Showing 18001 words to 21000 words out of 61883 words
Chapter 7 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
amai Mama ta fito da shi da yake yanzu su kaɗai ne a gidan FAROUQ ya tafi.
Bayan ya gama aman ne ya zauna a kan wani ɗan dakali da yake tsakar gidan, Mama sai kallonsa take da tausayawa, suna cikin wannan halin ne suka tsinkayi muryar ana sallama.
"SALIMAH ce Mama" ABBAS ya ce yana tashi tsaye yana faɗa jin muryar SALIMAH tana ɗaya daga cikin masu sallamar duk da bai ganta ba amma ba zai kasa gane muryarta ba amon muryarta yana ɗaya daga cikin sautuka masu muhimmanci a rayuwarsa. Mama hannu ya kai ta rike shi ganin yana karkarwa kuma duk ya ruɗe ga jikinsa ba karfi, sallamar ta amsa tana jin wani ɗaci a ranta jin ya ce SALIMAH ce.
Cikin gidan suka shigo, su biyu ne, ita da wata kawarta ƴar unguwarsu wacce kusan shekara uku da mutuwar aurenta, ita ma bata yi auren ba har yanzu. Suna wani gani-gani suka shigo gidan su duka suna taunar cingam tana kas-kas cike da rashin kamun kai mayafin nan sakale a kafaɗunsu ko arzikin yafawa bai samu ba.
"Mamar ABBAS ya kike?" SALIMAH ta ce cike da shekiyanci. Shi kuwa garau ya mata da idanu yana kallonta har ba ya son ya kiftawa ya zama tamkar wani zararre, gani yake tamkar yau ne rana ta karshe da zai sake ganinta a rayuwarsa tun da ya yarda ba zai sake zuwa gidansu ba ita kuma ba za ta dawo ba.
"Ina lafiya" Mama ta bata amsa cike da gatsali kamar yadda ta yi don Mama ji take ta tsani yarinyar nan yanzu ma bata so ta shigo mata gida ba za ta fama wa ABBAS mikin ciwon sonta da ta tabbatar ko jinyar nan da ya kwanta ita ce sila.
"Mukullin akurkin kajin can za a bamu za mu kwashe kayanmu" Kawar tata mai suna RUKY ta faɗa tana yi wa Mama kallon up and down.
Ko kala Mama bata ce ba ta ja ABBAS yana togewa amma a haka ta nufi ɗakinsa da shi, sai waiwayenta yake, Mama tana zaunar da shi ya yunkura zai tashi wata harara ta zabga masa da ta sa ya koma ya kwanta a katifar dama ba karfin jikinsa yake ji ba. Mukullin ta ɗauka ya fita daga kofar ɗakin ta tsaya ta jefa musu ta koma ɗakin ABBAS yana jin lokacin da suka fice idanunsa a rufe yana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa sosai.
Da motar ɗaukan kaya suka je da maza uku suka kwashe kayan tas don sauran kayan ABBAS ma a nan aka watsar masa su suna bi ta kai suna wucewa, hatta ledar tsakar ɗakin sai da suka naɗe kayan nasa a dandamalin kasa suka ajiye, da suka gama suka rufe musu gidan. Motar kayan tana biye da napep ɗin da su SALIMAH suke ciki, a kofar gidan Mama suka tsaya, ita da RUKY dai suka shiga da sallama suna wani yatsina. Mama da ta fito daga ɗakin ABBAS jin sallamarsu bayan ta amsa sallamar kafin ta yi magana SALIMAH ta cillo mukullin suka juya suka fice daga gidan. Sosai Mama ta jinjina rashin tarbiya da rashin girmama na gaba tabbas in ba kaddara ba ma babu abin da zai sa ABBAS ya auri SALIMAH don ko hanya basu haɗa ba ya bata rata a komai na daga nagartar tarbiya.
ABBAS da yake cikin bargon da Mama ta rufe shi yana jin karan dirin tsayuwar motar da shigowar su cikin gidan da kuma fitarsu, sannan ya ji lokacin da motar da napep ɗin suka tashi idanunsa kawai ya runtse yana jin wani zafi a ruhinsa.
SALIMAH basu yi masauki ba sai a ƴan kafintoci, in da ABBAS yake aiki saboda rashin mutunci wai a can za ta siyar da kayan haka suka je aka sauke kaya aka yi ciniki aka biya su, gida suka karasa ta sauke tarkace da sauran kayan kicin ɗinta ta sallami masu motar da napep ɗin bayan an shigar mata da kayan gida.
Dubu biyar ta ba RUKY a cikin kuɗin sauran kuma ta ba Umma ta ajiye bayan ta ɗauki dubu ashirin don har kujerun ta siyar.
"Yo ajiyar mai za a yi ke da idan kika fara samun kuɗin sai mun rasa yadda za mu yi da su, ai kawai mu yi cefanen kayan daɗi mi fara wankin ciki tun yanzu, ki ɗauki wani abun ki yi ɗinkunan kafin na kece raini ya zo wato na zawarawa" Cewar Umma.
09013181851
KU MATSO DOMIN JIN DADDAƊAN LABARI
💃💃💃💃💃💃💃💃
. ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM ƊAYA DUBU GOMA 1OK
Shin kin taɓa jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ɗina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc ɗinta ya cika wata shida zai buɗe sai ta cigaba da kwashe kuɗaɗenta.
Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851
[1/5, 8:57 PM] Sadiya Abdulrazak: *RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 6
*ZARIYA*
*Unguwar Gwalagwaji*
Kwance take a kan tsohuwar tabarmar wacce ta shimfiɗa musu zannuwa guda biyu, SABEER wanda ya ɗora kansa a jikinta duk ya takura saboda fitsarin da ya yi ɗan yalolon zanin da ta rufe su ta cire daga jikinta ta rufa masa, a haka bacci ya yi awon gaba da ita kasancewar ayyukan da ta yi ta gaji. Hajiya Rayyanatu wacce ta nufo ɗakin nasu da sanyin safiya ɗauke da ruwa a jug ta shigo ɗakin tana jan wani tsaki tare da toshe hanci, ruwan ta ɗaga ta sheke musu a jikinsu a gigice suka falka SABEER yana sakin kuka da sauri ta ja shi jikinta ta rungume shi tare da jijjiga shi alamar rarrashi duk da yake in da sabo ya ci a ce sun saba don kullum ruwan shi ne abin da ake tashin su da shi daga bacci sai dai hakan ya ki zama sabo kasancewar mai bacci ba ya son a zuba masa ruwa hakan yana zuwar wa mutum a bazata kuma duk wanda yake da ikon tsawatarwa kan cewa kar a zuba masa ruwa ko da ba a bacci bane zai tsawatar amma a inda yake da iko ba kamar su ba da basu da kataɓus maraici ne silar komai mutuwa mai yankan kauna da yanke jin daɗin duniya a lokacin da ba a zata ba, kuma ba a tsammata ba mai raba ɗa da mahaifi ta musu shigar sauri ta yanke musu rayuwa da mahaifansu a lokacin da suka fi bukatarsu a lokacin da suka sakankance suna rayuwar da basu kawo rabuwa da juna ba.
Sai dai shi tsari na ɗan adam da ban yake tsarin ubangiji na da ban yake, a lokacin da kake lissafin sherakara goma za ka yi kaza kai baka san cewa saura minti goma ka bar duniyar ba Allah ya bar wa kansa sanin wannan ya ɓoye shi ga ɗan adam sai dai zama koyaushe cikin shirin da sakawa a rai cewa ko da yaushe mutuwa na iya riskarka shi zai sa ka yi duk wani abu wanda zai kusanta ka ga aljanna, ka nesanci wanda zai kai ka ya zuwa wuta!.
"Ki tashi ki tafi ki haɗu da ƴan aiki kin zo kin kwanta gari har ya waye ko har yanzu dakikiyar kwakwalwarki tana miki tunanin rayuwarki ta baya ne? To nan ba da gidan ubanku bane gidan kanen ubanku ne, uban naku yana can cikin kasa a rufe" Hajiya Rayyanatu ta ce tana aika musu kallon mugun tsana.
Kallon ta Hauwa'u( Hawwa) Ta yi tana jin zafin kalamanta bata san irin zafin da take ji ba idan aka sosa mata mikin mutuwar mahaifanta wanda mutuwa ta ɗauke musu su a rana ɗaya a lokaci guda ba tare da ciwon komai ba sai kaddara da karar kwana.
"Ai Aunty Hawwa ta ce Ummie da Abbie za su buɗe kasar su dawo mu koma gidanmu ko Aunty Hawwa" SABEER ya ce yana karkarwar sanyi. Kai kawai Hawwa ta gyaɗa masa tausayinsu yana kara shiga zuciyarta har gwara ita yanzu shekarunta sha takwas, iyayanta sun rasu tana da shekara sha shida, shi kuma SABEER shekara bakwai lokacin yana ɗan shekara biyar suka rasu amma kasancewarsa yaro mai wayo da rashin mantuwa har yanzu bai manta komai ba.
"Kai dalla rufewa mutane baki uban waye ya ce maka idan an mutu ana dawowa duk wanda ya mutu ba zai taɓa dawowa ba, su ma suna can sun tafi kenan" Da kuka ya fashe yana kifa kansa a kirjin Hawwa ita ma Hawwa hawayen take tana jin kukansa har kasan ranta tana kuma jin haushin maganganun Hajiya Rayyanatu wacce ta kasance matar kanin mahaifinsu.
"Za su dawo mu koma gidanmu" Ya ce cikin kuka, Hajiyar ce ta karasa gabansu ta saka jug ɗin hannunta ta kai masa bugu ai kuwa Hawwa ta saka hannu ta kare dukan da ta kawo ita aka same ta a hannu, ganin haka sai Hajiyar ta juya akalar dukan zuwa gareta ta rangaɗa masa jug ɗin a ka da karfi. Bata ce komai ba kuma bata yi yunkurin komai illa iyaka ta sunkuyar da kanta kasa hawaye suna malala daga idanunta tana tunanin ranar da za su bar gidan nan su fita daga ukubar da ake musu da gallazawa.
"Idan kika kara minti biyar baki fito ba wallahi sai kin gwammace kiɗa da karatu shegiya mai farin fatar zabiya, wannan farin naki na maita ne gadon tsiya gayyar na ayya gayyar tsiya" Ta ce tana juyawa ta fita daga ɗakin. Hannu SABEER ya saka yana share mata hawaye n.
"Aunty Hawwa ki yi hakuri daga Ummie da Abie idan sun dawo za mu bar musu gidansu mu koma gidanmu ko? Inda muke kwana a saman bed, har Ummie take ce miki Hawwa in kara gani kin ce a ɗakin SABEER za ki kwana shi ɗakin naki dafawa za ki yi ki ci? Muke cin abinci mai daɗi direba ya kai mu makaranta ya dawo da mu Abie ya ka kaimu wurin wasa da gidan zoo" Ya ce har yana murmushi tunowa da ya yi da rayuwarsu lokacin iyayansu suna raye. Rungume shi ta yi tana tuno abin da ya ce Ummie tana cewa ɗin har jiyo sautin maganar ta yi yadda take mata faɗan cikin wasa saboda tsokana irin ta Hawwa sai ta je ta kwanta a ɗakin SABEER yana tashi ya ganta a kan gadonsa tana bacci sai ya ringa kuka wai ta zo masa ɗakin bayan fitsarin kwance ma yake.
Da sauri ta tashi tana kama SABEER ɗin suka fito suka nufi bayin wanda yake na ƴan aikin gidan ne, dama a ɓangaren ƴan aiki aka basu ɗaki. Ruwan ɗumi ta karɓa a wajen Baba Sadiya mai aiki dattijuwa mai sanin ya kamata sosai take tausaya wa yaran ganin yadda masu gidan suka mayar da su tamkar ba ƴaƴan zumunsu ba, har yau tana mamakin yadda duniya ta lalace wasu daga cikin mutanen cikinta suka ɗauki duniyar tamkar matabbata, yadda suka ɗauke ta wuyarta mutum ya mutu yanzu komai zai canja daga fari zuwa baki wani idanunsa ne mashi daga babu idanunsa shikenan komai an dainawa ƴaƴansa dama na ganin ido ne ake. Wani ko a kwnce yake ba ya iya komai amma albarkacin numfashin da yake da idanunsa da suke kiftawa sai ki ga ƴaƴansa basu tagayyara ba amma daga ranar da aka ce ya bar duniya sai komai ya sauya wani duk abin da yake maka na kyautatawa daga ranar ya daina wani ko magana mai daɗi ba zai kara maka ba.
Wanka ta masa ta je Baba Sadiya ta lakuta mata man shafawa ta shafa masa ta saka masa kayan makaranta wanda makarantar gwamnati ce aka saka shi bayan gabaɗaya yaran gidan a makarantun kuɗi suke amma shi a makarantar gwamnati yake. Lokacin iyayansu suna raye Abie ne yake biyan kuɗin makarantar har ƴaƴan kanin mahaifin nasu, makaranta ce mai tsada da sai wane da wance ne suke, duka a makaranta ɗaya suke kuma shi yake biya ba don kanin nasa bashi da hali ba sai don zumunci Allah, don hatta gidan kanin nasa shi ya gina shi ya bashi. Direban gidan Abie shi yake kai su makarantar tare ya ɗakko su ya kai su gida sai ya wuce da su Hawwa gidansu. Amma su Abie suna mutuwa Alhaji Bukhari ya cire su daga makarantar ya mayar da su ta gwamnati kuma a kafa suke zuwa su dawo a kafa suna gani za a ɗauki ƴan gidan a mota su kuwa kafarsu ce take aiki haka Hawwa take goyon SABEER a bayanta idan ya gaji da yake makarantar da nisa da gidan, har ta karasa secondry scul dama tana aji huɗu iyayan nasu suka rasu, yanzu kuma da ta kammala sai take raka SABEER ɗin ta dawo in an tashi ta je ta taho da shi.
Kasancewar dama ba sallah take ba, shi bayan ta shirya shi ta saka shi ya yi alwala ya yi sallah. A ɗakin ta bar shi ta tafi kicin inda masu aikin suke hada-hadar haɗa kayan karin kumallo, haɗuwa ta yi da su suka cigaba da yi tare don tun da ta dawo gidan komai na aikace-aikacen da ita ake yi jin daɗinta ɗaya Ummie ta koya mata girki da aikace-aikace, duk da kasancewar mahaifinta mai tarin dukiya amma Ummie bata bar su kara zube ba tarbiya da sanin ya kamata girmama na gaba. Duk da gatan da suke da shi amma tana fahimtar da su rayuwa. Sai da aka gama haɗawa ta fara kwasa tana kai wa kan dinning ɗin tana jerawa lokacin har takwas ta kusa ga shi tana so ta tafi kai SABEER makaranta kullum yana faɗa mata in ya je class ɗin su sai an masa bulalar makara kullum shi ne na karshen zuwa class, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba za a kai shi a mota ba sannan ita ba za a bar ta ta tafi ta raka shi da wuri ba, dole sai an yi karin kumallo an gama karin kumallon da ko a hannu basu isa an basu sun ci ba sai dai su ci abincin ƴan aiki da yake na ƴan aiki da ban na masu gida ma da ban.
."Wane shegen ne zai zuba abincin da kika gama jerawa za ki tafi Yaya Umar ya ce yana mata wani kallo"
.."Ban gama kawo wa ba " Ta ce cikin muryarta mai sanyi.
"Kai mene ne na tuna mata baka bari ta yi kuskuren jikinta ya faɗa mata" Alhaji ya ce yana aika mata harara ya tsani yaran ba don yana so ya yi kakagida da sama da faɗi da dukiyar da ubansu ya bari ba da babu dalilin da zai sa ya karɓi rukonsu da ko za suke yawo suna bara ba zai rike su ba!.
"Ai Baba yarinyar nan mugun taurin kai ne da ita wai jiya na dawo da dare na ce ta zo ɗakina ta mini taɗi wai taki har ni take faɗawa wai babu kyau namiji da mace su keɓe kamar dai wani saɓon Allah na ce zan yi" Ya faɗa yana kallon Hawwa da take zuzzuba musu abincin tana ajiyewa kowa a gabansa.
"Ai kai ne da jarabar naci ni ban ga abin so a wannan figaggiyar yarinyar ba ka nemi wayyayyi wacce take da cikakken gata amma sai ka kare a mai karatu iya sakandire marainiya da bata da wani gata" Hajiya ta ce tana taɓe baki.
"Ai na faɗa masa ya ki ji ga ƴaƴan abokaina nan, amma ya ce sai ita tun da ita ya ce zai aura zan aura masa don in nuna masa indai ina raye ba zai taɓa rasa abu ba, in ya so idan ya samu mata sai ya aura ko uku ne ya rufe kofa" Baba ya faɗa.
"Kai ma Yaya da wani abu wallahi ni fa yadda na tsani Hawwa bana jin akwai wani abu da zai haɗa ni da ita sai dai in aiki za ta mini, yarinyar nan ta fini kyau ta fini ilimi ga kokari kamar masifa ko lokacin muna makaranta ita take ɗaukan first position a class ɗin ni in yi na karshe wannan mataccen uban nasu ya ringa mini faɗan wai in dage in ke kokari yanyanyanyan ya ringa wata nasihar sa da ba shigata take ba illa mugun haushin sa da nake ji ita ma uwar tasu Ummie take ko Ummita bata da abu misali sai mu yi koyi da Hawwa...
"Ya isa Lawisa! Wasa ya yi wasa ban da tsikarin uwar miji, duk abin da za ki faɗa ji faɗa iya kaina sa SABEER bana so ki taɓo mini iyayena da suke kwance a cikin kasa" Hawwa ta ce cikin ɓacin rai idanunta suna ciko da kwalla.
"To mene ne saura idan