Showing 36001 words to 39000 words out of 61405 words

Chapter 13 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3783

on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 22




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




A tare muka shiga gidan ina gaba yana bina a baya, dan turus nayi ganin Yaya da Maryam wacce take rike da jaririn ta tana basa madara sai Umma da Umar a zaune da alama magana suke mai muhimmanci.


Dukkan su zuba mana ido sukai ganin haka yasa na shigo Ina yake gabana ban da faduwa ba abinda yake yi, tsoro na kar Umma ta dago shirin mu shiyasa duk nake ji na wani iri.


Gaisawa muka yi da su na shige daki nace bara na chanja Kaya.


Su dai nasu ido don yadda nake ta wani abu kamar mara gaskiya.


Abdallah da yake zaune a kusa da Umar ya kalli Umma yace “Umma magana ce mai muhimmanci nazo da ita”.


Mai da hankali Umma tayi kan sa tace “Ina jin ka Babana Allah yasa dai lafiya”.


Dan sosa girar sa yayi yana sunkuyar da kai haka kurin yaje Jin wani nauyin ta a ran sa.


Da mamaki Umma take kallon sa yadda yake yi din ya nuna kunya yake ji a akan abinda zai fada.


Da kyar ya jawo dauriya yace “dama mun daidaita kan mu ne da Husnaa..”


Zaro ido yaya tayi tace “wace Husna din?”


Dan kallon ta yayi ganin mamaki sosai a fuskar ta yasa ta fuske yace “Husna dai ta gidan nan”.


Umma da take zaune kamar an dasa ta kasa gane komai jira take yayi mata bayani wace Husna sai ji tayi yace ta gidan nan ita dai tasan Asma’u Husna daya ce a gidan nan kuma a yadda ta san Aasmaa baxa ta taba soyayya da kanin bayan ta ba.


Ganin dai dukkan su mamaki ya kama su yasa shi gyara zama yace “Umma ai tun kafin ki samu hatsari dama na san ta a restaurant din su kullum nan nake zuwa cin shawarma toh ita kuma taki kula ni sbd tana ganin nayi mata yaro da ywa”.


Dan tabe fuska yayi kalar tausayi yace “kwatsam kuma sai gani a gidan nan, toh daga nan dai na cigaba da takura mata har ta yadda take dan kula ni muyi hira a waya shima sai da aka kafa mun sharuda”.


Sosa kai yayi yana mamakin kan sa shifa bai iya karya ba gaskiya amma ji bi yadda ya zauna yana tsara zance kamar ya faru da gaske.


Maryam data matsu taji cigaban maganar sa tace “muna ji Yaya Abdallah”.


Watsa mata idon sa yayi jin ta Kira sa da yaya shi fa a iya sanin sa Abdallah take ce masa wato don yace yayar ta yake so shine zata fara ce masa wani Yaya ba, lumshe ido yai yana hasaso sai na sun ganta da cikin sa tukunna🏃‍♀️🏃‍♀️


“Cikin haka maganar aure na da Yusrah ya taso, nayi tunanin zata fara university ne kamar yadda muka tsara sai kuma wani dalili yasa aka mana auren, a so na da in auren ya tashi na hada su biyun na aura hakan bai yi ba”.


Yusrah kanwa tace “mahaifin ta shine a matsayin mahaifina, mijin Mamina neh kuma aminin baba na”.


Dan shiru yayi don tuno da cewa ko fuskar mahaifin nasa bai taba gani ba sai a hota kuma shima baban nasa bai san me aka Haifa masa ba mace ko namiji.


D’ago wa yayi yana murmushi don boye abin da yake taso masa yace “mahaifina ya rasu tun kafin nazo duniya, ni kadai ne dan sa sai ynxu da Mami ta haifa min wasu yan uwan”.


“Baxan boye muku ba Ina son Yusrah matata kuma ba wai don ta rage ni d komai zan kara aure ba tun da can kafin na aure ta dama Ina son auren Husna”.


“A cikin satin nan naga tana cikin damuwa ko waya muke bata bani attention shiyasa na je gurin aikin ta yau take sanar da ni maganar kawu shine nazo in kin amince Umma mune tare ni da Umar yau gurin Kawun gobe in sha Allah manya na zasu zo ayi maganar auren”.


Ajiyar zuciya ya sauka yana Jin kumatun sa na dan masa zugi sbd maganar da yayi da yawa.


Umma kuwa murmushi kawai take yi tana fadin Alhamdulillah a ran ta, hankalin ta bai kara kwanciya da Abdallahn ba sai da yace yana son Matar sa kuma ba abinda ta rage sa da shi wannan yana nuna ko gaba zai kara wani auren baxai wulakanta mata Aasmaa din ba.


Mike wa tayi kawai ta shiga daki, duk bin ta da kallo sukai kowa yana addu’ar Allah yasa ta amince don su fa dama tuni suke fatan wannan abin ya tabbata.


Karo muka yi da Umma don Ina labe a jikin kofa ina jin yadda yake tsaro zance Ina addu’ar Allah yasa kar ya kwafsa, da yace wai yana son Matar sa tabe baki kawai nayi Ina kokayar maganar tasa don haka kurin naji rai na ya dan sosu.


Kallona Umma take kallon daya sa na ji kunya ta Kama ni nayi saurin matsawa baya.


Murmushi tayi tace zauna Aasmaa magana zamu yi.


Gyada kai nayi na zauna akan sallayar dake shinfide akan red carpet din palon.


Ita ma zama tayi tana kallona tace “yaushe kuka fara soyayya da babana amma ban sani ba kuma da alama a cikin yan uwan ki ba wanda ya sani shima”.


Kara sunkuyar da kai nayi gaba na yana faduwa, da kyar na bude baki cikin rawar murya nace “gani nake kamar za’a min dariya ne Umma tun da na gama cika baki baxan yi soyayya da mai karancin shekaru ba”.


Murmushin manya Umma tayi tana hasaso wani abu a maganar su amma kuma koma meye tun da dai aure suka so suyi zata yi ta addu’a Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma zaunar da su lafiya har karshen rayuwar su.


“Nasan kinji duk abinda babana ya fada ynxu in har kin yadda zaki aure sa zasu je gurin Kawun ki kuma zai sanar da gida gobe azo ayi maganar aure kin yadda”.


Hawaye naji yana kokarin zubo min ga yadda gaba na yake faduwa ynxu in na yadda shikenan haka kowa zai dinga kallo na ana min dariya cewa zan auri yaro, tuno maganar mu da shi ne yasa na daga wa Umma kai kawai Ina mike wa na shige daki da sauri.


Hannu Umma ta daga tayi addu’a hawaye yana zubo mata, hawaye ne na farin ciki yau Aasmaa ta amince zata auri wani Alhamdulillah Ya Rabbi.


Fito wa tayi fuskar ta dauke da murmushi tace “nayi magana da ita Babana kuje tare da Umar din gurin Kawun naku Allah ya tabbatar da alkhairi”.


Wani guda Yaya da Maryama suka saki a tare suna cewa Alhamdulillah.


Shi kan sa Umar murmushi kawai yake yi yana addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi.


Tare suka fita a motar Abdallah Umar na nuna masa hanya har suka isa gidan Kawun.


A kofar gida suka tsaya Umar ya aiki yaron Kawun ya ma kawu magana yana tare da bako.


Suna tsaye kusan minti 10 sannan kawu ya fito yana fadin “meye kuma zaka wani zo da sanyin magribar nan to in ma kudi kuke bukata bani da shi”.


Kunya da takaici ne suka hadu suka rufe Umar, kamar yayi kuka don takaici yake kallon Kawu.


Gaisawa sukai da shi yana kallon Abdallah yana mamakin meye hadin wannan balaraben da Umar kuma.


Umar ne ya nuna Abdallah yace “kawu dama wannan shine saurayin Yaya Aasmaa yazo ne don ka gansa kamar yadda ka bata lokaci kuma yana so gobe ya turo iyayen sa”.


Zaro ido Kawu yayi cikin tashin hankali yace “Kace shine saurayin Asma’u kuma”.


Daga kai Umar yayi cikin tabbatar wa.


Goge gumi Kawu y shiga yi cikin tashin hankali shifa ya fada ne amma bai taba tunanin Asma’u din tana da saurayi ba, ya riga ya sakankance Alh Inuwa zai aura mata ko dan ya cigaba da karbar kudi a gurin sa.


Bude baki yayi zai yi magana Abdallah daya zuba masa ido kawai ya Mika masa bandir din 500 , 50k kenan.


Cikin rawar jiki Kawu ya damke kudin yana mici mici da ido yace “kudin zancen ne ka bayar ynxu na dauka dai iyayen ka sun zo ai”.


Girgiza kai Abdallah yayi yace “Baka nayi ka sayi goro”.


Zaro ido kawu yayi yana manne kudin a hammatar sa yace “duka ni ka bawa dubu hamsin ne fah”.


Daga masa Kai kawai Abdallah yayi.


Murmushi ne ya kwace wa Kawu yace “Sannu da zuwa Alhaji ai kayi hakuri dazu ban ma tarba mai kyau ba na zata irin samarin nan ne masu lalata yaran mutane ashe da gaske kake auren ne ya kawo ka”.


Shiru Kawu yayi yana tunanin yadda zai kara karbar wasu kudin a hannun Abdallah, ai shi yadda Abdallah ya masa kyauta dubu hamsin tashi daya Wallahi Aasmaa ko bata son sa sai ya aura masa ita, duk tsawon kyautar da Alh Inuwa yake masa in aka hada baza su kai 20k ba gashi tashi daya an basa 50k ai gaba ta kai sa.


Kallon Abdallah yayi yace “dama ban so fada maka ba amma ganin zaka aure ta y Kama ta na fada maka, da akwai kudin zancen ta dana karba a gurin wani wanda yake son ta, a tunani na bata da wani saurayi sai na karba kuma aka samu matsala kudin na cika na bayar a fara mata gado, kaga ynxu bansan yadda zan yi na mayar masa da kudin ba”.


Umar ne yayi saurin kallon Abdallah yaga mai zai yi ji yake kuwa kamar ya daura hannu a ka ya dinga zabga Ihu yana kukan bakin cikin da kawu ya jawo musu.


Murmushi Abdallah yayi yace “nawa ne kudin Kawu”.


Washe baki Kawu yayi yace “dubu dari ne dannan”.


Gyada kai Abdallah kawai yayi ya nufi gurin motar sa bai dade ba ya dawo hannun sa rike da rafar 1k guda biyu.


Mika wa Kawun yayi yace gashi ka basa kudin sa ragowar kuma a sha ruwa.


Godiya kawu y shiga masa har yana yi kamar zai durkusa kasa.


Shi dai Abdallah bai ce komai ba sai jan hannun Umar da yayi suka wuce suka bar Kawu yana ta zabga godiya.


Kawu kuwa kudin kawai yake yana tunanin yadda zai shiga gari ya zabo cancareriyar budurwa yayi wuf da ita…




A bakin layi ya sauke Umar ya wuce gida gabansu don samun Alhaji gabansa yana faduwa bawai fada wa Alhajin ne yake kayar masa da gaba ba sai Yusrah daya ke tuno wa….




Kuma ganin Alhaji da Mami zasu yadda


Ya Yusrah zata ji💔🥹












DijahAM
09066728387










Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️












*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃




*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 23


Dedicated to Maman Rumana❤️ Uwa ta gari Allah ya tsare ki a duk inda kike ya raya miki zuri’ar ki Ina alfahari da ke Mama❤️🥹




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Jikin sa a sanyaye ya shiga cikin gidan, bai nufi ko Ina ba sai part din Alhaji.


Da Sallama ya shiga palon sai dai yayi dana sanin shigowar don kuwa Alhaji ne zaune tare da Mami tana yanka masa fruit a wani plate mai kyau suna hira.


Ganin yadda ya tsaya a bakin kofar ne yasa Alhaji cewa ka shigo mana Abdallah.


Murmushin yake yayi ya shigo ciki a hankali, yaso matuka ace bai samu Mamin anan ba don yaso ace sai ya gama da Alhajin ya kuma amince sannan zai tunkari Mamin.


Gaishe su yayi ya ja gefe yayi shiru ya zuba wa TV ido yana kallon news bawai don yana fahimta ba.


Kallon juna Alhaji da Mami sukai kafin Alhaji ya budi baki yace “son”.


Juyo wa Abdallah yayi ya zuba masa idon sa da sukai jawur.


Murmushi Alhaji ya masa yace “mene yake damun ka son, ka fada mana damuwar ka kaji kaga gani ga mahaifiyar ka a zaune, tun da ka shigo na lura hankalin ka a tashe yake kuma magana ce a bakin ba”.


Ajiyar zuciya Abdallah yayi ya dan saci kallon Mami, kawar da kan sa yayi ganin yadda ta zuba masa ido tana kallon sa.


Jikin sa duk sanyaye don sai ynxu yaga wautar abin da yayi amma kuma in ya tuna da cewa Husnaa za’a aura ma wani sai yaji eh tabbas abinda yayi shine dai dai, da za’a aura mata wani ya tabbata haukace wa kawai zai yi.


Kara sauke ajiyar zuciya yayi yace “Alhaji abinda ke tafe da ni nasan ba yadda zai muku dadi amma don Allah kuyi hakuri dai”.


Murmushin karfin hali Mami tayi tace “muna sauraran ka”.


Sunkuyar da kai yayi murya a tausashe yace “dama kafin na auri Yusrah akwai wacce muke soyayya”.


Dan dagowa yayi yaga yadda iyayen nasa duk suka zuba masa ido, yana kallon yadda Mami take masa da ido alamun yayi shiru kar ya cigaba shi dai ya kawar da kai kawai.


Lumshe ido yayi yace “a da nayi tunanin zan aure su ne su biyu a lokaci daya toh komai sai ya chanja na auri Yusrah din, muna tare da ita na mata alkawarin bayan 2years zan aure ta toh ynxu matsala aka samu mahaifin ta ya rasu Abba, Kawun ta ya bata sati daya ta fito da miji in ba haka ba zai aura mata wani tsoho da yake nacin zuwa gurin sa”.


“Yau ne kwana shida dazu naje gurin sa na gaishe sa shine yace ba turo iyayena a gobe cikar sati, in ba haka ba jibi zai karbi kudin tsohon can, kuma auren ya hada dana yar sa ne nan da sati 5 yake so ayi”.




Mike wa Mami tayi da sauri tace “wallahi baka isa ba, sbd kana so ka jawo min zagi Abdallah so kake ace sbd kana auran yar kishiya ta shine na zuga ka zaka sake aure yarinya ko rabin shekara bata yi ba to bada yawu na ba baxan taba yadda ba Wallahi ne yarinyar nan ta maka da zaka saka mata da wannan abun Abdallah”.


Alhaji ne ya Kira sunan ta a nutse, idonta daya soma tara hawaye yake kalla, bakin cikin ta shine wani irin zagi zata sha ga Hajiya Bilki kusan kullum tana hanyar gidan tana cewa tayi hakuri ta sa Abdallah ya auri Meena wai Meena din duk ta zabga bata da aiki sai kuka ita dai sai dai tace mata tayi hakuri in Abdallah ya sauko zata masa magana ba wai don zata masa maganar ba kuwa don tuni ta gode Allah daya sa Abdallah din bai auri Meena din ba yarinyar Sam bata da tarbiyya.


Ko mawa tayi ta zauna tana kara hade rai sosai


Murmushi Alhaji yayi yace “Hajiya shin kallon baban Yusrah kike min kawai bakya kallona a matsayin baban Abdallah ko dan sbd bani ne ainahin mahaifin sa ba”.


Da sauri Mami ta juyo tace “Subhanallahi haba Alhaji taya zaka yi wannan maganar don Allah”.


Murmushi yayi yace “in har kina kallona a matsayin mahaifin Abdallah me yasa zaki ce bada yawun ki ba, Haba Maimuna ban san ki da haka ba, yaron nan kin ji abinda ya fada dama can suna tare da yarinyar nan kuma ynxu ga abinda Kawun ta yace so kike yana kallo ya rasa masoyiyar sa, yana da inda zai sa ta ba wai bashi da shi ba zai iya dauke mata dukkan bukatun ta kiyi hakuri don Allah ki bisu da addu’a kawai kin ji”.


Gyada kai tayi ta mike ya fice daga palon ta wuce bangaren ta.


Kallon Abdallah Alhaji yayi yace ka kwantar da hankalin ka kaji gobe in sha Allah ni da Alhaji Muhammad(baban Musbahu) zamu je muyi maganar auren kuma in sha Allah baxa a daga ranar auren ba kaji.


Gyada kai Abdallah yayi kunya ta gama lullube sa har bai san yadda zai daga ido ya kalli Alhajin ba.


Tunanin Yusrah daya fado masa ne yasa shi Jin wata faduwar gaba, dagowa yayi a hankali ya kalli Alhaji yace “Abba don Allah ka fada wa Yusrah kaji”.


Murmushi Alhaji yayi anzo inda yake so tun da aka fara maganar yake tunanin ta ko ya zata ji in maganar ta isa gare ta, kuma daga dukkan alamu ko wace Abdallah din yake son aura ba karamin kauna yake mata ba don kana iya gani a idon sa yadda yake maganar cike da shaukin da shi kan sa bai san yanayi ba, tsoro yake ji kar Abdallah da Matar da zai aura su wulakanta Yusrah din tunda ai yafi kowa sanin cewa Abdallah baya son Yusrah ya aure ta ne kawai sbd ya taimake ta.


Gyara zama Alhaji yayi yace “Abdallah shawara zan baka shine a yau in ka isa gida ka zaunar da Matar ka ka fada mata zancen auren da zaka yi, matukar ka bari gari ya waye muka je muka kai kudin gaisuwa to labari zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login