Showing 45001 words to 48000 words out of 61883 words

Chapter 16 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt

13 Jan 2025

10817

a hannuna yake mai ya sa kai ba za ka bayar da komai ba gare ni kai wa ka fi? Shegen shishshigi da neman wuri don Baffa yake ganin riƙon amanarka dama kullum yana yabonka so dai kake ya ɗauki matsayina ya baka to wallahi baka isa ba matsayina ya fi ƙarfin takawar ƙafarka" Ya ce yana haki wasu daga gefe suna ta bashi baki amma tamkar zuga shi suke.




"Haba Usman mene ne na ɗaga jikiyoyin wuyan ni fa kuɗin nan ba cin su na yi ba kuma ba nawa bane laifi ne don na ba Baffa, kuma ka saka ranka a inuwa ni ba zan taɓa karɓe matsayinka ba kana matsayin ɗan mai wurin nan baki ɗaya mu ai cin arziƙi muka zo"


"Uban waye da ya ce ka isa ka karɓe matsayinaa munafukin banza da wofi...


"Dakata! Usman wasa ya yi wasa amma ban da tsikarin uwar miji, ka mini komai ka ce mini komai amma ba zan ɗauko cin mutunci ba na tsani a kirani munafuki domin ba na munafurci saboda munfukin ko a cikin wuta yana ƙasan kafiri saboda girman munafurci don haka ka kiyaye bana son a kira ni munafuki ko a zagi iyayena saboda iyaye su ne gaba da komai iyaye su ne jigon kowa duk wanda ya rasa su ya yi kuka don haka na san muhimmancin su bana so a zagar mini su"


"Sosai HAWWA ta ji abin da Yaya Usman ya yi wa wanda ya kira da suna ABBAS ya taɓa mata zuciya, saboda bata ga laifin da ya yi ba kuma jiya a gabanta ta ga ya kawowa Baffa kuɗin ya ce ga cinikin amma Baffan ma bai karɓa ba bata sani ba ko bayan ya fita ba ya bashi, yadda ABBAS ɗin ya nuna iyayansa suna da muhimmanci abin ya burge ta sosai saboda ko ita a duniya ta ƙi jinin a zage ta ko a wulaƙanta mata iyaye tun suna raye bare yanzu da basa duniyar sai take jin abin ya ƙara shiga zuciyarta ya zauna daram! Sakarai ne zai kasa sanin muhimmancin iyaye, uwa ita take ɗaukan ciki ta raina ta sha wahala, ya zo ta sha wuya a naƙuda har ta haihu ba a nan abin ya tsaya ba ta shayar ta ba ƴaƴa kulawa har su girma aiyuka uwa suna da yawa haka uba komai shi ne ciyarwa shayarwa tufatarwa ɗaukan nauyin karatu duk mahaifi ne komai in babu sai dai a faɗa masa, tabbas wanda bai san muhimmancin iyaye ba ko bai ɗauke su bakin komai ba ya yi babbar asara.


Cikin sanyin jiki ta fara taka ƙafarta a hankali ta nufi wajensu, Yaya Usman bai lura da ita ba idanunsa sun rufe sai masifa yake shi ya tsani ABBAS ya ba Baffa kuɗi saboda ya fi so kuɗaɗe su biyo ta hannunsa ya ci karensa babu babbaka ya ba Baffa abin da ya samu, shi kuma Baffa ba ya tuhumarsa ko da kuwa kuɗin bai kai yadda ya tsammata ba kasancewar Yaya Usman yana nunawa Baffa shi mutumin kirki ne don ya yarda da shi amma a bayan idanunsa shi kura ne lulluɓe da fatar akuya.


Fuskar wanda aka kira da suna ABBAS ta kalla cikin sanyin zazzaƙar muryarta mai daɗin amo a kunnen mai sauraro ta ce


"Ka yi hakuri" Ta faɗa tana haɗe hannuwanta biyu wuri guda, saboda yadda ta ga yana magana cikin nutsuwa da kuma nuna abin da aka faɗa masa ya masa ciwo musamman zagin sai ta ji tamkar ita aka zaga sannan sai kuma da aka kira shi munafuki ya musanta hakan har yana nuna ƙyamar munafurcin yana kuma ambata makomar munafukin sai ta ji ya burge ta tana son mutum wanda ya san darajar kansa a rayuwa. Ƙurrr ya ɗago wannan kyawawan fararen idanunsa masu kallo tamkar na soyayya ya zuba mata su tare da son gaskata cewa shi ɗin take ba haƙuri a bisa laifin da ba ita ta masa ba, shin mai ya ja hankalinta har ta so bada haƙurin?. Yaya Usman kuwa maganarta ce ta ankarar da shi zuwanta wanda fitar furucin daga bakinta ya zuwa kunnuwansa sai ya ji tamkar an zuba masa dalma, wani turnuƙuƙin kishi ya yi wa zuciyarsa dabaibaiyi, yana hasko nan gaba kaɗan za ta zama matarsa kuma mallakinsa tabbas ba zai so ba kuma ba zai lamunci ta yi wa wani ɗa namiji magana ba bare har wani namijin ya mata. Yana da kishi matuƙa a nashi tsari da halayya tun yana ƙarami ya ƙi jinin su yi abu iri ɗaya da wani sabo da kishi irin nasa bare kuma yanzu da ya girma ya mallaki hankalin kansa kishin ma a kan wacce yake muradin ta zama mata kuma uwar ƴaƴansa.


Wata irin tsanar ABBAS ce ta shiga zuciyarsa ta yi masauki, a ƙufule ya ɗago ya kalle ta ya ce




"Wa kike ba haƙuri a tsakaninmu" HAWWA da har lokacin hannuwanta suke a haɗe ta lunshe kyawawan idanunta ta buɗe a hankali ta ce


"Haba Yaya da wannan nake mana ai kai ne ka masa laifi jifansa da ka yi da kalma marar daɗi, bayan laifinsa bai kai matakin hukuncin da ka ɗauka ba wato zagi...


"Ya ishe ki HAWWA, yaushe na zama sa'anki za har za ki nemi nuna mini abin da ya dace in yi... Fitowar Baffa daga gida ne ya dakatar da Yaya Usman daga dokin zuciyar da ya hau cikin iya kissa da wayincewa ya saki murmushi tare da dafa kafaɗar ABBAS ya ce


"Ina son riƙon amanarka ABBAS baka yadda ka ci ko da ƙwandala ba in har ta kasance ba mallakin ka ba ce ka cigaba da tsayuwa a kan turbarka lallai duk wanda hulɗa ta haɗa ka da shi ba zai so ka suɓuce masa ba" Ya ce yana dariya har haƙoransa suka bayyana. ABBAS ma murmushin ƙarfin halin ya saki don inda sabo ma saba da halin Yaya Usman na nuna halin rashin kirki a bayan idon Baffa amma a gaban idanunsa babu wanda ya kai shi kirki da girmama mutanen da suke ƙarƙashin su.


Cikin halin dattako Baffa ya ƙaraso gabansu fuskarsa cike da alamar abin da ya gani ya faranta masa ya zo, miƙa hannu ya yi ya dafa ABBAS da hannun dama hagun ɗin kuma ya dafa Yaya Usman ya ce


"Haƙiƙa ina alfahri da dukan ku, kamar yadda kake yabon ABBAS kai ma haka kake ɗana haƙiƙa na yi sa'a da samunku a matsayin jigon jingina wanda a zamanin nan ba kowa bane za ka ɗora shi a kan kasuwanci na harkar kuɗi kuma ya riƙe amana ba tare da ya cuce ka, tabbad kuna ƙyamatar cin haramun wanda haka ya dace kowane musulmi ya yi" Su duka murmushi suke daga ABBAS har Yaya Usman, ban da HAWWA da take tsaye sake da baki tana mamakin abin da Yaya Usman ya yi lokaci guda ya sawaya tamkar hawainiya daga tafiya irin ta ƙosasshen zaki zuwa tafiyar hawainiya wato yana cikin faɗa da tada jijiyoyin wuya sai kuma ya yi sanyi ƙalau tamkar ƙanƙara. Kallon fuskar ABBAS ta yi tana son gane wani abu wato dalilin da ya sa shi ma ya sakar da maganar ya goyawa Yaya Usman baya, wato ya bi yarima ake shan kiɗa maimakon ta ga ya cigaba da nuna ɓacin rai kamar yadda yake sai ya sakar shi ma ya nuna babu abin da yake faruwa kuma hatta sauran mutanen da suke wajen babu wanda ya tofa wani abu makamancin wannan.


Suna haɗa ido sai ta ga ya faɗaɗa murmushinsa tare da ɗan rausayar da kai yana son nuna mata hakan ba komai bane, ganin dai tana ta masa kallon mamaki sai ya kanne mata ido ɗaya da sauri ta juya har tana harɗewa ta bar wajen wanda hakan sai da ya sa dariya ta kusa suɓucewa ABBAS ɗin ganin ta tsorata kuma ta ɗauki kashe idon da ya yi a matsayin wani abu wanda shi kuma ya yi hakan ne don ya ƙara nuna mata komai normal kar ta damu.


"Hauwa'u" Baffa ya kira ta.


"Na'am Baffa " Ta ce tana juyowa duk ta duburburce.


"Ku je ku dawo ko SABEER yana can yana jiran dawowarku ya matsu a masa wanka"


Da to ta amsa sakin kafaɗar su ABBAS ɗin Baffan ya yi Yaya Usman yana murmushi ya juya ya nufi wajen machine ɗin, Baffa wajen kujerarsa ya wuce ya zauna ABBAS kuma ya cigaba da buga hannun drower a jiki.


Yaya Usman sai da ya tada machine ɗin HAWWA ta hau suka zo giftawa ta gaban ABBAS wani kallo Yaya Usman ya aika masa irin na da ni kake zancen. ABBAS kuwa kallo ɗaya ya musu ya ɗauke kansa ya cigaba da abin da yake amma ko ba komai ya ji daɗin abin da HAWWA ta masa a ƙalla dai gata yarinya amma tunaninta ya fi na Yaya Usman ɗin ta fi shi hangen nesa da sanin darajar ɗan adam, karon farko da ya ji wata mace ta burge shi bayan SALIMAH amma ba da so ba, burgewa kawai.




*SALIMAH*




Tun karon farko da ta farka babu wani bacci da ya yi nasarar ɗaukanta ko da kuwa ɓarawo ne, saƙa da warwara su ne abin da ta fi yi ta rasa wane za ta ɗauka daga cikin saƙar jakin da zuciyarta take mata. Ga shi kiran duniyar nan ta yi wa Alhaji Tahir amma wayarsa a kashe, ga shi da tsakar daren nan bata so ta kira kowa haka ta ɗauki na annabawa har aka faramkiran assalatu, cike da takaici ta sakko daga kan gadon tana duba iya haɗuwa da tsaruwarsa haɗe da lallausan bedsheet da ta yi oder wajen Maman Afrah amma a ce wai ita kaɗai ta kwana a kan gadon babu ango? Ita ɗin ma da ta kwana a kai babu wani bacci mai daɗi tunani bai bar zuciyarta ta huta ba. Wucewa ta zo yi ta gaban madubi kallon kanta ya yi a ciki sai da ta ba kanta da kanta tausayi yadda fuskarta ta sha make up amma duk ya caɓe a banza ango bai gani ba ɗaurin ɗankwalin da mai ɗaurin ɗankwali ta ɓata lokaci wajen tsantsara mata shi amma ya tashi a banzar bazara, a ce wai ko kayan bacci bata saka ba da leshin zuwa gidan mijin ta kwana ba ma wannan ba a ce tana amarya amma ko kazar amarci babu haka ta kwana da yunwa.


"To ina angon ma mai kawo kazar bare ita kazar?" Wani sashe na zuciyarta ya jefo mata tambayar da ita kanta bata san amsarta ba. Ganin eye lashes ɗin guda ɗaya ya farƙale ya mayar da ita kamar aljana haka ta saka hannu ta cisge ko zafin cirewa bata ji ba ta yi cilli da shi ta bar gaban madubin saboda kallon kanta a madubi yana ƙara ɗago mata da ɓacin rai.






Tana tafiya a tangamememan falonta tana kallon haɗuwa da kayan alatun da aka kashe kamar ba gobe, tunanin ranar farkonta a gidan ABBAS ya faɗo mata, a ranar sai da ƙawayenta suka yanka masa kuɗi mai tsoka ya bayar matsayin siyan baki duk da talaucinsa ya shigo da kaza da lemuka daidai ƙarfinsa yana ta nan -nan da ita yana lallashinta ba ya ma ganin kyara da nuna masa tsanar da take yi, amma sai ga shi yau an mata wulaƙanci iya wulaƙanci am bar ta babu ango abin takaicin ma bai ce mata ga uzurinsa ba sai ka ce wata marar galihu ai ƴan magana suka ce wai amarya ko ta kyankyaso ce ana riɗin ta. Da wannan takaicin ta ƙarasa bayin tana ganin yadda ya gaji da haɗuwa alwala ta yi ta fito ta yi sallah tana jin ƙugin cikinta haɗe da ciwon marar magungunan da ta bankamawa kanta. Hannu ta sanya ta dafe goshinta tana jin tamkar ta rushe da kuka amma sai ta dake ta tashi ta bar sallayar a wajen ko arziƙin linkewa bata samu ba.


Ganin shida da rabi sai ta nufi saman bene ta je windown ta tsaya tana ƙara ƙarewa gidan kallo, tabbas gida ya amsa sunansa gida musamman yauzu da yake da safiya ce ba dare ba sai ta ga ta fi ƙarewa komai kallo yadda ya kamata. A yadda gidan yake bata taɓa zato za ta zama ɗaya daga cikin wanda za su zauna a matsayin matar gidan ba ita ko a ƴar aiki bata taɓa zaton zuwa gida irin wannan ba amma sai ga ta a matsayin matar gidan. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana sakin labulen ta bar wajen, har ta juya za ta tafi ta dawo ta ƙara taɓa labulen tana ƙara jin ƙwari da nagartarsa .


'Lallai labulen nan yana da inganci tabbas maman afrah kayanta suna da kyau' Ta ce a zuciyarta tana barin wajen ta shiga ƙarewa ko ina kallo ganin bata gane wasu abubuwan saboda yunwa sai ta sakko ƙasa tana tunanin inda za ta samu abinci, ƙofar da take tunanin nan ne kicin ta nufa ta shiga komai tamkar a ƙasashen ƙetare murmushi ta saki ta fito ta nufi inda take tunanin nan ne a matsayin store tana buɗewa ta ga kayan abinci lodi guda katan ɗin indomie ta buɗe ta ɗakko guda biyu ta fito ta dawo kicin ta kunna gas ta ɗora ruwa yana tafasa ta zuba indomie ɗin, haka ta dafa ta da gishirin ta ta juye a plate. Har za ta ɗakki ƙwai ta soya sai ta ji tana jin jiri ba za ta iya soyawa ba haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kicin ɗin a falo ta zauna a ƙasan capet ko kan dining bata yi tunanin hawa ba saboda yunwa uwa uba babu ango bare ake bata a baki ita ma tana mayar da martani.


Har sha ɗaya a safe amma babu ango babu dalilinsa kuma har lokacin ta kira duka layilansa a kashe hatta whatsappa ma da ta duba shi ba ya hawa, ita kuma bata son faɗawa kowa a mata dariya Umma ta so faɗawa amma kuma ta kasa saboda bata son saka mahaifiyarta a damuwa tun da ita kaɗai ta rage mata. Saboda ta san duk wanda ya ji abin zai ji wani bambarakwai. Kiran Ummar ta yi don su gaisa ringin ɗaya biyu Umma ta ɗaga cike da zumuɗi.


"SALIMAH amarya" Ta ce bakinta har kunne tana samun wuri ta zauna saboda a yi maganar a nutse ta san akwai labarin yadda ta ga gidan nata.




"Na'am Umma ina kwana"


"Lafiya ƙalau ya kwana baƙunci"


"Alhamdulillahi"


"Oh kuma maimakon ki buɗe baki tiryan-tiryan ki hau bani labarin gidan ƴan gayu sai kike wani jan aji SALIMAH ko angon bai fita ba dama ai na san yanzu ba kasafai zai ke fita ba shi da ya ajiye amarya, ai jiya ƴan kai amarya har sai da na gaji da labarin yadda ake faɗa mini gida ya ƙawatu" Umma ta ce tana dariya.


"Umma ai abin sai wanda ya gani" Ta ce cikin ƙarfin hali don kaɗan kuka ya ƙwace mata gani ita angon ma ko ƙeyarsa bata gani ba. Nan dau suka taɓa hira suka yi sallama ta yi jigum bata son faɗawa kowa. Wasa-wasa har kwana biyu babu ango kuma babu wanda ya zo ya ce mata wani abu daga cikin kishiyoyin nata tana so ta je ta tambaye su ko ina mai gidan amma rana tsoron raini kuma hakan ma tamkar zubar da ajinta ne a ce tana amarya bata san inda ango yake ba sai ta je ta tambayi kishiyoyi.


Sawunta biyu wajen mai gadi amma yana tabbatar mata cewa tun ranar ɗaurin auren Alhajin bai zo gida ba. Haka za ta koma jiki babu ƙwari a kwana na uku ne ta dokawa RUKY kira ta ce ta zo tana son ganinta da yamma kuwa sai ga ta ta zo, amma sai ta kasa faɗa mata ganin tana ta yaba kyan da ta ƙara amma ta ce ta ga ta ɗan rame amma hakan ba ya rasa nasaba da shan amarci da ake yi.




"Kai SALIMAH kin samu duniya saura ƙiyama kai Allah ya saka mu a damshinku" Ta ce tana kai lomar jalof ɗin taliya.


Murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce


"Abin ba a cewa komai"


"Wai ya kyan magungunan na da kika babbaka?"


"Suna da mugun kyau kuwa" Ta samu kanta da kwararo ƙarta tun da ita mijin ma bata gani ba bare ta tabbatar da kyan magungunan.


"Kai ai kuwa in zan yi aure irin su zan saya"


"Ai kuwa" Ta ce tana damƙe baki jin mararta ta murɗa mata. Hannu ta kai ta dafe wajen tana yamutsa fuska, ta san tarin kwamacalar magungunan da ta sha ne suke tambayarta.


"Inyeee amarsu ko dai har ango ya yi ajiye ne? In k,uma priod ne zai zo gaskiya kar ya zo ya kawo cikas ana tsaka da cin duniya da tsinken tsire" Ta ce tana ɗaga ruwan roba ta kwankwaɗa.


Murmushi kawai ta yi.


"Ai dai kin cire inplan ɗin nan shi ya sa wataƙila ciki ne ya shiga, kin san ai dama an ce inplan wankin mara yake shi ya sa ana cire shi ake samun ciki" Ta ce tana tuno ranar da ta raka ta asibiti aka cire mata saboda kar ta haihuwa a gidan ABBAS ta saka shi dama.


"To sai dai abin da gogan nawa ya ce" Ta ce rana ƴar dariyar da bata wuce leɓenta ba. Haka suka sha zancen su kafin ta mata sallama ta tafi.


Da daddare ta watsa ruwa ta saka doguwar rigar bacci tana kwance ta yi nisa cikin tunani tana tuna yadda duniya ta juya mata baya lokaci guda, dama mace farin cikinta da walwalarta yana damfare ne a wajen mijinta da ta rasa hakan sai ta ji duk ta rasa mai yake damunta. Ƙaran wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula banza ta yi da wayar har ta gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login