Showing 48001 words to 51000 words out of 61405 words
ci sai dai in na sauko naga anci.
Gyara masa part ma har na dan fara sabawa kuma Ina bakin kokari na ganin ko Ina fess yake don gudun kazanta.
Gashi yau Yaya zata kawo min mai aiki shiyasa nake so duk inda 5 tayi ace Ina gida In sha Allah.
Turare na fesa kadan na fito Ina tunanin ya kama ta dai na kira mai gidan na fada masa zan fita tun da ai ba zaman kai na nake ba.
Sauko wa nayi Ina tunani gashi bani da number din sa balle na kira sa kuma bana son na makara don karfe 8 har tayi.
Ina sauko wa shi kuma yana shigo wa, zuba mata ido yayi yana kallon ta tun daga sama har kasa da mamaki a fuskar sa, ba wai ganin ta da hijab bane ya basa mamaki don in wannan ne ya riga ya saba ganin ta da jaka da alama kuma fita zata yi shine ya basa mamaki.
Kenan da bai zo ba fita zata yi kawai bata tambaye saba yayi wannan maganar a zuciyar sa.
Ni kuma tun da ya shigo gabanta yake faduwa irin kallon da ya min kawai yasa naji jikina yana rawa rawa, mamaki nake yi ni yadda in har na kasance a gaban wannan yaron nake jin wani abu kamar tsoro tsoro.
Cikin rawar baki nace “barka da Safiya”.
Sai da ya dauki wasu seconds kafin yace “barka ashe fita zaki yi?”
Da sauri na kalle sa Ina jin bugawar zuciya ta tana karu wa, dakiya na aro Ina tuna wa Kai na cewa wannan ba kowa bane fa a gaba na sai kanin baya na kuma ba wai Mijina bane kawai ya aure ni ne don ya taimaka min nan da shekara zai rabu da ni.
Wannan tunanin ne ya bani kwarin gwiwar ce masa “eh dama Ynxu nake tunanin yadda zan fada ma tun da bani da number din ka, restaurant zan koma yau”.
Folding hannun sa yayi ya jingina da jikin bango yace “da izinin wa”.
Kallon sa nake yi da mamakin sa Wanda ya kasa boyuwa a fuska ta, da mamaki nace “to izinin wa zan nema da”.
Ware manyan idon sa yayi yana kallon ta da tsananin mamakin wannan yarinyar, ynxu shi zata kalla tace masa da izinin wa.
Gyada Kai yayi yace “izinin mijin ki, kuma a iya sani na ni kadai ne mijin naki koh?”
Hade rai nayi na kawar da Kai gefe cikin haushi nace “plz ka dai na cewa wani Mijina don Allah, in muna tare mu biyu”.
Manyan idon sa da suke masa yaji sbd haushin ta yace “ynxu ni kike cewa na dai na kiran Kai na mijin ki to sbd me?”
Tabe baki nayi nace “ynxu kawai don Allah kana sa’ar autar mu kawai sai na ce Mijina ne Kai, ni Kai na fa kunya nake ji in na tuna cewa Ina matsa yin matar ka da fa gida daya muke har tsarkin pupu zan iya ma”.
Ran sa in yayi dubu ya gama baci a duniya baya kaunar a dinga masa kallon karamin yaro amma shi wannan yarinyar take duba haka, gyada kai yayi yace “in kin isa da kan ki don Allah ki fita”.
Daga haka ya juya ya fita yana banko mata kofa, Wallahi yayi alwashin yau dai sai ya koya wa yarinyar nan hankali ta yadda ko sunan sa taji sai gaban ta ya fadi lallai dole su raba rai ni ma wallahi, da wannan tunanin a ran sa ya fita ko kara leka part Yusrah bai yi ba don baya don ta gan sa cikin wannan yanayin.
Gaba daya ni ma sai naji rai na ya baci, hade rai nayi sosai na koma sama ba don naso ba na ajiye jakar da Hijab dina, yadda naga tan sa a bacen nan sai naji Ina shakkar fitar dole ba don naso ba na koma na kwanta kawai ina ajiyar zuciya har bacci ya dauke ni.
Ban tashi ba sai karfe 12, toilet ba shiga nayi brush na fito Ina kunkuni ni kadai duk rai na a bace, kasa na sauko na shiga kitchen na dora abinci gwanda nayi komai ynxu na huta.
Tuwon shinkafa nayi da miyar alayyahu da taji kifi sai pepper soup da nayi, nasa daban na sa masa a flask ragowar nasa a normal flask sbd Yaya, kunun aya naji Ina sha’awar sha kawai na shiga hada wa, da wuta don haka a blender na markada aya ta kafin karfe hudu na gama komai nasa kunun Ayar a fridge.
Dakin kasa na shiga nayi alwala nayi sallah ina kan dadduma naji door bell, mike wa nayi bayan na cire hijab din na fito ba bude.
Yaya ce bayan ta kuma wata yarinya ce da baxa ta wuce shekara 13 ba tana rike da ledar data saka kayan ta.
Matsa musu nayi cikin farin ciki nace sannu da zuwa Yaya.
Shigowa sukai ita ma tana Murmushi a ran ta kara godewa Allah take wai yau Aasmaa ce a gidan Mijin ta abinda suka dade suna fata gashi ynxu lokaci yayi har an yi sati biyu.
Gaishe ni yarinyar mai suna Binta tayi tana zaune daga gefen carpet.
Fuska ta dauke da Murmushi na amsa mata don na yana da hankalin yarinyar da alama tana da tarbiyya.
Zuwan Yaya ya dauke mun damuwa ta da haushin da na wuni da shi, falon sama muka je muka sha hirar mu Binta tana kasa tana kallo na kunna mata Arewa 24.
Gab da Magriba na ce na dauki abubuwan da zan bukata na gyara part din sa na dauki key na fito tare da Binta wacce na bata basket din dana zuba flask din abinci a ciki tun da Yaya tana naga gwanda na Kai masa can.
A bakin kofa nace ma Binta ta tsaya ni kuma na shiga ciki, sai da na ajiye abubuwan dake hannu na sannan na fito na karbi basket din nace ta koma.
Gyara part din na shiga yi duk da na wani datti amma haka na gyare shi tsaf, bedroom din sa na shiga don dama haka nake shi nake bari na karshe a gyara.
Kan gadon na nufa don na gyara na cire shinfidar, Ina jan bargon bra da pant sai boxer suka fado, da sauri nayi baya cikin wani irin bugawar kirji.
Gadon nabi da kallo hankali na yana tashi ni ba yarinya bace duk da Ynxu nayi aure kuma ba abinda ya shiga tsakanina da Mijin amma ai daga kallo daya na gadon nasan ansha gumurzo a Kai.
Kai na naji yana juyawa Ina sake bin boxer din da kallo, da sauri na rintse idona dai dai lokacin naji an bude kofar da sauri.
Juyawa nayi don ganin wane ya bude kofar ya shigo…….
DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 31
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kiran Sallah ne ya farkar da Abdallah daga baccin da yake yi, a nutse ya kalli Aasmaa shafa kan ta yayi yaji jikin ta yayi zafi sosai.
Sunkuya wa yayi ya manna mata peck a goshin ta sannan ya mike ya shige toilet, wanka ya sake yi yayi alwala.
Jallabiya ya zira ya nufo gadon don ya tashe ta suyi sallah, shafa kan ta ya shiga yi cike da zallar kaunar ta da yake ji tana kara ninkuwa a zuciyar sa ya shiga hura mata iskar bakin sa a hankali a kan fuskar ta.
Ganin bata motsa ba yasa shi dan bubbuga hannun ta, still bata motsa ba sai wani numfashi da take yi kamar mai asthma.
Cikin tashin hankali ya shiga toilet ya debo ruwa ac cup yazo ya shafa mata a fuska amma bata tashi ba, rasa in da zai saka kan sa yaji dadi yayi kawai ya juya a guje ya dauko jallabiyar sa ya saka mata, ko hijab bai iya tsayawa ya samata ba ya dauke ta cak ya fisgi key din motar sa dake ajiye akan mirrow ya fito a guje.
A bayan mota a ya sata ya shiga gurin driver yaja a guje already dama gate man ya riga ya bude masa kofar don tun da ga yadda yaga mai gidan nasa ya fito yasan ba lafiya.
Asibitin da su Mami suke zuwa ya kai ta kasancewar na kudi ne ko yaushe da akwai doctor, ya kuma ci sa’a Doctor Hafsa na nan family doctor din su.
Ita ta duba Aasmaa sosai tayi mamakin barnar da Abdallahn yayi tun da tana da labarin auren da ya sake yi, ana ganin sa shiru shiru ashe ya iya ta’asa har haka.
Dinki aka ma Yaya Aasmaa ta sha kuka abinta tana jawa Abdallah Allah ya isa a ran ta, ana gama mata dinkin doctor Hafsa ta mata allurar bacci.
Fito wa tayi daga dakin da aka kwantar da Aasmaa din lokacin har 6:30 tayi, ganin yadda Abdallah yke zagaye ya rungume hannun sa a bayan sa ya kusa sata dariya ta dai daure tace ya same ta a office.
Kallon Doctor Hafsa Abdallah yake yi kamar baya gane bayanin ta.
Da mamaki yace “ynxu doctor daga sharar fage har na yaga ta sai da aka mata dinki”.
Bata fuska Doctor Hafsa tayi tace “dinki ciki da waje na don haka plz Abdallah ka daga mata kafa ko nan da sati biyu ne kafin ka Kara”.
Kankance ido yayi yana kallon Doctor da iya gaskiyar sa yace “gaskiya baxan iya ba”.
Tagumi Doctor Hafsa tayi tace “kokari zaka yi ko dan ta warke sosai don taji rauni gaskiya”.
Gyada Kai kawai yayi ba wai don ya amince ba shi ai ba don anyi mata dinki ba bai ki ba ma ya mata dadin baki suna komawa gida a sake.
Duban ta ya sake yi yace “ynxu yaushe za’a sallame mu”.
“Eh zuwa anjima in sha Allah in ta farka zaku iya tafiya sai dai zaka dawo da ita nan da sati don na duba dinkin, amma in naga Ina da tym zan iya zuwa har gida ma na duba kawai”.
Godiya ya sake mata ya mike ya dauki takardar magungunan da ta rubuta ya fita.
Sai da ya fara zuwa masallaci yayi sallah sannan ya shiga mota ya koma gida, wanka yayi y shirya cikin manyan kaya farare kal don yau jin sa yke a angon sa sai fara’a yake yi.
Part din Yusrah ya shiga tana zaune akan kujera a kasa tayi wanka ya zira simple doguwar riga batai kwalliya ba sai dai tayi kyau sosai ta kara haske.
Ba karamin burgesa tayi ba har bai san lokacin daya isa kusa da ita ba ya zauna a kasa yana shafa fuskar ya da ta Kara laushi da kumatu masu kyau.
Cikin bacci ta bude idon ta, ganin sa a zaune a kasa ya sa ta kokarin mikewa don ya gaishe sa.
Bai bar ta ta mike ba shi ya tashi ya dauke ta ya shiga hawa sama da ita, a dakin ta ya sauke ta yaja hannun ta har kan gado ya kwantar da ita.
Mikewa yayi yana yarfe hannun sa cike da zolaya yace “gaskiya Wifey kin kara nauyi saura kadan na karya hannu”.
Harara ta sakar masa tana turo baki a shagwabe, dariya yayi cikin nishadi ya sunkuyo ya manna mata kiss a lips.
Bai fita ba sai da yaga ta koma bacci sannan ya fita yana murmushi, ya amince Yusrah mahadin farin cikin sace duk irin nishadin da yake ciki a yau da yayi arba da ita sai yaji farin cikin sa ya Kara nunkuwa, ya tabbatar duk wani kwanciyar hankali da nutsuwa da yke samu ynxu bisa jajircewar Yusrah ce, da ace lokacin daya zo mata da maganar zai Kara aure ta tashi hankalin ta da ba wannan zancen ake ba.
Murmushi ya saki yace “I love u Wifey Allah ya miki albarka”
********
A hankali na shiga bude idona, ganin kamar asibiti yasa ni saurin kokarin mike wa.
Doctor Hafsa data shigo Ynxu don ta duba ko ta tashi, ta taho da dan sauri ta kama ta cikin nutsuwa tace Sannu kin ji sister ki bi a hankali da akwai dinki a jikin ki.
Kallon ta nayi kamar ban gane mai take nufi ba, rigar jikina na kalla ganin Jallabiya ce yasa ni saurin rintse idona abinda yaron nan ya min yana dawowa a Kai na.
Kuka na fashe da shi kawai cike da takaici da bakin ciki, ni kadai nasan abinda nake ji akan wannan wulakancin da yayi min har ciwo yaji min ashe.
Ganin yadda take kuka yasa Doctor Hafsa fara rarrashin ta tana mata fada kuma a nutse akan yadda tayi gardama bayan mijin tane sbd yadda taga abin tasan tazo da gardama, cigaba da fada mata yadda zata kula da kan ta tayi har ta warke.
Suna cikin maganar ya turo kofar ya shigo hannun sa rike da yar karamar jakar daya sako mata hijab.
Ganin yadda take kuka yasa shi karasowa ciki da sauri, hannun sa yasa ya riko duka kafadun ta cikin kulawa yace “ina ke miki ciwo *NOORIE*”
Bakin ciki ne ya cika mun zuciya jin sunan daya kira ni da shi ni Wallahi tsanar sa ma nake ji a rai na sbd irin wulakancin da yamin bayan yasan auren da muka yi.
Ban dai ce komai ba sbd Doctor da take gurin, sallamar mu tayi shi da kan sa ya zira min hijab sai wani rawar jiki yake yana ta jero min Sannu.
Da kyar nake taka wa Ina hawaye sai goge hawayen nake amma wasu ke zubo wa, a mota ma ko uhm ban ce masa ba sai magana yake mun yana bani hakuri da lallashi ko kallon sa ban yi ba bare yasa ran zan basa amsa.
Muna zuwa gida na bude kofar na fito da kyar cike da dauriya na shiga takawa, Ina jin tahowar sa a bayana ban tsaya ba kuma ban juya ba har na isa kofar part dina.
Bude kofar nayi na shiga a dan tsanake nabi ko Ina da kallo ko mai fess sai kamshi palon yake da alama Binta ta gyara ko Ina.
Sama na shiga hawa da kyar Ina hawaye har na isa daki na, Ina zuwa na shiga toilet na rufe kofar, ruwan dumi na tara a bathtub mai yawa na shiga ciki Ina gasa jikina ina kuka, sai da naji dan dama dama sannan na nayi wanka nayi alwala na fito daure da towel.
Duk da na gan sa zaune akan kujerar dake dakin ban nuna na san yana gun ba na tsaya bakin mirrow na dibi abubuwan da nake da bukata na bude wardrobe ma na dauki kayan da zan sa na shige toilet.
Ajiyar zuciya Abdallah yayi cikin shakkar ta, shi Wallahi bai taba jin yana tsoron mace ba sai ynxu da yake jin tsoron Husna yana kama sa, so yake yaje yayi mata magana amma ya kasa sbd yana tsoron abin da zai fito daga bakin ta…….
DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 33
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
A hankali rayuwa take tafiya yau har nayi wata biyu da aure kuma wata daya kenan da sati biyu da abin nan ya faru.
A cikin kwanakin nan nayi matukar mamaki yadda Abdallah ya cika alkawarin sa, ko hannu na bai kara rike wa ba ko da a kuskure ya dan taba ni cikin azama zai matsa gefe yace min nayi hakuri, duk ranar daba ranar girki na ba zai shigo da Asuba ya duba ni kuma zai shigo da daddare ya min sai da safe, in kuwa ranar girki nane baxan iya kirga sau nawa yake shigo wa ba in har yana gida.
Tsakani na da shi sai dai gaisuwa da kuma girki da bana fashin masa breakfast da dinner In weekend ne dai nake masa lunch, a kan dining nake ajiye masa da daga baya kuma kawai in har na gama sai na kai masa part din sa, bana fashin gyara masa part dai duk ranar girki na.
In nace ban yi kewar sa ba nayi karya don duk da uwar azabar da na sha a hannun sa amma in na tuna da abubuwan da yamun kafin naji azabar sai tsigar jikina ta tashi, ni ynxu ba wai mai azabar nake so ba kawai dai ayi romance dai amma ban san yadda zan tunkare sa da wannan maganar ba don abin da kunya ai.
Gashi tun Ina nuku nuku da naji abin dai ni zai wahalar sai na fara shigar daukar hankali duk lokacin da nasan zai shigo sai na ki sa hijab in kuwa dare ne haka zan sa rigar bacci mai shara shara amma baya kallona in yaga irin shiga ta ma baya dade wa yake fita dà sauri, wannan abun ba karamin daga min hankali yake ba.
A bangaren Abdallah kuwa ba karamin tashin hankali yake ciki ba na rashin Aasmaa, duk ranar girkin ta a wahale yake kwana kuma ya riga yayi wa kan sa alkawarin baxan taba ta ba har sai da amincewar ta, shaukin sa daya yana da Yusrah wacce sai ynxu yake kara ganin kimar ta sosai.
Da akwai lokacin da yana bacci yana mafarki Aasmaa sai kiran sunan ta yake yi ashe Yusrahn wacce ta tashi tana sallah tana Jin sa, sai da ya farka take ce masa in har yana kewar Aasmaa din ne ta yafe masa kwanan ta yaje gurin ta daga haka ta mike ta dauki carbin ta ta bar dakin.
Wannan abun ba karamin kunyar Yusrah ya kara masa ba, Washe gari da safe haka yayi ta boye boyen ido baya so su hada ido ita kuwa tayi ta tsokanar sa tana kwaikwayon yadda yake yi daga karshe kawai sai ya biye mata shikenan maganar ya wuce.
Kullum cikin tura wa Aasmaa yake da sakon soyyaya baya gajiya da tura mata bata taba masa reply ba amma bai damu ba so yake ta amince da soyayyar sa ta kuma yadda cewa ba wai jikinta yake so ba.
Amma Allah ya sani ya jigatu matukar gaske da rashin ta, ko hannun ta yake rikewa yasan da ya rage har yar rama yayi sbd kewar ta shi dana sanin dandana zumar tata ma yake tun da ai da bai san yadda take ba yncu kuwa azabtuwa kawai yake yi akan ta.
*****
Ina zaune a palo sanye da riga