Showing 33001 words to 36000 words out of 61883 words
Chapter 12 - RUBABBIYAR IGIYA BOO1 Compelet by Maman Afra.txt
samu TV musamman da aka ɗauki tsawon lokaci bai saka ta a idanunsa ba tun ranar da suka je da FAROUQ.
Gabansa suka karasa tana wani yauki da jijki da kai ita ala dole tana son bayyana masa ta fi karfin talaka tana son kara tabbatar masa matar manya don da manyan ta dace.
"Sannu da aiki fa " Alhaji Tahir ya ce yana murmusawa.
"Yawwa Alhajin Allah barkan ku da zuwa" ABBAS ya ce cikin sakin fuskan.
"Barkan ku dai?" SALIMAH ta maimaita a zuciyarta tana mamaki don ABBAS ya shayar da ita mamaki sai dai tana zargin bai gane ta ba watakila ko saboda hutu ya ratsa ta sosai, amma dai a nata zaton ko wae irin canji ta samu bata zaci zai kasa gane ta ba. Satar kallonsa ta yi a nan ta ga abin mamaki ya kara fari ya yi kiba duk tunaninta za ta gan shi ya kare kamar hatsin guzuri amma sai ta ga saɓanin haka.
"Yawwa kujera muke so" Alhaji ya faɗa.
"Wace iri kuke so Hajiya" ABBAS ya tambaya yana kallon SALIMAH da duk ta sha jinin jikinta tun da ta zo don ta tada masa hankali sai ta ga ko a jikinsa wai an tsikari kakkausa.
"Eh kujerar za...za... zama "
"Haba Hajiya ke da za ki faɗi wace iri ai kowace kujera ta zama ce" Ya ce yana dariya. Duk ta diririce ji take tamkar ta ce ABBAS baka gane ni ba sai dai babu amfanin hakan.
"Ta zaman tsakar gida" Alhaji ya faɗa yana dariya, ɗakko musu ya yi ta ce guda biyu suke so, ya ce kowacce dubu biyu. Dubu ashirin ta lissafa daga cikin 50k ɗin da Alhajin ya bata yanzu, ta mika masa. Karɓa ya yi tare da ɗaukan kujerun ya bi bayansu da su da yake idan aka zo siyan kayan in za a saka a mota su suke kaiwa costomer mota. Alhajin ya buɗe masa ya saka a baya, Alhajin ya buɗe mata ta shiga ta zauna, ABBAS kuwa tsayawa ya yi daga gefe ya irgi kuɗinsa dubu huɗu ya zo gaban kofar da ta shiga ta zauna Alhajin yana kokarin rufewa ABBAS ya mika kuɗin ya ɗora mata a cinya yana mai cewa
"Hajiya kin yi mantuwa kuɗin sun zarta kimar wanda za ki biya" Ya ce yana mata murmushin gefen baki. Baki sake take kallonsa wato ma ba zai karɓi bajintar da ta masa ba, dama ba don tausayinsa ta bashi kuɗin ba sai don ta nuna masa a halin da ake ciki yanzu wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa, duk da ta san ta biya masa wannan karatun da baki amma sai ta ga dacewar yanzu ta biya masa shi a aikace.
"No ka bar shi ka kara cefane"
"Lah ki bar shi godiya nake" Ya ce ba tare da ya jira cewarta ba ya juya ya bar ta baki sake ga takaici shi kuwa Alhaji bai kawo komai ba saboda ya san akwai mutanen da suke basa son a musu kyauta ko an musu sai su ki karɓa bai san cewa ABBAS ɗin tsohon mijin SALIMAH ne da ta guda saboda talaucinsa....
*RUƁAƁƁIYAR IGIYA*
NA
MAMAN AFRAH
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga kawata HASSANA B.S Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 10
*HAJIYA RAYYANATU*
Tun da magriba ta tara Baba Sadiya da sauran ma'aikatan ta faɗa musu gobe HAWWA amarya ce don haka kar su jira ta shiga kicin su gabatar da break fast ɗin. Sun amsa mata inda kowa a zuciyarsa ya yi mamakin kalaminta ganin babu wani shiri a tare da HAWWA da zai nuna cewa ita ɗin amarya ce. Saboda haka ko da safe babu wanda ya lura da cewa HAWWA da SABEER basa gidan in banda Baba Sadiya da ta san sun bi dare sun gudu.
Hajiya Rayyanatu ce zaune a kujera a falonta ta harɗe ɗaya kan ɗaya sai Lawisa da take latsa waya, ɗaya daga cikin ma'aikatan ce ta shigo cikin ladabi take sanar da Hajiyar cewa HAWWA bata gidan daga ita har SABEER ɗin. Da farko ta ɗan ji wani irin don bata zaci cewa guduwa suka yi ba sai da aka duba gidan kaf aka ce basa nan sannan kuma daga sassafe har zuwa yanzu da ake karfe tara mai gadi ya ce bai ga fitarsu daga gidan ba. Ko da aka bincika cewa komai nasu yana ɗakin sai ta kuduri cewar ko ma ina ta tafi za su dawo ne su same ta. Wajen goma da rabi Baba ya fito daga ɓangarensa sanye cikin babbar riga shi dama gogan Umar yana get ya sha shaddar nan sai sheƙi take ya kafa hula sai kamshi yake shi a dole za a tafi masallacin unguwar a ɗaura masa aure, saboda haka Hajiya bata ma san sun fita ba saboda ma kayan amarya da ta bayar aka ɗinka yana ajiye a kan kujera a falo dama atamfa ce leda (Atamfa roba) Wacce ba cotton ba aka yi doguwar riga wata binjimemiya tamkar buhu wai a cewar Hajiya atamfa leda ta fi kwari kuma ɗinkin a mata maje gaba wanda za ta daɗe tana mora. Wata makociyarsu ce da Hajiya Rayyanatu da mata waya ta sanar da ita ɗaurin auren ta zagayo don ta ce musu auren za a ɗaura a gaba za a yi shagalin biki. Sosai ta shiga yaba ɗinkin amaryar a maimakon ta faɗa mata gaskiya cewar atamfar da ɗinkin basu dace da amarya ba amma sai ta shiga yabawa tana sam barka.
"Ni fa a yau ban saka yarinyar nan a idona ba" Hajiya Raytanatu ta ce tana kallon makociyarta.
"To ina suka je da duku duku ɗan mai gidana yake ce mini ya ganta ita da ƙaninta a tasha" Da mamaki Hajiya ta kalleta ta ce
"Tasha kuma wace irin tasha"
"Tashar hawa mota ai ya je kai abokin mai gidana da za hau mota da ya dawo yake faɗa mini ya gansu kasancewar jiya da kika kirani muna tare sai nake faɗa musu aurenta za a ɗaura yau shi ne da ya dawo yake ce mini ya ga amaryar da nake ce musu za a ɗaura mata aure" Ta kai karshen maganar tana fito da wayarta ta yi danne -danne ta kara a kunne.
"Ni wa ka ce mini ka gani a tasha da safe" Nan ya mata bayani Hajiya Rayyanatu da kunnenta ta ji da yake a handsfee ta saka wayar.
Wayarta ta ɗauka ta dokawa Baba kira, Baba da yake tsakiyar taro sai baza malun-malun yake wani maroƙi yana binsa yana ta masa kirarin uban amarya uban ango. Vibration ɗin da wayarsa da take cikin aljihu ta ɗauka hakan ya ankarar da shi ana kiransa fito da ita ya yi ya kara a kunnen nasa yana ɗagawa wasu abokansa hannu yana ta doka murmushi, Umar ango sai washe baki yake jin kaɗan ta gyara hula abinka da ba a saba sakawa ba.
"Alhaji wallahi kar a ɗaura auren nan, shegiyar yarinyar nan ashe bata kwana a gida ba ta ɗauke wannan zololon ƙanin nata sum je tasha sun hau mota sun gudu" Har ta gama bayanin bai ce uffan ba ya yi mutuwar tsaye yana hango Umar da yake ta gaisawa da mutane kamar abin arziƙi.
"To" Kawai ya ce wani gumi yana karyo masa ya shiga ƙarewa yawan bataliyar mutanen da ya tara domin halartar auren babban ɗansa, da kuma ƴar ɗan uwansa da ya gama yayatawa cewa suna kaunar junansu kamar su cinye juna. Hakan ya sa aka yi ta masa sam barka mutane suna ƙara ganin girmansa na ganin ya riƙe ƴar zumunsa har zai aurar da ita don wasu basu san halayyar Umar ɗin ba sun ɗauka mutumin arziƙi ne.
'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un' Ya ce yana sauke wayar daga kunnensa yana kallon jama'a yana ganin ga ƙoshi ga kwanan yunwa ba ya so a ɗaura auren bayan bai san inda ta tafi ba kuma bai san ranar da za ta dawo ba kuma bai san lokacin da za ta dawo ba sannan bai san mai zai faɗawa mutane a fasa ɗaurin auren ba. Hukunci ɗaya kawai ya yanke shi ne ya faɗi a ƙasa wannan ne kaɗai zai sa a fasa ɗaura auren.
Wayar ya ƙara mayarwa kunne da gangan sai kawai ya fata ambaton subhanallahi, kawai sai ya yanke jiki ta faɗi a take jama'a suna hayya-hayya aka yi kansa amma ya saki jiki har da ɗauke numfashi kinkimarsa aka yi aka saka a mota, nan fa wuri ya kacame da hayaniya wasu suna a ɗaura tun da an taru wasu suna cewa ya za a yi a ɗaura auren shugaban ɗaurin aure rai a hannun Allah, da haka mutane suka watse Umar zaman dirshan ya yi a ƙasa yana sharɓar kuka shi a dole ba zai tafi ba sai an dawo an taru an ɗaura masa auren wai Babansa baƙin ciki yake masa shi ya sa ya faɗi ana shirin mayar da shi ango dakyar direban gidansu ya lallaɓa shi ya shiga mota don ya mayar da shi gida don da alama shaye-shayen ya fata taɓa masa ƙwaƙwalwa.
*ABBAS*
Tun lokacin da ya hango SALIMAH da bazawarinta sarai ya gane ta amma kuma abin ban mamakin shi ne bai ji ya shiga tashin hankalin da yake tunanin zai shiga ba idan ya ganta, sannan ko a ransa bai ji wani kishi na ya ganta da wani namiji wanda a baya yake ganin idan har ya ganta da wani sai abin da ba a rasa ba ita kanta SALIMAH bai wani ji damuwa da ita ba, a baya ko wuri ta ziyarta in yana wajen sai jikinsa ya bashi, amma saɓanin yau bai ji komai ba illa iyaka ganin ba zatan da ya mata da farko ya so ruɗa shi amma sa ya shiga ambaton Allah sai ya ji ya saitu. Abin da SALIMAH bata sani ba ya gane don ta nuna masa matsayin da take takawa a yanzu ta je wurin sai dai ya lura har yau bata gama gane waye shi ba, a duniya abin wani abi tsone masa ido ba ko da a ce bashi da naira biyar ta kansa idan wani yana da miliyan ɗari ba zai damu ba ya san Allah ne ya ba wancan shi ma kuma ba ya cire rai daga rahmar ubangiji domin Allah ne yake azurtawa. Talaucinsa bai koya masa kyashi ko hassada da son kai wa matsayin wani da Allah ya yi wa arziki yake ji dama shi ne.
*HAWWA*
Tun da suka ɗauki hanya hankalinta ya kwanta ganin ta kuɓuta daga wannan kaddararran auren da ake son lakaba mata auren wanda bai sam kansa ba kuma bai san darajar ɗan adam ba, ba za ta taɓa yarda ya aure shi a matsayin uban ƴaƴanta ba don ba ta ga zai zame musu garkuwa ba. Kallon SABEER take da yake kwance a jikinta yana baccinsa tana tunanin rayuwa kenan yanzu ita yake gani madadin mahaifiya tana son ta faranta masa kuma ba ta so ya yi kunci ko bakin ciki a rayuwa amma ta san matsawar suna gidan Baba Bukhari to tabbas za su rayu a ƙunci saboda rashin amana.
A tasha aka sauke su lokacin SABEER ya falka amma bai ware daga baccin ba, goyonsa ta yi ta tsaya ta saya masa pure water jin yana cewa zai sha ruwa duk da ta san yunwa yake ji tun da bai ci abinci ba. Napep ta tare musu suka kama hanyar gidan Baffa Nasiru a kofar gidan aka sauke su ta bawa mai napep kuɗin ta kama hannun SABEER suna shirin shiga gidan ta hango Baffa.
"SABEER ka ga Baffan can" Ta ce cike da farin cikin ganin ɗan uwan mahaifiyar tasu mai kama da Ummien kamar an tsaga kara. Dariya shi ma ya yi yana ɗan tsalle alamar murna kasancewar yana matukar kaunarsu.
SABEER hannunsa ya kwace daga rikon da ta masa ya nufi wurin Baffa da yake tsaye a wajen amma shi da yake hankalinsa ba a wurin yake ba sai bai gan su ba, bai ankara ba ya ji an rungume shi ta baya cike da mamaki ya juyo don a tunaninsa ma cikin wasu yaran ne saboda shi mutum ne na yara.
"Baffa!" SABEER ya ce yana kara kankame shi don tun bayan mutuwar mahaifiyarsu tsawon shekara biyun bai sanya shi a ido ba, sannan a halin yanzu bayan HAWWA sai Baba Sadiya ne kawai wanda ya san masu kaunarsa sai yanzu da ya yi ido biyu da Baffa. Yaro kenan duk ƙanƙantarsa ya san mai ƙaunarsa ko da zare masa idanu kake wannan abin yana ƙwaƙwalwarsa ba zai manta da shi domin yaro ba ya mantuwa.
"SABEER kai ne" Baffa ya faɗa yana kama hannuwan yaron duka biyu yana kallonsa tamkar yau ya fara arba da fuskarsa. Washe bakinsa ya yi ya ce
"Ni ne Baffa ga can Aunty HAWWA" Ya ce yana nuno ya da yatsa, ɗago kai Baffa ya yi ya ganta tsaye tana murmushi. Idanunsa ne suka kawo ƙwallah ya daka hannu ya goge wacce ta gangaro ganin mutane a wajen sai ya kama hannun SABEER ɗin, wurin HAWWA suka ƙarasa, yana zuwa ita ma ta rungume shi don ganin kamannin mahaifiyarta a fuskarsa ya sa ta ga tamkar mahaifiyarsu ce.
"Hauwa kulu" Ya ce muryarsa tana rawa yana matukar kaunar yaran yana jin kaunar har cikin zuciyarsa tun da mahaifansu suka rasu ya nemi Alhaji Bukhari da ya bar masa yaran ya tafi da su Kaduna su zauna a hannunsa amma fafur ya ƙi wai dangin uba su ne suka fi cancanta da su riƙe ƴaƴa kuma ma a yadda ya fuskanta dukiya ce kawai a gaban Alhaji Bukhari har sai da Baffa ya ce shi ya amince a bashi yaran ba tare da an bashi ko da tsinke bane daga cikin dukiyarsu don shi dama tsoron cin dukiyar maraya yake, yana tsoron ranar da Allah zai tashi shi ya tambaye shi yadda ya ci shi hatta bashi tsoron cinsa yake, saɓanin wasu mutanen da basu ɗauki cin bashi a komai ba, suna mantawa da ranar karshe, suna mantawa da ranar sakamako suna mantawa da hisabi.
Bayanta ya bubbuga tare da janye ta daga jikinsa ganin a kofar gida ne hannunta ya kama yana rike da su suka kama hanyar kofar gidan.
"Baffa ga kuɗin kayan can da aka siyar ɗazu" ABBAS da ya zo zai ba Baffa kuɗin ciniki ya faɗa yana ɗan sunkuyowa ya mika masa da hannu biyu.
"Ka ajiye a wurinka ABBAS zan shiga gida ne in na fito ma yi maganar" Cewar Baffa yana ɓoye fuskarsa da ruwan hawaye ya taru a kwarmin idanun, yana so ya tuna dalilin da ya sa ya manta da ƴaƴan ƴar uwarsa, yana so ya tuna dalilin da ya sa ba ya zuwa ya gan su amma ya kasa tuna komai shi ba don ya gan su ba ma, ko a ƙwaƙwalwarsa ba ya tuno su. Ba tare da ya ƙara ko da bi ta kan ABBAS ɗin ba ya juya yana rike da hannayensu suka shiga cikin gidan. ABBAS har suka ɓacewa ganinsa yana tsaye a wurin riƙe da kuɗin a hannunsa bai taɓa ganin uban gidan nasa a yanayin makamancin wannan ba sai dai lokacin da ƴar uwarsa ta mutu a Zariya da ya dawo duk ya zama wani iri amma yanzu ya rasa wane yara ne da zuwansu a sauya shi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Da sanyin jiki ya juya ya koma wurin aikinsa ya san sai dai Usman ya musu rashin kyautawa kasancewarsa ɗan abokin Baffan da yake riƙewa sai ya yi ta musu ɗagawa da rainin hankali amma shi Baffa ya ɗauke su tamkar ƴaƴan da ya haifa.
Suna shiga gidan da sallama da take hura wuta ta ɗago tana amsa sallamar cike da mamaki.
"SABEER, Hauwa'u" Ta ce tana kallonsu, da gudu SABEER ya je ya rungume ta yana ta murna kasancewarta mace ta gari wajen Baffa kuma tana kaunar ƴaƴan ƴar uwarsa kamar yadda shi ma yake kaunarsu kasancewar ma su basu taɓa haihuwa ba sai ƴaƴan abokinsa kuma amininsa da ya mutu Malam Ashiru yake rikon ƴaƴansa guda biyu mace da na miji Usman da Amrah.
"Ina ka shige Alhaji SABEER " Ta tambaya tana kama hannunsa suka nufi baranda inda tabarma take a shimfiɗe.Lale marhabin da zuwanku ƴaƴana" Ta ce tana ta murma ta zauna tare da zaunar da SABEER a kan cinyarsa.
"Hauwa'u"
"Na'am Goggo"
"Ina can gidan Baba, kuma a ɗakin da muke kwana babu gado babu katifa, kuma babu abinci mai daɗi, kuma yageggen kaya nake sakawa" Ya ce yana kallonta, sosai Baffa ya ji maganar ta taɓa shi dama ya san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama Alhaji Bukhari ba zai iya riƙe amanar yaran nan ba shi kuma ya rasa mai ya sa ya manta da lamuransu duk da ganinsu da ya yi yau ya sanya shi fara zargin wani abu a kan mantuwar ta tsawon shekaru biyu ba tare da ya waiwayesu ba sai dai ba ya son zurfafa