Showing 1 words to 3000 words out of 61883 words

Chapter 1 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10800

[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1






*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*





NA






MAMAN AFRAH






☀️ *First Class Writers Asso* ☀️


Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation




*GARGAGAƊI*


Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.






PAGE 1




Zaune take a matsakaicin falonta kan kujera mai zaman mutum ɗaya, inda take tsefe gashin kanta wanda ya rage saura guda ɗaya rak ta gama tsifar. Sai da ta karasa, ta taje sannan ta fito daga falon ta nufi bedroom ɗinta wanda yake jere da falon da yake irin ɗakunan nan ne da ake yi wa lakabi da mu koma aji. Tsaye ta yi gaban mudubi tana karewa kanta kallo, fara ce tas sai dai tana da matsakaicin tsawo doguwar fuskarta mai yalwataccen gashin gira manyan idanunta da suke ɗauke da zara-zaran gashin ido, hancin ta irin wanda ake yi wa lakabi da tamkar biro, gashin kanta baki wuluk wanda ya zuba har bayan kafaɗarta. Cikakkiyar halittar da take da ita daga sama har kasa wacce kowace mace za ta so a ce ta mallaki hakan, wannan kyawun halitta da Allah ya mata shi ya sa kawayenta suke mata kirari da MATAR MANYA amma sai dai kash! An samu akasin lissafi domin kuwa buri da mafarkinta bai cika ba a nata ganin kenan da kuma ganin wasu daga cikin kawayenta. Kasancewar ta auri mutumin da take ganin ba shi da sunan da ya dace a kira shi illa mai na sama ya ci bare ya ba na kasa ba.


"Wannan ita ce kaddarata, sai dai na tabbata ba zan dawwama a hakan ba, dole na samarwa kaina mafita ko ba jima ko ba daɗe sai mafarkina na MATAR MANYA, ya cika domin ba zan lamunci zama da kaddararran auren kafinta ba" Ta furta a fili tana kara karewa cikakkiyar halittar da take da ita kallo wacce tana ganin har yanzu dai ruwa bai karewa ɗan kada ba akwai sauran rina a kaba.


Wani uban tsaki ta ja lokacin da ta hango hoton ABBAS ta cikin mudubin wanda yake jingine a gefen gado, tana jin wani haushi da takaici tabbas ba shi ne mafarki da burinta ba, shi ɗin da mai gadin gidanta ya dace sai ga shi kaddara ta haɗa aure a tsakaninsu, hakorinta ta saka ta dantse leɓanta na sama tana mai kankance idanu janyo ribon ɗinta da yake kan madubin ta yi ta haɗa gashin wuri ɗaya ta yi parking ɗinsa, dakyar ta samu ta haɗa wuri guda saboda tsawo da kuma cikarsa. Fitowa tsakar gidan ta yi ta rasa ma mai yake mata daɗi saboda kugin yunwar da cikinta yake, kicin ta karasa ta buɗe ragowar sauran tuwon jiya wanda kasancewar ba shi da yawa ABBAS ya hakura ya ce ita ta ɗumama ta ci gawayi ta kunna ta saka tuwon cikin miya ta ɗora. Karan wayarta da take ta ruri a falo ya sa ta taho kafin ta zo kiran ya katse har ta juya saboda idan ta ɗauko wayar ma hakan ba shi da amfani saboda bata da kati bare ta bi kiran, shigowar wani kiran ne ya dakatar da ita ta koma ta ɗauki wayar EESHART shi ne sunan da yake yawo a kan wayar.




"Wai ina kika shiga ne kawata na miki sako saman whatsapp na ga bakya online yanzu ina kiranki ma shiru"


"Data ce ta kare mini" Ta ce tamkar ta saki kuka.




"Kai innalillahi gaskiya SALIMAH kin saka kan ki cikin wani hali ke yanzu data ma sai take gagararki, kamar dai ke kika rako mata duniya to shi kuma kiran da kika ki ɗauka fa?".




"Ina kicin ina ɗumama tuwo...


"Tuwo!?" Ta ce tamkar ta faɗi wani mugun abu. Shiru ta yi saboda takaici ya gama cika mata zuciya.


"Dama abubuwan da ƴar aiki ta dafa mini wanda nake son na ci, na ɗauka a hoto na turo miki, yam balls, chicken pepper, wainar kwai sai shayin da na saka aka juye madarar gwangwani ta ruwa uku don ruwa ma kaɗan aka zuba" Ta ce jin ta yi shiru SALIMAH a take yawunta ya tsinke ta ji dama ita ce a cikin daular da kawar tata take.


"Ai tun da kika zaɓi zama cikin talauci kin dinga ganin takaici kenan, ni fa sai a wajenki ne nake jin sunan tuwo, don rabona da na saka shi a bakina tun ina gidanmu shi ma kin sanni sai na ga dama nake ci"


."To wai ya zan yi ne EESHART kin san dai bani da ikon sakin kaina shi kuma ABBAS yadda kika san da igiyar aurena aka halicce shi ya ce muddin yana numfashi ba zai taɓa sakina ba kin san irin mutuwar da ya yi a kan sona...


"Yo dama ya za a yi ya yarda ya saki mace kamarki, bayan ya samu tsuntsu daga sama gasasshe ai ya sani idan ya rabu da ke ba zai samu kamar ke ta aure shi ba, bayan ya san sa'a ya taka amma ki cigaba da gwadawa shi aure ai rai ne da shi daga wa'adinsa ya cika dole a rabu ko ba a so"


"Haba EESHART kina ganin shekara biyar kenan ina fama amma bai sake ni ba".


"Ki dai cigaba da gwadawa domin da gwado jirgin sama ya tashi"

Da to ta amsa mata suka yi sallama bayan ta ce za ta saka mata datar da kati. Da tunanin mafita ta ajiye wayar tana jinjina ranar da za ta dace ABBAS ya furta mata kalmar saki ko da a cikin baccinsa ne ko da suɓutar baki ne don ta fita ta auri miji na kece raini ta rayu a gidan hutu wannan shi ne mafarkinta wanda marigayin Babanta ya yi fatali da shi a cewarsa ABBAS ne da ya dace da ita shi ne mai kaunarta da gaskiya duk runtsi duk wuya sai ga shi bayan auren Baban ya mutu kuma ABBAS ya ki sakinta har yau.




Kicin ta koma tsabar tuno abin da kawarta za ta ci da kafa ta yi ball da karamar tukunyar tuwon da ta ɗora ya kuwa kife a kasa ta juya falon ta dawo kuɗin da ABBAS ya bata ta ba almajirinta ya auno shinkafa da kayan miya a yi abincin rana shi ta zari dubu ɗaya ta fita ta buɗe kofar gidan nasu wanda yake gidan haya ba mallakin ABBAS ɗin bane.


Tana buɗe kofar idanunta ya sauka a kan gidan makocinsu Alhaji ALI wanda gidan yana kallon gidan nata, iya ganinka gida ne da aka kashewa dukiya don kuwa gida ne aljannar duniya gida ne da take mafarkin samu irin gidan nan ko da mutum bai rayu a ciki ba in har yana sa hangen na sama da shi tare da raina matsayin da Allah ya ajiye shi to kuwa zai so ko sau ɗaya ne tak ya shiga gidan ya kashe kwarkwatar idanunsa. Ta yi nisa a zancen zuci ta shagala da kallon gidan bata ankara ba sai gani ta yi an wangale get ɗin gidan motar da aka buɗe get ɗin don ita ce ta fito kallon yadda motar ta haɗu tare da yin shekin sabunta ne ya ɗauki hankalinta bayan sauran da take hangowa daga cikin get ɗin wanda suke fake wasu a lulluɓe wasu a buɗe.


Alhaji ALI da yake bayan motar direbansa yana jansa ne ya yi gam da katar da ganin SALIMAH cike da mamaki yake ganin kyawunta da kuma kira da Allah ya mata kyakkyawa ce ajin karshe, tsantsar mamaki ne ya kama shi ganin cewar mace kamar wannan tana rayuwa a kaskantaccen gida kamar wannan domin yanayin shigarta ko ɗankwali babu ga rigar jikinta da ta kama ilahirin jikin nata hakan ya nuna matar gidan ce ba wai zuwa ta yi ba.




Tsabar kallonta da yake har sai da ya sauke glass ɗin motar, ido huɗu SALIMAH ta yi da shi da yake bakin glass ne baka ganin na ciki amma na ciki yana ganinka ita kuma kyan motar take karewa kallo tana kiyasta ranar da za ta shiga mota kamar wannan. Ganin sun haɗa ido sai kawai ta diririce ta shiga ɗagawa almajirin da ta gani yana bara a wani gidan da yake gefen gidanta hannu alamar ya zo, hakan ya yi daidai da saita hancin motar da direban ya yi a inda suka saka gaba. Har waiwayenta Alhaji ALI yake har sai da suka ɓace daga layin sannan ya daina waiwaye.


Karan rufe get ɗin ne ya saka ta sauke ajiyar zuciya tare da maida hankalinta kan almajirin ta ce.


"Je ka wurin mai biredin wancan ka siyo mini bidredi na ɗari uku kwai guda biyu madarar sachet guda ɗaya" Robarsa ya bata ya tafi ta dawo ta ajiye robar jim kaɗan ya shigo da sallama.


"Kwan ɗari biyu da hamsin-hamsin madara kuma ɗari da saba'in" Ya ce yana mika mata ledar da canjin naira talatin ɗin.




"Rike canjin" ,Kawai ta ce ta juya ya ce Allah karɓa ya ɗauki robar tasa ya juya ya fita, ko amsa masa bata yi ba ta wuce kicin ɗin saboda yunwar da take kwakular ƴaƴan hanjinta ta dafa ruwan zafi ta soya kwan ta dawo ta haɗa shayi ta zauna ta ci ta koshi. Sai lokacin ta ji dama-dama a kan kwaɗayin da EESHART ta tada mata.




Tana nan tana danne danne a waya ta shiga nan group ɗin a whatsapp ta fita saboda datar da EESHART ta turo mata, wani group na bussines ta shiga inda admin ɗin ta turo hotunan lesuna da dogayen rigunan abaya, wata mata da user name ɗinta aka rubuta matar mai kumbar susa ita ce ta zaɓi lesuna guda uku dogayen riguna guda biyu ta ce a mata total a tura mata acc no ta private ko ragi bata nema ba kusan dubu ɗari uku.


"Kuɗi sun yi a rayuwa" Ta ce tana kallon lesunan tana hango yadda da ita ce ta same su ba karamin kyau za ta yi a ciki ba amma ina bata da ko irinsa guda ɗaya ma dama ko kayan lefe bai mata ba Babanta ya ce ABBAS ya kawo kuɗin da ya sawwaka ai aure albarkarsa ake nema kuma aure yana kawo arziki.



Yanzu shekara biyar da auren amma babu wani ci gaba sai ma ci baya gabaɗaya talauci ya musu kaka gida ga tsadar rayuwa rashin isassun sutura ya sa ko biki da suna bata son zuwa idan ta je sai ta ga ta raina kanta musamman in ta ga kawayenta sun yi shiga ta kece raini ita kuwa daga atamfa leda sai leshin mama ta mutu irin na legas ɗin nan da ake sayarwa na hannu.




Saboda haushi bata san ma lokacin da ta fito daga bussines group ɗin ba, wajen status ta je nan ma ta shiga ganin hotunan da aka ɗaɗɗora a status wanda na jikin hotunan suke sanye cikin shiga ta alfarma wasu an musu make up gashi nan dai amma duk ciki bata ga wacce ta mallaki ko da rabin kyanta ne ko kirar halittarta. Wani hoton wata mata da ta gani a status ɗin wata kawarta matar tana zaune a kayataccen falonta da yaranta guda uku da alama yarinya ɗaya ce ake yi wa murnar zagayowar ranar haihuwar ta domin ga cake nan da lemuka.


"Gida na alfarma shi ne rayuwa" Ta ce a fili tana sauka daga whatsapp ɗin ma baki ɗaya ta ajiye wayar tana sauke idanunta a nata falon wanda sai ta ga tamkar a kufai take.




"Ga doya da kwai" Ta jiyo wata tana tallah. Kiranta ta yi ta saya ta dubu ɗayar ragowar kuɗin abincin ranar da yake doyar ɗari bibbiyu ce ta zauna ta ci ta yi sallah ta kwanta bacci ya yi awon gaba da ita.




ABBAS tun da ya baro gida ya nufi ƴan kafintoci inda yake aikin kafinta haka ya wuni yana aiki, ko da ya ji kewar matarsa SALIMAH ya yi ta kiranta a waya amma bata ɗauka ba haka ya gaji da kira ya hakura. Bai karya ba ya fita saboda tuwon kaɗan ne ko dubu biyun da ya bar mata ma rantowa ya yi haka ya wuni bai ci komai ba sai karfe biyar ya baro kafintocin. Tun da ya doso gidan gabansa yake faɗuwa duk da hakan ya san yana faruwa da shi amma sai yake jin kamar na yau ya fi kullum hannu ya saka a aljihu ya fito da kuɗin ladan aikinsa da aka biya shi dubu uku da ɗari takwas, mayar da su ya yi yana son gano ko kuɗin za su isa ya famshi kansa a wajenta duk da ya ranci kuɗi da safe don ba ya so ta zauna babu abinci, a duniya da SALIMAH ta rasa abu gwara shi ya rasa ko ta halin kaka yana iya bakin kokarinsa don ganin ya faranta mata amma bata ganin hakan kullum gazawarsa take gani kullum burinta ya sawwake mata auransa amma ba zai iya sakinta ba sakinta babbar barazana ce ga rayuwarsa gani yake ba zai iya rayuwa a wannan duniyar matsawar ba tare da ita ba, amma ita sheɗan da muggan kawayenta suna mata huɗubar banza ta ganin sun kawo karshen zaman sa da ita.




Da sallama ya shigo gidan amma shiru ba a amsa ba, dama ya saba da hakan amma kuma rashin amsa sallamar ba zai sa ya daina yi ba saboda wajabcin sallamar da kuma ladan da ake samu idan an yi sallamar.


Buhunsa mai ɗauke da kayan kwale-kwalensa ya ajiye a inda yake ajiyewa kicin ya nufa domin samarwa cikinsa da yake ta kugi abin da zai sa a ciki sai dai tun kan ya karasa kicin ɗin yake hango tamkar dai babu wasu alamu na an ɗora wani abu, hakan ce kuwa ta tabbata da ya karasa domin idanu huɗu da ya yi da tuwon safen da ya sadaukar shi ga SALIMAH shi ya ɗauki na annabawa. Wani ɓacin rai ne ya ziyarce shi shaiɗan ya azalzala zuciyarsa yana jin wani tukuki inda ya haɗu da ɓacin ran da yunwar ta haifar. Amma yaki ya yi da zuciyarsa wajen dannewa ya nufi falon.


Tana zaune a kasan ledar tsakar ɗakin tana yin magana da alama voice take yi sai da ya jira ta kammala ya dube ta ya ce




"Haba SALIMAH yanzu in fita tun safe in dawo amma babu abin da kika dafa, kuma tuwon da na hakura na bar miki kika zubar da shi a kasa yanzu a halin da mutane suke ciki na tsadar rayuwar nan wasu ma suna kwana da yunwa, wasu suna mutuwa da yunwa wasu dusar awara suke ci ke har da wanda suke sakawa ruwan ɗanwake suga suna sha amma ke...




"Kai ABBAS dakata! Ba fa haifata ka yi ba da za kake mini magana faɗa-faɗa"


"Haba SALIMAH mene ne na faɗan a nan daga faɗar gaskiya sai cibi ya zama kari...




"Bana son jin komai yanzu don ban yi girki ba za kake wani maimaita mini magana ai hukunta ni ya dace ka yi, sannan batun tuwo,tuwo,tuwo kana maimaitawa tamkar ka samu karatu mene ne don na zubar da tuwon bana ci sai kawai in ci kuma su masu kwana da yunwar ai su suka so dama rayuwa ai hawa-hawa ce tun da ba ni na hana su neman abin da za su ci ba, wasu ma basu san mene ne wani tuwo a rayuwarsu ba daga nama sai kayan daɗi irin rayuwar da nake mafarkin yi, irin burin da na ci ka zo ka mini shigar sauri ni ba tsararka bace ni ba sa'ar aurenka ba ce ba ajinka ba ce ni ABBAS sau nawa kake so in maimaita maka cewa na tsaneka ka sake ni in je in auri wanda yake daidai da tsarin rayuwata, inda zan huta wani nawa ma ya huta wallahi wallahi wallahi ba zan taɓa kashe yarintata a wannan kaskantacciyar rayuwar talaucin ba!"




Yadda take maganar cikin hargowa da ɗaga sauti ya sa gabaɗaya ya rasa bakin magana, ta saba masa hakan a kullum wani lokacin ma tsakar dare yana bacci take tada shi da wannan masifar da zancen saki ya sha faɗa mata babu kyau mace take neman saki a wajen miji ba tare da wani kwakkwaran dalili ba na cutarwa ko makamancin su amma kururuwar shaiɗan ba ta bari ta fuskanci komai sai ta ce ita kuwa take da hujja domin kuwa cutar da ita ake yi, saboda wata sabuwar rayuwar take so ba wannan ba. Sai dai yau maganganun nata sun masa zafi da yawa wani ciwo yake ji a zuciyarsa musamman saitin kirjinsa daga hagu inda zuciyarsa take dashe a wajen tabbas in bai yi wasa ba SALIMAH tana dab da saka masa ciwon zuciya don hawan jini tuni ya haɗu da shi.




"SALIMAH" Ya faɗa da sanyin murya yana jin yadda kwalla ta taru a idanunsa, ga wani nauyi da yake ji a zuciyarsa tamkar an ajiye dutse a wajen.


."Sunan da ubana ya dasa mini" Ta ce tana rike da kugu tana wani jijjiga jiki.


."Na sani dama, amma don Allah ki bar zuciyata ta huta ina kaunarki SALIMAH na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login