Showing 60001 words to 61883 words out of 61883 words

Chapter 21 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10813

yi ta faɗa mata amma banda dokokinsa da maganar haihuwa.


"Sakaran banza to ta Allah ba tashi ba da ya ƙi saninki ƴa mace kansa ya yi wa ai ya yi wa arziƙi dundu kuma zai dawo ya same ki ai kujera ce ke ko don ya zauna zai neme ki da tsohuwar zuma ake magani" Ta ce tana jin ciwon abin da aka yi wa ƴarta.


"Yanzu ni ban san ya zan yi ba ko na faɗawa su EESHART da RUKY su zo dannar kirji?"


"Hauka kike SALIMAH son a saka ki a bakin duniya, yadda muka cika baki muna daga ke ba ƙari ya samu mace kyakkyawa kuma yanzu a ji labari ya sauya to wallahi da fita waje ma sai ta gagaremu daga ni har ke, bakin ki alekum ki zauna ke kaɗai wani ma bai san an yi ba, shi kuma abin da ya yi ya je don kansa, saboda wallahi ba don mai kuɗi ne ba da a ce ABBAS ne ahalil fuƙara'u ba zan raga masa ba sai na wanke shi tas"




"Ai shi ABBAS cewa ya yi ba zai mini kishiya ba " Ta ce cikin sanyin murya tana tuna yadda yake roƙon ta zauna da shi ba zai taɓa haɗa ta wata ƴa mace ba amma ga shi a kwana uku da aure ranar na huɗu za a danƙara mata kishiya. Haka suka zanta da Umma suka yi sallama Umma sai ashat take luƙawa tana tsinewa Alhaji Tahir.


Nan ta kwanta bata tashi ba, yau ko yunwar ma bata ji, wajen ƙarfe takwas ta ji an turo ƙofar falo tana jin ƙaran sauran ƙofofin ɗakuna ana buɗewa ana rufewa wannan ya nuna mata cewa Alhaji Tahir ne ya zo nemanta shi ne yake duba ɗakunan ko zai ganta amma ganin bata nan bai kuma buɗe inda take ciki ba ya koma falon ƙasan ya zauna a kujera ya kame yana danna waya.




"SALIMAH" Ya ƙwala mata kira, sai da ya yi sau uku don ya ɗauka tana sama ma shi kuma ba ya son ya hau saman, fitowa ta yi ba tare da ta amsa ba, sanye yake da blue shaddar sabuwa dal sai sheƙi take ya sha babbar riga da hula ga agogo takalmansa suna ƙafarsa gabaɗaya falon ya buɗaɗe da ƙamshin turarensa. Sau ɗaya ya ɗago ya ganta da rigar bacci idanun nan jeme-jeme tana aika masa kallon tsana ta ƙaraso ta zauna a wata kujerar da ban.




"Kin tashi lafiya? Tsakanin sama da ƙasan wanne kika ɗauka? Zan fita ƙarfe goma za a ɗaura auren"


"Ƙasa" Shi ne kawai abin da ta ce.




"To ita amarya ASEEYA sai ta ɗau saman" Ya ce yana tashi tare da gyara babbar rigarsa ya fita, da harara ta bi bayan nasa tana maimaita sunan amaryar a zuciyarta.




Wai "ASEEYA" Ko daɗi babu.




Haka ta wuni suƙuƙu babu walwala yau ko charting ɗin ma ta kasa yi bata ganr komai zuciyarta kawai zafi take ashe haka mata suke ji in za a musu kishiya? Har gwara wasu sun ɗauki shekaru amma ita fa kwana uku a kwana ukun ko da ango bata tare ba. Bayan ta idar da sallar isha'i tana falon a zaune ta doka uban tagumi tana jiran zuwan ƴan kawo amarya, ƙaran buɗe get ne ya sa gabanta mummunan faɗuwa don ta ɗauka ƴan kawo amaryar ne amma abin mamaki ƙaaran shigowar mota ɗaya ta jiyo sai aka rufe get ɗin wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana fatan Allah sa ba a ɗaura auren ba, don a tunaninta Alhaji ne ya shigo gidan. Tsayuwar motar ta ji tare da buɗe ƙofa da rufewa sau biyu, tana ta saƙa da warwara ba ɗauki wani lokaci ba ta ji an turo ƙofar falo ido ta zubawa ƙofar, abin da ta gani ne ya so zautar da ita babu shiri sai gata a tsaye a kan ƙafafunta, Alhaji Tahir ne goye da wata zankaɗeɗiyar budurwa wacce fuskarta take a lulluɓe irin ta amare.


"SALIMAH rufe ƙofar amarya na goyo wai bata son a zo kawota a taru ni kaɗai na je na ɗakkota kuma shi ne wai ba za ta taka da ƙafarta ba sai na goye ta kin ji rigima irin ta amare ko" Ya ce bakinsa washe kamar gonar auduga yadda dai yake washe mata baki lokacin tana gidansu amma zuwanta gidansa ya sa dariyarsa ta yi ɓatan dabo sai yanzu da yake cike da shauƙin ya goyo amarya.




"Aunty SALIMAH ina wuni" Ta ji wata siririyar muryar amaryar da take bayan Alhaji ta faɗa. Basu jira cewarta ba kawai ya doshi matakala suka bar ta a tsaye tamkar an dasa ta a wajen, da kallo ta bi su sai da suka gama hayewa ta hango amaryar ta ɗaga mayafi ta mata gwalo ta rufe fuskar tare da ɗago mata hannu alamar bye-bye. Suna ɓacewa ganinta ta durƙushe a wajen ta saki kuka marar sauti, ta fara rarrafawa ta shige ɗakinta ko ƙofar falon da ya ce ta rufe bata rufe ba, a ƙasan cafet ta kwanta ta kamo sunan Umma ta rangaɗa mata kira.


"Allah sa an fasa ba a ɗaura ba" Shi ne abin da Umma ta ce.




"Umma an ɗaura shi fa ya ɗakko amarya goye da ita ya shigo falona, suka haye sama"


"Shegu aniyarsu ta bi su, marar riƙe alƙawari na mamajon banza na mamajon wofi" Umma ta shiga surfa faɗa tana kumfar baki ita kuma SALIMAH kawai kuka take.




*BAYAN KWANA GOMA*




Alhaji da amarya sai da suka kwashe sati guda suna cin amarci, ta sha ganin takaici tsantsa da bariki, tana zaune a falo za su sakko hannunsu maƙale da juna, amaryar budurwa ce kuma tana da nata kyan daidai gwargwado, sai dai kissarta kaɗai ta isa saka kishiya kuka, kissa take irin ƴar ƙasan nan don hatta zaman falon ƙasa sai da ya gagari SALIMAH saboda gani takaici sai bedroom ta mayar wurin zamanta. Kwanakin amarya suna ƙarewa ya yi tafiya wai zai yi sati guda, dama ko da amarya tana nan ma saboda riɗi a ɓangaren suke basa tafiya nasa ɓangaren kuma SALIMAH ta lura kullum sai ya fita da dare tsakiyar dare amma bata san ina yake zuwa ba. Ganin yau kwanasa uku da tafiya kuma ya ce sati guda zai yi ta saka a ranta yau sai ta ziyarci part ɗin Alhaji Tahir, kawai so take ta ga uwar abin da ya saka a ɗakin ya ce ba a shiga wataƙila ma amaryar zai bar wa. Sai da ta bari sawu ya ɗauke babu motsin kowa sha ɗaya da rabi ta ɗakko mukullin da ya bata guda ɗayan nan da ya ce za take amfani da shi ranar bakinta. Har ta ƙaraso part ɗin tana waige-waige na rashin gaskiya, hannunta yana karkarwa ta saka mukullin ta buɗe ta shiga ta rufe ƙofar ba tare da ta saka mukulli ba. Da fitilar wayarta ta haska kasancewar ɓangaren duhu ƙarin, direct sama ta hau duk da bata taɓa hawa ba gabanta yana faɗuwa saboda ya ce kar a shiga amma ita sai ta ga ƙwal uwar daka. Gabas ta yi kamar yadda ya ce tana xuwa ta ga ɗakin, ta haska ta ga sunansa da ya faɗa a rubuce hannunta tsabar karkarwa har wayar neman suɓucewa take amma a haka ta murɗa handle ɗin cikin sa'a ƙofar ta buɗe alamar babu mukulli da sauri ta kutsa kai ciki don ƙarfin hali har da mayar da ƙofar ta rufe.





Ɗakin ya fi kama da a kira shi ɗakin duhu don duk hasken fitilar hannunta ta waya sai ta ga tamkar an dushashe hasken bata gani sosai. Abubuwa da ta gani ne suka kusa tarwatsa ƙwaƙwalwa da zuciyarta, ƙwarangwal ɗin uban jikin mutane, ƙwarangwal ɗin ƙoƙon kan mutane, wasu jajayen kaya a rarrataye ga wasu ƙwarya masu ɗauke da wani abu ja tana haskawa ta ga jini ne a ƙwaraken. Zuciyarta tamkar za ta fasa ƙirjinta ta fito yanzu ta gane dalilin hana shiga ɗakin, wani abu ta gani jikinsa duka glass ne tana haskwa ta ga jarirai guda biyu suna wutsil-wutsil sai da ta toshe bakinta ganin bata saki ihu ba, tana cikin wannan halin ta ji ƙaran buɗe get ɗin gidan bata kawo komai ba duk da ta ji shigowar mota ta san Alhaji ba ya gari sai dai ko Khadija ko Aina'u don ASEEYA tuni ta haye sama ta san bata fita ba tana nan. Ita dai bata san ya aka yi ba amma ta ji an buɗe ƙofar part ɗin Alhaji sai gabanta ya yanke ya faɗi tashin hankalinta ya ninku, Alhaji Tahir da ɗaukan wani muhimmin abu a ɗakin sirrinsa ya dawo da shi, bai san ƙofar part ɗin a buɗe ba don da ya saka mukulli ya buɗe sai ya murɗa ta buɗu ya shigo, sama ya haye don ɗaukan abin da ya kawo shi.




Yana dab da shiga ɗakin wayarsa ta ɗau ƙara, ya ɗaga.


"Oga babu wani abu da ƙungiya za ta nema ban bada shi ba ko mene ne kuwa, ai in dai dodo ya faɗin jinin wanda zai sha a shirye nake na bayar kar ka manta fa uwar da ta kawo ni duniya ma na sadaukar da ita ga ƙungiya dodon tsafin ya yi awon gaba da jininta ta bar duniya ban ga wanda zan gagara bayarwa ba ai in dai a kan kuɗi ne to ba gudu ba ja da baya"




SALIMAH tun da ta ji an hayo sama ta shiga wani tsoron da tashin hankalin da ya fi na da, musamman da aka tunkaro ɗakin da take ciki, ƙaran wayar ya sa ta kusa zauncewa saboda ta san ringtone ɗin Alhaji Tahir ne bata gama sanin tashin hankali ba saka masa rana ba sai da ta ji maganar da yake yi. Jikinta muguwar karkarwa yake fitsarin da ya cika mata mara ne ya kufce yana bin ƙafafunta.


"Surukata? Wacce daga ciki ka san an bada jinin babar Hajiya Khadija fa, au babar ta ukun na gane babar SALIMAH kenan?" Wani bugawa ƙirjinta ya yi da ƙarfi nan take duniyar ta shiga juya mata jin ana maganar sadaukar da jini uwar da ita kaɗai ta rage mata, karkarwar hannunta ce ta saka wayarta kuɓucewa wayar ta faɗa kan wani kofin glass da yake ajiye a wurin cike da jini a take kofin ma ya fashe, wannan ƙaran ne ya daki kunnuwan Alhaji Tahir hakan ya ankarar da shi akwai wani mai ƙararran kwanan a cikin ɗakin...






*A NAN NA KAWO MUKU ƘARSHEN BOOK 1 WANDA YA KASANCE FREE MAI SON JIN YADDA ZA TA KAYA A LABARIN, MAI AKA SANAR DA ALHAJI BUKHARI HAR YA FAƊI BABU RAI? WANE SAKAMAKO ZA SU FUSKANTA A RAYUWARSU? MAI USMAN ZAI YI WA ABBAS? SHIN SOYAYYA TANA ƘULLUWA TSAKANIN ABBAS DA HAWWA? WA ZAI AURI ABBAS HAWWA KO AMRAH? YAYA USMAN FA? YA ZA TA KAYA DA SALIMAH??? DA WASU TARIN AMSOSHIN TAMBAYOYIN SUNA CIKIN BOOK 2 WANDA ZA A BIYA NAIRA 500 KACAL AMMA GA WANDA ZA SU BIYA DAGA YAU LAHDI 12/12025 ZUWA 14/1/2025 ZA SU BIYA NAIRA 400 DAGA NAN ZAI KOMA 500*





*ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHEDAR BIYA TA 09013181851*




*NGD SOSAI TAKU MAMAN AFRAH ALƘALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME* 🥰

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login