Showing 15001 words to 18000 words out of 61883 words
Chapter 6 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
ki je ki tauna tsakuwa don aya ta ji tsaro. Idan har kika masa sakwa-sakwa ya samu dama wallahi zai kore miki duk wani bazawari da zai zo wajenki da sunan so, idan baki sani ba ki sani, idan bacci kike ki farka duk wata bazawara da ta fito daga gidan aure to idan har tsohon mijinta zai ke diddiftu a kofar gidan su to babu mai cigaba da zuwa wajenta kowa zai ke ganin gidan tsohon mijin za ta koma ko da kuwa ita bata da niyyar hakan, shikenan zai sa ki yi biyu babu gwara ki fita a yi ta a watse" Umma ta ce cikin hargagi saboda gabaɗaya ta ɗauka wani Alhaji ne mai faɗa a ji ya zo ashe dai wancan ahalul fukara'un ne da bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba.
SALIMAH da ta cika ta yi fam gabaɗaya kuɗubar mahaifiyarta ta shiga kunnuwanta da kwakwalwarta, ta kara gane irin rusa mata burin da ABBAS zai yi in dai yana zuwa hakan ya sa ta ci alwashin taka masa birki.
"Wallahi Umma bai isa ba, na rantse da Allah ba zan lamunci wannan abin ba, wannan talakan ya ga makwacina da yawa wane shegen ne ya ce masa ni SALIMAH zan taɓa komawa gidansa wallahi ko a mafarki na ga na doshi cikin gidan ABBAS zan kwaɗawa kaina mugun marin da zai sa na farka daga mugun bakin mafarkin komawa gidan talauci" Ta ce a fusace don har ta fi Ummar ma fusata saboda sai yanzu ne ma Ummar ta haska mata wani duhun ta ga haske.
Buguzum-buguzum ta shige ɗaki sai ga ta ta fito da mayafi sakale a kafaɗa, wani karanin bokiti ta ɗauka ta nufi wajen gasarar kokon Umma wanda ruwan saman gasarar yake da tsami irin na ruwan tsari, tsiyaya ta yi sai da ta cika bokitin fal, ta nufi hanyar fita.
"Kar ki masa da sauki kin ji na faɗa miki" Umma ta ce amma SALIMAH ko amsa bata samu damar ba wa Umma ba, saboda yadda take jin tukukin bakin cikin jin ABBAS a kofar gidansu..
Tsaye ta same su, FAROUQ jingine da machine yayin da ABBAS yake tsaye yana rungume da hannunsa a kirjinsa, wurin gabaɗaya ya kaure da kamshin turare musamman na ABBAS da ya fi yawa da daɗin kamshi. Da yake dama kofar gidan yake fuskanta tun da yaron ya ce tana zuwa sai ya ji daɗi a ransa ko ba komai zai ganta don bai ma yi zaton za ta fito ba, don lokacin da ta yi yaji sai dai ya gaji da tsayuwa ya tafi ko ta cewa ɗan aiken ba za ta zo ba shi kuma ba shi da damar shiga gidan nasu yadda suke tsaki da tsakuwa shi da Umma tun da bata kaunarsa..
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke hangota da ya yi ta fito, a duniya ba ya ganin kowace mace sai SALIMAH ya ɗauke ta tamkar sarauniyar mata kasancewarta sarauniyar zuciyarsa, ganinta yake tamkar ɗawisu jin ta yake tamkar numfashinsa, rayuwarsa haɗe yake da ita saboda kaunar da yake mata.
Bai lura tana ɗauke da wani abu a hannunta ba, ya shagala da kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata da ya haske duniya. Tunani yake a ransa ya aka yi ya ɗaga hannu ya mari wannan fuskar da take da matukar daraja a wajensa.
"Waye yake kirana a cikin ku?" Ta tambaya cike da rainin hankali ko arzikin yin sallama basu samu ba. FAROUQ da dama a kufule yake na shanyar da aka musu suke tsaye zaman jiranta jin kalaman rainin hankalin da ta yi ya mayar mata da martani.
"Waye kike ganin zai zo wajenki a cikinmu? Ni dai ban miki kama da wanda zai zo wajenki ba ko cikin mafarkin ki"
"Haba FAROUQ kai da ka rakoni sasanci bai kamata ka mayar da martani haka ba, a kalla sai ka ce mata ABBAS ne"
"To kai in ba tambayar rainin hankali ba ai ta san waye ya zo wajen nata ko yaron da ka aika ai ABBAS ya ce yana kiranta, kuma abin haushin kai baka fahimci ko darajar ta mana sallama bamu samu ba?"
"Wa ya gayyatoku da har zai muku sallama? Ku kuka ɗakko kafafunku masu kama da na kwaɗo kuka zo, to bari ku ji in faɗa muku bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane iya gani iya kyalewa ni yanzu na maka nisa kwatankwacin nisan da yake tsakanin sama da kasa, sau nawa zan faɗa maka ABBAS na tsane ka! Na tsani mai kaunarka, bana son duk wani abu da ya danganceka, mai ya sa baka da zuciya mai ya sa ka bari kare ya cinye maka zuciya? Mai ya sa kai kawai hangena kake baka ganin mugun talaucin da kake ciki wanda ya maka kamun kazar kuku, ka rubuta ka ajiye na barka har abada yadda na fito daga gidanka da sunan matarka na fito fitowa ta har abada ko gawata na ji an saka a gidanka idan da hali zan yunkura in fito daga ciki" Tun da ta fara maganganun yake kallonta duk da yana jin ciwo a zuciyarsa amma kuma a wani sashen na zuciyarsa ya kasa ganin abin da take yi laifi ne, bai san mai ya sa ba ba ya ganin laifin SALIMAH ko abu ta masa zai ji haushi amma na ɗan lokaci ne daga abin ya gushe zai ji ba ya ganin laifinta sai dai wani ya ga laifin nata ko wani ya jiye masa ciwon abin da take masa shi kansa bai san mai ya sa ba, illa iyaka ya san so ne, son da yake mata ne ya lulluɓe laifinta.
"Kar ki ce haka SALIMAH ki tausaya mini, ba zan iya rayuwa ba sai da ke, da wane amon murya kike so na faɗa miki ina son ki ki yarda? Da wane martani kike so in fahimtar da ke irin son ki da kaunarki da nake yi ki yarda? SALIMAH ni kaina ban taɓa ji ko a labari akwai irin son da nake miki ba Allah ne shaidata bayan mahaifana ba na kaunar wata halitta sai ke. Da a ce ɗan adam yana iya tsaga kirjinsa ya nuna so a yarda da shi da na buɗe miki kirjina da kin duba cikin zuciyata ki ga yadda son ki ya cika zuciyata ko da ba za ki so ni ba idan kin gani za ki yarda da ɗimbin makahon son da nake miki wallahi ba na ji, ba na gani, bana gane rashin ki masifa ne a wajena sai kin yi nesa da ni, na yarda na amince ki koma gidana ki mini duk azabar da za ki gasa mini na yarda ki mini fiye da abubuwan da kike mini, zan ɗauki komai zan jure komai in har zan rayu da ke a inuwa ɗaya, wallahi, wallahi, wallahi ba zan taɓa butulcewa ba, ba zan taɓa haɗa ki da wata mace ba idan kika dawo gare ni ba zan taɓa miki kishiya ba ke kaɗai za ki rayu ki yi yadda kike so da ni, ni naki ne zuciyata taki ce SALIMAH" Ya kai karshen maganar rauninsa yana bayyana a cikin nuryarsa.
Wani uban tsaki ta doka, wanda ya sa hawayen da suke makale a kwarmin idansa gangarowa, wannan tsakin ya tabbatar da maganganunsa tamar busar sarewa ya yi wato sun shiga ta kunnenta na hagu sun bi ta kunnen dama ko alamar tasiri kalamansa basu yi ba. FAROUQ wani tausayin abokin nasa ya kara kama shi, ko shi da yake namiji maganganun ABBAS sun shige shi amma ita SALIMAH da ake yi wa kalaman sannan ita ce mace kuma an san mata da tausayi kuma zuciyarsu tana da rauni a kalla ko da bata amince za ta koma ba ta masa wata kalma mai taushi.
"SALIMAH" Ya furta a daidai lokacin da ya durkusa gwiwoyinsa a kasa yana durkushe a gabanta, bai yi la'akari da farin yadin jikinsa ba shi damuwarsa ma duk so da yake mata bata gaskata shi ba ya ma gabanta kwata-kwata.
"Ya kike so a yi, mai kike so in yi ko kina so in ɗayo miki fatar jikina ki yarda, ko akwai wani ɓangare na jikina ko koda ta kike so zan iya bari a cire guda ɗaya ko da kare kika ce a dasawa zan yarda ko da hakan zai zama siyar mutuwata ai a dalilin so ne son ma naki SALIMAH...
"Kai ya isa haka ABBAS mai ya sa kake kalami a inda ba za a tausaya maka ba? Wannan da kake gani ko ranka za ka cira ka bata ba za ta yarda ba kai alamunta sun nuna ko mutuwa za ka yi ba za ta tausaya maka ba, na lura mugun tsanar da ta yi maka ba iya kai take wa ba talaucin da kake ciki ne bata so da a ce kana da ɗimbin dukiya ba sai ka ka roke ta ba, dukiya ce kawai a ranta duniya ce kawai a gabanta ka daina ɓata gishirinka a dahuwar kaho, ka zo mu tafi ka roki Allah ya cire maka son ta ka samu mai kaunarka ka yi sabuwar rayuwa ka manta da ita...
."Ita nake kauna FAROUQ"
. Wani haushin su ne da ya turnuke SALIMAH ya sa ta kasa magana sun mayar da abu tamkar a wasan kwaikwayo ko littafin hausa, sai wani kalaman soyayya yake tamkar wani romeo, ita fa ko kalmar so bata damu sosai a furta mata ba ta fi damuwa ta ji dumus wato masu gidan rana, kuɗi da ake kira kare kukan ka, kuɗi aljannar duniya mai kuɗi ya huta sai yake shagalinsa.
. FAROUQ kuwa jin furucin da abokin nasa ya yi sai ya juya musu baya, don ya gaji da ganin abubuwan takaicin da ABBAS yake a kan so ana wulakanta shi. SALIMAH kuwa ganinsa durkushe a gabanta sai wata tsanarsa take tsarga mata zuciya musamman in ta tuno da maganar Umma cewa zuwansa wajenta barazana ne ga zuwan manyan Alhazan zawarawan ta, zuwansa zai zama shamaki ga cikar burinta hakan ya sa ta ji gwara ta masa hukunci.
"Dan Allah SALIMAH... Maganar ABBAS ta makale ne a daidai lokacin da SALIMAH ta ɗaga bokitin ruwan tsarin nan ta sheka masa tun daga saman hular kansa, har bayansa jigilif ya jike, FAROUQ da sauri ga juyo jin zubar ruwa sannan jin wurin ya ɗumame da wari, ya san kafin SALIMAH ta fito kamshi wurin yake amma tun da ta zo yake jin wani wari tunaninsa ko kwata ake kwashewa a wani wajen amma yanzu kuma sai ya ji warina dab da su hakan ya sa ya gane cewa ruwan wannan ne dama yake warin wanda ko kaɗan bai kawo a ransa cewa ruwa ne ma a bokintin hannunta ba.
"Wannan kaɗan kenan daga abubuwan da za ka fuskanta matukar ka ci gaba da zuwa kofar gidanmu, ba za ka hana ni rawar gaban hantsi ba, nan gaba zan iya watsa maka tafashashshan ruwan zafi ka ga idan fatar jikinka ta silsilge ka hakura da zuwa in kuma baka daddara ba akwai wasu abubuwan da na tanadar maka har sai ka janye kafarka ta fukara'u a kofar gidan nan" Lokacin da ta wasa masa ruwan sai ya ji wani sanyi ne da ruwan tamkar ruwan randa ko na firji, ga wani wari da ruwan yake har fuskarsa ruwan ya wanke, jikinsa jigilif babu inda ruwan bai taɓa ba a take wani kaikayi ya fara masa sallama a fatarsa. Duk wannan batutuwan da take masa ba ya ma fahimta, tsaye ya mike yana kallon kwayar idanunta bai ga salama ko tausayi ko rangwame daga idanunta ba. Laɓensa na kasa ya cije da hakoransa an kai gaɓar da bakinsa ya kasa furta komai da a ce wani ne ya masa haka ba SALIMAH ba da sai ya gwammace kiɗa da karatu.
"Ke wace irin wawiya ce, mai ya sa kika ɗauki ɗan adam ba a bakin komai ba, kike wulakanta ɗan adam, bayan ubangijinmu ma ya faɗa a littafinsa mai tsarki cewa ( Wakakadi karramana bani adama,,, hakika mun karrama ɗan adam)" FAROUQ ya faɗa a kufule yana jin tamkar ya hau ta da duka.
"Yanzu zan nuna maka wawiya ce ni" Ta ce tana juyawa wajen kwatar gidansu inda aka yi wa makwararan wanke-wanke hanya ruwan yake taruwa a kwatar simintin da aka yi bokitin ta saka ta kwalfo ruwan ta nufo su a wanna lokacin su duka za ta watsawa don shi ma abokin hakan ya zama izna gare shi nan gaba ba zai sake yarda ya rako shi ba. Tana ɗagawa za ta fara shekawa ABBAS FAROUQ ya yi saurin ɗaga hannu zai wanka mata mari, cikin sauri ABBAS ya saka hannu ya rike masa hannun nasa, ba wai don abin da ta yi bata cancanci mari ba sai dai ba ya so a taɓa lafiyarta gani yake da a mare ta gwara shi a mare shi zai fi jin saukin abin a ransa.
."Da ka bar shi ya mararwa kansa bala'i wallahi sai na saka an kulleka har igiya ta yi saura, ba kai kaɗai abin zai shafa ba har danginka, kuma in kara gani wani ya zo wajen na" Ta ce tana nuna FAROUQ da yatsa tare da shekar da ruwan kwatar a waje ta yi jifa da bokitin ta juya abin ta tana dab da shigewa gidan ABBAS ya ce
"SALIMAH" Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba.
"Idan har hakan zai sa ki farinciki na yarda na amince ba zan sake zuwa ba na zaɓi na rayu da kuncin rashinki ke ki yi farin ciki"
."Hahahaha wa ya faɗa maka barno gabas take, ai in ka ji mutum yana cewa ba zai iya ba bai kama shi bane ka ji uwar bari" Ta ce a zuciyarta wani daɗi yana baibayeta ganin ta yi galaba a kansa ashe akwai barazanar da za ta masa ya kyale ta.
A fili kuma sai ta ce
"Naka ya rage ABBAS za ka iya cigaba da zuwa ni kuma ba zan gaji da maka hukunci ba, kuma gobe za mu zo mu kwashe kayanmu daga wannan gidan kaima ka huta da biyan kuɗin haya" Tana gama faɗa ta juya.
"Za ki yi da na sani wata rana, za ki dawo ga ABBAS a lokacin da ya miki nisan da sai dai ki hango keyarsa daga nesa, yadda kika wulakanta shi na tabbatar Allah ba zai barki haka ba, yadda kika raina matsayi da samunsa na tabbatar akwai lokaci yana zuwa ki rubuta ki ajiye za ki ce dama FAROUQ ya faɗa mini indai auren mai kuɗi ne, auren jari, auren da ba don Allah ba ga wurin nan wasu masu kuɗin suna da kirki da duk kyawawan abubuwa tun da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba amma ke saboda abin da kika yi wa ABBAS sai Allah ya jarabce ki! " FAROUQ ya ce cikin ɗaga murya dama da ta juya ba tafiya ta yi ba sai da ta gama ji tsaf. Dogon tsaki ta ja ta ce.
."Bakin ka ya sari kashi, kuma mugun fatanka ya koma maka, babu abin da zan gani, sai dai ya kare a kan ka" Bata jira cewarsu ba ta shige gida.
Har ta ɓace wa ganin ABBAS amma bai ɗauke idanunsa daga wurin ba tamkar dai zai ganta haka ya kurawa wajen ido. A hankali FAROUQ ya yi taku ɗaya biyu ya dafa kafaɗarsa ya ce
."Abokina" Ya ce cikin tausayawa ABBAS ɗin. Ya san ba laifinsa bane so abu ne da yake cikin zuciya idanu ba ya ganinsa bare hannu ya taɓa shi.
ABBAS kawai juyowa ya yi ya rungume FAROUQ duk da jikinsa a jike kuma yana warin ruwan tsarin da ta watsa masa amma bai ji tsantsani ba, yana jin irin yadda kirjinsa yake bugu da sauri da sauri.
."Ka yi hakuri ka ji, idan so cuta ne hakuri magani ne" Kai kawai ABBAS ya gyaɗa masa saboda ya ma rasa bakin magana ba ya gane komai kuma ba ya fahimtar komai. Da lallashi FAROUQ ya saka suka hau machine ɗin suka tafi. Da sallama suka shiga gidan Mama inda ta shiga kallon yadda ABBAS ɗin yake a jike.
"SALIMAH ce ko?" Mama ta jefa musu tambayar don ta san ita ce kaɗai za ta aikata wannan aikin. Shi dai ABBAS bai ce komai ba, FAROUQ ne ya bata amsa amma bai faɗa mata yadda suka yi ba ya dai ce mata ta ce ba a ta koma ba gobe za su zo su ɗauki kaya.
"Allah kawo su lafiya, ya sa haka ne ya fi alkairi' Mama ta ce tana jin ciwon wulakanta mata ɗa da SALIMAH take.
ABBAS ɗakinsa ya shiga ya kwanta rubda ciki, jinsa yake tamkar ba shi da lafiya, ga jikinsa ma ya ɗau zafi jin sa yake tamkar a wata duniya ta da ban.
"ABBAS baka jin yadda kake warin ruwan nan?"
"Ba na jin warin abu ɗaya na sani ina jin kamshi"
"Kamshi fa ka ce?" FAROUQ ya tambaya da mamaki.
"Ai tun da SALIMAH ce ta watsa mini ba zan ji warinsa ba, kuma zuciyata bata ganin laifinta sannan kuma har abada ba zan daina sonta ba" Ya ce har lokacin yana nan kwance rubda ciki.
"To majnun na Laila ai sai ka tashi ka je ka yi wanka ka cire jikakken kayan nan, ni na tafi sai da safe" Bai jira cewarsa ba ya fita daga ɗakin ya wa Mama sallama ya tafi. Mamar ce ta shiga ɗakin take masa nasiha dakyar ta shawo kansa ya yi wankan ga zazzaɓi mai zafi ya rufe shi magani ta bashi ta rufe shi sai numfarfashi yake.
Washe gari da yamma Mama tana waje makwarara ta rike ABBAS ɗin da yake ta kelaya amai, da yake da zazzaɓin ya kwana ga ciwon kai mai tsanani hakan ya sa da safe ta kira FAROUQ suka je asibiti magunguna allurori da drip aka rubuto masa, wani abokin su FAROUQ ya kira ya zo gida ya saka masa drip ɗin bayan ya masa allurorin. Bayan an cire ne kuma ya ce zai yi