Showing 51001 words to 54000 words out of 61883 words

Chapter 18 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10812

juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️


JAN HANKALI


Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.




SADAUKARWA


Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.






PAGE 14






*HAWWA*






Siyayyar da suka yi kaya sun yi kyau sosai Yaya Usman sai wani shishshige mata yake yi, yana so ya fara fahimtar da ita akwai ɓoyayyan sirri a zuciyarsa sai dai ba wai da baki yake son faɗa mata ba so yake ya fara nuna mata a aikace ta yadda za ta fara fahimta da kanta, ma'ana zai ke yin abu wanda za ta fara gane ya mutu a kan soyayyarta duk da yau ya ji haushi sosai abin da ta yi wa ABBAS amma kuma ganinsa gata ga shi sai ya wanke duk wata damuwarsa.


Sun biya shago ta bayar da ɗinkinta amma na SABEER sun bayar sai Yaya Usman ya ce zai kawo shi su gwada shi, da yake shagon ɗinkin akwai masu yin na zama da masu yin na mata.


Baffa ya yi murnar ganin kayan, SABEER kuwa sai murna yake an siyo masa kaya, bawan Allah cewa yake


"Na huta da saka tsohon kaya yagagge" Wanka HAWWA ta masa aka saka masa ɗaya daga cikin kayan sai murna yake yana farin ciki. Baffa ma daɗi ya ji a ransa ganin ya faranta zuciyar maraya. Kuɗin zoben nan HAWWA ta ɗakko ta ba Baffa tare da masa bayanin kuɗin zoben ta ne Baba Sadiya ta sayar mata, suka yi kuɗin motar ta sanar da shi ta ba Baba Sadiyar wani abu daga ciki.


"Wannan kuɗin ai naki ne Hauwa'u zan mayar da wanda kuka ɗauka kuka yi kuɗin motar sai a juya miki sauran" Ya ce yana kallon kuɗin wanda shi ne kaɗai ya yi saura daga cikin maƙudan kuɗaɗe da ƙadarorin da suke da shi, mararsa tsoron Allah sun cinye kuɗin ba tare da tunanin makomarsu ko azabar da Allah zai musu a kan cin dukiyar marayun ba.


Islamiyar unguwar da Amrah take zuwa nan aka karɓowa HAWWA form za a saka ta, har an bata hijabin ɗinkakke da suke siyarwa tare da form ɗin, har ƙasa hijabin. A wayar Baffa ta saka lambar Baba Sadiya da ta haddace ta kira ta da daddare cikin raɗa ta ce.


"Baba Sadiya" Da sauri Baba Sadiya ta tashi zaune daga kwancen da take cikin farin ciki ta ce


"Ɗiyata!"


"Na'am Baba"


"Baba babu kowa a kusa da ke?"


"Babu kowa duk suna waje ni ma ban daɗe da shigowa ɗakin ba" Nan suka gaisa cikin tsananin farin cikin jin muryar juna. Baba take tambayar yadda suka je Kadunar nan take faɗa mata lafiya suka je, ta shiga bata labarin yadda suka samu sauyin da suka, samu sosai ta ji daɗi da farin cikin daddaɗan labarin tana son yaran tamkar ƴaƴan cikinta tana son ta ga sun samu rayuwa mai inganci sun yi farinciki, abin da ya gagari ƙanin mahaifinsu ya basu kulawar da ta dace ko don maraicin su.


HAWWA ta tambaye ta yadda suka yi da suka fuskanci basa nan, Baba bata ɓoye mata komai ba da ya faru har sanarwar mutuwar su ta hanyar haɗarin da mota ta ƙone da zaman makokin da aka yi. HAWWA har da kuka tana mamakin duniyar nan da take sabuwa dal a wajen wasu mutanen, da basa ganin ƙarshen ta ya zo ga tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu ta yadda suka yi watsi da zumunci har a ce ƴaƴan ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya amma ka ci amanarsu har ka sanar da barin su duniya ba tare da ka tabbatar da sun mutun ko suna raye ba.


Lallashin ta Baba Sadiya ta shiga yi har ta samu ta yi shiru, ita HAWWA ba komai take tunowa ba sai yadda Baba ya nuna musu soyayya da ƙauna lokacin iyayansu suna raye, hatta Hajiya Rayyanatu ta nuna musu ƙauna tamkar ƴaƴan cikinta ashe dai so ne na ganin ido so ne da zai gushe ya juya zuwa ƙiyayya a bayan ƙasa ta rufe idanun iyayan nasu.


"Baba takarduna suna nan?"


"Haba Hauwa'u ai takardunki suna nan na ɓoye miki su, yadda na sanki da son ilimi ina zan yi wasa da takardunki"


"Dama Baffa ne zai sama mini admission shi ne nake so ki kai tasha ki saka mini a mota wannan lambar da na kira ki ita za su kwafa idan sun kawo su kira sai a je a karɓa a basu kuɗin motar" Sosai Baba ta ji daɗin maganar ta san yadda HAWWA take da son karatu amma iyayan riƙonta suka daƙushe mata ba don komai ba sai don su tauye su a ko ina suna son nuna maraya bashi da galihu. Sun yi sallama cike da kewar juna kasancewar an saba ana tare kullum.


Sai da ta yi kuka mai isarta ta ta share don ta ji ciwon zaman makokinsu da aka yi bayan suna raye, kenan da ba wurin Baffa bama suka nufa wata uwa duniyar suka nufa shikenan ba za su neme su ba, tun da har sun tabbatarwa da duniya mutuwarsu kai duniya ina za ki damu?!.


Fitowa ta yi daga ɗakin ta kai wa Baffa wayar ta faɗa masa yadda suka yi da Baba Sadiyar a kan takardun, sai dai ganin yanayinta ya sauya sai da Baffan ya tambaye ta, wani kuka ne ya ƙwace mata lokacin da take bashi labarin shi ma sai da ya yi hawaye Goggo kuwa kasa tsayar da nata hawayen ta yi saboda abin ya yi matuƙar ɗaure musu kai, lallai su Alhaji Bukhari sun ci dubu sai ceto. Haƙuri ya bata tare da nuna mata cewar gwara ma hakan don wannan zai basu damar rayuwa babu fargabar za su neme su bare su katse musu walwala da jin daɗin da suka samu bayan dawowarsu Kadunar


Amrah yau ma wunin gidan Mamansu ta yi tun zuwanta ta ce da yamma za ta aike ta gidan ƙawarta da suke islamiya ɗaya, da yammar kuwa ta bata saƙon turaren wutar da za ta kai mata. Sanye take da hijabi iya gwiwarta ta nufi gidan kamar yadda ta kwatanta, sallama ta yi bayan an amsa ta shiga zaune ta samu Mamar ABBAS a kan tabarma tana yankan farce, ladabin kunamar nan dai da take a idanun wanda ta ga dama shi ta yi wa Mama domin har ƙasa ta durƙusa ta gaishe ta amsa mata Mama ta yi tun bata san daga inda take ba ta ji yarinyar ta kwanta mata a rai. Bayan ta ce ta zauna a tabarmar dakyar ta zauna daga gefen baranda alamar ba za ta haɗa wurin zama da babba ba, sosai hakan ya ƙara burge Mama.


"Ga shi in ji Mamata ta ce na kawo miki" Ta ce tana miƙa mata da hannu biyu.


"Lah wai yarinyar wajen Habiba ce? Amrah ko?"
Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi haɗe da wasa da yatsun hannunta.


"Ah ma sha Allah" Ta ce tana jinjina tarbiyar yarinyar. Ko ruwa da Mama ta kawo mata ƙin sha ta yi, da za ta tafi Mama ta ce ta miƙa mata saƙon godiya tare da bata ɗari biyar ta hau napep duk da ba wani nisa bane tsakanin amma ta ƙi karɓa hakan ya ƙara saka wa ta ji yarinyar ta ƙara kwanta mata. Tashin da ta yi za ta tafi abin da idanunta suka mata tozali da shi, sai da ta kusa kasa shaƙar numfashi.


'ABBAS' Ta ce a zuciyarta hango hotonsa kafe a ɗakin Mama, dakyar ta saisaita kanta don kar Mama ta gane.


"Yes! Tsuntsu daga saman gasashshe lallai na samu wurin kamun ƙafa, wannan mutumin mai taurin tan tsiya da nuna mace bata dame shi ba Allah ya kawo mini sassauƙar hanya" Ta ce a zuciyarta lokacin da ta fito daga gidan.






*SALIMAH*




Wata irin bugawa zuciyar SALIMAH ta yi fat-fat jiri ya fara ɗibanta duk da a zaune take, gabaɗaya tangameman falon ya shiga juya mata tamkar jirgin sama yana shawagi a sarararin samaniya, jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari cikin zafin nama ta fusgi jikinta ta fara ƙoƙarin raba shi da kan kukerar duk da tana jin yadda sagaggun ƙafafunta suke barazanar gaza ɗaukan gangar jikinta, saboda mugun kashe ta da mamaki da Alhaji Tahir ya yi. Duk da ta ci nasarar tsayawar a kan ƙafafunta amma karkarwa suke mata, za ta iya cewa tun da ta baƙunci duniya ba a taɓa mata abin da ya bata mamaki ba ya daki ƙwaƙwalwarta lokaci guda lissafi ya rikice mata ya ƙwace mata ba, sama da wannan furucin na Alhaji Tahir. Gabaɗaya sai ta ji kalaman da ya furta sun dame tare da shanye laifukan da take taƙamar ya mata, na rashin zuwa gare ta tun daga ranar farkon da aka mata masauki a gidansa kawo yau da ta cika kwanaki uku!.


A nata ra'ayi da tunanin wannan ne laifi mafi muni da ya mata wanda take ganin ba zai ƙara mata wani makamancinsa ba, sani ne bai yi ba a duniya tana da mugun kishi ta tsani kishiya, kai ko sunan kishiya aka ambata ɗaci take ji a zuciyarta!. Abin da ya sa ma ta yarda za ta aure shi bayan yana da mata har biyu saboda amanna da ta yi da kyau da zubin halittar da Allah ya mata, a nata bahagon tunanin tana ganin babu wani gida da za ta saka ƙafarta da sunan zaman aure idan har da mace a gidan face matar ta zama sorry, ta sakar mata akalar mijin. Ganin za ta zama tauraruwa mai haske a gidansa da yadda yake nuna so da ƙaunarsa gare ta wannan dalilin ne ya sa take ganin in ta shiga gidansa matansa ba za su zame mata kishiyoyi ba sai dai su zama tamkar bayi a wajen sarauniyai!!!. Niyyarta ta gallaza musu ta ci karenta babu babbaka a ƙarshe duk wacce ta gaji da gashin ƙumar cikin gidan ta cikawa bujenta iska. Sai dai kash! Yau ta gane akwai bambanci tsakanin aya da tsakuwa ashe dai kallon haddirin nesa ne ya sa ta yi wanka da kashi, tabbas kallon kitse take wa rogo.


A yau ɗaya ta gane karin maganar da bahaushe yake cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta. Bata taɓa zaton duk kyan da take taƙama da shi ba za ta samu wacce ta fi ta ɗari bisa ɗari a cikin gidan Alhaji Tahir ba, kyan da shi ne makamin da ya sa ta kashe aurenta don tana ganin kyan nata zai sa ta samu mai kuɗi inda za ta yi amfani da zallar son ta ci duniyarta da tsinken tsire. Sai ga shi matarsa da ta fara shigowa ta kere ta a komai ko ɗayar ma ta fi ta komai haske kawai za SALIMAR za ta faɗa mata, domin irin matan nan ne da ake wa laƙabi da black beauty.






Idanunta tamkar za su faɗo take kallonsa wanda shi ɗin ma ita yake kallo da mamakin ganin ruɗewarta a ƙanƙanuwar maganar da ya yi, wacce bata fi kalmomi ƙalilan ba, taku ɗaya biyu ta yi za ta ƙarasa gabansa saboda yadda take jin zuciyarta tana azalzalarta dole ta tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro dole ta ankarar da shi mummunan kuskure zai yi don idanunta a rufe suke basa tsoron ta mutu ko ta yi rai.


"Alhaji Tahir! Haka muka yi da kai? Ni SALIMAH za ka ci wa mutunci ka wulaƙanta a idanun duniya sa...


"Da na miki me?" Ya tari numfashin ta har yana ƙanƙance ido ɗaya saboda shayar da shi giyar mamakin kalamanta.


"Tambaya kake ko neman sani? Idan ka manta in tuna maka yau kwanana uku kacal a cikin gidanka ko wulginka ban gani ba, a matsayina na amaryar da ka yi wa furucin kalmar so da ƙauna ba wacce aka laƙaba maka auren dole da ita ba, amma kake ikirarin gobe za a ɗaura maka wani auren? Ni kuma a wane matsayi ka ajiye kenan? To bari ka ji ni SALIMAH ba zan lamunci raini ba kuma ina so ka sani shi rashin mutunci biki ne idan ka mini ramawa zan yi don wallahi! Wallahi!! Ba zan ɗaga maka ƙafa ba" A fusace ya miƙe tsaye cikin zafin nama yana nuna ta yatsa ya ce




"SALIMAH ki sani nan ba wajen warginki bane, idan kin saba duk wani abu da kike taƙama da yinsa to ki sani shi fa bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri!. Da kike ikirarin duk abin da kike faɗa yanzu shin sakin ki na yi? To ko sakin ki na yi baki da hurumin tuhumata tun da ni nake aurenki ba ke kike aurena ba. Aure kuma babu fashi ki kalle su mai suka rasa? Kyau ko diri? Duk wani abu da ƴa mace za ta yi taƙama da shi kowaccensu tana da shi amma na auro ki" Ya ce yana nuna mata matansa da suke zaune, samun kanta ta yi da waiwayawa ta kalle su kamar mai son tabbatarwa da maganar tasa. Farar ganin SALIMAH ta juyo har da gyara kafaɗar rigarta irin ta kalle ta da kyau, baƙar kuma sai ta gyara ɗaurin ɗankwalinta wanda ya kasance ture ka ga tsiya ya sake iyowa gaban goshinta, wani mugun haushin matan nasa da tsanarsu ne suka dirar mata a zuciya.


"Ka san suna da komai amma ka auro ni"


"In kin manta in tuna miki ko lokacin da kika yi kuri da kyau wata rana da muna magana, in za ki lura ai ban yi magana ba kawai dariya na yi saboda na san mai na ajiye a cikin gidan"


"Ba wannan ba Alhaji dole ka fasa maganar aurenka, tun da su wannan na san da zaman su da wacce kake ƙoƙarin ba ƙofar shigowa nake, idan ma har ya zama dole za ka yi sai dai idan na gama cin amarcina!"


"Baki isa ba SALIMAH ni bai mace bata juyani, kuma ina so ki sani a gobe idan an ɗaura aure a goben amarya za ta tare, sannan bakin kwananta ne don naki ya wuce a ƙa'ida ita dama bazawara kwanaki uku ne nata kacal!!!. Kuma kin cinye naki domin kuwa sun wuce gobe kwanankin amarya ne in suka ƙare sai na uwar gida, sannan na mai ɗakin tsakiya daga ita kuma a sannan ne aka zagayo kan ki ina fatan kin fahimta!" Ya faɗa babu ko alamar wasa don yadda ma yake magana ko walwala babu a fuskarsa yana yi ne cikin hargowa tamkar zai kai mata duka.


Ɗif ta yi tamkar ruwa ya ci ta, ashe wulaƙaci ba shi da daɗi? Ashe akwai damuwa a nuna maka baka isa ba a inda kake ganin ka isa har ka yi yawa? Ashe abu ne mai cin rai a nuna maka kai ba kowa bane a inda kake ganin ka isa, yau ita SALIMAH za a yi wa tonon silili ina dirin jikinta da yake ɗaukan hankalin maza? Ko shi Alhaji Tahir makaho ne? Amma in makaho ne ya aka yi ya ga diri da kyan nata har suka ruɗe shi ya aure ta, yanzu duk kyan da ya zame mata jari take ganin za ta juya namiji kamar sitiyarin mota amma wai ake nuna mata kwananta ya wuce, wai ake tabbatar mata kwananta uku ne na bazawara bayan shi da kanshi ya sanar da ita ta fiye masa budurwa, kuma kwana ukun ma ba a mata shi ba, tunaninta sai sun kwashe wata uku currr suna cin amarci ba tare da ya waiwayi kwanan sauran matan nasa ba sai ga shi ko saninta bai yi ba a matsayin mace yana ambaton kwanakin sun wuce sai kuma sun zagayo, wannan shi ne ƙalubale babba a wajen ƴa mace mijinta ya nuna mata raya sunnar aure da ita ba bakin komai bane don hakan ya nuna Alhaji Tahir ba ya mararin sanin wace ce ita a cikin mata shu ya sa ya ce kwananta ya wuce.




"Ka ha'ince ni wallahi" Ta ce wani kuka yana neman ƙwace mata.


"Na ha'ince ki ko kika ha'inci kan ki? Auren nera kika yi kuma ga ki ga nairar, ki kalli Khadija da kyau " Ya faɗa yana nuna baƙar matarsa.


"Ita ce uwar gidana, kuma mahaifinta mai kuɗin gaske ne, haka ma Aina'u" Ya ce yana nuna farar da yatsa.


"Ita ma mahaifinta mai mugun kuɗi ne, zan iya cewa babu wacce ta aure ni saboda dukiyata, kuma a ranar da Khadija ta tare washe gari aka ɗaura aurena da Aina'u kuma a ranar aka kawo ta babu wacce ta yi musu da magana ta kuma har yau tsawon shekara goma da auren mu babu wacce ta ƙetara umarni na sai ke? Ke da ba ƴar kowan kowa ba ke da na auro a duhun talauci na fito da ke hasken arziƙi bari ki ji daga bakin abokanan zamanki ku faɗa mata doka ta" Ya ce yana kallonsu.


"Ba a musayar zance da kai" Khadija uwar gida ta faɗa.


"Ba saɓa magana ko karya dokar ka" Aina'u mai ɗakin tsakiya ta ce.




"To dawo nutsuwarki idan za ki ci arziƙi ki ci ki idan kuma za ki koma ƙangin talauci to dama daga shi kika zo, sai dai ki sani fita daga gidan nan akwai haɗari, haɗarin da ba za ki so jin wane iri bane"


Hawaye ne suka fara sintiri a kumatun ta jin ya mata gorin arziƙi wai har yana cewa ta zo daga ƙangin talauci, wato

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login