Showing 60001 words to 61405 words out of 61405 words
sa ya kwanta, Murmushi na sakar masa nima cike da tsokana nace “ynxu ka dawo Yayanmu da muka sani”.
Murmushi ya saki shima yace a da ai rabin zuciya tace kawai a gefena a ynxu kuma na samo ragowar rabin kinga an tashi zuciya daya kenan ai dole ki ganni fess.
Dariya nayi nace Maa sha Allah.
Hannu na Mika masa muka yi musabaha nace “barka da sallah Hub”.
Murmushi ya saki yace “barka da sallah Nisful Hayat”.
A tare muka fito sai fara’a muke yi, a zaune a motar na samu Yusrah tana zaune ita ma da Hijab din ta tayi kyau sosai.
Tana hango mu ta fito tace “Barka da Sallah Aunty”.
Hararar wasa na mata nace “sai ynxu kika tuna kika da Auntyn”.
Rufe fuska tayi tana dariya tace “afuwan Auntyna kiyi hakuri don Allah”.
Murmushi na sakar mata kawai kafin mu tafi sai da muka yi hotuna sosai, ni na fara karbar wayar sa nace bara na musu shida Yusrah, sannan Yusrah ta karbi wayar ta mana mu biyu ni da shi sai muka yi mu uku sannan ya mana ni da Yusrah.
Mun yi kyau sosai tun a gurin ya turawa kowa hoton wayar sa.
Haka muka je idi muka dawo cikin farin ciki, a part din sa muka zauna muka ci abincin Sallah gaba dayan mu a tray daya sannan kuma muka sake shirya wa muka fita.
Gidan mu muka fara zuwa muka yi wa Umma Barka da sallah sanna muka tafi gidan su anan muka wuni sai dare muka dawo.
Yawo muka sha da sallar nan don da mota ta nake je gidan mu na wuni, a rana daya kuma naje gidan Yaya da gidan Maryam.
Tun bayan sallah na dai na lafiya kenan kullum bani da lafiya da yau ciwon Mara gobe ciwon kai.
Abinci kuwa na dai na ci ma gaba daya kullum kunu ne abinci na, ko girki zan yi sai na sa face mask in ba haka ba amai zan ta kelaya.
Ranar dana kwana da zazzabi Washe gari ya dauke ni muka tafi asibiti aka dibi jinina.
Doctor Husna ce ta mana albishir din cikin da nake dauke da shi na wata biyu.
Sosai ya dinga murna don tun a asibitin ya Kira Yusrah ya fada mata.
Kullum cikin tattali na suke shida Yusrah sbd cikin yazo min da laulauyi sosai bana sati sai an kara min ruwa a haka Yusrah ta haihu lafiya ta samu baby boy ne Kama da Abdallah.
DijahAM
09066728387
You should read "Aasmaa" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/story/329112037?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=DijahAM&wp_originator=V1PLaustqUbJzsXd6Subht8nHXyopa29268W8RAoajngqkxEg2myYkKSL8%2BgemhwRtCBFS0idZMmpBlNdLrJFDkBvLIngq8aYPr%2FYKDw7NXYIN%2BZSJnKcMsdvHLZJFHj
🥀🥀🥀🥀🥀
Aasmaa
🥀🥀🥀🥀🥀
Written by
DijahAM
Free book neh 🥰
Page 40
🔚🔚🔚🔚🔚
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Yusrah taso tafiya gida amma Abdallah ya kekashe ido yace ba inda matar sa da dan sa zasu tafi dole haka ta hakura.
Ranar suna yaro yaci sunan baban Abdallah Ahmad muna ce masa Aryan.
Nayi mata kayan barka masu kyau na kai mata har Umma dasu Yaya kowa sai da ya kawo mata atampa.
Haka har suka yi arba’in kusan kullum Aryan yana guri na sai yayi kuka ne kawai nake bayar wa a Kai ma Yusrah ta basa nono.
Kwanci tashi har cikina ya shiga watan haihuwa lokacin watan Aryan 4 yayi kiba sosai ya fara zama ga wayo a cikin sa.
Ranar Juma’a Allah ya sauke ni lafiya na haihu lafiya wanda da har za’a min aiki sbd yadda na jigata sai kuma gashi na haifo baby girl dita katuwa Tubarkallah mai Kama da Baban ta sak.
Lokacin dana farka yana zaune a gefena sbd haihuwar dare ne bai fada wa kowa ba bayan Yusrah da tasan mun taho.
Kallon sa nake naga yadda ya zuba wa babyn ido yana kallon cike da so.
Murmushi na sakar masa nace “Hub”.
Da sauri ya tashi ta taho kusa dani fuskar sa dauke da Murmushi, yarinyar ya ajiye a kan gadon ta sannan ya dago ni ya gyara min za mana.
Dauko min ita yayi ya dora akan cinya ta yace “kinga Babyn mu Husnaa ta” We .
Lumshe ido nayi hawaye yana zubo min na riko hannun sa a sanyaye nace “don Allah Hub ka yafe min dukkan abinda na maka”.
Murmushi yayi yace “ni ba abinda kika min Yar Aljanna”.
Sunan daya Kira ni da shi ne yasa ni lumshe ido nace “I love u Abdallah”.
Da sauri ya zagayo ta gabana ya zauna akan gadon yace “me kika ce Noorie”.
Murmushi nayi Ina sunkuyar da kai nace “I love U Babyna”.
Wata kyakyawar runguma ya min nida Babyn cikin tsantsar farin ciki yace “ina kaunar ki Nima sosai Noorie ta”
Washe gari aka sallame mu muka koma gida anan na cigaba da je go na Aunty Murja ce tazo ta zauna da ni, tana kula da ni da babyn data ci sunan Mami muna ce mata Iyman.
Sai da ta min kwana arba’in sannan ta tafi ta bar mu cike da kewar ta.
Zaman lafiya muke yi a gidan Abdallah don yana kokarin yin adalci a tsakanin mu wannan yake yayyafawa kishin mu ruwan sanyi.
Kamar yadda rainon Aryan ya dawo hannu na haka na Iyman ya koma hannun Yusrah.
MEENA
A ynxu rayuwa ta mata zafi sosai don kuwa baban ta da ya gaji da yawan samarin da take yi Kai tsaye ya bawa abokin sa auren ta don dama ya taba masa maganar ya nuna kin amince wa.
Ba kalar borin da Aunty Bilki bata yi ba daga karshe dole ya hakura don kuwa baban MEENA yace ko ta yadda ko kar ya yadda aure ba tashi amma ta sani in har ta cigaba da daga masa hankali zai bata red card dole ta hakura tayi shiru.
Tana ji tana gani aka yi auren MEENA da abokin baban ta.
Ita ma Meenan da farko ta tayar da hankalin ta sosai daga baya dole ta hakura tabi Mijin ta duk kuwa da cewa Abdallah na nan makale a ran ta.
Bayan auren MEENA na dade wa Baban ta ya Kara aure, ba kalar haukan da Hajiya Bilki bata yi ba karshen dauke matar sa yayi suka bar kasar bai dawo ba sai bayan wata hudu lokacin matar ciki ne ma da ita.
Da farko har yaji sai da Hajiya Bilki tayi ta tafi mamabila amma Iya da kan ta ta dawo da ita dakin ta dole ta hakura ta zauna.
Bayan wasu shekaru…..
A ynxu yaran Abdallah 10 cif, Yusrah nada hudu uku maza mace daya sai Aasmaa dake da hudu 3 maza 3 mata.
Daga haihuwar Iyman tayi twins duka maza, sai ta kara haifo namiji sai autan su suma twins ne mata.
Kan yaran a hade yake baka iya banbance wace mamar su don sun hada ne gaba daya sun runguma.
A ynxu Yusrah da Aasmaa ko wannan su ya mallaki supermarket manya guda biyu biyu bayan shagunan da Abdallah ya mallaka musu a kasuwar kwari.
Sauri nake na karasa shiri na don ma yaran basa part dina gaba dayan su suna part din Yusrah wai yau acan zasu kwana.
Kara mulke jikina da lafiyyar humra nayi sannan na zira hijab na dau karamar waya na nufi part din Hub dina.
Ban same sa a palo na daki na shige kawai, yana zaune kuwa yana danne danne a system din sa.
Murmushi nayi na nufe sa Ina Murmushi, shima ture system din yayi ya janyo ni kan cinyar sa.
Cikin tsokana yace “kin kara nauyi Noorul Qalb”
Turo baki nayi a shagwabe nace “naji din”
Murmushi yayi yana zare hijab din yace “meye sirrin Noorie kullum kara kyau kike yi”.
Shafa gemun sa nayi nace “kai ne sirrin Mijina, tun daga ranar daka shigo cikin rayuwa ta nake ganin haske Kai Alkhairi nane Mijina, Allah ya saka maka da gidan Aljanna ya baka ikon cigaba da yin adalci a rayuwar ka”.
Murmushi kwance a fuskar sa yace “Ameen Noorie gaskiya aure zan kara ma don yadda kuke sani kwanciyar hankali imagine na karo muku wata”.
Wata harara na sakar masa ina Murmushi nace “lallai ni da kanwata da kuwa mun murkushe ka daga Kai har amaryar tak”.
Dariya yayi shima ya mike dani a hannun sa yace “ni ma kun ishe ni a duniya dai in sha Allah, Allah ya muku albarka”.
A zuciya ta na amsa da Ameen don bakin tuni ya hade da nasa yana bani zazzfan sako ni kuwa Ina anshewa….
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH
Allah na gode ma daka bani ikon gama wannan littafi lafiya abinda na rubuta dai dai Allah ka bamu ladan sa Wanda nayi na kuskure Allah ya yafe mana.
Ngd sosai My Fans da irin kaunar da kuka nuna min a wannan littafin Allah ya bar mu tare.
Fatan zaku nuna min soyayya a sabon book din da zan yi in sha Allah na kudi🥹🥰❤️
Mrs AM AKA DijahAM
09066728387