hira muke yi a nutse cike da shakuwa da akwai shakuwa mai karfi tsakanina da Umar ko dan sbd dade wa ta a gida ne kuma shi kawai nake gani bayan Umma a cikin gidan.
Sallamar Umma ce ta samu mike wa da sauri fuskar mi dauke d murmushi sai dai kuma ganin tana tafiya a hankali kuma hannun ta an daure sa ga kanta da bandage yasa mu nufar ta da sauri.
Dukan mu rikice wa mukai gurin tambayar ta abinda ke damun ta, ba bude baki zan sake magana ta makale a wuya na ganin sa ya shigo hannun sa rike da jakar Umma da kuma wata leda ta asibiti.
Shima tokare wa yai ya zuba mata ido yana kallon ta cikin son gasgata ita ce dai ko ba ita bace a tsaye haka yana kallon ta ba Hijab.
Tun daga sama yake kallon ta yadda rigar ta lafe a jikin ta duka surar ta ta bayyana a fili, wani yawu ha hadiye yana Jin yadda wuyan sa ya bushe lokaci daya.
Da kyar ya maze yana hade rai ya Kawar da kan sa kamar bai ga komai ba, idonsa ne ya sauka akan Umar sai kuma ya mai da duban sa jikin Aasmaa wani irin mugun hade rai yayi yana jin yadda ran sa yake baci, Ynxu haka take zaune ita da wani gardi yana kallon ta a haka duk da yaga kamanni amma toh meye zata zauna gaban wannan sangamemen saurayin kusan tsirara……..
Comments nd share please
Mrs A.M🥰
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
Mrs A.M
Free book neh 🥰
Page 12
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Cikin seconds 30 hankalin na ya dawo jikina da sauri na matsa daga kusa da Umma na shige daki a guje don dauko hijab dina, zuciya ta tana bugawa da sauri da sauri.
Rai na gaba daya a jagule ga tunanin halin dana ga Umma a ciki ga kuma tunanin wannan yaron da na gani yazo gidan mu tare da Umma.
Da sauri na zira Hijab din nawa na fito a zaune na samu Umma akan tabarma ta mike kafafun ta, shi kuma yana daga tsaye a gefe yana kallon ta.
Hada ido mukai na ban ka masa harara na wuce gurin Umma Ina zama.
Hannun ta da ba’a daure ba na kama cikin rawar murya nace “Umma lafiya kuwa me ya samu hannun ki?”
Murmushi tai tace “Alhamdulillah nazo tsallaka titi ne wata mota ta buge ni kuma wanda ke ciki ya gudu, shine da Allah ya kawo babana yaron kirki ya kai ni asibiti aka gyara hannun karaya ceh”.
Zaro ido mukai nida Umar a tare muka ce “karaya kuma Umma?”
Murmushi tai tace “naji sauki ai, an riga an d’ora hannun kuma an bani magunguna abin ma yazo da sauki ai”.
Sannu na shiga jera mata sannan na shiga daki da sauri na debo mata ruwan randa the wanda yayi sanyi.
Kawo mata nai ta karba tasha tana kallon Abdallah da yake danna wayar sa kamar bai san da mutane da gurin ba.
Murmushi Umma tai tace “babana zo ka zauna mana a zubo maka abinci”.
Da kyar ya bude baki yace “I’m ok zan tafi”.
Da sauri tace “A’a zo ka zauna kaci abinci.”
Kallona tai tace “tashi ki zubo masa abinci Aasmaa..”
Dan dai kawai Umma ce shiyasa na mike ba tare da nace komai ba na shiga daki, abincin na zubo masa a plate na sa spoon sannan na debi ruwan randa a wani cup din silver nawa ne ma da shi nake shan ruwa sbd yana da murfi, ban san me yasa na zuba masa ruwan a ciki ba bayan bana barin kowa ya taba mun, tabe baki nai a rai na nace sbd shi naga bako ne ai.
Sai da na gama jera komai a kan wani tray sannan na fito Ina hade rai, kallon Umar nai da yake ma Abdallah magana da alama hira yake jan sa da ita.
Kara hade fuska nai cikin bada umarni nace “Umar je ka dauki tray a palo ka kawo masa”.
A nutse ya mike yace “toh Ya Aasmaa”.
Abdallah bai san lokacin daya d’ago Kansa ba ya kalle ta ya kuma kalli Umar, ko shakka baya yi ya girme sa amma yake cewa waccan yarinyar Yaya, tabe baki yai irin I don’t care dinnan ya mai da kan sa kan wayar sa.
Abincin da Umar ya ajiye masa ya kalla yana dan sakin murmushi kadan Wanda ta tsaya masa iya saman lips, yana son shinkafa da wake sosai cikin abincin hausawa shine fav dinsa.
Da farko bai yi niyyar cin abincin ba amma ganin shinkafar yasa shi yin bismillah yana ci a nutse, duk da ba Nama ko kaza ko kifi ko egg amma abincin ya masa dadi sosai.
Sai da ya duba yaga ya cinye tass sannan kuma ya dan ji kunya, d’ago wa yayi ganin hankalin kowa ba’a kan sa yake ba gashi kuma shi abincin ba wai ya ishe sa ba ya kalli Aasmaa dake zaune a kusa da Umma yace “keh!”
Gaba dayan mu juyo wa mukai muka zuba masa ido.
Shima idon sa a cikin nawa yace “ban koshi ba, karo min..”
Wani mugun hade fuska nai Ina banka masa harara kamar wacce idon zasu fado nace “kai waye sa’an ka anan gurin wai me yasa Kai baka da kunya neh eh”.
Bude sexy eyes dinsa yai yana zaro su yace “ni kike cewa mara kunya, lallai ma yarinyar nan kin mugun rai na ni…”
Da sauri na kalli Umar da ya sunkuyar da kan sa kasa tana kokarin hana kan sa dariya, cikin tsawa nace “Umar wanka wa wannan yaron mari plz, naga alama sai an sai ta masa hankali Sam bashi da kunya”.
Umma ce da tunda muka fara magana take bin mu da kallo tana murmushi tace “meye haka Aasmaa da girman ki kike wannan abun, bakon mune fa shi”.
Idona daya soma ci kowa da hawaye nace “Umma kina kallo fa amma yadda yake min magana kamar wani mijina ko ubana keh fa yake ce min”.
Wani shegen murmushi ya saki yana shafa gemun sa yace “uhmm waya sani ko Mijin naki neh?”
Ban san lokacin dana fashe da kukan da nake rikewa ba na mike da sauri nace “Allah ya kiyaye na auri sa’an kannen baya na Wallahi”.
Daki na shige da sauri Ina rufe fuskata Ina kukan takaici, Ina jiya dariyar Umma da Umar suna magana kasa kasa.
Ban san lokacin daya tafi ba tun da na shige daki ban sake fito wa ba har sai da Umman suka shigo ciki….
*********
Cikin fada fada Ya Waleeda tace “don Allah Yusrah ki sawa ran ki hakuri da dangana mana haba don Allah, kina jin doctor tace jinin ki ya hau sosai gashi zuciyar ki ta kusa tabuwa so kike ki mutu ne a banxa a kan soyayyar wanda bai ma san kina yi ba”.
Shiru kawai Yusrah tai tana share hawayen ta, gaba daya duniyar ta mata zafi ne sosai ta yadda yake Jin ita gwanda ma mutuwar ta, tana ji tana gani aka kai kudin auren Abdallah da Meena kuma aka sa biki shekara daya lokacin Abdallah ya gama school dinsa.
Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi wacce har sai da ta bawa Yaya Waleeda tsoro.
Dafa ta tayi cikin lallashi tace “don Allah kanwa ta ki sawa ranki salama kinji, ki dage da addu’a kawai kinga har Abba na samu na fada masa amma cemin yayi shi baxai taba iya rokar Abdallah ya aure ki ba baya son yaga kamar sbd duk abinda ya masa ne yasa shi cewa ya auri yar sa duk da shima yaron sa ne kuma yasan in ya fada masa ya aure ki din baxai musa ba”.
Kuka sosai Yusrah ta kara fashe wa da shi, only hope dinta dama Abban nasu ne ynxu kuma shima ga abinda yace.
Cikin rawar Murya tace “don Allah Yaya Waleeda ki taimaka min wallahi ina son sa sosai, in ya kubuce min mutuwa kawai nasan zanyi, zo ki taba kirjina Kiji yadda yake min zafi”.
Kallon ta kawai Waleedan take ita ma hawaye ba zubo mata, wannan kaddara ce babba a gare su, kafin ta sami Abban nasu da maganar sai da ta fara zuwa gun Mummy ta mata bayanin duk abinda ke damun Yusrah din.
Cikin rashin mafita Mummyn tace ita ynxu bata san yadda zata warware wa Yusrah damuwar ta ba tun da dai kowa yasan irin cin kashin data yiwa Mami farkon zuwan ta gidan kuma dai tana gani ynxu ai ko kowa ya amince da auren Mami baxa ta taba amin cewa ba, ganin ba mafita a gurin Mummyn ne yasa taje gurin Abba amma shima dai haka ta dawo jiki a sanyaye.
Tari ta shiga yi sosai har hakan yasa jikin ta ya soma rawa tayi gaba zata fado daga kan gadon asibitin.
Cikin zafin nama ya tallafo ta gaba daya ta shige jikin sa tana lumshe ido Jin kamshin turaren data san cewa a jikin masoyin ta kadai take jin sa.
Idonsa a kan fuskar ta data kara haske hancin ta ya sake tsayi yake kalla.
Gyara mata kwanciyar yai yana zama a kan kujerar dake gaban gadon, da sauri Yusrah ta yunkura zata tashi ganin da gaske Abdallah din ne ba wai gizo bane kamar yadda ta saba yi.
Hade rai yai sosai yace “koma ki kwanta bana son musu”.
Jiki a sanyaye ta koma ta kwanta din, sai dai kuma gaba daya jin ta take cikin wani irin nishadi, ynxu har ta kai matsayin da Ya Abdallah din zai zo duba ta.
Wani murmushi ta saki sai dai maganar da yayi mata tasa a take murmushin ya bace.
Ganin irin kallon da take masa yasa shi kara cewa zaki aure ni Yusrah?
Da sauri ta juya ta kalli Ya Waleeda wacce ita ma idon ta tuni sun soma zubar da kwalla.
Ganin kamar bata fahimci abinda yake nufi ba yasa shi riko hannun ta a nutse yace zaki aure ni Yusrah ki zama matata?
Kuka kawai ta fashe masa da shi tana kankame hannun sa………
Mrs A.M
09066728387
Salamu alaikum💃💃💃💃
Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse