Showing 45001 words to 48000 words out of 61405 words

Chapter 16 - Asma Book Completed by Dijamah.txt

06 Jan 2025

3793

naki nan”.


Murmushi nayi nace “Allah ya saka da alkhairi kuwa”.


Hira muka shiga yi na dauko musu breakfast din da Yusrah ta kawo suka ci.


Aunty Murja ce sai Yayar Umma sai kuma matar kawu sai Yaya da Maryam da Basma.


Aunty Murja ce ta mike ta kalli matar Kawu tace “to mu tafi Furera tun da mun zo mun ga yarinyar kuma Alhamdulillah guri yayi kyau Allah ya bada zaman lafiya”.


Hade rai furera tayi tace “ke kuwa Murja daga zuwan mu sai mu tafi ko huta wa bamu yi ba”.


Tabe baki Aunty Murja tayi tace “me zamu zauna yi Toh Furera Ina ce mu manya ne ai abin kunya ne ma sirikin mu ya shigo ya ganmu gotai gotai da mu a zaune”.


Yayar Umma ce ta mike ita ma tace “da gaskiyar Murja fa Furera ki tashi mu tafi kawai ai ga su Maryama nan zasu dan taya ta zama ko”.


Ba dan Furera ta so ba ta mike suka fita tana bata rai.


Dariya muka sa dukkan mu bayan fitar su, Yaya ce taja tsaki tace “Allah y shirye ta Wallahi daga ita har mijin nata duk ba halin kyau”


Ni dai ban yi magana ba sai Murmushi kawai da nayi, taya ni suka yi muka gyaro gidan gaba daya aka Kara sa turaren wuta, wajen 2 sai ga mai aikin Yusrah ta kawo mana abinci.


Godiya nai mata na bata basket din safen da basma ta wanke ta juya dasu.


Yaya ce tayi Murmushi tana cin white rice din tace “Allah dai ya baku zaman lafiya Aasmaa amma da dukkan alamu kishiyar ki bata da damuwa”.


Murmushi nayi nima nace “gaskiya bata da matsala Yaya da safen ma fa da kan ta ta kawo min breakfast din da alama tana da hankali”.


Sai bayan La’asar su Yaya suka tashi tafiya kafin nan sai da Yaya ta matsa na sake wanka ta fito min da wata doguwar riga fitted gown wacce ta kama ni sosai duk motsin da nayi sai jikina ya motsa.


Tire kaga tsiya nayi wanda ya matukar daukar kan nawa sosai nayi kyau har na gaji sai kamshi nake, mayafi na yafa muka sha hotuna dukkan mu akan Maryam zata nuna wa Umma sannan muka sauko.


Robobin dana zubawa Yusrah dukkan kayan garar na bawa Basma a cikin wata babbar leda tun da sun ce zasu leka gurin ta in suka fita.


Kamar zanyi kuka haka nayi musu sallama na koma sama ba tare dana rufe kofar ba, tunanin Umma ne yake damuna da kuma kewar Umar gaba daya sai nake ji na wani iri.


Waya ta na janyo na kunna data wacce ban cika kunna wa ba don chatting ba wai ya dame ni ba.


Ina zaune Ina kallon reels a instagram wanda sai ynxu da nake zaman kadaici sannan nake jin dadin sa naji kamar an bude kofar palo an shigo.


Shiru nayi don jin ko waye ni sai ynxu ma na tuna cewa ban rufe kofar ba.


Jin kamar muryar Yusrah tana kiran Aunty ne yasa na mike na zira flat shoe dina red color mai gashi a jiki Wanda na ware don yawon cikin gida na shiga sakkowa a nutse.


Tun da na soma sauko wa suka zuba min ido dukkan su ukun, ni dai fuska ta dauke da Murmushi har na Kara so cikin palon.


Zama nayi akan kujerar dake fuskantar wacce suke zaune a Kai nace “Sannun ku”.


Murmushi Walida tayi tace “lafiya qalau Amarya Ina wuni”.


Murmushi nima na mayar mata nace “lafiya qalau ya gida”.


A hankali tace “Alhamdulillah”


Mai da kallo na nayi gurin Yusrah wacce take kallona tana Murmushi a ran ta kuwa addu’a kawai take amma maganar gaskiya ta rude da ganin surar Aasmaa, ba wai ita ma bata da structure mai kyau bane kawai dai na Aasmaan kirar ta mai jan hankali ne sosai.


Murmushi na sakar mata nace “Sannu Aunty”.


Dan zaro ido tayi da mamaki tace “lalala Aunty ni kike cewa Aunty kuma”.


Yadda tayi din sai ya bani dariya don haka nayi Murmushi nace “eh mana ai gaba kike da ni a gidan nan dole na baki girman ko”.


Girgiza Kai tayi tana Murmushi tace “A’a gaskiya Aunty bana son Auntyn nan kawai ki ce min Yusrah”.


Bata bani damar magana ba ta nuna Walida tace “wannan yaya tace” sai ta nuna Teema tace “wannan kuma yayata ce ita ma dakin su daya da Yayana”.


Murmushi nayi nace “Sannun ku da zuwa”


Kallon Teema din nayi naga sai wani yatsine yatsine take Murmushi na sakar mata nace “sannu kanwarmu”.


Kallona tayi tana tabe baki tace “yauwa amarya”.


Mikewa nayi na shiga kitchen don kawo musu abin sha.


Teema ce ta kalli Yusrah tace “tabdijan ynxu wannan ce kishiyar ki kalli fa yadda ta matse jiki kamar wata karuwa sai wani Murmushi take”.


Hade rai Walida tayi tace “Teema ban miki magana ba wai wallahi kika kara wata maganar sai na fada wa Abba”.


Ba don ta so ba tayi shiru a ran ta kuwa mamaki take wai wannan ce ta girmi Abdallah.


Babban tray dana dora drinks da cups na ajiye sai wani tray din dana dora kayan gara.


Yusrah ce tayi saurin cewa “Aunty da kin bar su Allah kin kai min da yawa fa”.


Murmushi nayi nace “ai wancan a part din ki ne nima anan sai na samu ladan”.


Suna zaune ya shigo yana amsa waya, kamar zanyi kuka haka nake ji sbd yadda nake ta samun sabani sai lokacin da nake zaune cikin shigar da bana so sannan yake zuwa.


Kashe wayar yayi suka gaisa dasu Walida sannan ya kalli inda nake na zuba wa TV ido kamar wani abu nake kalla bayan ba abinda nake kalla din.


Murmushi yayi yasan dalilin ta na juyawa shi kuwa ai haka yake so yayi ta zuwa a lokacin da bata so din


Juyowa nayi jin ido a kai na ai kuwa idona ya shiga cikin nasa, kallon da yake min yasa na fahimci abinda yake nufi kawai sai na samu kai na da rage kaifin kallon da nake masa cikin tattausan harshe nace “barka da zuwa”.


Lumshe idon sa yayi yace “yauwa Husnaa”.


Walida data lura da yanayin da kanwar ta ta fara shiga ce ta mike tana Murmushi tace “bara mu wuce amarya”.


Mike wa nayi nima nace “Ngd sosai kuwa Allah ya mai da ku gida lafiya”.


Raka su nayi har bakin kofa suka fita sannan na rufe kofar.


Nazo daidai tsakiyar palon Ina kokarin juya akalar lafiyar tawa zuwa sama kawai naji yasa hannu ya fisgo ni jikin saa….










MEENAA






DijahAM
09066728387










Salamu alaikum💃💃💃💃


Kuna ina mata masu daraja wadan da suke son su gigita Oga a tsotse masa man kai🥵🥵🥵🥵


Ga dama ta samu ku garzayo gurin Innar Nawaz domin ta tsuma amarya da uwar gida, sai dai Kiji ana gidan dadi na na baki kyaurar Nigeria gaba dayan ta😎😎😜.


Muna siyar da tsumin tabajeee🥵🥵🥵, Zumar kiba kiyi bulbul gwanin sha’awa ko Ina ya cicciko ki dinga juyi kina rausaya ana tana hankalin mai house😎💃💃


Muna gumba Kala Kala da gari wanda ake sha da madara ko nono, da akwai ragumi da akala daga Jin sunan kun san cewa ba’a magana kawai a ozar room🥵🔥🔥🔥🔥


Bafa anan muka tsaya ba muna da dan matsi, wato gangariya ne ko hannun ki baxai shiga ba sbd yadda zaki matse kina kamo Oga😉😉.


Kun san ita mace yar kamshi ce, a ko yaushe mu an san mu sa tsafta da kamshi, muna siyar da turare Kala Kala masu kamshi da dadi wanda zasu kwantar da hankalin Oga ya dinga manne miki yana lalubar ki😉😉🔥🔥


Domin samun wannan Kaya masu sauki ku tuntubi wannan number din
+234 809 699 9490


Bissalam❤️❤️












*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃




*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰




Page 28




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM








MEENAA


Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba ita da Hajiya Bilki lokacin da suka ji maganar Abdallah zai Kara aure.


Kuka ta shiga yiwa Hajiya Bilki ta daga mata hankali ita kuma ta shiga zarya gidan Mami akan kar ta yadda ayi auren ta tilastawa Abdallah ya auri Meena kawai tun da ita yar uwar sace kuma tana son sa.


Ita ce tayi bincike mai zurfi akan Aasmaa din taje ta fadawa Mami cewa tsohuwa Abdallah zai aura don ta fi shekaru 30 ta girme sa.


Da Mami taga abin nasu ba hankali ne taja wa Hajiya Bilki babban warning akan Abdallah cewa bata isa tasa ta yiwa dan ta dole akan ya auri yar ba, tun da ya nuna baya son ta su rabu da shi mana suyi nata addu’a ta samu wanda ya fisa, wannan abin ya bakan tawa Hajiya Bilki rai sosai ta kuma yi alkawarin in sha Allah Meena ta rabu da Abdallah har abada.


A bangaren Meena din ne dai ita wannan sam bai dame ta ba don haka tama ci damarar neman yakin Abdallah don tayi rantsuwa ko da bala’i sai ta aure sa……






******


Wani mugun kallo na masa Ina kokarin raba jikina da nasa, kara janyo waist dina yayi dole kirjin mu suka hadu.


A masifance na kalle sa nace “wani irin Iskanci ne wannan Abdallah ko ka manta wace ni ceh..”


Lumshe idon sa yayi yana tura kan sa cikin wuya na yana shakar kamshin dake tashi a jikin ta.


Da sauri na rintse idona jikina yana fara rawa, ni kadai nasan kalar tashin hankalin da nake ji, tun da su Umma suka fara bani kayan da’a dauriya kawai nake yi amma gaba daya a rikice nake gashi kuma wannan yaron yana neman dagula min lissafi.


Dago kan sa yayi ya zuba ma fuskar ta ido ganin yadda ta rintse ido jikinta na rawa, murmushi yayi cikin wata kasallaliyar murya yace “Husnaa sha’awa kike ji”.


Da sauri na bude fuska ta ba tare dana shirya ba, wani mugun kallo na jefa masa kafin na tattaro duka karfina na hankada sa.


Daki na shige na rufe kofar Ina sauke ajiyar zuciya gaba daya hankali na a tashe yake, sai mammatsa kafa nake sbd azaba wata kwalla ce ta zubo min nasa hannu na goge ina ja masa Allah ya isa.


Shi kuwa Abdallah lumshe idonsa yayi yana sauke ajiyar zuciya, gaba daya ma ba’a nutsuwar sa yake ba don haka a daddafe ya fita ya shige part din sa don naso da ya leka Yusrah.


Cikin kwanakin da suka wuce nayi su cikin kewar gida matuka da taka tsan-tsan, in har bana daki to da hijab na ke yawo kuma har yau ban far girki ba Yusrah ce take kawo min.


Oga kuwa tun ranar daya min iskanci ban kara ganin sa ba, in na ajiye breakfast da lunch din da aka kawo min zan samu ya ci ya bar plate din akan dining, ni hakan ma yafi min sbd dama don shi take guduwa falon sama in ta sauko kasa to an yi knocking ne ko kuma zata dibi abinci.


A lissafi ta yau take cika kwana bakwai kuma yau zai koma gurin matar sa rai na fess ko ba komai zan dan sake a part din.


Zaune nake a falon sama da misalin 10 na safe, chatting nake da Salma ina fada mata nan da sati daya in sha Allah zan koma aiki.


Ban ji tsayuwar sa ba sai kamshin turaren sa dana ji ne yasa ni juyawa a hankali na kalle sa, yana tsaye cikin shigar kananun kayan da suka masa kyau sosai suka kuma fito da kuruciyar sa.


Dauke kai na nayi kamar nan gan sa ba na juya Ina jira ya gaishe ni tun da ai nice gaba da shi.


Shi ma hade rai yayi sosai don so yake ya fara nuna mata waye gaba da ita, a dake yace “baki iya gaisuwa ba”.


Juyo nayi na zuba masa lumsassun idona da suke rufe wa kamar mai jin bacci, harara ba sakar masa Ina hade rai nace “wace zata gaishe ka?”.


Gira daya ya daga min yace “Amaryata mana”.


Tabe baki nayi nace “kasan dai ni ba sa’ar wasan ka bace ko?”


Zame takalmin sa yayi ya shiga takowa kan carpet din a nutse, zuba mata ido yayi fuskar sa a hade ya ciro key a aljihun sa ya ajiye akan kujerar da take zaune.


Zuba mata sexy eyes din sa yayi cikin hade gira yace “kije ki gyara min part dina, shi ne a tsakiyar naku kuma ki ajiye key din a gurin ki duk ranar girkin ki kije ki dinga gyara mun kuma a gurin ki zan dinga cin abinci”.


Wani kallo na masa Ina so nayi magana amma yadda ya hade tan nan sai naji baxan iya fada masa maganar da zata kara harzuka sa ba don haka kawai na sauke ido na na mayar kan TV.


Tabe baki yayi ya juya ya fice yana tunanin dole fa sai ya koya wa Husna hankali don ya gama karantar sa ita gaba daya auren su baya kan ta shi kuwa ai ko yanka sa ake yi baxai iya sakin ta ba.


Sai da naji rufewar kofar palo sannan na turo baki gaba Ina kunkuni, a rai na nake cewa bawai don ya isa ya sani aiki bane zan dinga gyara masa part din kawai dai sbd kar matar sa ta shiga girki taga part din a hargitse ta mun kallon kazama.


Mike wa nayi na dauki Hijab dina da yake gefena na zira na sa takalmi na dauki wayata da key din na fito, rufe kofar part dina nayi da key na nufi part din sa da yake tsakiyar namu.


Key na sa na bude kofar na shiga baki na da sallama, palo ne babba wanda zai kai nawa na kasa girma sai wata kofa daga gefe da alama guest toilet ne, daga karshen palon kuma corridor ne don haka na nufi corridor din kawai, ban yi wata tafiya mai tsayi ba na bulli cikin wani katon palon da zai yi biyun na farko, ware ido nayi Ina bin palon da kallo cike da mamaki, kujeru sai ti biyu ne a palon sai daga karshe dining ne wanke gefen sa kuma kichen ne dan dai dai irin na cikin palon nan.


Ajiyar zuciya na sauke ina tunanin yadda zan gyaro wannan katon palon, kofofi biyu na gani gefe na nufe su na farko bedroom ne kato da toilet na biyun kuwa girman sa za’a iya yin palo da daki da kitchen da alama shine master bedroom hadda kujeru shima anan.


Zage wa nayi na shiga gyara part din ban samu Kai na ba sai wajen 1 don ba inda ban gyara ba kuma ban wanke ba, koma wa part dina nayi na dauko turaren wuta nazo na saka, sai da na jira duk suka gama kone wa har a toilets na saka sannan na rufe part din a gajiya ba koma nawa.


Ga yunwa Ina ji kuma nasan dai dole yau zan shiha kitchen ai tama yi min kokari sosai.


Wanka ma fara yi na zira simple doguwar rigar atampa na sauko kasa don yunwa nake ji sosai duk na gaji gashi dama da safe ni ma na gyara part dina ba inda ban gyara ba, gashi Yaya tace sai nayi sati biyu zata sa wacce take kawo mata mai aiki ta samo mun don aikin gidan da wuya sosai.


Noodles kawai na dafa a kitchen din ma naci sbd wahala ko wanke wanke ban yi ba na fada dakin kasa na kwanta akan gado Ina sauke ajiyar zuciya.






YUSRAH


Yau ta tashi da farin ciki sosai sbd zata karbi girki ba karamin missing din Yayan nata tayi ba don ya riga ya saba mata da kullum sai ya neme ta shiyasa yau da zata karbi girki sai rawar jiki take yi.


Tsawon sati dayan ta yi su ne cikin Ibada kullum karfe uku na dare take farkawa baxa ta koma bacci ba sai tayi asuba ta mika lamuran ta ga Allah shiyasa take jin ta cikin kwanciyar hankali.


A gefe guda kuma gyara kan ta take sosai, Mami da kan ta ta aiko mata da babbar jarka ta tsumin baure da tabaje, wuni take tana shansu ai kuwa tana gani aikin su gashi yau tun safe bata ci abinci ba hadin kankana tayi kwallo biyu ta wuni tana shan kayan ta, da kwakwa da dabino a gefe(kun san kuwa yau dole Aasmaa ta toshe kunne don za’a haukata Oga ne😜)


Kafin 4 ta gama girkin ta tsaf, jira tayi har 5 tukun ta mike ta nufi part din Abdallah don gyara masa, a gyare ta same sa sosai bata san lokacin da Murmushi ya kwace mata ba ga kamshi mai dadi da part din yake.


Ko Ina ta shiga ta duba taga komai neat sannan ta koma ta shirya.


A daren ranar kuwa ta gurzu a hannun Yayan nata don sai da ta dawo tana rokon sa ya taimaka ya rabu da ita, ganin da gaske ta ji gata ne yasa shi kyale ta ba wai don ya gaji ba.


Ita kam Yusrah bin da take da ido kawai tana mamakin yadda yake ta rawar kafa kamar ba daga gurin amarya yake ba…..










DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj




🥀🥀🥀🥀🥀

Aasmaa

🥀🥀🥀🥀🥀



Written by
DijahAM


Free book neh 🥰

Dedicated to Abubakar Musa Sulaiman😂😂


Page 29




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




Wanka na fito ina tunanin wai yau ni ce wacce nayi sati biyu da aure, ajiyar zuciya na sauke ina sauri sauri na shirya don na tafi restaurant.


Gama shirya wa nayi cikin Riga da zani na dora Hijab babba har kasa, so nake nayi sauri na je kar naji magriba don yau zan karbi girki Ina so na dawo na masa abinci, tun da na fahimci baya wasa da cikin sa yasa nima bana masa wasa da abinci breakfast da dinner kullum suna kan dinning table na shirya plates da su serving spoons, bana sanin lokacin da yake zuwa yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login